nooor-alhuda
28,212 3,169 61
#1 in halal romance 27-08-23#1 in hausa romance 02-09-23#1 in soyayya 10-11-23#1 in arewabooks 29-06-23#1 in arewastories 29-06-23#8 in romance-freindship 27-10-23* * *Bata san lokacin da ta ษora hannu a ka ba, "Na shiga uku!"Dariyar mugunta ya fara mata, "Dare! Dare!! Dare!!!"Yawu ta haษiye da ฦyar gabanta na faษuwa. Mafita ษaya ta hango shi ne tayi addu'a yayi daring ษinta abu mai sauฦi, kuma ba wanda zai ba ta kunya ba."Toh kin shirya ji?"Sai da ta langwaษe masa kai sannan ta amsa da muryar tausayi, "Eh.""Act your favorite romance scene from a movie with your partner.""Haba dan Allah! Haba dan Allah!""Idan zaki daina borin nan ma gwara ki daina dan wannan karan ba ษaga ฦafa."Hawayen ฦarya ta fara ฦoฦarin matsowa kamar ษazu amma wannan karon sai suka ฦi tsattsafowa. Da taga haka kawai sai ta cigaba da bubbuga ฦafafuwanta a ฦasa tana faษin, "Me yasa kake min haka? Ya za ayi ka rinฦa bani abinda ka san ba zan iya ba?"Jotter ษin ya rufe yana mata dariya, "Za ki iya mana, me abin wahala a ciki? Any romance scene fa kawai za kiyi acting tare da ni. Kuma ban ce ga abinda nake so ba, ban ce hug me, ko kis..." Siririn hannunta mai ษumi da ya rufe masa bakin ne ya hana shi ฦarasawa. A hankali ya zame hannun ya riฦo shi yana dariya ฦasa-ฦasa, "Da kika hanani ฦarasawa kin san me nayi niyyar faษa ne? Wa yace miki kis..."Da sauri ta saka ษaya hannun ta sake rufe masa baki ruf, "Ka bari, ka bari ba na so."Hannun ya zame sannan ya haษe shi da ษaya hannun nata dake riฦe a hannunshi, "Da na yi niyyar canja miki amma na fasa, na lura rigima kawai kike ji amma za ki iya.""Na rantse da Allah ba zan iya ba.""Ki daina rantsewa, ke da kika yi wannan me kuma zai gagare ki?""Da nayi me? Me nayi?""Ohh bama ki sani ba?"Shiru tayi tana kallonshi blankly, da gaske bata san me tayi ba."Rug da jikina duka ษaya ne a gurinki ko?"Sai lokacin ta lura da yadda ta haye kan cinya da ฦafafuwanshi tayi kane-kane.โฆ