Tags: love
LABARINSU

LABARINSU

1,049 20 17

Kowa ya na da Labarin da zai bayar.Kamar yanda ƙaddarar kowa take da ban.Tabbas, akwai tsanani a rayuwa.Akwai ƙunci da baƙin ciki a rayuwa.Shin menene LABARINSU?…

BAKAR WASIKA

BAKAR WASIKA

18,118 1,027 11

Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? Yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke?Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa? BAKAR WASIKA...! _Mai farin rubutu_…

RAYUWAR BADIYYA ✅

RAYUWAR BADIYYA ✅

254,648 20,656 61

"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanji dadin rayuwata, babu yadda na iya haka na biyoki inda kika doro mani karan tsana, kullum sai kin zage kin dukeni, sunan mahaifiyata kuwa ya zama abun zagi a gareki a koda yaushe, kin hanani abinci, kin sakani wanka da ruwan sanyi lokacinda ake matukar sanyi, kin cuceni iya cutuwa, a haka Allah ya rayani. Sai ke yau dan rana daya kince zakici uwata nace nima zanci taki shine zakiyi kukan munafurci? Ni kin taba laakari da irin kukan danake cikin dare kullun? Dukda mahaifiyata ta rasu hakan bai hanaki zaginta ba. To na fada da babbar murya, wallahi duk kika kara cewa zakici uwata to sai naci taki uwar nima, and that's final!" Zuwa yanzu duk bakin cikin dake zuciyar Badiyya saida ya fito, kuka take kamar ranta zai fita, mahaifiyarta kawai takeda bukata, bakin ciki ya mata yawa, batada wanda zai saka ranta yayi sanyi bayan Momynta, amma tayi mata nisan da yakeda wuyar isa. Ta buda baki zatayi magana kenan Ahmad ya wanke ta da marika kyawawa guda biyu, ta dama da haggu, rike wajen tayi tana kallonshi.Magana ya fara cikin tsananin bacin rai, "Yanzu Badiyya a gabana kike cewa zakici uwarta? Uwata kenan fa Badiyya! To ko Yaya kika zaga bazan kyaleki ba balle wadda ban taba gani ba, dan haka wallahi zakiyi mugun dana sani," ya fada cikeda tsananin fushi, yana kara kai mata mazga saman kai.Kukane ya kara kwace mata "Kai kenan da baka taba ganin taka ba, nifa? Nifa Dady?! Na taba ganinta, nasanta, nasan dadin uwa, amma haka wani azzalumin ya raba ni da ita, sannan kai da nake tunanin zaka share min hawaye kaine kake kara sakani kuka, me na maka? Me Momyna ta maka?" Ta tambaya tana kureshi da idanu._______Me zai faru a rayuwar yarinya yar shekara goma data rasa mahaifiyarta? Wace irin rayuwa zatayi a gidan yayar mahaifinta?…

CIWON ƳA MACE..

CIWON ƳA MACE..

