Amor Sanguinum (Yandere Vampire Feitan x Reader)

Amor Sanguinum (Yandere Vampire Feitan x Reader)

2,488 46 6

Something terrible has happened to Feitan, now something terrible is going to happen to you. Warnings: vampire!Feitan, animal death (including death of pet dogs), animal violence, gore, murder, stalking, yandere content, blood-sucking, forced consumption of blood, fem reader.…

Stark and Parker || romance ||

Stark and Parker || romance ||

164,547 3,291 27

The daughter of the multi millionaire, Tony Stark , meets the loner Peter Parker. ORAlissa Rose Potts Stark is 17 and daughter of Tony Stark. Being a young Stark has it ups and down, specially since her mother is gone. At least she gets to have breakfast with Thor and dinners with Captain America right? Peter Benjamin Parker lives in a small apartment at Queens with his aunt May. People at school know him as a loner, nerd and awkward. If they only knew who he really was...…

Rogan: A love story

Rogan: A love story

8,512 215 15

Rory and Logan after the proposal…

Repreive (Yandere Floch Forster x Reader)

Repreive (Yandere Floch Forster x Reader)

103 1 1

Floch offers you a way out.Warnings: yandere content, abuse of power, unbalanced power dynamics, gunplay, implied baby trapping, fem reader, faux-job???…

Benefit of Doubt (Yandere Floch Forster x Reader)

Benefit of Doubt (Yandere Floch Forster x Reader)

212 4 3

Your friends don't like Floch, Floch hates your friends. Warnings: modern/college AU, theft, stalking, floch is a closet creep, reiner x reader in the mix too, floch being disgusting…

KUNDIN QADDARATA

KUNDIN QADDARATA

1,451,611 118,072 110

Kalmar QADDARA kalma ce dake rataye bisa wuyan kowanne bawa,haka rayuwa ta gada,tafe take da QADDARORI kala kala,masu zaqi da akasin haka.............SUMAYYA na kallon yadda KUNDIN QADDARARTA ke ta bude mata shafi bayan shafi na TATA QADDARAR kowanne shafi kuma da irin nasa salon karatun da yake biya mata.....Shin wai sai ko yaushe KUNDIN ZAI QARE?sai yaushe zata kammala bitar QADDARORINTA?Kuyi nitso da linqaya cikin labarin don samun amsoshin kalolin qaddarar tata da kuma ranar yankewarsu'Yar mutan HUGUMA kuma UWA GA MUHAMMADIYYA ke riqe da alqalamin jagorancin labarin..........…

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)

499,762 41,508 59

MAFARI...komai yana da farko, komai yana da tushe, komai yana da asali, HARGITSIN RAYUWA kan faru cikin ƙanƙanin lokaci. Duniyar daka saba da ita zata iya birkicewa zuwa baƙuwa a gareka cikin ƙanƙanin lokaci.Tafiya mabanbanciya da sauri a cikin kaddara da dai-daito…

TAFIYAR MU (Completed)

TAFIYAR MU (Completed)

12,053 751 20

Rayuwar auren masoya biyun na tafiya daidai yanda suka tsara tun farkon fari, kwanciyar hankali da son juna ya kafu a cikin gidansu wanda hakan yasa suka zama abun burgewa ga jama'a da dama har wasu suna fatan ina ma su ne! Suna tsaka da wannan jindaɗin ne rayuwarsu ta canja salo wanda hakan yayi sanadiyyar bankaɗuwar wani tsohon alƙawari mai wuyar cikawa. Ko yaya rayuwar tasu zata ƙaya?…

