RUWAN DAFA KAI

Background color
Font
Font size
Line height

RUWAN DAFA KAI 141~145
Na SUMAYYA DANZABUWA

Suna zaune bayan sallar ishai,Ya kira Hajiya donsu gaisa,bayan sungaisa dinne take shaida mishi cewar fa ga dansu nan yatadawa jamaar gida hankali tun dazu yake rigima,da har zata sa akawoshi dazun to kuma sai yayi barci,yar dariya yayi,"to ai yamayi kokari Hajiya,don tun jiya ma ni nake sa ran kiran naku ai,bakomai idan Allah yakaimu gobe inshaalah zamuzo sai mu tafi dashi"yace yana yar dariya,haka dai suka cigaba da taba hira inda Hajiyar tadinga jaddada mishi hakuri da kai zuciya nesa azauna lafiya kar taji karta gani,itama Abun baa barta a baya ba don saida Hajiya tace abata wayar itama don mata tata nasihar.

"Kinaji fa danki yanacen ya tubure"yace bayan ya kashe wayar,yar dariya kawai tayi,don batasan mezatace ba,tunda dama itama a kage take ta ganshi don ba yadda zatayi ne kawai,bataso tayi magana aga rashin kunyarta ko rashin kara amma dan kwanakin nan datayi bata ganshi ba Allah kadai yasan halinda ta shiga ita ba abin tace akawoshi ba ko aje a dauko mata shi,tunda dole da nauyi wajen Hajiya yake,kuma ma zaa iya cewa ta zake shiyasa tayi shiru ta hakura har sai sanda aka dawo dashi din ko shi yusuf din ya daukoshi,tunda ita Hajiya gata tamusu saboda su samu su sake shiyasa tace abarmata shi acen.
Cigaba sukayi da kallo, abinsu cikeda so da kauna suna dan taba hira kafin daga bisani su tafi bacci.

Abubuwa dai nata tafiya yadda farida takeso,don a halin daake ciki ma Su Abdallah har sun kawo kudin aure an saka rana nan da wata biyu dukda dai taso taga wata biyun kamar shekara biyu,taso tayi magana sai dai tabawa zuciyarta hakuri tadaure kar yace tafiya mita ya fasa.
Kuma yace ba lefe,shima bidia ne amma yayi alkawarin idan ya aureta sutura sai irin wadda takeso.

Tabbas farin cikin datake ciki bazai misaltu ba wane aurenta na fari,?tunda lokacin aurensu da yusuf zuciyarta bata kai haka lalacewa ba kuma batada wata mummunar niyar bakantawa wasu amma yanzu inaa abubuwan sun chanja sun shallake hankali tazama tantiriyar mai bakin hali,kafin kuce kwabo tafara duk wasu gyare gyare da shirye shirye irin na amare,Abba kuma yayi order kayan daki da sauran tarkace gida wayanda ta zaba kamar dai wancen lokacin(aurensu da yusuf).
"Yanzu shikenan saboda baason gaskiya daga haduwarki da mutum sai a saka rana?shin hakan ya dace?har yaushe ma kuka gama sanin juna?ke bakya ganin wani laifi a tattare da abin ida shi (Abban)ya biye miki ne don ya faranta miki?wannan wace irin rayuwace kuka zabarwa kanku?"cewar mama cikin wata murya mai dauke da tsantsan nasiha"mama ni so nake kicire duk wasu tunanika daga ranki donAllah,kiyi fatan alkhairi kawai,wallahi Abdallan nan dakike gani mutumin kirki ne,don dai baki zauna das....."duk kirkinshi shikenan k......"wayyo Allah na,"ta katse manan,"wai meyasa duk abinda nakeso shi kike tsana?nifa yanzu ba kamar da bane mama ni bazawarace nafa taba auren nan nasan yadda abubuwa suke,na girma,idanuna sun riga sun bude shiyasa ma nasan wane irin miji ne yadace dani don Allah kibar irin wannan zancen"tace cikeda kaguwa don ta gaji dajin wannan nasihar kullum abu daya,"ni bawani abu nace ba,rayuwa tariga ta chanja mutane babu wanda zaka yarda dashi rashin gaskiya y......"kasa kai aya maman tayi sakamakon matsanancin kukan karyan da faridan ta fashe dashi"to Allah ya sawwake,kije kiyi duk abinda kikeso"ta tashi ta barta.
"Hmm wai wannan wane irin zancene da maman nan zata wani matsanta sai an zurfafa bincike? wayake wannan a zamaninan?tab"ta tabe baki" gashinan yanzu da baa matsa ba anyi abinda zaayi amma da ance zaa biye ta tata datuni baa kaiga haka ba,irin wannan ne ma zaa takura ayita bin kwakwafi har mutum yaga takurar tayi yawa ya gudu nikuwa bawannan nake fata ba atoh "tayi zancenta afili,tareda daukan waya takira rabin ran nata,abin mamaki tunda aka saka musu ranar daga ta kira yake dauka yadaina jan ajin hakan ma ba karamin dadi ya mata ba.