1,122 83 15

Rayuwa cike take da kaddarori da dama, dan Adam baze ce tayi imani ba kuma Allah ya kyale shi kawai, dan yadda da wannan imanin se Allah ya rubuto series of jarrabawowi din tabbatar da ingancin imanin namu.Se dai san rai da son zuciya na jagorantar dan Adam ga munanan ayyuka, wanda daga karshe suke jinginawa ƙaddara, akwai ƙaddara, amma kuma a boye cikin kaddarar nan akwai jagorancin wasu munanan halaye, son kai, hassada, bakin ciki, da ire iren su.Akwai wani karin magana da Bahaushe ke amafani da shi,musamman a tsakanin mu mata, wanda nake da ja akan shi, da kwarin gwiwa ta, da dukkan zuciya ta, haka da dukkan murya ta nake faɗin CIWON ƳA MACE BE TAƁA ZAMA NA ƳA MACE BA!.Ban yarda da karin maganar wai CIWON ƳA MACE NA ƳA MACE bane, ban kuma aminta ba, shiyasa tun tasowa ta nayi watsi da shi, bangarori da dama da na duba na rayuwar mu mata ya karya ta shi.Ina tunanin bahaushe be fahimci rayuwar mu ba, be karanci mata ba, da na tabbata baze fadi wannan zancen ba balle har ya shiga jadawalin karin maganar mu na Hausa masu tushe da dimbin tarihi.Bari kuji, mace ita ce matsalar mace yar uwar ta, dukkan kukan mace in kun yi duba daga tushe zaku ga daga mace yake, kyashi, bakin ciki, hassada, son kai, munafunci da wasu sauran mugayen halaye da dabi'u sun tare a wajen mata ne.Ba zan ce duka ba dan ko a cikin gidan karuwai akan haifi malami, sedai da yawan mu haka muke, bana tunanin akwai macen da in aka binciki rayuwar ta ba za'a samu tabon yar uwar ta mace ba, in one way or the other, se kuma da na fara fahimtar rayuwa na fahimci DOLE ACE MATA SUN FI YAWA A WUTA.!Ban tsani mace ba dan nima itace, mahaifiya ta ma itace, akwai kuma tarin yayye da kanne, sedai na tsani munanan halayen mu, na kyamaci gurbatattun mata na daga cikin mu, dan sun taka rawar gani cikin KADDARAR RAYUWA TA!.Dan Allah kar ku yanke min hukunci batare da kun saurare ni ba, ina rokon ku ku bani aron lokaci da hankalin ku, ku biyo ni dan jin muguwar rawar da mace ta taka cikin ra…

 AFRA

AFRA

70,870 7,650 58

Murmushi tayi mishi wanda ya tafi da imanin sa yayin da ta juya kallonta ga duɓɓin mutanen wajen. Dogayen yatsunta biyu wanda suka sha jan lalle ta buga akan speakern dan ta ga ko yana aiki. Illai kuwa sai ta ji ƙaran bugun da tayi. Murmushi ta ƙara sakar wa mutanen da duk ita suke kallo, da mamaki a idanuwansu, kafin ta buɗe baki tafara magana kamar haka." Assalamu alaikum " sai ta ɗan dakata kaɗan don su amsa mata, ba laifi wasu sun amsa mata wasu kuma sunyi ƙum da bakin su. " dama na zo ne don na nuna farinciki na game da taya abokin mu, kaninmu da yayen mu Salim murna " tace yayin da take kallon angon wanda tun tahowarta stage yake warwara ido kamar baƙin munafuki, gashi yanda zufa yake ta keto masa, zaka zata ba ac a wajen.Kau da idanunshi yayi kafin su hadu da nata. " amma kuma abin da ya sosa min rai game da wannan abin shine ni nafi chanchanta da a kira in zo in bada tarihin wanan bawan Allah. " ta ƙara dan dakatawa yayin da ta runsunar da kanta kamar mai wani tunani, sai kuma ta k'ara daga kanta ta kalle mutanen da duk suke yi mata kallon mahaukaciya wadda batasan abin da take ba.Budar bakin ta ne sai tace. " duk da dai an kira abokin ango yayi nasa bayanin barin in ɗan baku tak'aitaccen nawa "." amarya Salima " tace tana kallon amaryar da tace kwalliya a cikin doguwar riga kalar ja itama, sai dai na amaryar bai kai na wannan budurwar kyau da tsaruwa ba, dan inbaka san wacce amaryar ba sai kazata itace.Salima wacce tun da yarinyar tafara magana ta ke ta faman bankamata harara, taja wani ɗan tsaki game da sake sakarmata wani hararan.Afra , yarinyar da ta ke kan stage in ta murmusa kafin tace ." ina taya ki murnar auran munafukin namiji, azzalume wanda bai san darajar mutane ba, ina kuma ƙara tayaki murnar samun daƙiƙin na namiji wanda ban da wata shakka ƙarshen sa bazai yi kyau ba, kuma ki kasa kunan ki kiji mijinko mayaudari ne, me bin mata ne kuma zan iya rantse miki fasiƙi ne "Read and find out…

KAUTHAR!!