A JINI NA TAKE

A JINI NA TAKE

56,315 2,946 12

Labari ne daya kunshi masarautu biyu; Masarautar Katsina, wacce take cikin Nigeria da kuma Masarautar Damagaran, wacce take cikin Kasar Niger. Labarin yayi duba ne da rayuwar Yarima Bilal, wanda rashin magana da miskilanci ya kanja ya shiga tarun matsaloli, wanda hakan yake haifar mashi da auren Zeenah Kabir Muhammad. Diyar Bafade da kuma baiwa. Me zai faru a rayuwar auren da aka hada miskili da kuma masifaffiya? Wanda dama tun farkon haduwarsu da masifa aka fara har yakai ga ya kure hakurinta ta sharara mashi maruka biyu? Shin ko zasu samu zaman lafiya kuwa? Bilal wanda ya kasance zuciyarshi a kulle take tun bayan rasuwar mahaifiyarshi zai bude ma Zeenah ita? Ya rayuwa zata basu bayan Zeenah ta fada soyayyarshi sai kwatsam Juwairiyya ta kunno kai? Wane hali Bilal zai shiga a lokacin da Fulani ta bankado wani tsohon sirri dake tsakaninsu?Fulani fah? Wacce take uwar gida kuma mai kula da hidimomin Masarautar Katsina gaba daya? Zata rufe sirrin data gano tsakanin Zeenah da Bilal dan gujewa tarwatsewar farin cikinsu? Abu daya ne zai kai ga na biyu, wanda har Bilal zai tsinci kanshi an mashi shamaki da Masarautar Katsina, hakan zai dangantashi da Masarautar Damagaran! Ku biyo Yar Malumfashi domin jin yadda labarin zai kasance.…

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅

129,260 17,382 71

Littafinnan Ingausa ne; wato hadakar turanci da Hausa.Shin ko ya rayuwar yan mata guda biyu zata kasance, a yayin da iyayensu zasu turasu aikatau; wanda ta hanyar iyayen keso su yiwa kansu kayan daki idan hidimar bikinsu ta taso.Shin wannan hanya da iyayen suka dauke zata bulle kuwa? Bayan dukansu yaran ba so suke ba?Me zai faru ga Sakeena wacce take fitsarin kwance, gata da rashin hakuri? Shin zaman gidan aiki zaiyi mata sauki kuwa?Habeeba fah? Wanda hakuri da juriya sune halinta. Shin aikatau zai chanza mata halayenta?Ku biyoni domin kuji yadda tafiyar zata kama.Aysha Malumfashi ce.…

 AFRA

AFRA

69,816 7,643 58

Murmushi tayi mishi wanda ya tafi da imanin sa yayin da ta juya kallonta ga duɓɓin mutanen wajen. Dogayen yatsunta biyu wanda suka sha jan lalle ta buga akan speakern dan ta ga ko yana aiki. Illai kuwa sai ta ji ƙaran bugun da tayi. Murmushi ta ƙara sakar wa mutanen da duk ita suke kallo, da mamaki a idanuwansu, kafin ta buɗe baki tafara magana kamar haka." Assalamu alaikum " sai ta ɗan dakata kaɗan don su amsa mata, ba laifi wasu sun amsa mata wasu kuma sunyi ƙum da bakin su. " dama na zo ne don na nuna farinciki na game da taya abokin mu, kaninmu da yayen mu Salim murna " tace yayin da take kallon angon wanda tun tahowarta stage yake warwara ido kamar baƙin munafuki, gashi yanda zufa yake ta keto masa, zaka zata ba ac a wajen.Kau da idanunshi yayi kafin su hadu da nata. " amma kuma abin da ya sosa min rai game da wannan abin shine ni nafi chanchanta da a kira in zo in bada tarihin wanan bawan Allah. " ta ƙara dan dakatawa yayin da ta runsunar da kanta kamar mai wani tunani, sai kuma ta k'ara daga kanta ta kalle mutanen da duk suke yi mata kallon mahaukaciya wadda batasan abin da take ba.Budar bakin ta ne sai tace. " duk da dai an kira abokin ango yayi nasa bayanin barin in ɗan baku tak'aitaccen nawa "." amarya Salima " tace tana kallon amaryar da tace kwalliya a cikin doguwar riga kalar ja itama, sai dai na amaryar bai kai na wannan budurwar kyau da tsaruwa ba, dan inbaka san wacce amaryar ba sai kazata itace.Salima wacce tun da yarinyar tafara magana ta ke ta faman bankamata harara, taja wani ɗan tsaki game da sake sakarmata wani hararan.Afra , yarinyar da ta ke kan stage in ta murmusa kafin tace ." ina taya ki murnar auran munafukin namiji, azzalume wanda bai san darajar mutane ba, ina kuma ƙara tayaki murnar samun daƙiƙin na namiji wanda ban da wata shakka ƙarshen sa bazai yi kyau ba, kuma ki kasa kunan ki kiji mijinko mayaudari ne, me bin mata ne kuma zan iya rantse miki fasiƙi ne "Read and find out…

