KOWA YA GA ZABUWA...

KOWA YA GA ZABUWA...

16,092 1,144 47

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko sede mu zubawa sarautar Allah idanu zuwa sadda ze kawo mana karshen shi walau Mutuwa walau sakamako na farin ciki.HIDAYAT yarinya me ƙarancin shekaru marainiya gaba da baya, bata da kowa bata san kowa ba, ta taso cikin kangin rayuwar marikiya an aura mata mafi zaluncin miji cikin maza a rashin sani, wadda ya kasance ɗa ga marikiyarta Kaddarar ƴaƴa ta Haɗa ba tare da wannan azzalumin miji yayi maraba da su ba, ya rayuwa zata zame mata? Ta ina zata iya Kula da kanta da kuma yaranta? Cin su shan su, suruturarsu? Anya zata iya tsallake wannan jarabawar kuwa? Anya ba zata gaza a hanya ta fawallawa Allah lamuranta ta zubawa sarautar shi idanu ba? Shin da dangin miji zata ji ko da Shi karan kanshi mijin ko kuwa da baƙar rayuwa da take ciki? Shin zata iya tsira daga wannan taskar na Tsaka mai Wuya? Duk ku biyo ni cikin wannan littafi na KOWA YA GA ZABUWA... Na muku Alkawari ba Zaku taɓa yin nadama ba, Alqalamina a feke yake don Nishad'antar daku, fad'akantar daku da kuma ilmantar daku duk a cikin wannan littafi.. karku bari a baku labari.…

TAFIYAR MU (Completed)

TAFIYAR MU (Completed)

10,619 684 20

Rayuwar auren masoya biyun na tafiya daidai yanda suka tsara tun farkon fari, kwanciyar hankali da son juna ya kafu a cikin gidansu wanda hakan yasa suka zama abun burgewa ga jama'a da dama har wasu suna fatan ina ma su ne! Suna tsaka da wannan jindaɗin ne rayuwarsu ta canja salo wanda hakan yayi sanadiyyar bankaɗuwar wani tsohon alƙawari mai wuyar cikawa. Ko yaya rayuwar tasu zata ƙaya?…

A JINI NA TAKE

A JINI NA TAKE

55,201 2,930 12

Labari ne daya kunshi masarautu biyu; Masarautar Katsina, wacce take cikin Nigeria da kuma Masarautar Damagaran, wacce take cikin Kasar Niger. Labarin yayi duba ne da rayuwar Yarima Bilal, wanda rashin magana da miskilanci ya kanja ya shiga tarun matsaloli, wanda hakan yake haifar mashi da auren Zeenah Kabir Muhammad. Diyar Bafade da kuma baiwa. Me zai faru a rayuwar auren da aka hada miskili da kuma masifaffiya? Wanda dama tun farkon haduwarsu da masifa aka fara har yakai ga ya kure hakurinta ta sharara mashi maruka biyu? Shin ko zasu samu zaman lafiya kuwa? Bilal wanda ya kasance zuciyarshi a kulle take tun bayan rasuwar mahaifiyarshi zai bude ma Zeenah ita? Ya rayuwa zata basu bayan Zeenah ta fada soyayyarshi sai kwatsam Juwairiyya ta kunno kai? Wane hali Bilal zai shiga a lokacin da Fulani ta bankado wani tsohon sirri dake tsakaninsu?Fulani fah? Wacce take uwar gida kuma mai kula da hidimomin Masarautar Katsina gaba daya? Zata rufe sirrin data gano tsakanin Zeenah da Bilal dan gujewa tarwatsewar farin cikinsu? Abu daya ne zai kai ga na biyu, wanda har Bilal zai tsinci kanshi an mashi shamaki da Masarautar Katsina, hakan zai dangantashi da Masarautar Damagaran! Ku biyo Yar Malumfashi domin jin yadda labarin zai kasance.…

DOCTOR EESHA👩‍⚕️

DOCTOR EESHA👩‍⚕️

15,348 471 56

labari ne data kafu aka kadara🙇🙇 Kubiyoni ku ji yanda LabariDr. Essha Ahmad zata Kaya da Young Tycoon Namji Mai ji dankashi Aliyu Umar Tycooon 💃💃💃💃💃Ko ya ya zai kasance 🤔🤔🤔 Sai mu Haduuu…

MAI ƊAKI...!