KAUTHAR!!

4,829 250 6

Yadda ya daga kai yana kallonta ne yasa ta shiga taitayinta babu shiri. Ya fara dumfararta gadan-gadan, kamar wanda yake shirin cinyeta danyarta. Duk dauriyarta kasawa tayi, ta fara ja da baya a rikice, idanunta sun fito waje kuru-kuru, dankwalin dake hannunta ta sanya tana kare fuskarta kamar shi zai kwaceta daga hannunshi. Sai daya danganata da bango, ta jita ta lafe a jiki kamar zata shige ciki.,Ya duka yana kallon tsakiyar idanunta da wani irin murmushi na gefen baki kwance akan fuskarshi, taji wasu abubuwa masu kama da jan wutar lantarki na yawo a sassan jikinta.... Murmushi ya sake saki, "kina ta babatu da daga murya akan Anty Ummynki Kauthar, sai dai, me yasa dana kalleki nake ji a jikina kamar ba ita kike tayawa kishi ba? Me yasa nake ji kamar.... kishina ne yake cinki? Me yasa nake hango tsabar kishina kwance a cikin idanunki, iye Kauthar? Me yasa??!!!".Ganin yadda take faman zare idanu kamar kazar da aka lakume za a yanka, yasa ya ja da baya, wannan murmushi nashi dake matukar bata mata rai yana kara fadada akan fuskarshi, sai ya juya ya fita daga dakin. Ta sani, kamar yadda ya sani, bashi da sauran ta cewa, don kuwa ya riga ya gama daureta kam da jijiyoyin jikinta!Ta silale a jikin bangon, zuciya na bugu kamar zata fasa kirjinta, ta samu kanta da maimaita tambayarshi a gareta, 'Me yasa? Kuma me yake nufi?!'.********************Zaku iya samun cikakken labarin a HIKAYA BAKANDAMIYA yanzu***…

A JINI NA TAKE

A JINI NA TAKE

57,070 2,971 12

Labari ne daya kunshi masarautu biyu; Masarautar Katsina, wacce take cikin Nigeria da kuma Masarautar Damagaran, wacce take cikin Kasar Niger. Labarin yayi duba ne da rayuwar Yarima Bilal, wanda rashin magana da miskilanci ya kanja ya shiga tarun matsaloli, wanda hakan yake haifar mashi da auren Zeenah Kabir Muhammad. Diyar Bafade da kuma baiwa. Me zai faru a rayuwar auren da aka hada miskili da kuma masifaffiya? Wanda dama tun farkon haduwarsu da masifa aka fara har yakai ga ya kure hakurinta ta sharara mashi maruka biyu? Shin ko zasu samu zaman lafiya kuwa? Bilal wanda ya kasance zuciyarshi a kulle take tun bayan rasuwar mahaifiyarshi zai bude ma Zeenah ita? Ya rayuwa zata basu bayan Zeenah ta fada soyayyarshi sai kwatsam Juwairiyya ta kunno kai? Wane hali Bilal zai shiga a lokacin da Fulani ta bankado wani tsohon sirri dake tsakaninsu?Fulani fah? Wacce take uwar gida kuma mai kula da hidimomin Masarautar Katsina gaba daya? Zata rufe sirrin data gano tsakanin Zeenah da Bilal dan gujewa tarwatsewar farin cikinsu? Abu daya ne zai kai ga na biyu, wanda har Bilal zai tsinci kanshi an mashi shamaki da Masarautar Katsina, hakan zai dangantashi da Masarautar Damagaran! Ku biyo Yar Malumfashi domin jin yadda labarin zai kasance.…

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)