MURADIN ZUCIYA

MURADIN ZUCIYA

36,411 2,523 20

'yan biyu ne masu tsananin kama ďaya masu mabambanta halaye. Maryam ta kasance miskila marar ďaukar raini, yayinda Mariya ta kasance mai son mutane da saurin sabo, tana da saurin fushi amma kuma tana da saurin sauka. Imran yaya ne a wurin Maryam da Mariya haka nan kuma daďaďďan saurayi a wurin Maryam wanda suka yiwa juna alkawarin aure. Me zai faru idan Maryam ta gano shakikiyar 'yaruwar da bata da kamarta a faďin duniyarta ta faďa tsundum a cikin son Imran. Zata hakura ta sadaukar mata da soyayyarta ne ko kuwa zata jajirce wajen ganin cewa bata rasa abin kaunarta ba. Ku biyoni cikin labarin sarkakkiyar soyayyar dake tsakanin Imran, Maryam da kuma Mariya.…

RAYUWAR BADIYYA ✅

RAYUWAR BADIYYA ✅

253,317 20,551 61

"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanji dadin rayuwata, babu yadda na iya haka na biyoki inda kika doro mani karan tsana, kullum sai kin zage kin dukeni, sunan mahaifiyata kuwa ya zama abun zagi a gareki a koda yaushe, kin hanani abinci, kin sakani wanka da ruwan sanyi lokacinda ake matukar sanyi, kin cuceni iya cutuwa, a haka Allah ya rayani. Sai ke yau dan rana daya kince zakici uwata nace nima zanci taki shine zakiyi kukan munafurci? Ni kin taba laakari da irin kukan danake cikin dare kullun? Dukda mahaifiyata ta rasu hakan bai hanaki zaginta ba. To na fada da babbar murya, wallahi duk kika kara cewa zakici uwata to sai naci taki uwar nima, and that's final!" Zuwa yanzu duk bakin cikin dake zuciyar Badiyya saida ya fito, kuka take kamar ranta zai fita, mahaifiyarta kawai takeda bukata, bakin ciki ya mata yawa, batada wanda zai saka ranta yayi sanyi bayan Momynta, amma tayi mata nisan da yakeda wuyar isa. Ta buda baki zatayi magana kenan Ahmad ya wanke ta da marika kyawawa guda biyu, ta dama da haggu, rike wajen tayi tana kallonshi.Magana ya fara cikin tsananin bacin rai, "Yanzu Badiyya a gabana kike cewa zakici uwarta? Uwata kenan fa Badiyya! To ko Yaya kika zaga bazan kyaleki ba balle wadda ban taba gani ba, dan haka wallahi zakiyi mugun dana sani," ya fada cikeda tsananin fushi, yana kara kai mata mazga saman kai.Kukane ya kara kwace mata "Kai kenan da baka taba ganin taka ba, nifa? Nifa Dady?! Na taba ganinta, nasanta, nasan dadin uwa, amma haka wani azzalumin ya raba ni da ita, sannan kai da nake tunanin zaka share min hawaye kaine kake kara sakani kuka, me na maka? Me Momyna ta maka?" Ta tambaya tana kureshi da idanu._______Me zai faru a rayuwar yarinya yar shekara goma data rasa mahaifiyarta? Wace irin rayuwa zatayi a gidan yayar mahaifinta?…

MATAN GIDA

MATAN GIDA

910 89 16

Labarin matan gida labarine tsararre da aka gina akan abu ɗaya wato zamantakewar ma'aurata da mu'amalarsu, labarin ya ƙunshi, cin amana, zamba cikin aminci,yaudara, soyayya mai ban sha'awa da kuma uwa uba tausayi ku dai kawai ku kasance tare da wannan littafin.…

