AMARYAR ZAYYAD
Sanin abinda ke cikin labarin sai an bini daki daki amma akwai sarkakiya.…
Sanin abinda ke cikin labarin sai an bini daki daki amma akwai sarkakiya.…
Rayuwar gidan aurena ta kasance izina ga masu burin auren kud'i koda babu kwanciyar hankali. gidana ya kasance tamkar kabarin bature daga waje akwai kyau da k'yalli amma na ciki ne kawai yasan abinda yake wakana. Tabbas naga rashin amfanin kud'i da kayan more rayuwa a zamantakewar aure, nayi tunanin ina ma talakan da bashi da komai na aura indai zai bani kulawar da nake buk'ata a duk sanda na nemi hakan. Na samu ciwon damuwa tun ina da k'arancin shekaru ba tare dana farga ba, bani da abokin shawara na kasance marainiya mara uwa da uba. Na tabbatar mijina yana sona nima ina sonshi, shin meye ya jawo min hakan ni Ameenatou Laifina ne ko kuma laifin sane?.Auren mai kud'i shine riba a koda yaushe, na kwana a gida mai kyau, na tashi a waje mai kyau, naci abinda nake so, na hau motar da nake so, naa kuma fita duk k'asar da nake so ba tare da damuwar komai ba. Wannan shine kwanciyar hankali da walwala mai kawo farin ciki da annushuwa a zuciyar wanda yake cikin ta. Tabbas ni Fiddausi sai na kasance matar mai kudi ko ta wacce hanya.…
Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? Yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke?Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa? BAKAR WASIKA...! _Mai farin rubutu_…
Strange Love story…
labari Mai tab'a zuciya…
A captivating story of romance,betrayal,passion,Guilt,heartbreak,love and mystery.…
Rayuwar auren masoya biyun na tafiya daidai yanda suka tsara tun farkon fari, kwanciyar hankali da son juna ya kafu a cikin gidansu wanda hakan yasa suka zama abun burgewa ga jama'a da dama har wasu suna fatan ina ma su ne! Suna tsaka da wannan jindaɗin ne rayuwarsu ta canja salo wanda hakan yayi sanadiyyar bankaɗuwar wani tsohon alƙawari mai wuyar cikawa. Ko yaya rayuwar tasu zata ƙaya?…
Zanen ƙaddaransa yana cikin zuciyarta, kamar yanda zanen nata ƙaddan ke cikin tasa zuciyar. Idan zuciyoyi suka haɗe waje guda akan samu wata irin zazzafan ƙauna. Ako da yaushe jinsa yake kamar wani baƙon halitta, RAUNI DAMUWA sune abun da sukayi tasiri wajen cika rayuwarsa, yasani kowani bawa da irin tasa ƙaddaran Amma shitasa Ƙaddaran takasance me girma ne agareshi.... ***hearttouching and destiny!!!…
labarine da ya kunshi rikitacciyar soyayya da ramuwa,Wanda masoyan suna son juna Amman sun kasa gasganta haka Wanda har suka kusa su rasa juna hmmmm me zai faruuuu…
Kaddara!Mece ce ita?Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta cikin mummunar kaddara, irin kaddarar da ba ta da magani?Shin dukkanin mutane ne ke jingine mafarkai da burikansu, su sadaukar da duk wani farincikinsu domin aminnansu?Ba matsalarta ce kadai ta dauka matsala ba, har matsalar aminiyarta ta mayar da ita tata, yayin da ta ci alwashin daukar fansa , ta ajiye burinta a gefe.Ku shigo cikin labarin DARE DUBU, na muku alkawarin ba za ku yi nadamar bibiyarsa ba.…