51,932 3,561 32

Zazzafar shari'a ce a cikinsa, wacce take kunshe da rikici da tashin hankali. Me ya sa rashin 'yancin kai ya yi yawa a wannan zamanin? Me ya sa talaka yake ba a bakin komai ba? Fyade, kisan kai tamkar kiyashi. Babu abin da littafin Wata Shari'a bai kunsa ba. Ku shigo daga ciki a yi tare da ku. Ku biyo Amrah a cikin labarin Wata Shari'a, inda za mu shiga cikin rayuwar Ummima da babbar kawarta Gentle. Ehem ehem! Lets go!…

ALMAJIRA ✔

ALMAJIRA ✔

1,459 75 23

Story of a girl living a miserable life as the agony of her life is too painful for them to survive, She finds her self begging in the middle of the street because she had no one to stay with no parent and no other choice than to be a beggar. As life goes they begin a new life with two blind people Anna and her Husband Baffah.~ALMAJIRA~sabon saloKallo ɗaya za kayi ma yarinyar dake tsaye a tsakiyar titin tana ta ƙokarin yin ihun barar ta da murya mai sauti wanda Allah ya bata, a kiyasance ba zata wuce shekaru goma sha biyar zuwa shidda ba amma tana ɗauke ta cikin da bazai wuce cikin wata shidda zuwa bakwai ba, sa'annan tana goye da karamar yarinya mai shekaru biyu da rabi cur a duniya.Fuskar ta kawai zaka kalla ka gano tsantsar rama, wahala, baki dake tattare da fatar jikin ta shima ba'a magana.Shin wannan yarinyar mai shekara biyu da rabi ƴar tace ko ƙanwar tace kuma da gaske ne ciki ne a jikin ta? in kuwa hakane to taya ya ta samu wannan cikin? Ko kuma tana da aure ne?Labarin ya kunshi abubuwa daban daban ko ince salo kala kala wanda ya danganci rayuwa na karamar yarinya mai suna HADIZATOU...Ya kunshi bangarori na wahalar rayuwa da yadda almajirai suke shan wahala da kuma rayuwar mabarata.…

KADDARA CE

KADDARA CE

316 20 11

KADDARA!Shin me cece ita?.KADDARA na ɗaya daga cikin hukuncin Allah da ya kan zartar a kan bayinsa tun yayin hallita.KADDARA tamkar zagayen zobe take, wanda ɗan adam ke rayuwa a tsakiyarsa.Duk wani abu da ya samu bawa tun daga ranar haihuwarsa zuwa ga ranar da zai koma ga mahallicinsa sunansa KADDARA.KADDARAr ko wani bawa na rubuce ne tun kafin ya iso zuwa duniya.Kowa da ka ga yana rayuwa a doron duniya yana yin ta ne a doron KADDARA.KADDARA na ɗaya daga cikin manya manyan siffoffin Allah subhanahu wata'ala.Domin duk abin da ya samu bawa a rayuwa muƙaddari ne daga wurinsa. Wa lau me kyau, ko akasinsa.…

