AmeeraAdam60
SHU'UMAR MASARAUTAR Cmplt

SHU'UMAR MASARAUTAR Cmplt

5,227 101 10

"Na sadaukar maka da kishiyata a wannan daren, shi ne tukwicin da zan iya yi maka." Ba ta jira cewarsa ba ta ɗora rigar a jikinta. Bamaguje ya gyaɗa mata sannan ya furta. "Za ku iya tafiya." Umaima ta yi masa jinjina da hannu sannan ta sake ɗiban ruwan da ta wanke fuska da shi ta nufi wurin da Maimuna ke zaune hannunta ɗauke da kunamar da Bamaguje ya damƙa mata. Abin da suka aiwata a farkon zuwansu yanzun ma haka ne ya faru, sai da suka koma daidai wurin da suka buɗe ido suka gan su tun farkon zuwansu sannan, Fulani Umaima ta ɗaga ƙahon ta runtse ido ta busa haɗe da kiran sunan Bamaguje. Ƙamshin ɗakin Fulani ne ya ankarar da Maimuna dawowarsu gida, cike da girmamawa ta zube ƙasa ta furta. "Allah huta gajiya uwar gijiyata."…

BAƘAR DAULA

BAƘAR DAULA

598 12 10

Ƙaddara wata abada ce da take sarƙe da gangar jiki da ruhi! Ni tawa ƙaddarar salonta mai tafiyar kura ne, ko a tarihi ban taɓa riskar makamanciyar irin tawa ƙaddarar ba. Na fito daga cikin jinsin Maharba da Mafaruta, don haka na fi jin daɗin rayuwar cikin dabbobin daji akan mutane. Sai dai kash! Na tsinci ruhina a jikin wani gangar jikin da ba ta ahalina na Maharba ba, na rasa yadda aka yi nake iya rayuwa cikin jinsi biyu.…

'YAR ZAMAN ƊAKI CMPLT

'YAR ZAMAN ƊAKI CMPLT

4,716 279 10

Ledar kazarta ta nuna masa tana maƙale hannu ta ce, "Kazar nan ce take cizo na a hannu, kuma ni ka zo ka kwanta a nan." Da mamaki Khalid ya furta, "Kaza kuma? Gasasshiyar kazar ce take cizonki..." Khalid bai rufe baki ba ya ji ledar kazar ta bada ƙaraas alamun taunar ƙashi, da sauri Khalid ya sake buɗe wa sai dai ga mamakinsa yana buɗe ledar ya ga sai taunannun ƙashi, wasu ma an yi dugu-dugu da shi. Cinyoyin kazar ne kawai aka cinye tsokokin ba tare da an tauye ƙashin ba. Yana shirin yin magana ya ji Walida ta saki ƙatuwar gyatsa sannan ta ce, "Uncle zan sha ruwa." Khalid ya ƙwalalo ido waje ya ce, "Ina kazar cikin ledar?" Walida ta ce, "To ai sai na sha ruwa zan ci." Khalid ya sake bankaɗe ledar ya ce, "Ba yanzu na nuna buɗe kazar har kika ce ba gashin inji ba ce?" Walida ta sake sakin gatsa haɗe da ɗaukan tsinken sakace tana kwakwule haƙoranta.…

ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

1,950 63 10

Kuka haɗe da dariya ne suke ta shi a cikin dajin, zuwa can ta hango inuwar wata hallita na tunkaro ta, matsananciyar guguwa ce ke tashi bishiyoyi na kaɗawa da ƙarfa yanda kasan za su jijjigo daga jikin jijiyoyinsu. Cikin wani irin gwamamman yare ta riski muryar inuwar tana cewa, "Sai kin halaka ke da abin da yake cikinki, kin zama halakakkiya keda tsiron da ke cikinki." Ba ta yi aune ba ta fara jin abu na bin ƙafarta zuu! A daidai lokacin da ta ji wani irin nishi ya taso mata. Durƙushewa ta yi a wurin tana murƙususu, nan take wani irin kukan Jarirai mai haɗe da kukan Jaki ya fara karaɗe lungu da saƙon da ke cikin dajin tamkar zai tsage gida biyu. Sannu a hankali Jarirai suka fara rarrafowa suna zageta kamar ana zagaye wainar gero. Duk da halin da take ciki bai hanata yunƙurin tashi domin tseratar da rayuwarta ba, amma ina! Haihuwa ta tunkarota gadan-gadan nan take jaririn ya faɗo. Sannu a hankali ya rinƙa bin duk wurin da jini ya zuba yana lasa shi da sauran 'yan uwansa Jarirai, tamkar waɗanɗa suke da'irar ƙungiyar asiri. Raihan da ke durƙushe da sauri ta zabura kamar wacce aka ɗanawa ruwan dalma, tana yunƙurin tashi nan take mabiyiya ta faɗo. Kamar yanda Kura take ƙishirwar nama haka suka afkawa Mabiyyar kafin wani lokaci tuni suka gama da ita.…