Tun bayan Dawowar Amin yusuf yaso ya daukowa Abu mai aiki koda dattijuwa ce tunda har wajen ajiye maiaikin ya tanada just in case,amma taki kememe,saboda aganinta idan ta yarda da hakan kamar zata kasance mace mara godiyar Allah ne ita kam metake nema yanzu a rayuwarta?duk wani rufin asiri da gata Allah ya bata to mezatayi dawata mai aiki,wacece ita?tayi ma ada wanda bai zama wajibinta ba bare yanzu dazata samu lada?kuma ma da yaushe tagama yiwa wasu dazaace itama zaa kawo mata,babu yadda baiyi da ita ba akan ta manta da baya komai ya wuce amma kememe taki,harda kuka,dole ya hakura ya kyaleta don tace babu abinda zai gagareta a gidan zata iya komai kula dai da Amin dama tasaba ai.

Haka rayuwa tacigaba da gudana abin nasu abin shaawa,tanata kara kilewa,yusuf na koya mata soyayya,don gashi cikin wata daya ta murmure ta kara kyau,kamar ba ita ba,anata rayuwar aure mai dadi yusuf anata kiba,ansamu abinda akeso Bash yana mishi iskanci.
Bayan biki da sati Biyu kuwa ya kawo Amina,koda suka hadu da Abu take jininsu ya hadu kwarai da gaske,cikin kankanin lokaci suka saba suka zama aminai kullum cikin chatting ko waya kuma Aminar na kara wayar mata da kai tana koya mata abubuwan dabata sani ba,amfanin kawaye na gari kenan,itama kuma Amina ta nata bangaren tabbas tanajin dadin kawancen nasu don akwaita da son mutane kuma rabonda tasu tazo daya dawata ma ita tamanta amma gashi sun hadu da Abu yarinya mai nutsuwa da mutumci,duk wanda zaizo gidan ya tafi saiya bada kyakkyawar shaida akanta ance yusuf yayi dacen mace.
Haka sauran yanuwa da matan abokananshi idan sukazo tayita nan nan dasu da yayansu don indai mutumci ne da karrama jamaa ba baya ba,wanda hakan ba karamin birgesu yake ba gata dai yarinya karama amma akwai sanin ya kamata abinda farida bata iyaba takuma kasa koya,irin wayannan kanana kananan
abubuwan ne suke kara saka mishi kaunar ta azuciyarshi a kullum saboda kara kasancewa take irin macen dayake buri yake muradi,shidai kam ahallin daake ciki babu abinda yake sai hamdala ga Rabbussamawati,don duk yadda yake mafarkin rayuwar aurenshi hakace ke faruwa ashedai komai lokacine sai yanzu yasan yayi aure.

Su farida kuma ana cen shirye shiryen biki sunyi zurfi,tanata rawar kai da rashin mutumci musamman ga safina,tun tana biye mata hartayi banza da ita.
Taso ayi bidioi kala kala,don yazama dole tanunawa wayanda takeson bakantawa cewar aure fa zatayi auren soyayya bawai takura mata akayi ba,aa aurene cikeda farinciki amma Abdallah yace bayason bidiah,don akoda yaushe yazo wajenta hira rabin zancen shi Allah yace ne Annabi yace,hakan ne yake kara tabbatar mata da irin rikonshi da addini,dukda dai ita tasan sai ahankali.
Ganin cewar fa aurenshi ne na fari yasa taso tadan gamsar dashi,wajen ganin an gudanar da bidiar,amma saboda karta sauya irin kallon dayake mata na mai nutsuwa da hankali,yasa ta hakura saboda batason abinda zai bata mishi rai,batason kuma tsawalawa bare har yakaiga cewar batada kunya tana ja da umarninshi,tunda dai Allah yasani tayi iyaka bakin kokarinta tun haduwarsu wajen ganin ta boye munanan halayayenta shiyasa duk abinda yace bata musawa saidai tace eh kawai ko toh,shikuma hakan kara birgeshi yake yana kara tabbatar da tsananin nutsuwarta da tarbiyya.

