SAKAYYAH NA AISHA GARKUWA
Sakayyah…
Sakayyah…
Garin Bauchi akwai hamshakin mai kudi Alhaji Adam Sulaiman wanda ya rike muka mai iri iri......Farhan watau duk maganar mahaifin naka ba jinshi kake ba koh sau nawa za'a maka zancan aure iyye?..... Farhana meh sa kike mana hassada manya mutane suna sonki kina wulakanci..... labari akan cin amana yaudara zalunci ha'inci sannan kuma soyayya da sakayya.…
Labari ne maicike da tausayi izaya makirci da kuma soyayya da sauransu…
Alokacin da rayuwa tayima wani tsanani alokacin ne wani yake jin dad'inta.Yadi matashiyar bodurwa ce,wadda ta tashi cikin rugar fulani.Yidi matashiyar budurwa ce wadda ta tashi cikin rashin gata, babu limin addini bare kuma na zamani, Allah yaba mahaifiyar Yidi baiwar gane sihiri ajikin mutum. Ƙanwar mahaifiyar Yidi ta d'auki Yidi ta kaita balaguro birni.Shin wata rayuwa Yidi zata yi abirni? Hajiya sai kin shiga cikin littafin BAK'AR SAKAYA .Awani b'angaran kuma Yazeed matashin saurayi ne Wanda ya tashi cikin daular arzik'i,sai dai kash Matar Mahaifinsu ta tasa komai ta rik'e,bata yadda ba Modibbo ko ƙaninsa Yazeed su gaji dukiyar Mahaifinsu,inda ta fara k'okarin salwanta rayuwarsu,inda Allah ya bata sa'a ta Maida Yazeed majinuni, saurayi Mai ji da kud'i da kyau ,ya zamana kamar wani sakare, anjuya halittar da Allah yayi mai an maida shi mai dilalar da miyau,wa'iyazubillah .Ko wata k'addarar ke had'a YAZEED da Yidi,har mahaifiyar Yidi ta sanar da shi tana da maganin lallurar shi? Shin Kuna ganin Yazeed zai yadda ya auri Yidi? Idan kuma ya aureta Kuna ganin ko idan ya warke zai ci gaba da zama da ita?.Wai duk ba haka ba ma idan YAZEED ya yadda zai auri Yidi ya Yidi zatayi da saurayinta na ruga da yayi hijira da zaman rugar su ya biyota birni ? BAK'AR SAKAYYA salon shi da banne ,anyi amfani da salo na burgewa Hajiya ,nisha d'antarwa, fad'akarwa,Ilimantarwa,Wa'azantarwa.ku dai ku ci gaba da bibiyar Autar mama daga ta kammala Zuciya zata nisha d'antar da ku da BAK'AR SAKAYYA akan fara shi mai sauk'i da rahusa kawai dan jin dad'in ku masoya. Zaku iya magana da marubuciyar kai tsaye ta wannan Number 08142904255.…
Shekararsu bakwai da aure,amma be tab'a gazawa da ita ba duk da itad'in takasance makauniyace bata gani,amma hakan be rage masa soyayyartaba aransa kulawa daidai gwargwardo yabata girki ,wanke-wanke da duk abinda take buqata yana mata ,inkazo gidanta bakace gidan makauniyabane,duk d tsananin kyaunta amma danginta basu kawo cewa zata samu mijin daze auretaba,kasancewarta nakasashiya,amma sega ISHAQ ya basu mamaki inda ya nemi aurenta tun tana shekara 16 ,yafara bata kulawa harkawo yanxu datake d shekara 23 ,duk yakasance talaka me qaramin qarfi Amma hakan be hanawa wajen siyamata maganinta me tsadaba,amma ranar data bud'i idonta takalli kanta amadubi ranar ta tabbatar d ita d'in ba matar talakabace,Ashe haka take da kyau Amma take zaune awannan lokon agidan gado tabbas ishaq be dace da itaba ,wannan kyawunnata baze tafi awajen talaka matsiyaci irin ishaq ba !!!!…