BA UWATA BACE

BA UWATA BACE

65,742 5,206 47

BA UWA TA BACEZaune take gefe guda cikin gidan nasu, tana kallon abinda Yan gidan nasu sukeyi k'awar tace Hadiza zaune gaban mamar tasu tana mata lissafin kud'i da tasamu, daga daren jiya zuwa yau da safe.Mamar sai washe hak'ora take tana murna sannan tace "Ai na fad'a Miki idan Kika bi Alhaji Hamza kwanan gida sai ya Baki mamaki."Hadiza tace gashi kuwa ya bani mamaki mama domin tunda Nike arayuwata bantab'a kama irin kud'in Dana kama yau gugu na gugur naira har dubu hamsin mama tawani wutsilo daga kugerar da take Yar tsugunne, ta fad'o k'asa sannan ta d'aga Kai ta dubi Hadiza ko zafin fad'uwar bataji ba tace da gaske kike ko da Wasa Yar nan.Hadiza tace "wallahi mama kingansu ma" ta fito dasu ta nuna mata kud'in hannu na rawa mama ta k'arbesu ta tashi tana juyi da rawa agaban d'iyar Tata.Bilkisu ji tayi k'amar ta kurma ihu Dan bak'in ciki wannan wata irin uwa ce Allah ya Basu, wasu hawaye masu zafi ya zubo mata ganin yadda ita Tata rayuwar zata Kaya kenan ga wata uwar yunwa datakeji, Amma saboda tak'i bin abinda uwar Tata takeso ta hanata, gashi ita tashin hankalinta shine idan dare yayi wani irin tuggu zasu had'a mata Dan taji mamarta da yayanta na zancen, zuwan Alhaji kamilu zuwa gareta ko tanaso ko bataso yau sai ya kwana da ita, Anya kuwa wannan ita d'in uwa ce agaresu tana cikin wannan tunanin taji k'ara bud'e kyauren gidansu na langa langa daga Kan da zatayi Dan taga Mai shigowa sai taga k'awarta ce ta biyu zainab.Shigowa tayi cikin wata irin shiga domin kayan jikinta amatse suke sosai duka sun fitar da surar jikinta rabin breast d'inta duk awaje cikin takun yauk'i da yanga tashigo, tana yatsina ko sallama babu mamarta ta k'alla sannan tace "wallahi mama yau nagaji Dan wannan d'an iskan Alhajin bak'aramin sasuk'a ta yayi ba tun dare yake abu d'aya har safe gashi bak'arami ba ga abun tashi kamar tabarya, gaskiya ya cika d'an iska…

WANI GARI

WANI GARI

11,306 572 16

A wani gari, da al'ummarsa basa hada jini da mutanen wajen garin, akwai wata yarinya da alkalamin kaddara yayi mata zane a garin da bata da kowa ciki kuwa har da masu jin yarenta!Garin da babu masu cin irin abincintababu ma su kalar addinintaballe kuma al'adar da ta ginu a kai! Ta fallasa wani sirri da aka dade da binnewa shekaru ashirin da bakwai a baya, ta yi nasarar sauya rayuwar Maleek. Hakika wani mafarkin baya nufin cikar burin mai shi, wani burin kuma yana tabbatuwa ne tun kamin zuwa mafarki. Ya Ameer zai ji idan ya farka daga dogon bachin da ya dauke shi mafarkin shekarun da babu wanzuwarsu a rayuwarsa ta baya da kuma wanda za ta zo a gaba? Mi ya haifar da gaba a tsakanin yan'uwa jini? Anya wuta da ruwa za su hadu? Find out in WANI GARI.Rikicin cikin gida.Labarin soyayyar da bata jin yare...…

GIMBIYA SA'ADIYYA (Aljana Ko Fatalwa?)

GIMBIYA SA'ADIYYA (Aljana Ko Fatalwa?)

156,408 19,405 55

Haka rayuwarta ta kasance tsawon lokaci a cikin kwalbar sihiri. sai dai kuma a lokaci guda BOKA FARTSI ya yi watsi da alkawarinsa da KURSIYYA, ya fiddo ta tare da umurtar ta kan cewa ta ci gaba da bibiyar rayuwar KURSIYYA domin ta kwato wa kanta da kuma shi kanshi fansa. Ko wace ce wannan Kursiyyar? Wace ce wannan daga cikin kwalba? Wace irin fansa ce za ta kwatar wa kanta da boka FARTSI? Ku biyo ni a cikin labarin GIMBIYA SA'ADIYYA don jin bayanai game da abubuwa da dama.…

NANNY(Mai Reno.)

NANNY(Mai Reno.)