MAI ƊAKI...!

709 40 22

Rayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da kayan more rayuwa a zamantakewar aure, nayi tunanin ina ma talakan da bashi da komai na aura indai zai bani kulawar da nake buk'ata a duk sanda na nemi hakan. Na samu ciwon damuwa tun ina da k'arancin shekaru ba tare dana farga ba, bani da abokin shawara na kasance marainiya mara uwa da uba. Na tabbatar mijina yana sona nima ina sonshi, shin meye ya jawo min hakan ni Ameenatou Laifina ne ko kuma laifin sane?.Auren mai kud'i shine riba a koda yaushe, na kwana a gida mai kyau, na tashi a waje mai kyau, naci abinda nake so, na hau motar da nake so, naa kuma fita duk k'asar da nake so ba tare da damuwar komai ba. Wannan shine kwanciyar hankali da walwala mai kawo farin ciki da annushuwa a zuciyar wanda yake cikin ta. Tabbas ni Fiddausi sai na kasance matar mai kudi ko ta wacce hanya.…

SUMAYYA(Paid Book💰)

SUMAYYA(Paid Book💰)

1,005 19 25

Ban taɓa zuwa asibiti ba tunda nake a rayuwata ba, mu 'yan gargajiya ne, sai dai karon farko dana je asibiti shi ne abu na biyu daya ƙara ruguza rayuwata. Na shiga ɗimuwa, na yi nadamar da ban taɓa yin irinta a rayuwata ba, wani lokacin idan na kalli kaina sai naga kamar ni kaɗaice Allah ya jarabta da mummunar ƙaddara irin wannan, sai dai wasu lokutan sai na tuna cewa wannan ba komai bace face jarabawar rayuwa. Ni aure sam bai min rana ba, har mamaki nake idan wasu na farin ciki da aure, ni aure a damuwa ya jefani wadda tayi min tabo na har abada!Ku biyoni cikin labarin dan na warware muku zare da abawa.…

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)

497,949 41,379 59

MAFARI...komai yana da farko, komai yana da tushe, komai yana da asali, HARGITSIN RAYUWA kan faru cikin ƙanƙanin lokaci. Duniyar daka saba da ita zata iya birkicewa zuwa baƙuwa a gareka cikin ƙanƙanin lokaci.Tafiya mabanbanciya da sauri a cikin kaddara da dai-daito…

MATAR K'ABILA (Completed)

MATAR K'ABILA (Completed)

374,348 29,070 58

Anwar Bankudi, the Handsome Young Millionaire ke zagaye da matan Aure uku, kowacce da salon halinta da matakin matsayinta a zuciyarsa. Shin wacece Tauraruwarsa?Rayuwar gidan Bahaushe mai cike da sark'akiya had'e da zallan zaman aurenmu a yau.…

RAYUWAR BADIYYA ✅

RAYUWAR BADIYYA ✅

251,775 20,475 61

"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanji dadin rayuwata, babu yadda na iya haka na biyoki inda kika doro mani karan tsana, kullum sai kin zage kin dukeni, sunan mahaifiyata kuwa ya zama abun zagi a gareki a koda yaushe, kin hanani abinci, kin sakani wanka da ruwan sanyi lokacinda ake matukar sanyi, kin cuceni iya cutuwa, a haka Allah ya rayani. Sai ke yau dan rana daya kince zakici uwata nace nima zanci taki shine zakiyi kukan munafurci? Ni kin taba laakari da irin kukan danake cikin dare kullun? Dukda mahaifiyata ta rasu hakan bai hanaki zaginta ba. To na fada da babbar murya, wallahi duk kika kara cewa zakici uwata to sai naci taki uwar nima, and that's final!" Zuwa yanzu duk bakin cikin dake zuciyar Badiyya saida ya fito, kuka take kamar ranta zai fita, mahaifiyarta kawai takeda bukata, bakin ciki ya mata yawa, batada wanda zai saka ranta yayi sanyi bayan Momynta, amma tayi mata nisan da yakeda wuyar isa. Ta buda baki zatayi magana kenan Ahmad ya wanke ta da marika kyawawa guda biyu, ta dama da haggu, rike wajen tayi tana kallonshi.Magana ya fara cikin tsananin bacin rai, "Yanzu Badiyya a gabana kike cewa zakici uwarta? Uwata kenan fa Badiyya! To ko Yaya kika zaga bazan kyaleki ba balle wadda ban taba gani ba, dan haka wallahi zakiyi mugun dana sani," ya fada cikeda tsananin fushi, yana kara kai mata mazga saman kai.Kukane ya kara kwace mata "Kai kenan da baka taba ganin taka ba, nifa? Nifa Dady?! Na taba ganinta, nasanta, nasan dadin uwa, amma haka wani azzalumin ya raba ni da ita, sannan kai da nake tunanin zaka share min hawaye kaine kake kara sakani kuka, me na maka? Me Momyna ta maka?" Ta tambaya tana kureshi da idanu._______Me zai faru a rayuwar yarinya yar shekara goma data rasa mahaifiyarta? Wace irin rayuwa zatayi a gidan yayar mahaifinta?…

