RUWAN DAFA KAI 146~150
Na SUMAYYA DANZABUWA
Bata farka ba sai Goma ma tawuce na safe gashi duk jikinta asage,"kai har goma tayi ko asubah banyi ba"tace aranta bayan taja dan tsaki ta kalli agogon dake bangon dakin,juyawa tayi gareshi,taga baccinshi yake tsakaninshi da Allah ko ina yawun bacci,ga uban minshari dayake ko ya akayi ma ta iya bacci da wannan gurnanin akusa da ita oho?(hmm gajiya)"ikon Allah ga namiji dai har namiji amma kuma dai sai ahankali,Ganin tana batawa kanta lokacine yasa ta tashi tashiga tayo alwala tazo tayi sallah,"na tabbata ya tasheni na kasa tashi,ya rabu dani,kodayake dama ya zaayi in iya tashi,irin wannan gajiya"tacigaba da zancen zuci,tanata kissima irin zaman dazasuyi,dakuma lokacin dazasu diba tare,don idan abubuwa basu mata yadda takeso ba ko kuma idan taga wani wanda yamata babu tilas,dolene tasa yasaketa don ita kam yanzu tafara aure,saidai duk abinda mutanen duniya zasu fada su fada,bakinsu dai bazai fito mata ajiki ba,karkari ace takafa tarihi.
Tana kan daddumar tana latse latsen waya,sai yunwa takeji tana kuma jira yatashi yasamamusu abinda zasuci,gani tayi yayi wata wawar mika,ya wangale baki yana hamma,bako salati,(sai kace ita yi take)hakan ne yasa ta binshi da kallo kawai don tsakani da Allah bata sani ba ko tanasonshi ko kuwa akasin haka,batasan metakeji ba a zuciyarta game dashi,tasan dai kawai tazabeshi ne don yanada duk abubuwan datake bukata a namiji don yin auren huce haushi amma bawai don zuciyarta ta aminta dashi ba.
Hada ido sukayi ta sakar mishi murmushi,shima haka bawanda daiyace dawani uffan yazo yawuceta yashiga bandakin.
Baiwani dade ba yafito yazura jallabiya,da alamun wanka yayi,sannan yazo ya dare dadduma lokacin wajen shabiyu,kuma har sannan baayi magana ba bawanda yace dakowa komai.
Saida ya idar ya juyo ya fuskanceta,"amarya amarya"yana washe baki don badai faraa ba,"naam"ta saki murnushi,"tun yaushe kika tashi kuma?"yasake cewa,"wallahi bandade ba kasan jiyan ne sai ahankali,nasan ka tattasheni sallah ko?"tace bayan ta cire hijabin jikinta ta wurgar a wajen"don babu wani amfanin boye bakaken halayenta kuma tunda bukatarta ta biya,ai tayi kokari,ina laifi?dama dai auren ne tadamu taga anyi to anyi idan yaga bazai iya jure zama da ita da halayenta ba sai ya sawwake mata,don tasan har duniya ta nade namiji daya zata taba so shine yusuf,amma duk irin son datake mishi ya bade idanunshi da toka ya zabga mata rashin mutumci ya wulakantata,kodayke bakomai ai dole ahankali zata cire soyayyarshi daga zuciyarta takuma guji kara fadawa wani tarkon(son wani)tunda soyayya bata karbeta ba,mazan duk makaryatane mayaudara tadawo daga rakiyarsu.
"Hm,wallahi nima haka fa,tabbas nagaji fiyeda misali,kuma duk laifinki ne,tunda ke kika jawo,saboda kin hadu ta koina,gaskiya ke karshe ce"yasake washe baki,"Allah ko"tabashi ansar har lokacin bata bar latsa wayar tata ba(wai wanda bai taba kusantar wata mace bane,yasan ni karshe ce dan rainin hankali)tacigaba da zancen zuci,"Allah kuwa,gashi nima sai yanzu natashi"yasake yin yar dariya,shekeke ta tsaya kallonshi bayan tabar abinda take ta kureshi da idanu,"wai kananufin kaima sallar asubah kayi yanzu?"ah,eh mana,amma bansaba makara bafa,tun kafin ki fassarani,yau ne dai kawai kuma shima ai da dalili,kinsan abinki da farinshiga"ya kyalkyale da dariya,dan murmushin karfin hali tayi,cikeda mamakinshi,dakuma yadda yake saurin dariya akan lamura,ko ita data shahara wajen makara a sallah,dai duk lattinta takan dan damu taji ba dadi amma shi hankalishi kwance babu wani damuwa atattare dashi,ikon Allah,gashi dai ko ajikinshi,kuma wai ita zai maida yar iska ma kenan wato bata ma san metake ba dazai wani ce wai shi farin shiga ne mtsw,yamaci uwar rainin hankali wannan zancen farin shigan yana bata bakinciki,idan yafada kamar ta shako shi takeji"tsakin datayi a zuciyarta ne ya fito fili,"ya daga na fada miki magana kike min tsaki kuma laifin me nayi?"fuskarshi dauke da damuwa yayi maganar,"tsaki kuma?bada kai nake ba ai"ta bashi ansa batareda ta kalleshi ba,"to gwara dai don ni dakika ganni nan,babu abinda na tsana duk duniya kamar tsaki wallahi ki kiyaye daAllh ""toh"kawai tace don ya isheta da zance.
