RUWAN DAFA KAI 121~125
Na SUMAYYA DANZABUWA
Ana idar da sallar laasar su Ango yusuf aka fara shirin juyowa saboda gudun kada dare yayi musu a hanya Ga Dinner da aka shirya zaa gudanar da misalin karfe takwas.
Abu ansha kukan rabuwa dasu Baba,bawai don bata taba barin gida ba kowani abu, aa sai don sanin wai gidanta zata tafi, gidan aurenta,don ko farkon zuwanta gidansu yusuf saida akayita fama,saboda mutum ce da bata son barin gida ko da wasa,lokacinma don abubuwa sun tsananta ne agidan nasu,ba yadda zatayi shiyasa,fada kuwa da nasihohi ta shasu harta gode Allah,ita kuka su Baba kuka,dahaka aka rabu suna shi mata albarka damata fatan alkhairi.
G laure dawasu yanuwan nasu dabasu wuce mutum biyar bane aka taho tare dasu rakiya dakuma ganin inda zata zauna.
Yusuf yaso ace mota daya zasu shiga shida ita,Amma ina kafin yagama sallama da jamau,ya karaso ya tarar yanuwanta sun sakata a tsakiya shikuma tsananin kara da kunya yasashi kasa magana,dole ya hakura,don indai girmama na gaba dashi ne ba wasa,haka yashiga tasu shida bash da Amin yadda sukazo suka kama hanya.
Basu shigo gari ba sai bayan Maghrib,ko daaka karasa gidan Amarya bakin jamaun daaka tafi dasu kasa rufuwa yayi saboda tsananinmamaki don ko tangamemiyar gate din gidan abar a kalla ce,haka zalika dasuka karasa cikin gidan,sunji mata dadi kwarai da gaske,don su ba makiyanta bane,masoya ne na kwarai masu kaunarta tsakani da Allah,hakika suna tayata murna kwarai da gaske"chab,yo wannan gida ai shine aljannar duniya ke kuwa Abu kin huta abinki Allah ya baki Allah yasa gidan zamanki ne ya kauda fitina"shine kawai abinda suke cewa.
ya Asmau suka tadda don Aisha bata gari da wasu yanuwansu yusuf din agidan dasuka zo tarbar amarya,inda suka samu kyakkyawar tarba,don sun karbesu hannu bibbiyu abin sai wanda yagani.
Dakin daaka saukesu suka shiga,suka bar Abun da su Ya Asmaun don yadda suka ga sunata nan nan da ita abin gwanin ban shaawa,tabbas Abu tayi dacen miji da dangin miji,Allah yasa adore sukace bayan sun shiga,tabbas dakin nasu shima ya kawatu sai kace na amaryar.
suna zaune suna hutawa ne daya daga cikin matan dasuka tarar tashiga ta sanar dasu cewar fa su shirya akwai liyafa daa ka shirya wa Ango da Amarya,yar dariya G laure tayi,"to ai mu ba saimunje ba ko don bamu masan zaayi ba"aa ku kuwa dai ai kwaje bansan ya akayi ma bai sanar daku ba tun acen din kai yusuf akwai shiririta fa shima wani lokacin",tace tareda yar dariya,suma suka dan murmusa,"ku shirya don Allah Zainab bazataji dadi b itama idan bakuje ba,ga lokaci yariga ya tafi"tajuya tafita,"to Allah yasa dai cikin kayan nan naku kun taho da abin kirki"G laure tace dasu bayan ta fita,"ah bazaa rasa ba"sukace tareda janyo jaka"zamuzo birni kema dai kinsan ai mazo da sabon dinki"sukace sannan akayi dariya,kafin kuce kwabo sun chachanja sun shirya,ba laifi dai kunsan mutumin kauye yan atampopinsu suka saka,kuma dama dukansu manya ne babu wasu yanmata acikinsu,don duk yanmatan dangin nasu sunyi aure Abunce dama kawai ta rage kuma gata batada ko kawaye.