SIRRIN MU

SIRRIN MU

7,545 254 12

_Duniya makaranta a lokacin da wasu suke shiganta a lokacin ne wasu ke barinta,wasu na zuwa Duniya wasu kuma na barin Duniya, Rayuwa kamar shafin littafi ce,baka sanin abinda yake bangwan baya dole saika buɗe shafin gaba,muna zuwa Duniya ne ba tare da sanin abinda ke cikinta ba,wasu na zuwa a makance, wasu a kurmance,wasu kuma babu ido,kunan jin magana,uwa uba wasu basa zuwa da ƙafar takawa__Nakasa bata taɓa zama kasawa,haka kuma ƙaddarar data mai dashi nakashasshen zata iya sauya, kullum cikin zullumi yake, shin tayaya ne rayuwa zata kasance masa? tayaya yana nakashasshen zai iya mulkan dubban jama'a? Cikin ana tsangwamarsa bare ace ya zama shugaba,yaya jama'ar gari zasu ɗauke sa?tayaya zai gabatar da mulkin bayan Allah ya taushe ta hanyarsa rasa wani ɓangare na jikinsa?__Zuciya nada abubuwan ban mamaki,abinda kake so ita bashi take so ba,kullum yana ganin abin kamar mafarki amma yadda abin ke zamar masa a gaske shike masa mamaki,me zaiyi wanda zai samu farin ciki?me zaifi wanda zuciyarsa zata daina kewa ta daina ƙunci,duhun dake cikinta haske ya mamaye shi, FARAUTA shine abinda zuciyarsa ta yanke masa,abin mamaki shine tayaya nakashasshe zai iya zama mafarauci? Tayaya farauta zata masa maganin damuwarsa?.._ '''SHIN ZAI IYA KO A'A?YANA CIN RIBA A FARAUTAR KO A'A?KUNA TUNANIN WATA RANA NAKASAR SA ZATA IYA ZAMA RIBA GARESA?…

MAKAUNIYAR RAYUWA

MAKAUNIYAR RAYUWA

12,459 606 53

MAKAUNIYAR RAYUWA-KASHI NA UKU-BABI ASHIRIN###Fatan alkhairi gareku masoyana a duk inda kuke,alherin Allah ya kai gareku, ubangijin Allah ya biyawa kowa buƙatansa na alkhairi ya shirya mana zuri'a shirin addini musulci ameen####…

TSINTACCIYA

TSINTACCIYA

17,553 297 16

Rayuwa mai ɗauke da ƙunci da kuma tarin baƙin ciki, Yayinda hasken wata ke fitowa yana haskaka samaniya, a lokacin ne kuma zuciya keyin zafi da wani irin tafarfasa, Idaniya sun makance dalilin zubar Hawayen da ban san yaushe ne zai tsaya ba, Ina jin inama zan iya kashe kai na! Ko hakan zai sanya zuciyata ta samu nutsuwa da kuma salama, a lokacin da kowa ya kamata yayi farin ciki a lokacin na kejin duniya nayi min zafi, Idaniyan zuciyata na tafarfasa, ban sani ko zan zama dai-dai kamar kowa? Ban san yaushe rayuwa zata juya min daga juyin wainar fulawan da take dani ba, rayuwata ita ake kira da GABA GAƊI rayuwa mara ƴan ci, ko wacce mace na amsa sunanta dana mahaifinta yayinda ya kasance ni kuma ina amsa sunana kana na bashi makari da TSINTACCIYA!…