Wayannan dalilan ne yasa bata wani damu ba ko ajikinta,tunda yace shidai adaura aure kawai akawo mishi amaryarshi shikenan ya wadatar haka addini yace auren ma zaifi albarka.
"Dama Meyasa ma zan damu kaina badai na tabayin bidioin ba?ai nayi a aurena na fari ni ba wannan bane damuwata ,wayasan nawa zanyi nangaba(auren)?indai ga anyi wannan din yanzu,wayanda kuma suke tunanin shikenan sunci bilis suncimin mutumci sun gama dani sai susha mamaki mtsw.

Tun ana sauran sati biyu daurin aure tadinga posting katin daurin auren aduk accounts dinta na social media duk inda tasan dole yusuf kowani nashi yagani akai mai rahoto,
A watsapp kuwa kusan kullum sai tasaka,don tayi unblocking duk wayanda tayi blocking da(yusuf da yanuwanshi) don dai sugani koda shi din baigani ba yasamu labari dai.
Haka kuwa akayi yana zaune,suna hira da Abu sai ga sako daga farida a watsaapp shi saboda ma bashida lokacinta ma ko blocking din nata ma baiyi ba,don shi irin mutanen nanne dabasu iya fushi ba,tariga takaishi bango hakurinshi ya kare akanta,shiyasa yagama da ita,bashida lokacinta,idan ya raina kasuwa ko sautu baya badawa,itace dai taketa aikin wahala,tana batawa kanta lokaci.

"ikon Allah duba kigani"ya mikawa Abu wadda kanta ke kan cinyarshi wayar,don gyangyadi ma take,Amin yadade dayin bacci shima,dan goge idanunta tayi ta karba cikeda nutsuwa,ta fara karantawa tadaiga sunan amaryar farida amma batama gane wacce faridan bace,"waye zaiyi aure?"tace cikeda rashin fahimta,"Farida ce yanzu ta turomin"yayi dan murmushi,"oh Allah sarki ashe kuna gaisawa har yanzu"tamika mishi wayar,"aa wallahi bawani gaisawa,neman magana ne kawai irin nata, ni nasan halinta ai wai da gayya ta turo don dai insani zatayi aure tunda nima nayi ita atunaninta ai wai ramuwa ce wannan kuma competition ake"ya kyalkyale da dariya,cikeda mamakin wauta irin tata da tsananin hauka,itama Abun yar dariyar tayi cikeda mamakin karfin hali irin na farida dakuma haukanta,to don zakiyi aure meye na turowa tsohon mijinki kati?,"nidai nasan wannan dai abin ba gayyata bace tunda tasan dai ko me zaayi ai bazuwa zanyi ba niba mahaukaci ba bakomai ba"ya kara,"Allah sarki Allah yasa ta gane gaskiya to"cewar Abu","Amin Amin matata,"yayi deleting hoton sannan yayi blocking dinta.

Koda ta duba watsapp din gani tayi anga sakon nata amma babu wani reply,"oho dai kanka akeji,dan bakin ciki,dama ba turawa nayi da cin burin ganin ansa ba na tura ne saboda mutum ya shaida eh ehe yan bakin ciki su mutu,nasamu wanda yafika komai,shashasha"taja tsaki,"wai meyasa ma takejin haushinshi ne?shi waye?mtsw wanda ya fifita maiaiki akanki har wani abin damuwa ne?Ai kawai kicigaba da ja mishi Allah ya isa kullu yaum"wata zuciyar tace da ita,hakan ne yasata janyo wayar ta fara tura sakon cin mutumci don zuciyarta har wani zafi take,saidai kuma me tana sending sai taga baya tafiya alamun fa anyi blocking dinta haka ne yasa ta kunduma wata uwar ashar,"lallai ma wannan ni zaka rainawa hankali?to wallahi inkasan wata bakasan wata ba"ta fara rubuta sakon text message "bakasanni bane har yanzu nafika duniyanci wallahi duk wanda yaci tuwo dani miya yasha"na tabbata kaga sakona,to burina yacika,idan kayi tunanin zan zauna ne inyi kwantai don na rabu dakai to kuwa kayi babban kuskure don kasan nafi karfin haka wallahi,nasamu wanda yafika komai,baka isa ka hada kafada dashi ba,masoyi na tsakani da Allah ba munafuki ba irinka Azzalumi shashasha wallahi kayi asara shege,"ta tura mishi,karar shigowar sakon da Abu tajine yasata mika mishi wayar sakamakon game datakeyi,"duba kigani waye"toh tace ta duba sai taga babu suna,"babu suna"tace"bude ki karanto"don yariga yasha jinin jikinshi yasan irin rashin hankalin farida,koda ta bude gani tayi kalaman sun mata girma gashi harda zagi aciki agaskiya bazata iya karantowa ba,"kayi hakuri bazan iya karantawa ba"tace tareda mika mishi wayar,karba yayi ya duba yaga shashancin data turo yaja dan karamin tsaki,"Allah ya kyauta yakuma shiryeta,mai hali baya fasa halinshi wanan halayyar dai duk inda zata da ita bazata taba zama lafiya da mutane ba"yace bayan yayi deleting text din yayi blocking numbar suka cigaba da hira abinsu suna soyayya.