AURE UKU(completed)

AURE UKU(completed)

22,681 1,171 32

DR UMAIMAH USMAN BULAMA,Mace yar kimanin shekara ishirin da tara ,Babbar surgeon A asibitin CITY TEACHING HOSPITAL ,Aure Uku, ƴaƴanta uku .Mace mara san hayaniya wadda tasan kan Aikinta ,babu abunda tasa a gabanta illa bawa Aikinta babban muhimmanci kana yaranta wadda kaɗdarar samunsu ta rarraba mata Aure .Kalma ɗaya zaka faɗa ta bata mata rai shine kushe mata Aikinta ko nuna wasa a duk wani abu da ya shafi Aikinta .Ita ɗin kwarariyace kuma gogaggiya akan duk wani abu da ya safi surgery,ba kasar ta ba hatta a wasu kasashen tana zuwa aiki.Bangaren soyayya fa?Bata dauki soyayya a bakin komai ba tunda dukkan Aurenta guda ɗaya ne tayi na soyayya kuma shima bai karbe ta ba wanda hakan yasa ta yanke shawarar saka soyayya a ƙwandan shara duk da kuwa tayin da ake kawo mata ,ta gama yanke imani da soyayya akan duk wani ɗa namiji wanda haka yasa mutane da dama ke mata kazafi da mata take so duba da ƙin mazanta karara a fili.Amma menene dalilin tsanar tasu da tayi?Menene yasa ta cire mazan daga tunaninta da zuciyarta baki daya?Shin zata faɗa soyayyar wani ɗa namiji ko a'a?Idan zata faɗa wanenen wannan mai sa'ar?.DR IMAM MUKTAR PAKI,Saurayi dan kimanin shekaru Ishirin da tara ,bai taba Aure ba,Dalibi wanda yake neman sake gogewa akan Aikin surgery ,shekara ɗaya wadda kareta ne kaɗai zai bashi kwali da kuma lasisin Fara yin surgery ,kaddara itace tayi aikinta ta ɗauko sa kan kachakar ta kawosa CITY TEACHING HOSPITAL inda yake ƙarkashin jagorancin likitar da kowa ke tsoro da shakka,Mene zai faru idan shi bai ji wannan feelings ɗin ba sai wani daban wanda shi kansa bazaya iya fassarawa ba?Shin ya wannan kaɗdarar tasu zata kasance?Shin Wanne irin chakwakiya Imam ke shirin ɗaukowa kansa domin wannan likitar da ya ke kan giyar so AURENTA UKU ,Ƴaƴanta uku a yayin da shi ko na fari bai taba yi ba.Ku biyo ɗiya jamilu domin jin yarda wannan labarin na IMAM da UMAIMAH zai kasance !…

FATU A BIRNI (Complete)

FATU A BIRNI (Complete)

55,777 2,146 18

"I promise you Mami, zan nemo miki ƴar'uwarki a duk inda take a faɗin ƙasar nan. SULTAN promises you that." Sultan ya shiga ya fita, har ya aikata abunda ba'a tsammani domin ya cika wannan alƙawari da ya ɗaukawar mahaifiyarshi, aka yi dace ya gano inda take. Wani abun takaici shine a maimakon ya samu ƴar'uwar Maminshi kamar yanda ya ci buri, sai ya haɗu da ƴarta kwalli ɗaya tak da ta haifa a duniya ta bari cikin ƙauyanci da kuma rashin wayewa. Baƙin cikinshi bai tsaya a nan ba, domin dattijon da yake riƙe da ita a take ya aura masa yarinyar ba tare da ya iya kaucewa wannan mummunan ƙaddaran ba. Ya tafi ya barta ba tare da ya sake waiwayarta ba, ya kuma tafi da wani kaso na zuciyarta ba tare da ya sani ba. Fatu (Fatima) ta ji haushi, sannan tana cikin baƙin cikin tafiyar da mijinta yayi ya barta. Tun tana tsumayinshi tana fatan ya dawo ya ɗauketa, har zuciyarta ta daskare da tsantsar tsanarshi na wofintar da ita da yayi, da kuma banzatar da igiyar aurensa dake kanta. Tayi alƙawarin ɗaukan fansa, ta kuma yi alƙawarin raba tsakaninsu ko da duniya zasu taru su hanata. Sai ta nemo shi a duk inda yake. Ta shiga cikin Birni nemansa, a nan kuma ƙaddara ya gifta tsakaninsu suka haɗu a lokaci da kuma yanayin da basu yi tsammani ba. Shi kuma ganin kyakkyawar baƙuwar fuska mai ɗauke da kamala, ya sashi faɗawa cikin sonta dumu-dumu ba tare da ya shiryawa hakan ba, kuma ba tare da ya gane cewa Matarsa ce ta Sunnah ba, Halal ɗinsa.Me zai faru idan Fatu ta haɗu da mutumin da ta ƙullata tsawon shekaru a yayin da shi kuma yake jinta a zuciyarsa tamkar ruhinsa?Me kuma zai faru Idan wasu sirrikan suka bayyana a lokacin da ba'a shirya musu ba? Fatu mace ce ɗaya mai hali mabanbanta; Fatu- Matar Sultan.Fatima- Budurwar Sultan.…