_Duniya makaranta a lokacin da wasu suke shiganta a lokacin ne wasu ke barinta,wasu na zuwa Duniya wasu kuma na barin Duniya, Rayuwa kamar shafin littafi ce,baka sanin abinda yake bangwan baya dole saika buɗe shafin gaba,muna zuwa Duniya ne ba tare da sanin abinda ke cikinta ba,wasu na zuwa a makance, wasu a kurmance,wasu kuma babu ido,kunan jin magana,uwa uba wasu basa zuwa da ƙafar takawa__Nakasa bata taɓa zama kasawa,haka kuma ƙaddarar data mai dashi nakashasshen zata iya sauya, kullum cikin zullumi yake, shin tayaya ne rayuwa zata kasance masa? tayaya yana nakashasshen zai iya mulkan dubban jama'a? Cikin ana tsangwamarsa bare ace ya zama shugaba,yaya jama'ar gari zasu ɗauke sa?tayaya zai gabatar da mulkin bayan Allah ya taushe ta hanyarsa rasa wani ɓangare na jikinsa?__Zuciya nada abubuwan ban mamaki,abinda kake so ita bashi take so ba,kullum yana ganin abin kamar mafarki amma yadda abin ke zamar masa a gaske shike masa mamaki,me zaiyi wanda zai samu farin ciki?me zaifi wanda zuciyarsa zata daina kewa ta daina ƙunci,duhun dake cikinta haske ya mamaye shi, FARAUTA shine abinda zuciyarsa ta yanke masa,abin mamaki shine tayaya nakashasshe zai iya zama mafarauci? Tayaya farauta zata masa maganin damuwarsa?.._ '''SHIN ZAI IYA KO A'A?YANA CIN RIBA A FARAUTAR KO A'A?KUNA TUNANIN WATA RANA NAKASAR SA ZATA IYA ZAMA RIBA GARESA?…
Ban taɓa zuwa asibiti ba tunda nake a rayuwata ba, mu 'yan gargajiya ne, sai dai karon farko dana je asibiti shi ne abu na biyu daya ƙara ruguza rayuwata. Na shiga ɗimuwa, na yi nadamar da ban taɓa yin irinta a rayuwata ba, wani lokacin idan na kalli kaina sai naga kamar ni kaɗaice Allah ya jarabta da mummunar ƙaddara irin wannan, sai dai wasu lokutan sai na tuna cewa wannan ba komai bace face jarabawar rayuwa. Ni aure sam bai min rana ba, har mamaki nake idan wasu na farin ciki da aure, ni aure a damuwa ya jefani wadda tayi min tabo na har abada!Ku biyoni cikin labarin dan na warware muku zare da abawa.…
Labarin soyayya,da nadama…
Nadama…
Matar shi ce ta farko bata san haihuwa, idan ta samu ciki sai ta zubar, as ending yake yin auren sirri da mai aikin gidan…
Labari ne daya kunshi masarautu biyu; Masarautar Katsina, wacce take cikin Nigeria da kuma Masarautar Damagaran, wacce take cikin Kasar Niger. Labarin yayi duba ne da rayuwar Yarima Bilal, wanda rashin magana da miskilanci ya kanja ya shiga tarun matsaloli, wanda hakan yake haifar mashi da auren Zeenah Kabir Muhammad. Diyar Bafade da kuma baiwa. Me zai faru a rayuwar auren da aka hada miskili da kuma masifaffiya? Wanda dama tun farkon haduwarsu da masifa aka fara har yakai ga ya kure hakurinta ta sharara mashi maruka biyu? Shin ko zasu samu zaman lafiya kuwa? Bilal wanda ya kasance zuciyarshi a kulle take tun bayan rasuwar mahaifiyarshi zai bude ma Zeenah ita? Ya rayuwa zata basu bayan Zeenah ta fada soyayyarshi sai kwatsam Juwairiyya ta kunno kai? Wane hali Bilal zai shiga a lokacin da Fulani ta bankado wani tsohon sirri dake tsakaninsu?Fulani fah? Wacce take uwar gida kuma mai kula da hidimomin Masarautar Katsina gaba daya? Zata rufe sirrin data gano tsakanin Zeenah da Bilal dan gujewa tarwatsewar farin cikinsu? Abu daya ne zai kai ga na biyu, wanda har Bilal zai tsinci kanshi an mashi shamaki da Masarautar Katsina, hakan zai dangantashi da Masarautar Damagaran! Ku biyo Yar Malumfashi domin jin yadda labarin zai kasance.…
Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko sede mu zubawa sarautar Allah idanu zuwa sadda ze kawo mana karshen shi walau Mutuwa walau sakamako na farin ciki.HIDAYAT yarinya me ƙarancin shekaru marainiya gaba da baya, bata da kowa bata san kowa ba, ta taso cikin kangin rayuwar marikiya an aura mata mafi zaluncin miji cikin maza a rashin sani, wadda ya kasance ɗa ga marikiyarta Kaddarar ƴaƴa ta Haɗa ba tare da wannan azzalumin miji yayi maraba da su ba, ya rayuwa zata zame mata? Ta ina zata iya Kula da kanta da kuma yaranta? Cin su shan su, suruturarsu? Anya zata iya tsallake wannan jarabawar kuwa? Anya ba zata gaza a hanya ta fawallawa Allah lamuranta ta zubawa sarautar shi idanu ba? Shin da dangin miji zata ji ko da Shi karan kanshi mijin ko kuwa da baƙar rayuwa da take ciki? Shin zata iya tsira daga wannan taskar na Tsaka mai Wuya? Duk ku biyo ni cikin wannan littafi na KOWA YA GA ZABUWA... Na muku Alkawari ba Zaku taɓa yin nadama ba, Alqalamina a feke yake don Nishad'antar daku, fad'akantar daku da kuma ilmantar daku duk a cikin wannan littafi.. karku bari a baku labari.…
*Yana da kyau a duk lokacin da IDANIYAR RUWA tayi wahalar toshewa acikin WATA ALAƘA ta rayuwarmu muyi tunani akan cewa TSARIN ALLAH ne, shi ya ƙaddara hakan kuma da sannu sauki zai zo ba tare da mun biyewa zukatanmu ba har suka kaimu ga shuka BISHIYAR TSIYA a cikin GONAR SHARRI, domin kuwa hakan zai kaimu ga girbar ƴaƴan nadama marasa adadi, Ya Allah ka warware muna damuwoyin mu albarkacin fiyayyen halitta*_NASIHA CE KYAUTA DAGA ƳAN TAGWAYENKU😍_…
Revenge…
Ga rayuwar da yawa daga cikin ƴan Adam sukan iya fakewa da ƙaddara ko ruɗin shaiɗan. Sai dai a rayuwar wasu duka babu ɗayan da ke kasancewa daga cikin biyun da na lissafa, ciki kuwa har da ni kaina. Na tsammaci shiga gidaje masu manyan benaye da zama a cikin su kan iya mantar da kai wani mataki kake a yanzu?Haka na iyakance adadin motocin da zuciya ke muradin hawa. Ga irin rayuwar da nake gudanarwa na tasamma ware nau'ikan ababen cimaka don gudun gamuwa da wata lalurar, ko da kuwa jariri ce. Duk wata kusafa da na san zan iya gamuwa da talaka ko mai matacciyar zuciya da baya ɗauke da buri, ina iya kokarin don ka da mu gamu.A lokacin da lamarin zai soma ne duniya tamin atishar tsaki ta yadda komai da komai da ya wanzu a cikin rayuwa ta sai da ya zama ya disashe tamkar bai faru ba, hatta lafiyar da nake ganin ta jima tana walankeluwa dani wuri guda, yo i mana. Duk sa'adda wannan lamarin ke wakana ciwon kai banyi, sai dai a yau cutar dake tare dani, ko kuma ince cutuka, baza su zamo silar kai ni ƙas ba, sai dai lamarin da ya haɗoni da komai tunda fari ya zame min sanadi.…