"Yunwa nakeji wallahi tun dazu kai nake jira katashi"tace cikin salon shagwaba har tana rike ciki,bai bata ansa ba saima washe baki dayafara yana nufota tareda cire jallabiyarshi,"nasan irin yunwar dakike ji,na je gano,yanzu kuwa zan kosar dake"yace bayan ya wurgar da rigar,yana kara nufota,hakan ne yasata fara ja da baya tana zaro idanu,tasan tanada jarraba ta wannan fannin itama amma wannan bawan Allahn da alamun ya damata ya shanye,gashi don ya rainata wai zai ce mata shi farinshiga ne,"yanzu fa muka tashi don Allah don Annabi kabarni na huta haka kuma wallahi dagaske nake yunwa nakeji lokacin breakfast dina ya dade da wucewa"tace kamar zatayi kuka, "wane irin hutu kuma amarsu,haba amarsu ta ango,wannan ai shine babban hutu mu agaremu yanzu,damace fa tasamu abinda ake nema"yacigaba da washe baki,"ai kin zama mallakina,haba kekuwa,kar fa ki kasance irin matan nan da malaiku suke tsinewa mana,ta...."don Allah don Annabi k....."ai bata kai Aya ba ya hankadata kan tsadadden gadon nata,ganin tana neman bata mishi lokaci,shikuwa ta wannan fannin bashida hakuri ko kadan,bai sarara mata ba kuwa duk tureshin data dingayi,tana koke koke,saida ya tabbata yasamu nutsuwa tukun sannan ya rabu da ita yashiga maida numfashi kamar wanda yasha gudun fanfalaki,"wanan wace irin masifa ce wai?abin nashi yazama son kai da rashin mutumci ma kenan,to agaskiya bazan iya ba,wannan iskancin haukan badani ba"tace aranta,tana kuka afili,ko kallonta baiyi ba bare ya rarrasheta yasake mirginawa,ganin hakan ne yasata sake fashewa dawani matsanancin kukan bakinciki,jin yafara minsharin nashine yasata share hawayenta a fusace ta mike ta zura rigarta "wallahi kayi kadan ni zaka maida yariska?"ta daka mishi wani mugun duka,ga hannunta mai zafi dama,andade ana gaya mata,a zabure ya farka don jin dukan yayi babu zato babu tsammani,gashi ya shigeshi,dama ba riga,"ka isa kayi barci donka rainamin hankali?kanaji ina kuka bazama ka iya rarrashina ba kabani hakuri don iskanci shine zaka min banza kafara bacci wato nizama ka maida yariska kenan?ko kuwa ni baiwarka ce dazaka zaka dinga raping duk sanda kakeso?to wallahi bazan dauki wannan dabbancin da wulakancin ba kayi kadan,ko kuwa dama don haka ka aureni?""ni kika sa hannu kika daka saboda na karbi hakkina?haba fareeda bafa zina nayi dake ba karki manta ke matata ce ta sunnah"yace cikin tattausar murya,"bayan ya tashi zaune,"nasan ba zina kayi ba,to don meyasa zaka dinga min dole,kawai don ka biya bukatarka,ai abin yazama son kai ma kenan meyasa bazaka iya hakuri ba idan nace banaso?"tace cikin kuka,tasowa yayi zai rikota tayi saurin ja baya,"don Allah baby kiyi hakuri wal....."karka kuskura"ta daga mishi hannu alamun ya dakata,",wannan abin shi kayi jiya,gashi yanzu kasake maimaitawa bayan jiyan ma cewa kayi bazaka sake ba h...."kiyi hakuri don Allah wallahi baason raina ban....""wallahi bari kaji"ta katseshi,"bawai don kaganni haka ba kazata kanwar lasa ce ni,banida mutumci,baamin aci bulus,wallahi kabi ahankali,banida hakuri,idan ka kuskura kace zaka sake gwadamin haukanka wallahi tallahi saika sakeni don bazan cigaba da zama d....."saki kuma?"ya katseta cikeda mamaki tareda zaro idanu jiya fa aka daura mana aure,amma kike zancen rabuwa?haba kekuwa,ya kike zance kamar ba auren soyayya mukayi ba,nazata auren mu mutu ka raba ne?"wata muguwar harara ta zabga mishi kamar idanunta zasu fado,"a hakan zamu zauna mutu karaba,kana neman hallakani?nace ahaka zamu zauna cikin rayuwa irin ta dabbobi?"ta hayayyako,"kiyi hakuri wallahi zan gyara nayadda nayi kuskure,kin riga kinzama rabin raina jinin dake kwarara ajijiyoyin jikina,iskar danake shaka,atakaice dai kin zama rayuwata dabazan iya komai ba saida ke,kidaina zancen saki mana babu kyau"Yace bayan yayi nasarar rungumeta"kiyi hakuri nayi alqawarin bazan sake ba ki yafemin,hakan kwata kwata ba halina bane wallahi nima bansan ya akayi ba,ina matukar sonki"yayi kissing goshinta,"shikenan ya wuce amma ka kiyaye gaba","zan kiyaye,yanzu dai muje inbaki abinci don nasan harda yunwa a sanadin fushin da bacin ran"ya kyalkyala dariya,itama yar dariyar tayi suka fice tare suka nufi kitchen.