Rana bata karya,Ayau aka daura auren Farida da angonta Abdallah daurin auren daya samu halattar yan tsararin mutanen,kunsan auren bazawara sai godiya.
A masallacin unguwarsu aka daura bayan sallar jumuah don daurin auren ma saida Yaga Abba ya dage,don da cewa yayi basai anwaniyi taron mutane ba shi Allahn dayayi shi bayason taron jamaa shiyasa duk yake gujewa taron bikin,yan mutanen dasuka hallara ba laifi dasu aka shafa fatiha,dama jiya anje anyiwa amarya jere a katafaren gidanta abin sai wanda yagani.
Jira ake kawai ayi laasar ango yazo ya dauki amaryarshi don haka suka tsara,shi da ita,kiri kiri farida take tapka rashin mutumci tana rashin kunya,Abba na goya mata baya,daga anyi magana sai tace ita bazawara ce,dama mama bata fiya saka baki ba a lamuran yanzu ta zuba musu ido kawai suyi abinda sukeso,wai ita ce (faridan)ta tsara yadda zata tafi gidan mijin,ita tace batason rakiya anyi mata a aurenta na fari yanzu kam bata bukatar gulma,mijinta ne kawai zaizo ya dauketa.
Hakan kuwa akayi gab da maghriba yazo ya dauki matarshi tanata washe baki,suka kama hanya cikeda so da kaunar juna.

Ta bangaren su yusuf kuwa,wata  tafiya ce ta kamashi harkar kasuwancinshi zuwa uk,da baiyi niyyar zuwa ba to amma kuma ganin zai shafe wasu yan watanni kuma dama yanaso yayi PHD,hakan ne yasashi yanke shawarar tafiya da iyalinshi kawai,don satin daya gabata ma aka fara saida form din jarabawar jamb har ga siyowa Abu ma tacike,to amma tunda ga tafiya ta tashi,yana ganin gwara kawai su tattara su tafi ko da course din shekara uku ne zuwa hudu tayi tunda A halin daake ciki Allah ya rufa mishi asiri babu abinda zai gagara.

Babu bata lokaci aka fara shirye shiryen tafiya,tunda dama taci WAEC,dinta don ba laifi mutuniyar akwai kokari,ana sauran sati daya zasu tafi yakaita cen gumel din wajensu gwaggo tadan musu kwana biyu na sallama.
Abu dai tazama kamar wata halitta ta daban,don har saida suka rufe gida da tsakar rana sakamakon matan gari dasuke ta tuttudowa ganinta,wai ance tayi kiba tayi fari,abin sai wanda yagani.
A gaskiya kullum yusuf kara bata mamaki yake,yana kara saka soyayyarshi acikin zuciyarta,zuwan nan datayi gida taga abubuwa dayawa sun chanja,ba kamar da ba,tasan dai kawai sau dayawa idan sunyi waya dasu baban suna cewa tayiwa yusuf godiya yanata dawainiya dasu,ashe aika musu da kayan abinci da kudade yakeyi akai akai baji bagani ita batama sani ba Allah sarki masoyin kwarai kenan,gaskiya batajin akwai namiji irin yusuf aduniya,kullum kara godewa Allah take da wannan baiwa.

Kwanansu biyu da dawowa sukaje yiwa Hajiya sallama itama da su bash da sauran abokanan arziki,washegari kuma jirginsu ya daga zuwa kasar ingila.

A hanya ya tsaya ya sai musu kaza,da dan kayan ciye ciye irin dai na amarya da ango sannan suka karasa gida.
Koda suka karaso gate din katafaren gidan nasu tsayawa sukayi Abdallan yagaisa da maigadin sannan taga ya mika mishi kudi,suka shiga.
"Yacemin zai sai wani abune ahiyasa"ya tari numfashinta ganin tana shirin tambayar dalilin bada kudin dayayi,"oh Allah sarki"tayi dan murmushi cikeda jin dadin yadda yakeda kyautatawa.

