RUWAN DAFA KAI 126~130
Na SUMAYYA DANZABUWA
Koda suka shiga basu zame ko ina ba sai dining table,inda aka shishirya abinciccikan da Hajiya tasa a aiko musu,tabbas dayawa dukda dai su Gwaggo ma sunci.
zaunar da ita yayi kan daya daga cikin kujerun, dinnig table din,sannan yashiga kitchen ya dauko musu plate,abinciccika ne kala kala kowanne da flask dinshi,tambayarta abinda zai zuba mata yafarayi bayan ya lissafo mata komai,ta girgiza kai alamun ta koshi,rabuwa yayi da ita yacigaba da zube zubenshi,ya hada mata tea,saida duk yagama sannan yaja kujerar dake kusa da ita yazauna yajuyo da ita yadda suke fuskantar juna har lokacin batabar hawayen ba "kiyi hakuri kibar kukan nan haka kinji muci Abinci don nasan yunwa kikeji"yace bayan yadebo soup din naman a cokali zai kai mata baki,kallonshi tayi taga yadda yayi narai narai da ido saikuma suk yabata tausayi itama,haka ta bude bakin yadinga ciyar da ita don batason tayi mishi musu,"kai bazaka ci ba"tace dakyar ganin sai bata yake shi baya ci,"zanci amma nafiso yar amaryata tafara koshi tukun"yadda yayi maganar ne yasata dan murmusawa,"ko kefa gashi dakikayi dariya harkin kara kyau"yace cikeda zolaya itadai shiru tayi saida takoshi tukunna ya dakata sannan yace tazuba mishi nashi,ba musu ta tashi ta zuba ta ajiye mishi ya bita da kallo,"like seriously?"kallonshi tafara cikeda rashin fahimta,"banganeba"tace cikin sassanyat muryarta,"hmm dole kiki ganewa ai tunda kinci kin koshi,wato ni ba dangatanki bane kenan,"sunkuyi dakai tayi don tagane abinda yake nufi,"shikenan dama baso kike inci ba indai hakane"cikin sanda ta dauki cokalin tana debowa kamar mara jini ajiki,"hmmm ina jira fa"yasake cewa tareda nade hannunshi a kirjinshi donma wai tasan cewar fa bashida niyar ci din dakanshi don ya fuskanci dasauranta sosai dole ya dorata akan hanya shi dan soyayya ne,ita kuma komai kunya yake bata amma dai ahankali zaisan yadda zaisata tadinga sakin jiki dashi,yar dariya tayi cikeda jin kunya sannan tafara bashin cikeda nutsuwa,yanata janta da hira wai don duk ta wartsake don baya kaunar ganinta cikin damuwa,saida yakoshi shima sannan ta dakata,tareda tashi don fara gyara wajen saboda bata kaunar ganin waje a hargitse kwata kwata,riko hannunta yayi,hakan ne yasa ta juyo takalleshi,"wai gyarawa zanyi naga duk m..."bakyson hutu baby na kefa amaryace ko kina mantawa da alqawarin dana miki nacewar zan shagwabaki? dagaske nake fa,kiyi zamanki ki huta ni zan gyara tunda nima ai na iya yafara hada kan kwanukan,"da dai k..."saifa na gyara komai duk abinki naki wayon kije ki zauna ki huta"yamata nuni da kukerun dake palon dama tv a kunne take,ganindai da gaske yake bazai barta tayi aikin bane yasata hakura ta nufi kujerar ta zauna,juyowa tayi tasake kallonshi ya mata gwalo hakan ne yasata yar dariya,remote tadauka tafara chanja channel tana neman abin kallo don tanason kallo abinta,"kai anya kuwa abinda tayi yakamata?ace tabar mijinta da gyare gyare shi kadai ai aikinta ne,ita datake fatan kasancewa mace tagari"wata zuciyar tace da ita,hakan ne yasata binshi kitchen din da ragowar kwanukan dazai dawo ya dauka,"ni ban taba ganin mutum mai gudun hutu d....."aa wallahi"ta tari numfashinhi tun kafin ya karasa"zan tayaka,sai muyi tare"tace bayan ta ajiye kwanukan cikin sink din,"dats my baby inye ashe dai yarinyar badaga nan ba,irin soyayyar nan,irin dinnan,haka akeso"yace cikeda sonta yacigaba da tsokanarta don yusuf mutum ne mai son wasa da tsokana amma farida dole tasashi yazama wani iri don batason duk abinda yayi da wasa ganinshi take gaske ita ta chanja maana dole ya hakura,don bakomai yake gaya mata ba saboda azauna lafiya shes too serious.