Abu kuwa tana cen,har anyi nisa dafara tsantsara mata kwalliya don musamman aka dauko wata shahararriyar mai kwalliya data kware akan aikinta kowa kuma yasanta,wato masu karatu duk wanda yasan Abu ada,yakuma ganta da kwalliyar nan karyarshi yace ya ganeta don wani sheki take tana walwali,tasha irin eyeshadow dinnan mai walwali,da daukar ido, ga wata winged liner daaka ja mata kamar da ita akayita tsabar tsaruwa,hakika tayi wani mugun kyau,ita kanta data ganta amudubi saida tadan tsorata.
yusuf ne yasake shigowa karo nawajen nawa kenan tun fara kwalliayar yana cewa ayi sauri an riga an makara already sai waya ake mishi don yaga kwalliyar tana daukan lokaci,"ka rabu damu mana kai kuwa muyi abinmu a nutse kadaina azalzala ko bakaso tayi kyau ne?"cewar yaya,"so kai,ai tariga tayi ma,mashallah fa tabarakallahu Ahsanul khalikin"yace bayan sun hada ido da ita,tayi mai wani fari dayasashi rikicewa don wani mugun kyau datayi ga Eyelashes din sun karawa idanunta kyau,"ko kunya"Yayan tace dashi,"toh mutum da matarshi"kalamanshi ne yasa kowa nawajen dariya,Abu dai kuny taji,shima yar dariyar yayi yajuya ya fita.
ko da aka gama kwalliyar wani dakin suka shiga inda yaya ta dauko wata riga doguwa maroon datasha ado,sai kyalli take tana sheki,ku kuna gani kunsan wasu makudan kudin aka kashe anan,don bama a nan Nigeria aka dinka ta ba,shiga rigar tayi don bazaace sawa ba takuwa fito das da ita,kamar ajikinta akayi dukda dai ba fitted bace,saida tagama saka rigar yaya ta gyaggyara mata sannan suka fito mai kwalliyar tamata dauri irin turban dinnan yayan dakanta tasaka mata sarka da dankunne dasu Abin hannu da agogo don haka kawai takejin son yarinyar da kaunarta,ga nutsuwa da kunya,tun ranar dasuka farazuwa tamusu girki taji tabirgeta tun lokacin tafadawa su Hajiya tayiwa kanin nata shaawar kasancewarta matarshi to ashe dai ashe shima ya dasa,"Abu kamar ba ke ba ni laure lallai wato kwalliayr nan tazamani mayar da mutum take wani daban,jibi yadda idanunta suka kara girma nikam "cewar g laure bayan sun shigo,"wallahi kuwa ikon Allah" sauran sukace ita dai Abu ba abinda take sai dan murmushi don dama bata fiya magana ba kuma ma ai dama manya ne mezatace musu,"hotuna g laure tayiyyi mata don idan ta koma tanunawa su gwaggo dasauran yanuwa.
Wani takalmi kirar Christian Loubuotin mai shegen kyau,dakuma uban tsini,yayan ta dauko da yar jakarshi irin wadda amare suke rikewa,ganin Abu ta zaro ido fuskarta dauke da damuwa da tsoro ne yasa yayan dakatawa,"Zainab tsoro yabaki haka?Ya miki tsaho ne dayawa"?gyada kai tayi alamar eh,"chab ta ina dama zata iya hawa wannan takalimin tserere,ai yayi tsaho dayawa wannan ai saita karye" daya daga cikin gwagganin nata tace,"bazata karye ba ai,ki gwada kinji zaki iya bazaki fadi ba kinga angon naki mai tsahone sosai,ko ke bakyaso ki dan kamo shine"Yayan tace tana dariya tareda kokarin kakaba mata shi akafa,"Nidai tsoro n...."shiru tayi bayan sun hada ido da g laure taga ta galla mata wata harara,don ta tsani kauyanci,"ki gwada mana akace kigani idan kin kasa ai ba dole saiki cire,amma baki gwada abu ba kice bazaki iya ba"ta kara,dakyar zuciyarta na harbawa kamar zata fito waje,ta tashi tana rirrike antin cikeda tsoron karta fadi,"jeki bangon cen ki dawo mugani idan kin kasa din sai a chanja"bangon ta tafi ga mamakinta saitaji kuma ashe dai zata iya gashi bata ko gurdewa kawai dai tsahon takalmin ne a zahiri mai tsoratarwa amma gashi data sakashi kamar bata saka komai ba,jinta take dai kamar a tsauni gawani tsaho data kara,murmushi tayi"zan iya dai ashe"hakan ne yasa dukkaninsu dariya.