Suna shiga a palo suka baje,suka fara ciye ciyensu kamar yan yunwa,don da alamu ma yafita jin yunwar yadda taga yafarwa komai,saida suka koshi sukayi nak,sannan suka tashi don gudanar da sallar magahriba, lokacin har an fara kiran isha ma hakanne yasasu hadewa harda ishar.
Dama shi yamusu limanci,yana sallamewa ya juyo ya jawota yafara shafata yana kokarin rabata da kayan jikinta,"Darling a palor fa muke"tace dakyar,ganin yadda yake shirin gudanar da abubuwa a hargitse ko duk farin shigancin ne haka oho?banza yayi da ita yacigaba da abinda yake,"baby mutafi daki kaga fa a kasa mu..."nasani ai anan nakeso"yabata ansar kai tsaye hakan ne yasata sandarewa cikeda mamaki ta tsaya kallonshi,"lallai wannan a matse yake"tace a zuciyarta,ai bai sarara mata ba saida ya tabbata yasamu nutsuwa ga mamakinta wanda yace bai taba aure ba shine ya iya gudanar da abubuwa haka salo salo cikeda kwarewa?ko ita matar auren wasu abubuwan dayadinga aikatawa bata taba sani ba?to ko dai dama ya saba harkokinshi da sauran mata auren ne dai bai taba yi ba?gaskiya kanta ya daure,"to ke meye na damun kanki da wannan,ke din a budurwa ya aureki?kemafa ragowar wanice karki manta,kuma dama mazan yanzu ai daidai ne zakiga sun girma ba aure basa neman mata sai dai kuma masu tsananin tsoron Allah amma yadda naiman matan nan yayi yawa ai sai godiya kawai"aah!!!gani tayi anata gudanar da lamari babu kakkautawa ana neman awa kusan nawa,sai rokonshi take ya kyaleta haka tagaji amma inaaa,kamar kara zugashi take,ganin dai bazai sarara mata bane yasa ta fashe dawani matsanancin kuka,"wai wannan wace irin jarraba ce?"tace cikin kuka,"jarraba?hakkin nawa ne jarraba?in biya sadakinki ki karbe kice ina jarraba?"ya bata ansa a hasale batareda yabar abinda yake ba,"ka kyaleni to nace banaso nagaji dolene,?"tace cikin tsiwarta,saurin shiru tayi hade da mutuwar jiki data sameta sakamakon wani mari daya sharara mata.

Saida yagama abinda yake don kanshi sannan ya kyaleta,ganin bata bar zubda hawaye ba har lokacin ne yasa yafara rarrashinta cikeda tausayinta, duba da yadda ya wahalar da ita,ga kuka datake kamar ranta zai fita,ita bakin cikinta ma bawai marin ba,sai na ga gadonta na miliyoyi da babanta ya sai mata amma wai ace ta kwana da miji a kasa,wane irin abune wannan?,wannan shine babban bakin cikinta,yadda yadinga lallabata yana cewa ta yafe mishi yayi kuskure ne yasa zuciyarta karaya dole ta hakura don yace mata kasa hakuri yayi yana mutuwar sonta ne shiyasa yakasa kyaleta,kuma wannan abu ne daya dade yana burin yasamu shiyasa,duk abinda ya aikta ba laifinshi bane sharrin zuciya ne ta yafe mishi,"ya kai ayar zancen harda sheshekar kuka,saboda tsananin tausayinta da jin haushin kanshi dayayi,"bakomai na yafe maka"cewarta,tana mai share mishi hawaye,hakanne yasashi jin dadi ya dauketa cak yayi dakin da ita ya direta kan tsadadden gadon da baban nata yasai mata cikeda kaunarta.
Neman gefenta yayi yaja pillow,yakwanta ko minti biyar baayi ba,tayi magana taji shiru,sai ji tayi yana gurnanin minshari abin tsoro,(tunda suke da yusuf bata taba jin yayi minshari ba,ko kuma ya kwanta bacci da janaba,ke meye ne na hadashi da wancen mara mutumcin,mtsw aikin banza ai dai kowa da yanda yake)tace aranta.

Dakyar ta tashi tashiga bathroom ta gyara kanta,tayo wanka tafito,tanemi gefen gadon ta kwanta itama,saboda tsabanin gajiya,sai lokacin sallar da maaurata sukeyi a daren farko ta fado mata,sun manta basuyi ba,koda yake Haka Allah ya tsara"cewarta,tunane tunane tadingayi kala kala kafin bacci yayi awon gaba da ita.

😍😍I LOV U ALL,keep voting,commenting,and follow me,if u r not following already,🏃🏽‍♀️SHUKRAN

You are reading the story above: TeenFic.Net