Haka kuwa akayi yana wankewa tana kifewa tana goge wajen ana yar hita,harsuka gama suka fito,inda aka ajiye mata kayan turare ta nufa ta dauko coal tashiga ta kunno tasako a wata hadaddiyar burner ta turaren wuta,hakan ne yasa yusuf jin dadi don tabbas Abu itace abokiyar rayuwarshi saboda abubuwansu dayawa sunzo daya,zama sukayi 3 seater suka fara kallon wani American movie the equallizer,ganin tadan takure gefe ne yasa shi janyota jikinshi ya kankameta,tayi luf abinta.
Masu karatu lamarin farida fa yazama abin mamaki duk inda tasan sun taba haduwa da mayenta take bi wai ko zata samu wanda yasanshi ko inda zata sameshi don wallahi ita yanzu shi kawai takeso dukda dai bata wani ji irin muguwar soyayyar nan tashi aranta ba amma dai koba komai yanada kyau yanada tsaho kuma daga ganinshi mai kudine haka takeson namiji yakasance,shiyasa zuwan yusuf wajenta karon farko ta aminta dashi saboda duk qualities din datake bukata a namiji,yana dasu.
Duk inda taje ta tambaya sai suce tun daga ranar su basu kara ganinshi ba,wasu ma suce su basa tunashi,hakan ne yasa tafara karaya tafara saddaqarwa amma idan ta tuno bakin cikin da yusuf ya jefata na auren Abu dayayi sai taji fa kai dole ta tashi haikan don bazata bari yaci bilis ba dolene ta nuna mishi idan yakita akwai masu sonta.
Baki ne yanuwa da abokan arziki sukayita bullowa don ganin amarya,wasu dayawa daga cikinsu masu zuwa gidan gulma ke kawosu,don sun shaidata sun gano itace wannan mai aikin wasu ma dama don su tabbatar da abinda ake fada ne don dayawa daga mutane gani suke abune dabazai taba yiwuwa ba ace wai namiji kamar yusuf ya auri maiaikinshi to ya zaayi duk lamari dai irin na mutane ikon Allah yafi ga haka duk yadda Allah yaso haka zaayi duk wanda yazo da wannan niyyar ma yatadawa yusuf zancen bayako bada fuska saima gargadi dayakeyi akan duk wanda yasan zai dinga zuwa badon Allah ba to yabar ziyarar angode,don bayason abinda zaazo a samu matsala,ya tsani gulma,kananan maganganu da tsugudidi.
Allah yaso ma dai duk masu zantukan ba agaban Abun sukeyi ba da an shiga uku yadda take da kukan nan abu kadan sai kuka duk tabi ta tada hankalinta tashiga damuwa,gashi kafin a rarrasheta ma aikine.
Wankan dare tayi kamar yadda tasaba tasaka yar doguwar rigar baccinta tayi yan shafe shafen turarrukanta sannan tayi isha tafara shirin bacci,saida ta kammala komai sannan ta kashe fitila abinta tabi lafiyar gado.
Da sallamarshi yashigo dakin yaji shiru,ga duhu,wayrashi ya zaro daga aljihu ya kunna flashlight,ya fara haske haske,koda ya hasko gadon hango ta yayi a dukunkune cikin bargo,hakan ne yasashi karasawa tareda bude fuskarta,yafara kallonta,daga dukkanin alamu ta dade da fara baccin,tashinta yafarayi dukda baiso hakan ba amma kuma bataci abinci ba ai,a hankali tafara bude idanunta,"baby daga inje salah in dawo shine zaki sheme haka,bakifa ci abinci ba maza tashi"yace tareda yaye bargon duka don yaga batada niyya,"nako...."nafa dade da fuskantar bakyason cin abinci to zan koya miki kuwa don bazai yiwuba kiyita rama Haka kawai dama gakinan jiki ba jiki ba"yace bayan ya kunna dukkanin fitulun dakin gashi ta tsani haske idan tana bacci yanzunnan baccin zai gudu,hakan ne yasata tashi dole tana tafiya dakyar tashiga bandakin don wanko bakinta tunda ya dage.
Zaune ta taddashi gefen gado yana jiran fiowarta,"Gud girl to maza mu sauka muje muci abinci"yakamo hannunta suka sauka itadai binshi take kawai.