58,629 4,931 24

MARAINIYACE BATA DA UBA..SAI UWA..SUN TASO CIKIN WAHALAR RAYUWA...KWATSAM TA TSINCI KANTA AGIDAN WANDA TAKE KALONSHI AMATSAYIN UBA A MTSAYIN NANNY..YAZAMA GATANTA GABADA DA BAYA..RANA TSAKA YA ZAME MATA BAKIN KADDARARTA.…

Daugther of Rogers

Daugther of Rogers

245 36 3

Sandalyelere karşılıklı olarak bağlanmış iki asker dikkatle birbirlerine bakarlarken içeriye intikamcıların üç üyesi girmişti Tony, Steve ve Natasha. "Bağlı olduğunuz cihaz her yalanınızı ortaya çıkaracak." Tony'nin cümlesi üzerine iki asker birbirine bakıp gülmüştü. "Geçmişine dair ne biliyorsun?" Steve'in sorusu sandalyeye bağlanmış olan sarışın kadınaydı. "Her şeyi." Natasha ekrana baktıktan sonra bakışları Steve'e doğru dönmüştü. "Doğru." "Anlat." Tony konuştuğunda kadın bakışlarını ona doğru çevirdiğinde mavi gözlerindeki duyguları ayırt etmek oldukça zordu. "Şakaydı, bilmiyorum." Natasha'nın bakışları tekrar ekrana döndüğünde kaşlarını çatmıştı. "Ve bu da doğru." "Gerçekten bunun işe yarayacağını mı düşündünüz? Tahmin bile edemeyeceğiniz eğitimler almış iki ajanı bla bla makinesine bağlamak pekte mantıklı değil." "Steve'in kızı olduğu şüpheli." Tony alayla konuştuğunda Steve'in bakışları sandalyede oturan kadını bulmuştu. "Peggy'le uzun süreli ilişkimiz olmamıştı, ayrıca doğru olsaydı Peggy onu asla bırakmazdı." "Sonuç olarak ilişkiniz oldu Steve, dna testi yanılmaz. Özellikle benim yaptığımın yanılma ihtimali bile yok." Steve derin nefes alıp bir kaç adımla sarışın kadına yakınlaştıktan sonra yüzünü onun yüzüne doğru eğdiğinde saçını kulağının arkasına sıkıştırınca karşı sandalyede oturan adam hızla demir kolunu çeker kolunu zincilerden kurtardığında diğer elindeki kelepçeyi kırdıktan sonra Steve'e hamle şansı tanımadan boğazından tuttuğu gibi duvara yaslayıp dişlerinin arasından sinirle konuştu. "Ona bir daha dokunursan seni öldürürüm."…

ANYA BAIWA CE?

ANYA BAIWA CE?

10,503 197 11

Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa, " Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Babu damar dakatar da zuwan nata? Ya za'ay na gane ita ce dan na ɗauki matakin daya dace akanta?? " Boka ya ce, " Daga ni har sauran matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da yarinyar domin ita ɗin FILSIFI ce, abinda muke kira da FILSIFI kuwa aharkar bokan ci, tarraya ko haɗakar shuɗaɗɗun ruhika mabanbanta daga jinsi Mabanbanta, zo ki duba nan " ya ƙarasa faɗa yana buɗe mata wannan jan littafin da ke gefensa. Zanen wasu matasan mata ta gani guda uku sai dai duk cikinsu babu wacce zanen fuskarta ya fito sosai daga ƙasan kowacce anrubuta wani irin gwamammen rubutu, ta farko ya fara nuna mata yace, " Wannan da kike gani ita ce Muhaibish ita ta rayu ne tsawon dubbannin shekarun da suka gabata, Ƴar Sarkin jinsin Fararen Aljanun ƙarƙashin ƙasa ce, tunda take bata taɓa taka doron ƙasa ba " Zaro idanu Fulani Maryama tayi tana mamakin abinda ya faɗa, ta biyu ya nuna mata ya cigaba da cewa, " Wannan kuma sunan ta Kalimsiyat Ƴar sarkin fararen Aljanu ce amma ta nan doron ƙasa itama ta rayu atsawon dubbanin shekaru, acikin wani littafin bincike na karanta cewar ta yi rayuwa ne tun bayan zuwan Annabi Yusuf (A.S) ita kuma tunda ta ke bata taɓa nutsawa ƙarƙashin ƙasa ba a matsayinta na jinsin aljanu, kuma ita Kalimsiyat mace ce mara haƙuri mai faɗan gaske, kuma abinciken da nayi dukkan su biyun kashe su akayi bisa doron zalinci, kuma abinda zai baki mamaki kusan duka ruhinsu guda ne, sai dai banbancin nahiya da zamani. Sai ta Ukun su ita ce aka ce zata xo aƙarshen zamanin nan, sunanta Rayzuta ita ta haɗa dukkan abubuwan da waɗancen suke dashi harma da wanda suka rasa, ƴar baiwa ce me ɗauke da ɓoyayyun al'amura, ita kanta batasan da wannan baiwa tata ba."…