Tashi yayi a sanyaye ya fita ya daga falon dan zama a ciki zai iya saka shi hauka na wucin gadi, mota ya shiga ya fita daga gidan a guje. Sai da yayi nisa ya tsaya a kan hanya ya kifa kansa a kan sitiyarin motar cikin tashin hankali da tsoro mai yawa. Zuciyar sa bugawa take yi sosai ji yake kamar yayi hauka, tunanin sa yana ga abinda Abba ya faɗa masa, da gaske dai matar Manal ƙanwar sa ce ta jini ko wasa ake masa?, in hakan ya tabbata ya zai yi? In hakan ya tabbata me zai faru wanne hali zai shiga? In hakan ya faru ya zai yi da ransa?. Allah ya sani yana matuƙar qaunar Manal, yana kallon ta matsayin abokiyar rayuwar sa kuma bugun zuciyar sa, kallon matar sa ma'ajin sirrin sa yake mata, kallon Manal yake matsayin uwar yaron sa da yake cikin ta. Taya rana tsaka ake so a juya ta ta koma ƙanwar sa wacce suke uba ɗaya?, in hakan ya faru da wanne ido zai iya kallon ta matsayin ƙanwar sa da suke jini ɗaya? Ya matsayin ɗansa da yake cikin ta? Ɗan sa ne ko ɗan ƙanwar sa?.…
soyyaya, cin amana, taɓa zuciya, yaudara dss.…
labarine da ke tafeda ɓoyayyan al'amari, da fari lamarin da tausayi ya fara,saiya rikiɗe ya zama wani babban al'amari dake buƙatar ɗaukar fansa ko ƙiyayya , daga ƙarshe, wata daɗaɗɗiyar ɓoyayyar soyayya ta tono kanta da kanta, sakamakon wani ɓoyayyan al'amari daya bayyana gaf da yankewar numfashin wata halitta…
labari akan wata yarinya me rawar kai da rashin jin magana sam, labari akan taɓarɓarewar zumunci, tarbiyya da rayuwar 'ya mace idan ta rasa me jiɓantar lamarinta, Yayin da ake zaton wuta a maƙera katsam se ta bayyana a masaƙa, ku kasance dani dan jin me ze faru a wannan littafin…
Labarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma mahaukacin masoyi umar da yake son yi mata fin karfi?…
#Love Romance#family and destiny…
Zazzafan soyayya, tashin hankali, taƙaddama a tsakanin ya da ƙanwa a kan namiji ɗaya, nadama mara amfani tare da tausayi mai narka zuciya.…
DR UMAIMAH USMAN BULAMA,Mace yar kimanin shekara ishirin da tara ,Babbar surgeon A asibitin CITY TEACHING HOSPITAL ,Aure Uku, ƴaƴanta uku .Mace mara san hayaniya wadda tasan kan Aikinta ,babu abunda tasa a gabanta illa bawa Aikinta babban muhimmanci kana yaranta wadda kaɗdarar samunsu ta rarraba mata Aure .Kalma ɗaya zaka faɗa ta bata mata rai shine kushe mata Aikinta ko nuna wasa a duk wani abu da ya shafi Aikinta .Ita ɗin kwarariyace kuma gogaggiya akan duk wani abu da ya safi surgery,ba kasar ta ba hatta a wasu kasashen tana zuwa aiki.Bangaren soyayya fa?Bata dauki soyayya a bakin komai ba tunda dukkan Aurenta guda ɗaya ne tayi na soyayya kuma shima bai karbe ta ba wanda hakan yasa ta yanke shawarar saka soyayya a ƙwandan shara duk da kuwa tayin da ake kawo mata ,ta gama yanke imani da soyayya akan duk wani ɗa namiji wanda haka yasa mutane da dama ke mata kazafi da mata take so duba da ƙin mazanta karara a fili.Amma menene dalilin tsanar tasu da tayi?Menene yasa ta cire mazan daga tunaninta da zuciyarta baki daya?Shin zata faɗa soyayyar wani ɗa namiji ko a'a?Idan zata faɗa wanenen wannan mai sa'ar?.DR IMAM MUKTAR PAKI,Saurayi dan kimanin