Wani abincin tagani daga gani baa dade da kawoshi ba,sannan ta zauna yafara zuba musu,"au kinga namanta da kazar ki fa ta jiya tana fridge inmiki warming mana"yace yana niyyar tashi,alamun bama ya bukatar jin ansarta don idan yace zai bi abina zatace cewa zatayi ta koshi,shigewa kitchen yayi tabishi da kallo,"wai wannan wane irin namiji ne ita kam soyayyar ai tayi yawa,komai ace sai an mata?"tacea ranta cikeda mamakinshi,baa jimaba kuwa ya fito dayake microwaving yayi ya sakosu a plate,"oya fara,aci dakyau"yatura mata plate din gabanta,"wallahi tallahi na koshi,kar cikina ya fashe"tace cikin wata irin murya data bashi dariya,"ke tunda kike kin tabajin wanda cikinshi ya fashe saboda cin abinci?babu abinda zai sameki kinada ni"yace bayan ya gutsuro naman ya nufi bakinta ya mata alamar ta bude yasa mata,hakika cikinta ya cika,amma daga wannan bazata iya kara cin komai ba kuma,ai sai tayi amai,"ci tadingayi dakyar"ya lura da hakan dole ya kyaleta gudun kada wani abin yazo yafaru ko cikinta ya baci,ko tasamu indigestion,shima dan tsatsakura yayi sannan suka tattare kan kayan kamar dai dazu dasafe sukaje suka wanke suka gyara komai,abindai gwanin ban shaawa.
Saida sukayi kallon kusan awa biyu wai don dai asamu abincin yadan sauka tunda bai kamata daga anci akwanta ba.
"Muje mu kwanta"saboda lura dayayi kawai daurewa take don Abu akwai baccin wuri,shiyasa take iya tashi sallar asubah,"toh"kawai tace"sukayi saman.
Suna shiga taje ta wanke bakinta tadan kimtsa,sannna tasake darewa gado,bai ce mata komai ba,shima yashiga yayi wanka da duk abinda yakamata yafito yanata kamshi ya kashe fitilar ya haye gadon,tareda jawota jikinshi,dama bata fara baccin ba tukunna,zuciyarta ce tafara dukan tara tara,duba da yadda taga yusuf yana abubuwa kuma abin yafara bata tsoro,shikuwa hankalinshi kwance yake gudanar da lamura cikeda kwarewa,atakaice dai bai sarara mata ba saida ya tabbata ya mallaketa tukun,tabbas Abu ta dabance don ta wannan fannin babu yadda zaayi ya hadata da farida,bawai yana nufin faridan ma baya samun nutsuwa da ita ba ne,aa,Kawai dai Abun ta dabance,bazai iya misaltata ba,tabbas duk hukuncin da Allah ya yanke shine daidai,na sakin farida yayi,he hav no regrets whatsoever,don da tana nan,baiga tayanda zaayi kuma yasake yin adalci ba tsakaninsu,don bazai iya ba,wato mata dai kawai a kallesu kowacce da irin baiwar da Allah yamata,mace zata iya kasancewa fara kyakkyawa kirar larabawa dabatada wata makusa tsananin kyau da diri amma ta fannin auratayya kuma sai ahankali,haka zalika mummunar bakar mace,wadda batada wani abin birgewa ajikinta Allah zai iya mata baiwar irin wannan niima shi kam babu abinda zaiyi sai godewa Allah dakara son matarshi.
Rarrashinta yafara sakamakon kukan datake amma inaa shima dai yasan sauran Abu ce fa dama kadan take jira,dole ya hakura da rarrashin yatashi yashiga wanka.
Saurin jan Bargon tayi ta rufe kanta,cikeda tsananin kunyarshi,don bata kaunar ma su sake hada ido wannan abu damai yayi kama,wai yau itace wani namiji yaganeta tsab,tanaji tana gani.