Fesheta akayi da turarruka kala kala masu dadin kamshi,aka kawo dan mayafi aka dan yafa yadda dai amare sukeyi,aka fara hotuna.
Su yusuf suna tangamemen palon dake kasa ne sukaji alamun mutane na saukowa,"Allah yayi angama"yace,koda su gwaggo suka sauko ja gefe sukayi suka tsaya,Sannan Amarya tabayyana,ai daga yusuf din har abokan nasu kowa maida dubanshi yayi gareta don tayi matukar kyau irin kyau dinnan sosai fa bazaku gane ba,yusuf ji yayi kamar yaje yayi hugging dinta amma kash su gwaggo na wajen kuma yana kunyarsu,itadai Abu dataga kallon yayi yawa kasa tayi dakai tana wasa da Agogon hannunta,gaba su gwaggon suka farayi da sauran jamaar,hakan ne yabashi damar yimata hotuna kala kala shima sannan suka fice duka don shiga mota atafi,itada shi suka zauna Abaya,Bash dawani Abokinsu agaba rikeda Amin.
A wani kayattacen Event centre aka shirya abin,dangi baki daya da abokannan arziki na yusuf din sun hallara,koda sukaje kafin ashiga duk wanda yaga amarya sai yace tayi kyau,itadai murmushi kawai take,yanmata ne ke yawo sunsha anko peach kala,ko ina,tunda dai Amarya batada kawaye yaya tasa duka yanmatan dangi suyi anko,da akazo shiga ango yarike hannun amaryarshi suka jera suka shiga.
Anci ansha anyi zumunci anyi rawa don taro ne na kowa harda manya,wasu dabasusan ya lamarin yake ba ganin tayi mugunnkyau ga kayyaki masu tsada ajikinta ne yasa aka dinga tambayar ko yar gidan waye,itakuwa Hajiya duk wanda ya tambayeta sai tace "yar babanta ce"dole aka hakura aka saurara dajin kwakwaf,kai mutane akwai gulma.
Anyi taro angama lafiya inda suka wuce gidan Hajiya,wanka su yaya suka sata tayi sannan aka bata wata Abaya tsararriya mai mugun kyau tasaka ta yafa mayafin,sai kamshi take tana walwali,"wayannan kayan naki,(rigar dasu taklamin daduk abubuwan data saka) zan kai miki su Mota ,ki ajiye tarihi" cewar Wata yaruwar su yusuf din Abida tana dariya,don kusan saar Abun ce itama tayi aure baa wani dadeba,tun dazu suke dan kawancensu,yar dariya Abun tayi,"to zan ajiye nagode".
A palon Hajiya suka hallara dukansu hardasu gwaggo dama akaje, nasiha Hajiya tamusu mai ratsa jiki sannantadinga jaddada hakuri dukda dai ta lura Abu batada matsala amma dai duk nutsuwarta dole a kara mata,don bata fatan ta kasance munafuka irin farida,(kai Allah yarabamu da irinsu farida).
saida aka kammala komai don lokacin har sha biyu ma ta wuce sannan suka kamo hanya,Dama Hajiya tace abar Amin a wajenta idan an kwana biyu ko in yatada rigimarshi ta rashin uwarshi adawo dashi don yadan kara girma ya rage kyuya.
Bash ne direba shida ita suna baya sai janta suke da hira ita kuwa duk wani iri abin wai itace yau tazama matar wani hmm,magana daya zai mata sai yawani tabata.
Shima Bash din yan nasihohin dasuka kamata yayi musu a hanya,don babu wani lamarin siyan baki anan,tunda dai amarya ita kadai ce babu kawaye bakowa,A gate ya ajiyesu,yamusu saida safe ya juya abinshi.