shekaru Ishirin da tara ,bai taba Aure ba,Dalibi wanda yake neman sake gogewa akan Aikin surgery ,shekara ɗaya wadda kareta ne kaɗai zai bashi kwali da kuma lasisin Fara yin surgery ,kaddara itace tayi aikinta ta ɗauko sa kan kachakar ta kawosa CITY TEACHING HOSPITAL inda yake ƙarkashin jagorancin likitar da kowa ke tsoro da shakka,Mene zai faru idan shi bai ji wannan feelings ɗin ba sai wani daban wanda shi kansa bazaya iya fassarawa ba?Shin ya wannan kaɗdarar tasu zata kasance?Shin Wanne irin chakwakiya Imam ke shirin ɗaukowa kansa domin wannan likitar da ya ke kan giyar so AURENTA UKU ,Ƴaƴanta uku a yayin da shi ko na fari bai taba yi ba.Ku biyo ɗiya jamilu domin jin yarda wannan labarin na IMAM da UMAIMAH zai kasance !…
A fictional character…
Inara seorang gadis biasa yang tinggal bersama adiknya , dia membatalkan niatnya untuk sambung belajar kerana ingin menjaga adiknya itu selepas kematian ibu bapanya . Setelah bertemu Rayyan hidupnya mula berubah , adakah jodoh mereka berkekalan lama ?Rayyan anaqi seorang leader's mafia yang berkacukan Malay + Turkish . Character : anak pertama dalam 2 adik beradik dan seorang yang berwatakan cool + romantic + tegas . *aku seorang yang pendosa inara , tak layak untuk kau , adakah tuhan akan terima orang yang pendosa macam aku ni* - rayyan anaqiInara sofeya seorang gadis biasa yang berkacukan melayu tulen . Character : seorang yang lemah lembut + friendly + kind person .*sejahat mana pun awak , saya akan mencintai awak buat selamanya rayyan* - inara sofeyaAdakah cinta antara rayyan dan inara akan berkekalan lama ?? Atau mungkin ada orang ketiga dalam percintaan mereka berdua ?? Saksikan rayyan anaqi .Start : 17 / 4 / 2022End : ??Amaran !1) Banyak menggunakan perkataan kasar !2) takthu jalan cerita cmne…
Labarin sanyayyar tacacciyar soyayyar ruhi biyu.. Wanda akai wa auren dole da juna, Amman basu san da hakan ba. Shin ya zaman nasu zai kaya idan suka gano? NAUFAL da AYOUSH. Growing in Love is a beautiful love story. A heartfelt and emotional adventure of two young lovers AYUSH AND NAUfAL willing to take a chance. The two discover they may be better suited for each other.…
LABARI MAI TABA ZUCIYA, BAN TAUSAYI, YAUDARA, CIN AMANA, BUTULCI, ZAZZAFAR KIYAYYA, ZALINCI FADAKARWA, NISHA DANTARWA, BANDARIYA, DA KUMA SASSANYAR SOYAYYA MAI TAFE DA TSAFTA DA YARDA.…
Rayuwar auren masoya biyun na tafiya daidai yanda suka tsara tun farkon fari, kwanciyar hankali da son juna ya kafu a cikin gidansu wanda hakan yasa suka zama abun burgewa ga jama'a da dama har wasu suna fatan ina ma su ne! Suna tsaka da wannan jindaɗin ne rayuwarsu ta canja salo wanda hakan yayi sanadiyyar bankaɗuwar wani tsohon alƙawari mai wuyar cikawa. Ko yaya rayuwar tasu zata ƙaya?…
labari ne kan wata yarinya data tashi cikin so da kwnar Yan uwa Wanda kaddara guda daya ta tarwatsa Mata farin cikin ta…
Labari ne akan zazzafar soyayya me tsayawa a rai saide shin anya wannan soyayya zata kai labari kuwa saboda ganinta haram da ake a al'adance?? Ku biyo ni don jin yadda zata kaya.…