Koda ya fito jallabiyyarshi yasaka,ya zauna gefen gadon kusada ita yafara kiran sunanta ahankali kememe taki kulashi, tana ji tamishi shiru,hakan ne yasashi yaye bargon,tasa hannuwanta duka biyu ta rufe fuska ta rintse ido ita adole fa bazasu hada ido ba,gakuma jiki abude, yar dariya yayi,dubada irin wautarta da yarinta"cikeda kaunarta yafara magana"kunyata kuma kike?lallai kinada Abin mamaki wato fuskarki kike kunyar nagani banda jikinki ko"yace yana murmushi,shiru tayi don bataga ta yadda zaayi ta iya bada ansa ba,"tashi muje kiyi wanka,ko saina daukeki namiki dakaina tuku..."saurin girgiza kai tayi alamun aa,don tasan ba karamin aikinshi bane ya aikata,baydadda baiyi da ita ba taki,ganin dagaske zai dauketan ne yasa ta kwala ihu don wallahi ji take kamar ta nutse a kasa don kunya,"kibar ihun nan haka dare ne"yace yana dariya,tareda toshe mata baki,"to kabarni zanyi dakaina ai"to tashi kishiga ina gani,na zuba miki ruwa cikin bathtub kishiga ciki haka akeyi tunda bazaki yarda in kula dake ba,"ki tashi mana,yasake cewa,"naga dai sallah zakayi kayi sallarka zan shiga nace don Allah"tace cikeda shagwaba,"to"kawai yace yanufi kan daddumarshi ya tada sallar,ai tana gani ya tada din dagaske,ta jawo rigarta ta zura,ta mike dakyar tashiga bandakin.
Bayan ya idar ne,Yadan fara gyagyara gadon dubada yadda ya hargitse duk ya yamuste,sai lokacin yaga inda ya baci,ya tabbata abinda take boyewa kenan dazu bataso yagani,murmushi kawai yayi ya dauko sabon bedsheet ya cire wannan din ya gyara komai yazauna jiran fitowarta.
"Banason zance dallah kafiya magana,nace maka duk sanda yasake zuwa ka kirawoni h..."Amma ranki yadade naga kwanaki dana kawo miki katin daya bani yace da lambar wayarshi ajiki ki kirawoshi saida kika kusan sawa na rasa aikina s....."mtsw To naji,ada kenan yanzu kuma ni nace inaso ai,shikenan bazan chanja raayi ba?mal Bala banaso in sake maimaita zancena,idan kuma baso kake ka rasa aikin naka ba dagaske"tace cikin fada,"Allah yabaki hakuri,zaayi yadda kikace din"yace kanshi a kasa,wani tsakin tasake ja tajuya abinta tashige ciki.
(Malam Bala,dattijo ne irin masu aikin nan nasu ne na office,dan shara da dan aike,kuma sau wajen nawa duk sanda mayenta yazo shi yake bawa kati yabata,duk sanda yakai sai fatattaka dacin mutumci kowa dai yasan halin farida,ganin tayi mishi barazana da sallamarshi daga aikine yasashi shiga hankalinshi yadaina karba,to kuma yau gashi tazo dakanta).
"Amma fa ba karamin kuskure bane wannan,kodayake ma dai nima meye amfanin yin maganar,tariga ta faru ta kare"cewar Sammy bayan farida tabata labarin abinda yafaru,"nima bansan meyasa nagaya miki ba ai,don dama nasan bazaki taba goyon bayana ba kullum ni din dai nice"hmmm Allah dai yasawwake,kinsandai kafin ki kara samun namiji mai hakuri irin yusuf s......"wai meye hakane duk wanda yaji zancen nan sai yawani fara cewa mai hakuri mai hakuri,aikin banza aikin hofi,shikadai ne namiji aduniya?Allah na tuba maza ko ina sai wanda mutum yazaba,mtsw,shi baa ganin abinda yamin kenan shi ba laifi yayi ba saboda ni aka raina don ina kokarin kwatarwa kaina yanci shikenan banida hakuri aikin banza kai,wallahi yayi kadan shidin banza shidin hofi,"kinada damar dazakiyita zaginshi daga yanzu har illa mashaallah tunda ba mijinki bane,amma fa kisani baxan daina gaya miki ba kin tapka babban kuskure kuma dole kiyi dana sani,"wallahi babu danasanin dazanyi saidai shi yayi,ni da aka zalumta kuma ni zanyi dana sani?tayaya?ni walahi mutane kuna bani mamaki"hmm Hajiya farida kenan,lamarinki ne abin mamaki ai,h....."kinga ya kuma isheki burinki dama ke koda yaushe kisani gaba kicimin mutmci"ni d...."sararki ce ai"ta kasteta,na dade da gano hakan,wane irin abune zaace ko sau daya bazakiyi supporting dina ba,kullum saidai kiga laifina? Ke wace irin kawa ce"shiru sammyn tamata don bakinta bazai iya fadawa farida komai ba face gaskiya,abinda takeso taji daga gareta kuwa bazata taba ji ba,na goyon bayan nata datake zance,idan tace zata cigaba da biye mata suyita cece kuce saisu sami sabani yanzunnan,tunda itadai bata taba yarda itace mara gaskiya.
You are reading the story above: TeenFic.Net