Tun a compund din gidan ya wani rikota wai shi mai mata,sai dan fifizgewa take don gani take kamar bai kamata ba,duk wani iri abin,rashin sabo,dakyar ta iya daurewa suka karasa cikin gidan,tanata Fatan Allah yasa babu kowa kar aga ya rikota,don bata fata wani yagansu ahaka,saboda yadda yabi ya kankameta ya kanainayeta kamar wani zai kwace ta, dakyar take tafiya,sai zuba yake yana kalamun soyayya,koda suka shiga palon basuga kowa ba da alamun su gwaggo suna daki kenan,hakan ne yasa tasaki ajiyar zuciya,tareda saurin fizge hannunta,ta juya zata shige dakin nasu itama,saurin rikota yayi,yayi hugging dinta tsam abinda ya dade yana buri kenan,harzata fara kokawar kwace kanta ta tuno wani waazi dataji jiya na hakkin miji akan matarshi,da yadda malaiku suke tsinewa duk macen data hana mijinta hakkinshi,itakam tsinuwar makaikun nan ita take bata tsoro shiyasa bazata kuskura tabari ran mijinta ya baci ba akan hakan bare tayi sakaci ya kwana da bacin ranta,hakan ne yasata sakin jiki tareda kara shigewa jikinshi itama,kankameta ya karayi don hakan yamishi dadi kwarai da gaske,saboda dama bayaso yaga tana gudunshi tana tsoronshi.
"Kazar ki fa tana kitchen tun dazu aka kawota muje kici"wace kaza?"ta nanata,dan murmushi yayi bayan ya dago fuskarta ya kalleta ido cikin ido,zata dauke kai ya juyo da ita, ta kalli kasa,"saifa kin kalleni,wannan kunyar tamin yawa" yace,dan murmushi tayi ta kalleshin don tanaso ta kasance mace tagari mai kokarin kaucewa aikata duk abinda zai batawa mijinta rai,bata fatan taga ranar dazata kasance sanadin bacin ranshi,"yawwa kokefa i lov u more"yayi kissing goshinta,ai ji tayi kamar ta nutse a kasa,"baki bani ansa ba"i lov u too"tace dakyar tanata jin kunya,"muje kici kazar,kazar kice ta siyan baki"girgiza kai tayi alamun aa don ta koshi wallahi a wajen dinner saida ya takura taci abinci kuma dasukaje gidan hajiya ma saida aka kara sata taci "kin koshi ko,nima nakoshi dama yace,"yana kallonta yana murmushi tana mayar mishi,ganin yana shirin zurfafa lamarin ne yasata magana kasa kasa"zan danje wajensu gwaggo"tace"ok to bari in hau sama,",koda tashiga taddasu tayi duk sun kwanta sunyi shirin bacci,saboda angaji G laure kuma tana bandaki,"aa mezan gani haka!me kike anan?"Tace bayan ta fito taga Abu adan kishingide gefen gado,kamar wata yar bora duk ta takure waje daya",zuwa nayi in kwana" duk idanunta sun cicciko,(wai kamar ba yanzunnan ita tagama tunani da tsoron tsinuwar malaiku ba da kare hakkin miji?),har gwaggon zata fara fada sai kuma tausayinta ya kamata,don tasan dole da rashin sabo,to amma ya zatayi kowa dahaka ya saba ai,"kiyi hakuri Abu"tace tareda zama gefen gadon ta dafata," ki tashi ki tafi wajen mijinki kinji,nasan kina cikeda fargaba da tsoro, Amma bakomai,kowa dakika gani sabawa yayi kinji yar albarka,ke fa kika ce kinmin alkawarin kasancewa mace tagari mai kare hakkin miji ko har kinmanta?"girgiza kai tayi alamun aa"to kuma,maza ki tashi ki tafi sai dai kuma idan so kike mijinki ya kwana yana fushi dake malaiku suyita tsine miki har garin Allah ya waye"kuka tasa,hawaye sharshar,kowa yana bata baki ana rarrashinta,"kiyi hakuri ki tashi ki tafi,saida safe"ganin dai bazata tashi bane yasa gwaggon dagota daga gadon ta rakota har kafar benen,"karfa in leko in ganki?maza ki haye,ki tabbata kuma kina zuwa kin shiga wanka,wayannan turarurrukan dana baki ki shafasu yadda nagaya miki,"toh"kawai tace dakyar,tacigaba da tsayuwa,"jeki mana ina gani"hawa benen tadingayi daya bayan daya tana juyowa taga ko gwaggon ta tafi don idanta tabbata takoma daki ita kam a palon zatazo ta kwanta,amma ina taki tafiya,dagaske take sai taga hawanta zata shiga,bayadda ta iya dole takarasa.