KWANTAN ƁAUNA

KWANTAN ƁAUNA

3,383 146 27

Izza, mulki, k'asaita sun tattara a gare ta ita kad'ai. Y'ar sarki ce, jikar sarki, matar sarki. Bata k'aunar talaka bata son had'a hanya da talauci, burin ta d'aya tak ya rage a duniya shi ne d'an ta ya zama sarki ta zama babar sarki kuma kakar sarki ta gobe; Sai dai kash! Y'ay'anta maza har guda uku masu matuk'ar kama da juna sun kasance babu wanda yake da qualities d'in rik'e ragamar Al'umma. Na farko shaye-shaye, na biyu kurma ne, na uku ba ya da lafiyar k'wak'walwa. A Lokacin da burinta ke gab da cika kwatsam Y'ar talakawa, bak'a, gurguwa mai tallan abinci ta shigo rayuwar samarin 'ya'yan nata guda biyu, gurgurwar da ta zama silar girgizawar duniyarta da burinta, gurgurwar da ta haddasa mata raunin da bata da shi, gurguwar da ta zamar mata inuwar dodo...shin me zai faru? Ta wacce hanya gurguwa ta kutso cikin rayuwar wad'annan sarakunan...? Waye zai zama sarki cikin su ukun duk da kasnacewar su masu kama d'aya......? ina alwashin da ta ɗauka na ganin cewar sai taga bayan duk wanda ya nemi ya ruguza lissafinta?, ina alwashinta na cewar sai ta kassara rayuwar wanda ya kawo kutsen hana ɗanta zama sarkin gari....? Zai cika ko A'a?.*KWANTAN ƁAUNA*…

IGIYAR ZATO....💕 || PAID NOVEL (COMPLETED✅)

IGIYAR ZATO....💕 || PAID NOVEL (COMPLETED✅)

15,843 306 7

Labarin ruguntsumin gidan *MATA TARA* gidan da tarbiyya tai karanci, Hassada, Makirci, Tuggu, Sihiri. Gidan da rashin daraja ke arha.. Gefe d'aya kuma tacacciyar kauna ce mai sanyaya ruhi marar sirke.Mai dauke da labarin BATOUL! Yarinya mai tarbiyya da kwazo. Shin wa zata aura HAYSAM wanda ta rena shekarun sa be kai rabin hamsin ba (25) duk kuwa da shi ya dau nauyin karatun ta? Ko kuwa MUHAMMAD MUBEEN? Matashin saurayi dan gwamna wanda take koyar dashi a karkashin ajin ta na level one? 😂😂Ya take ne? Ya zata kaya da soyayyar ruhi uku dake cikin cakwakiyar rayuwa..????…

K'abila...

K'abila...

761 73 4

Aurenta da Khalil kaddara ne. Zuwanta gidansu a matsayin mai aiki jarabta ne. Zama gidanshi tare da matarshi kuma bala'i ne. Da wanne zataji? Miji wanda ya tsaneta tamkar mutuwarsa ko kuwa matarsa da bata da burin daya wuce ta tozartata dukda kuwa batasan itadin matarsa bace? Ko kuwa karyata musulunci da kowa yakeyi?Tabbas, K'abila...itama musulma ce. Amma a rayuwar Fatima Batul, hakan abu ne mai wuyar bayyanawa. Kyara, tsangwama da wulakanci sune abubuwan da tafi sabawa dasu a duniya har tana ganin bazata tabi jin dadi ba a rayuwarta. Kasantuwar mahaifiyarta Igbo, tunda Batul ta bude ido babu abunda ta sani face kunci da bakin ciki sai tarin hawaye. Wai dama shi musulunci idan ba a ciki aka haifeka ba Allah baya amsarka ne?Ko kuwa dai dole sai kai bahaushe ne ko bafulatani sannan musuluncinka yake zama ingantacce? Ana kiranta K'abila, ko kuma ace mata Tubabba, kai harma muna musulma ana kiranta wai duk dan kasancewar mahaifiyarta inyamura duk kuwa da cewar ta musulunta daga baya. Batul bata gara jefa kanta cikin ukuba ba sai bayan aurenta da Khalil, ga bala'in mahaifiyarsa da yan'uwansa, dangi da abokansa...shin ina zata saka rayuwarta ne?Data sani da bata gudu tabar gida ba, data tsaya dangin mahaifinta sunyi duk yanda sukeso da ita, da bata roki alfarma ta auri Khalil ba...---Labari ne mai cike da darussa daban daban akan addini, al'ada, zamantawa da kuma tsantsar soyayya. Ku biyoni dan ganin yanda labarin Fatima Batul da angonta Ibrahim Khalil zai kasance...…

RAYUWAR AURENA

RAYUWAR AURENA

118,572 5,106 63

Labari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,…

BA KOWANE SO BANE.......