Bakuwar Fuska

Bakuwar Fuska

36,361 3,723 50

"Babu wata mace da nake son kasancewa da ita bayan ke Boobah. Babu macen da zan iya rayuwar aure koma-bayanki. Ki amince ki share mini hawayena, na yi alkawarin share miki naki hawayen, na baya, na yanzu, da kuma na gaba wanda ba na ma fatansu, zan kokarta yaki da su ta yadda za su nisance ki, ke da hawaye sai dai na farin ciki, da izinin Ubangijin al'arshi mai girma." Cewar Ishraq Sulaiman, hannunshi dafe da zuciyarshi da ke bugawa da sauri.…

DR NAMEER

DR NAMEER

613 3 16

A captivating story of romance,betrayal,passion,Guilt,heartbreak,love and mystery.…

NANNY

NANNY

24,952 2,108 24

MARAINIYA CE BATA DA UBA... SAI UWA SUN TASO CIKIN WAHALAR RAYUWA... KWATSAM TA TSINCI KANTA A GIDAN WANDA TAKE KALLONSHI A MATSAYIN UBA A MATSAYIN NANNY... YA ZAMA GATANTA GABA DA BAYA.. RANA TSAKA YA ZAME MATA BAƘIN ƘADDARARTA..…

Zuciya Da Hawaye

Zuciya Da Hawaye

2,309 203 24

Wani irin zufa mai yawa yake sharcewa a ko wace kusurwa ta jikinsa. Tun tana 'yar ƙanƙanuwar ta yake ɗauke da buri a kanta, yake so ya biya buƙatarsa gareta dan cimma wata manufa ta shi guda ɗaya da yake rayuwa domin ta a doron ƙasar nan.Amma ko da yaushe ya yi yunƙurin cimma burinsa a kanta komai sai ya taɓarɓare masa.Shin hala bata san ta hanyarta kaɗai ce dukkanin burikansa za su cika ba? Shin hala bata san ita kaɗai ce shamaki ga dukkanin buƙatunsa ba? Har sai yaushe ne zai cika burinsa? Har sai yaushe ne zai samu biyan buƙatarsa? Shin har sai yaushe ne dukkanin mafalkansa za su zamo gaskiya?Kallonta ya yi a karo na farko da ya kunna wutar ɗakin."Me ke tare dake ne da ke min katanga da buƙatuna Rumana?, Me ke tare dake ne?." Ya faɗa yana mai kafeta da manyan idanuwansa da suka zamo sak irin nata. Kasancewar ita ɗin kanta daga garesa aka sameta.Ku biyo ni dan jin cikakken wannan labari mai cike da sarkakikya iri iri. labari ne da zai iya taba zuciyar makaranci har ya iya fitar da kwalla a idanuwan mai rauni. zaku ji dadinsa zaku yi alfahari da shi zaku kuma soshi insha Allahu.…