Da sallama Ta shiga tana fatan taga yayi bacci,don bata lokacin datayi acen harda burin ta na kafin tadawo Allah yasa yayi bacci,amma ina sai ganinshi tayi kan dadduma da alamun ya idar da sallah,ga qurani a hannunshi yana karatu "bama yajin bacci wato?"tace aranta,maida dubanshi yayi gareta bayan ya ansa sallamar tata"har anyi sallamar kenan?"gyada kai tayi,"toh mashalalah kinada alwala,ko zakiyi?"Inada ita "yawwa yarinyar kirki,yar albarka,to zo muyi sallah mugodewa Allah ko"yace cikeda rarrashi don yadda yaga tana abubuwa yasan inda ta dosa,yasan kwanan zancen shiyasa yake lallabawa,dadduma ya shimfida mata ta dare sukayi nafilfilu da suka idar kuma yayimata adduar da addini ya tanadar duk sanda mutum yayi sabon abu.
Hamma tafara alamun bacci har tana dan gyangyadi,"lallai bacci kikeji baby"eh wallah sosai" tace tana hamma,"to ki tashi ki chanja kayankki ko,don bakya kwana da wannan Abayar ba ai,tanada nauyi"har lokacin bai bar kan daddumar ma,"bako..."tayi saurin shiru don gudun yiwa miji musu don ance karta kuskura tadingayiwa miji musu in yasata abu matukar abin bai sabawa addini ba to ta aikatashi banda gardama,ita kuwa aljannarta take nema ido rufe,tashi tayi ta shiga wani dan sashe na dakin,inda aka shirya mata wajen kayayyakin sakawa dasu takalmanta dakomanta closet dai,sannan ta bude wata drawer da yaya tanuna mata dazu ta kayan bacci don komai saida aka nuna mata inda yake,wata doguwar riga ta dauko har kasa irin ta cotton dinnan mai dogon hannu,sannan tashige bandaki,kallo yabita dashi yayi yar dariya,yarinta ho, yace azuciyarsh wai ni ake boyewa jiki kar na gani,Allah sarki,yacigaba da latsa wayarshi.
Brushing tayi don tasaba tun agida tayi da safe kafin ta kwanta tayi,don Abu badai tsabta ba fa masu karatu,saida takammala sannan tasaka rigar ta yafo mayafi ta fito,ko turaren bata tsaya shafawa ba tadai dan fesa na fesawa sama sama,don Allah yasani bacci takeji.
Abaya data cire tashiga ta rataye a closet din akwai hanger ta idan an cire kaya arataye,duk yusuf yana ta kallon yanda take komai cikin tsari a nutse yayi imani inda farida ce watakila saidai yashiga bandakin ya dauko Abayar don ta shiga kenan batada damuwa,tunda ita duk abinda tayi amfani a wajen zata bari.
Gefen gadon tazauna tanata hammar dai,"kiyi kwanciyarki baby kinga dare yayi sosai har biyu saura fa"yace bayan ya kalli agogon hannunshi,"toh Allah ya tashemu lafiya"tace tareda kwanciya taja bargo,"to tunda dai banga yayi niyyar yin komai ba akan hakkinshi ai shikenan sai inyi baccina cikin kwanciyar hankali Allah yana gani,bahanashi nayi ba"tace aranta.
Saida yagama duk abinda yake sannan ya kashe musu fitila yahau gadon shima, yajawota jikinshi,baccinta yayi nauyi ko ji mabatayi ba,don tagaji sosai,kafin kuce kwabo shima yayi baccin mai dadi.
Alarm dinta ne na sallar asubah ya tasheta zumbur kuwa ta tashi tashiga tayo alwala,tafara tashinshi don tasan ko da cen baya fashin zuwa masallaci sallah,kodaya tashin ganinta yayi ta tada sallah,hakan ne yasashi yafara godewa Allah,daya bashi salihar mace data damu da ibada,tunda suke da Farida bata taba rigashi tashi sallah ba,bare har akaiga wai ta tasheshi ya tafi masallaci tabbas Allah ne abin godiya tunda ya mallakamishi Abuwa.
koda ya fito daga alwalar,tadda ta yayi tana karatunta,baice komai ba ya shirya yayi masallaci,harya dawo bata bar kan abin sallar ba tanata karatun tana adduointa,saida ta idar sannan suka shafa tare,hakan ne yasata kallonshi ta sakar mishi murmushinta me kasheshi.
