TSERAN ƁERA
labarin RHAUDHA da Umar.TSERAN ƁERATafiya ce suke cikin turba na Auratayya mai mutuƙar gajiyarwa,gefe guda kuma an saka nacin sai anyi wannan tafiyar wadda bata da wani riba ko hanyar billewa.A bangare guda Umar yana ganin Alaƙarsu TSERAN ƁERA ce, tafiya wadda kake tayi baka ganin wata riba,ya riga ya saka a ransa tafiyar tasu confusion ne tsantsa a ciki babu wani purpose na yinta,.Duk da baya jin santa amma yayi ƙokari wajen ganin ya koyawa kansa hakan musamman idan yana duba irin abubuwan da tayi masa wanda a duk inda ya juya hallarcinata shine ke ƙetawa cikin kunnuwansa wanda dalilin hakan yasa baya ganin hallarcin nata rather sai yake ganin tayi amfani da hallarci tayi masa ƙutse cikin rayuwarsa ,a zahiri bai taɓa maraba da shi ba,yafi yarda da tana san mallakar sa domin mayar dashi damisar takarda amma ya sakawa idanunsa ƙwalli sannan ya ɗaura ɗamarar dambe da dukkan ƙudiranta akan sa. A duk wannan tunanin da ya saka a ransa ita a tata zuciyar bata ganin laifinta,duk abin da tayi tafi danganta shi da domin shi tayi,tana masa so ainun a cewarta ,tayi amfani da soyayyar da take ikirarin tana masa domin samun yanci daga cage ɗin da Mutanen media ke neman sakata su kulle, maganar su guda ɗaya ce wanda shine "she's a feminist wadda bata san daraja da haƙoƙin Allah ba",wani bangaren suna mata ikirarin ba za ta taɓa Aure ba ta zauna dan haka tayi ƙoƙarin basu kunya wajen faɗawa gidan Umar wanda standards ,beliefs, sociality ,way of thinking nasu akwai banbanci mai tsanani.Shin ya wannan zama nasu zai kasance ?Zai ɗaure ko zai ƙunce?Ku kasance dani cikin journey ɗin Rhauda da Umar,zaku ƙayatu,zaku nishaɗantu,sannan zaku wa'azantu Insha Allahu.…