A cen kasar Ingila kuwa,su yusuf ana cen an tare a birnin landan.
Bayan sun dan huta,nawasu yan kwanaki,yafara abinda yakaishi,sannan yafara hidimar nemawa Abu addmission,a university of london,baa wani bata lokaci ba,kuwa sukayi admitting dinta saboda tanada duk wasu requirements dasuke da bukata,saida suka zauna da yusuf kafin azabi course din dazatayi tunda batasan metakeso ba ko meya dace da ita,ahankali yamata bayanin komai yadda zata fahimta sannan yabata list din science courses din dasukeyi a makarantar yace tadinga googling tana gani har ta zabi wanda takeso,idan tazaba tafada mishi sai yagani idan yayi.
Hakan kuwa akayi,don duk courses din data dubo babu wanda yafi kwanta mata kamar medicine,don tasha burin ganin tazama likita wata rana,amma kodata fadawa yusuf shawara yabata akan ta hakura dashi indai har tanaso tayi rayuwar aure mai dadi tadinga samin lokacin zama da iyalinta,don duk macen datazabi medicine shikenan kuma ita,shikuma rayuwarshi tazama wani abu na daban,na daya dai shekarun karatun sunyi yawa,na biyu abubuwa ne zasuzo su mata yawa tarasa inda zata saka kanta saboda ba karatu bane na wasa sai wanda ya shirya,na uku zatazo tagama ta dawo nigeria tayi licesing exam(MDCN)wanda idan bataci ba tofa zama zatayitayi agida bata komai har sai sanda taci,karatun zai iya zama babu amfani ma kenan,kuma dazarar tafara aiki shikenan zasu shiga wani hali saboda zata kasance batada lokacinsu sai lokacin aikinta kuma idan haka tafaru matsala zata iya faruwa,ai wayannan dalilan su suka saka Abu sarewa,taji abin yafitar mata daga rai kwata kwata,don wannan ba fanninta bane,ita maison kyautatawa miji,lura da yusuf yayi tanason karantar abinda yashafi fannin lafiya ne yasa yace tasaka Health science tunda kobakomai shi shekaru uku ne zuwa hudu,wanda hakan yayi daidai bashida wani matsala da lokacin,kuma idan tanason aiki zatayi batareda abin ya shafesu ba sun shiga kunci.
Haka kuwa akayi,online yatayata sukayi registeration sannan ya rakata suka dan karasa dan abinda baa rasa ba.
Abindai gwanin ban shaawa,haka aka fara zuwa makaranta kullum saiya rakata wai don karta bata,sannan idan tagama yadawo ya dauketa,tunda shi yawanci da daddare yake nashi karatun,ahankali har tazo ta saba tagane hanya ta iya zuwa dakanta,kullum cikin Abaya take abinta,Amin kuma dama yana gida da yusuf,duk ranar dasukeda lecture dukansu kuma akaishi daycare,rayuwar tasu dai gwanin ban shaawa.
Assalam Alaikum,zuwaga makaranta wannan rubutu mai dinbin albarka anan nakawo karshen part one na RUWAN DAFA KAI,saura part 2 inshallah,nagode da goyon bayanku agareni akoda yaushe, da kuma kaunar dakuke nunamin,Allah yasa mudace baki daya,Abinda narubuta daidai kuma mai amfani Allah ya bamu lada dani daku,wanda kuma nayi kuskure ina rokon Allah daya yafemana baki daya Nagode taku a Kullum ❤️
Dr.Sumayya Danzabuwa
You are reading the story above: TeenFic.Net