Gaisheshi tayi cikeda girmamawa, ya ansa cikeda farinciki sannan yace su kara dan bacci zuwa tara ko goma,hakan kuwa akayi don bata tashiba sai goman,koda ta farka bata ganshi ba,batasan shi dakyar ma yakoma baccin ba dama.
Wanka tashiga ta fito ta dauko wata doguwar rigar tasaka bayan tashafa dan manta yadda tasaba dama ita ba wai kwalliya take ba harta yafa mayafinta zata fita tatuno fadan g laure akan yiwa miji kwalliya don tasan tabbas idan ta kuskura tabari taganta ahaka fada zata mata,dole tadawo tadauki jambaki ja tashafa da yar hoda,tadan shafa turarrukan ta fito.
Bataga kowa a palon ba hakan ne yasata shiga dakin dasuke tagansu duk sun hada kaya sun shirya gashi har abinci ma sunci,"Amarya Amarya "cewar Su bayan sun gaisa,ita kuma tanata murmushi,"to Amarya dama ke muke jira mu mun gama shiri zamu wuce Allah ya kaddara saduwa"take idanunta suka ciko dagaske dai kowa tafiya zaiyi yabarta ita kadai kenan,"don Allah ku kara..."kujimin jairar yarinya mu ba kannenki ba bakomai ba shine don rashin ta ido zamu miki zaman daki?"ki kiyayeni fa"daya daga cikinsu tace,wani kuka Tafashe dashi harda durkushewa akasa,"laaaa kunjimu da yarinya ji tabara fa,dama tare aka auromu dake kenan dazamu zauna"to ma banda abinki Abu,waye yace miki ma wai yanzu amare suna wani kukan rabuwa ne?duk andaina an waye,kina abu kamar bakyason mijin shima idan yaganki fa bazaiji dadi ba"itadai G laure ko uffan ma batace ba,don tasan zatayi duk abinda zatayi ne tagama na dan lokacine dole tasaba"jin knocking ne ya katse musu zancensu"kashigo" yusuf ne yabudo kofar dakin don duk ashirye suke da mayafansu,a kofa ya tsaya,"aa meya faru?"yace ganin Abu a tsugunne tana aikin kuka,duk yadda sukayi da ita aka kwashe mishi,hakan ne yasashi sakin murmushi kawai don baisan mezaice ba rarrashinta ya kamata yayi dakyau to amma bazai iya ba yadda ya kamata a gabansu,kuma ma ai dolene tayi kuka,ganin dai ba shiru zatayi bane yasasu gwaggon rarrashinta da kwantar mata da hankali duba da yadda tabasu tausayi,"dama direban dazai kaiku ne ya karaso"yace,"to sannu fa mungode Allah yasaka da Allkhairi yayi albarka"suka dinga godiya "haba,haba bakomai nine da godiya ai,"yace cikeda ladabi,kayansu yafara dauka yana kaiwa motar da abubuwan arzikin da hajiya ta hada musu,sai kudi masu tarin yawa dayabasu,dakyar suka karba,sannan akayi sallama,Abu naji tana gani motarsu ta fice daga gidan,cikin sanyin jiki yusuf ya rikota suka shiga ciki yanata aikin rarrashi.
Farida nacen tun daren jiya take zazzabi,har yanzu tun bayan ganin hotunan dinner datayi,tama rasa me ke mata dadi,don duk hoton dazata gani na biki hakoran yusuf a waje ya washesu alamun fa shi acikin tsananin farin ciki yake yama manta da babinta bashida wata damuwa,ga Abu data saka kaya masu uban tsada tayi mugun kyau,don ko ita da bikinta bata saka irin rigar da yarinyar tasaka ba,hmm abubuwa dai sai faruwa suke kamar tattsuniya,wai dagaske dai maiaikinta ta aure mata miji, wallahi yusuf yayi da gwana,karyarshi yaci bilis,don wallahi yadda yasa ta kunshi bakinciki da auren nan nashi itama saita sashi ya kunsa danata auren.
Barkanmu da warhaka lovelies,ina fatan duk
You are reading the story above: TeenFic.Net