suwaibamuhammad36
MATAR K'ABILA (Completed)

MATAR K'ABILA (Completed)

365,838 28,719 58

Anwar Bankudi, the Handsome Young Millionaire ke zagaye da matan Aure uku, kowacce da salon halinta da matakin matsayinta a zuciyarsa. Shin wacece Tauraruwarsa?Rayuwar gidan Bahaushe mai cike da sark'akiya had'e da zallan zaman aurenmu a yau.…

FATU A BIRNI (Complete)

FATU A BIRNI (Complete)

51,022 2,098 18

"I promise you Mami, zan nemo miki ƴar'uwarki a duk inda take a faɗin ƙasar nan. SULTAN promises you that." Sultan ya shiga ya fita, har ya aikata abunda ba'a tsammani domin ya cika wannan alƙawari da ya ɗaukawar mahaifiyarshi, aka yi dace ya gano inda take. Wani abun takaici shine a maimakon ya samu ƴar'uwar Maminshi kamar yanda ya ci buri, sai ya haɗu da ƴarta kwalli ɗaya tak da ta haifa a duniya ta bari cikin ƙauyanci da kuma rashin wayewa. Baƙin cikinshi bai tsaya a nan ba, domin dattijon da yake riƙe da ita a take ya aura masa yarinyar ba tare da ya iya kaucewa wannan mummunan ƙaddaran ba. Ya tafi ya barta ba tare da ya sake waiwayarta ba, ya kuma tafi da wani kaso na zuciyarta ba tare da ya sani ba. Fatu (Fatima) ta ji haushi, sannan tana cikin baƙin cikin tafiyar da mijinta yayi ya barta. Tun tana tsumayinshi tana fatan ya dawo ya ɗauketa, har zuciyarta ta daskare da tsantsar tsanarshi na wofintar da ita da yayi, da kuma banzatar da igiyar aurensa dake kanta. Tayi alƙawarin ɗaukan fansa, ta kuma yi alƙawarin raba tsakaninsu ko da duniya zasu taru su hanata. Sai ta nemo shi a duk inda yake. Ta shiga cikin Birni nemansa, a nan kuma ƙaddara ya gifta tsakaninsu suka haɗu a lokaci da kuma yanayin da basu yi tsammani ba. Shi kuma ganin kyakkyawar baƙuwar fuska mai ɗauke da kamala, ya sashi faɗawa cikin sonta dumu-dumu ba tare da ya shiryawa hakan ba, kuma ba tare da ya gane cewa Matarsa ce ta Sunnah ba, Halal ɗinsa.Me zai faru idan Fatu ta haɗu da mutumin da ta ƙullata tsawon shekaru a yayin da shi kuma yake jinta a zuciyarsa tamkar ruhinsa?Me kuma zai faru Idan wasu sirrikan suka bayyana a lokacin da ba'a shirya musu ba? Fatu mace ce ɗaya mai hali mabanbanta; Fatu- Matar Sultan.Fatima- Budurwar Sultan.…

RUWAN ZUMA (completed)

RUWAN ZUMA (completed)

29,681 2,516 24

Shin wani irin kallo kake yiwa masoya biyu wad'anda akwai tazarar shekaru tsakaninsu, musamman ma in aka ce Macen ta fi Namijin yawan shekaru?Tayi wuff dashi, ko Tsoho yayi wuff da yarinya. To ga labarin wani matashin saurayi mai farin jinin 'yan mata amma shi hankalinsa kwata-kwata ba ya kansu dalilin tun asalin fari Aliyu Haydar yafi son auren mace wacce ta girmeshi da yawan shekaru. Ana haka ne kuma ya had'u da Laila Kashim wacce ta dace da duk tsari na matar aurensa.A yanzu kuma da mutanen duniya suke kyama game da kushe irin wannan tarayya shin Aliyu Haydar da Laila zasu cika burinsu ko dai zasu iya hak'uri da juna don gujewa zagin duniya a kan tarayyar da Allah ya halatta?Soyayya... RUWAN ZUMA…

TAFIYAR MU (Completed)

TAFIYAR MU (Completed)

7,171 564 20

Rayuwar auren masoya biyun na tafiya daidai yanda suka tsara tun farkon fari, kwanciyar hankali da son juna ya kafu a cikin gidansu wanda hakan yasa suka zama abun burgewa ga jama'a da dama har wasu suna fatan ina ma su ne! Suna tsaka da wannan jindaɗin ne rayuwarsu ta canja salo wanda hakan yayi sanadiyyar bankaɗuwar wani tsohon alƙawari mai wuyar cikawa. Ko yaya rayuwar tasu zata ƙaya?…

CANJIN MUHALLI

CANJIN MUHALLI

1,553 207 8

Ana kiranta Jidda Sufi, ƴar auta ga Governor Sufi Adam. Duk da jindadi haɗe da tsaron da suke dashi a matsayinsu na iyalan Governor bai hana wani mummunar al'amari faruwa da zuriyarsu ba. Cikin son nisanta kanta da mahaifinta wanda take ganin laifinshi ne sanadiyyar rugujewar farin cikinsu yasa Jidda ta ƙaura daga Nigeria zuwa USA domin ƙarisa shekararta ta ƙarshe na secondary school. A wannan sabon muhallin ne Jidda ta haɗu da mutane farar fata wanɗanda wasu daga cikinsu suka ɗauki duniya gurin baza koli. Shin wace irin rayuwa Jidda zata yi a cikin su? Kuma menene zai faru idan tarihi ya nemi maimaita kanshi? Labari ne mai salo na daban akan waɗanda muke karantawa kullum. And it's a FREE BOOK!!! NOTE: May contain some matured contents.…