BA KOWANE SO BANE.......

1,781 93 21

So da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar takamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda na kasa fin karfin zuciya ta in karba nasa kafa nayi shuri da ita.Abinda na manta shine a lokacin da wani ya jefar da abinda yake ganin ba shi da amfani gare shi, a lokacin ne kuma wani zai tsinta ya danke da hannu bibbiyu.Ya so ni da dukkan zuciyar sa, ya kauna ce ni da gaba daya rayuwar sa haka kuma ya bauta min da duk lafiyar sa, amma da me na saka masa?, da mafi munin sakayyar da duk wani dan Adam ze jura.Na wulakanta shi a inda ake ganin darajar sa, na zubar mai da kima a inda ake mutunta shi, kai nayi masa abubuwa da yawan da duk ya jure har zuwa lokacin da ƙaddara ta raba mu ta karfi da yaji wanda na bada gudunmawa ga wannan ƙaddara ba kadan ba.Sedai ba'a dauki lokaci me tsayi ba na gane nice da asara, haka kuma abinda na kwallafa rai din ban samu ba, banda gare gare da kwallon da ƙaddara ta dinga yi da rayuwa ta.A lokacin da ya hakura dani taa dole, ya karbi ƙaddarar rayuwa da zavin Ubangiji gare shi, a lokacin ne wata kaddarar ta sake daure zare me karfi tsakanin mu.Shin da wani ido zan dube shi, da wane karfin halin zan yaki rauni na na karbi kyakkyawar ƙaddara ta?, shin shi ɗin ze bani dama ko kuwa ya rufe babi na? shin har yanzu akwai digon alfarma tsakani na dashi????#Aimah#Sa'adah#Masdooq#hatred#jealous#depression#destiny all in;#love_story_2024…

MUTUM DA DUNIYARSA......

MUTUM DA DUNIYARSA......

116,179 9,245 41

Wannan labari labarine da ya taɓo rayuwar da mafi yawan mata ke fuskanta a wannan rayuwar, tare da rayuwar kishi na gidajen aurenmu, da nuna jarumtar mazan ƙwarai da ke aiki da hankali da ilimi wajen tafiyar da ragamar rayuwar aurensu. Magidanta da yawa basa son a haifa musu ƴaƴa mata, abin kuma zai baka mamaki idan zaka tarasu wajen buƙatar jin dalilinsu, musani UBANGIJI ya fimu sanin mu su wanene? miyasa yayimu jinsi-jinsi, yare daban-daban, zuri'a daban-daban. kai dai ka roƙi ALLAH ya baka mai albarka kawai shine magana.…

MATAR AMEER

MATAR AMEER

16,504 889 71

'Ammi ya zan yi da rayuwata? Ya kuke so in yi da zuciyata? Ban taba ba...daidai da rana daya ban taba mafarkin yin rayuwar aure ba tare da Ameer ba. Na roke ku da Allah ku zuba idanuwanku kawai a kaina, ina ji da kun san yadda zuciyata ke tafarfasa a duk lokacin da kuka yi min zancen auren wani wanda ba Ameer ba da tuni kun daina...' Kuka sosai take yi, kukan da ke fitowa tun daga k'asan zuciyarta yana ratsowa tsakanin idanuwanta.'Na sani akwai zafi da radadi Ameerah, na san miye so, na san gubarshi saboda ni ma na tab'a dandana. Sai dai Ameerah ba za mu zura miki idanuwa ba, shekarunki ashirin da takwas kenan babu aure, kina zaune jiran gawon shanu. Waye ya san inda Ameer yake yanzu? Wa ma yake da tabbacin yana da rai ko babu?'…

RAYUWAR JIDDAH ✔

RAYUWAR JIDDAH ✔

10,721 875 42

RAYUWAR JIDDAHLabari ne akan rayuwar wata ya' mace mai suna Hauwa'u Jiddah.Let embark on the journey together and see for ourselves.Happy Reading 😉…