YAR AREWA(THE NORTHERN GIRL)Paid

YAR AREWA(THE NORTHERN GIRL)Paid

2,357 174 21

YAR AREWA (THE NORTHERN GIRL)Meet JASMINE BILAL SHAREEF In her journey of becoming a lady pilot"Kalma daya ta daddy i need a mom shi ne mafarin tarwatsewar gidansu ,Haduwarta dashi shine babban challenge na rayuwarta saboda yarda a kullum yake nuna bata iya ba bazata iya ba sabida she's just a naive girl who Can't even we wear her pilot pants properly and take expecting zama jagoran mutane dayawa, bashida aiki sai tunatar da ita cewa kitchen shine gurin da ya dace da ita,Kiyayarsa tun tana damunta har ta daina damunta tayi alkawarin nuna masa ba kitchen ne gurin daya dace da itaba ,Bata rabu dashi gurin aikiba tazo gida ta tarar dashi ,Yea ta tsinci kanta zaman gida daya dashi"CAPTAIN SHURAYM ABUBAKAR SADAUKI"Meet the cocky captain .Coming soon!!!…

FURUCI NA NE

FURUCI NA NE

44,774 3,650 37

"Baba meyasa kazama boka bokanci fa haramun ne kuma k'arya ne shirka ne Allah baya yafewa mushirki....."ke Izza ki kiyayeni idan kika nemi d'agamin hankali abin bazai miki kyau ba dan ni zan iyayin komai akan cikar burina na kashe Faida ma balle ke zaki kawo min maganar banza yanzu kinga wani abin da ya Dan ganci bokan ci ne atare dani na dena aikin ki kad'ai zan cigaba dayi shima idan burin mu yacika kika auri daya daga ahalin gidan nan zan bari na tuba meye Allah baya yafewa nide nasan zai yafemin".shiru tayi can ta nisa tace'' to shikenan Baba ance idan zaka sha giya shata dubu ni megaba dayan nake so Nasuru din".dariya yayi yace"shegiya Naira ba babba ba yaro ni kai na naso haka naso ace Nasara kika mallaka amma sam taurari sun nuna ba al'kairi taurarin ku basu hadu ba ba aure a tsakanin ku da Nasara shine na hakura amma ina lefin Aiban ko Agrif din'."tace'' amma Baba nafison Agrif din dan shine akusa da Nasara kaga yafi sauran sanin sirrin komai na dukiyar ".murmushi yayi yace"yanda kike so haka za ayi wa gareni inba keba".…

🤍Dr.TAHEER🤍

🤍Dr.TAHEER🤍

91,053 5,179 58

Dr.TAHEER labari ne mai cikeda soyayya mai tsuma zuciya...labarin wani matashin likita daya kamu da matsananciyar soyayyar yarinyar da ya raineta a hanunshi..yarinyan dake kiranshi da suna daddy kasancewarshi cousin brother din mahaifiyarta daya girme mata da shekaru biyu...it's an interesting love story indeed 😊…