DUBU JIKAR MAI CARBI

DUBU JIKAR MAI CARBI

8,330 272 13

Da sauri Yaya babba ta matsa baya tana zaro ido ta ce, "Dubu me nake gani kamar aski akanki." Dubu ta rushe da kuka ta ce, "Inno wallahi aski ya mini kuma wallahi ɗan iska ne." Cak Yaya Babba ta tana ƙarewa Dubu kallo sannan ta ce, "Dubu je ki can mu gani." Dubu ta tashi tana ƙobare ƙafafuwa saboda irin gwale-gwalen da ta sha. Ba su yi aune ba sai ga ni suka yi Yaya babba ta faɗa ɗaki ta rushe da kuka. Da sauri suka bi bayanta saboda kusan kowa bai ji daɗin abin da Aseem ya yi ba musamman Mahaifinsa, faɗa yake yi masa sosai sannan suka shiga ɗakin. Yaya babba kallonsu ta yi fuska a murtuke ta ce, "Garba ka tara mini ƴan uwanka saboda wannan ba maganar tsaye ba ce. Kuma idan har Aseem ya farke mini Dubu na rantse da Allah ba ita kaɗai ya yi wa illa ba, ya fi kowa shiga uku domin babu makarin maganin ƴan shafi mu lerar da za a bashi. Kai ni wallahi ban lamince ba ke Nafisa ke ce uwarsa wuce ki je ji bincike shi tas, don wallahi Idi ɗan wanzan ya mutu babu wani magani da zai karya laƙanin aikin, saboda aikin har da haɗin ƴan shafi mu lera." Tana gama maganar ta fisgo Dubu tana shafa mata suɗaɗɗen kanta ta ci gaba da cewa, "Ka ga yanda Kan Dubu ya sulle kamar bayan sulba. To kwarankatsa dubu idan har ka farketa kaima haka wurin zai shafe kamar bayan silba."Kallon-kallon aka fara yi da juna, jikin Hajiya Nafisa ya yi sanyi dukda ta san a tarbiyyar da suka bawa Aseem ba zai taɓa yi wa Dubu fyaɗe ba. Amma shaidar ɗan yau bata da tabbas, domin ɗa ne ka haifshe baka haifi halinsa ba. Babban abin da ya fi ɗaga hankalinta da ta ji an ce Aseem ɗin ta ya koma kamar bayan silba. Ita da take yi masa tanadin Yusra ƴar aminiyarta ya aura.…

WUUF HAUSA SERIES NOVEL

WUUF HAUSA SERIES NOVEL

847 103 10

Abuh bata damu ba ta ci gaba da jijjiga ƙafar tana cewa, "Chogal wallahi ka kiyaye ni, na rantse da Allah idan ka takura wata rana sai na jirge ƙafa na mayar da kai Audu gundul ba audu chogal ba." Tana gama faɗa ta saki ƙafar ta wuce cikin gida, sai a lokacin Abokansa suka ƙarasa suna masa sannu. Alhaji Audu Chogal ya jinjina kai yace, "Ƙwal uba ni yarinyar nan za ta yi wa lalata, ta jawa kanta da wata biyu na yi niyyar a saka rana amma wallahi sati biyu za a saka."…

JARIRI COMPLETE

JARIRI COMPLETE

15,931 1,065 25

A daren ranar da suka koma da daddare kimanin karfe biyun dare Inno ce ta fito fitsari ahanyarta ta dawowa, ta hango ƙaƙanin abu na tafiya idan yayi gaba sai ya dawo baya ya rangwaɗa kai gefe. A ɗan tsoroce Inno ta ce, "Toooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani da tsohon daren nan" ta ƙarasa magana tana haskashi da ƴar fitilarta. A zabure ta ja baya ganin jaririn Nusaiba ne tumɓur ko wando babu, washe mata baki yayi ya dafe ƙeya yana wani irin layi kamar wanda yasha ya maku, cikin wata irin murya ya cafe irin maganar Inno yace, "Tooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani da tsohon daren nan" tana faɗa yana wani irin tsalle kamar zai faɗo kan Inno, wurgar da butar tayi saboda tsoro ta fara gudu. Tsalle yayi ya caɓe zanin Inno har ya taɗe ta ta faɗi da rarrafe ta dingan rarrafawa tana ƙwala ihu, lokacin da ta ƙarasa ɗakinsu tuni ta daɗe da wurgar da zani daga ita sai ɗan fatarinta.…

ANYA BAIWA CE?

ANYA BAIWA CE?

9,156 192 11

Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa, " Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Babu damar dakatar da zuwan nata? Ya za'ay na gane ita ce dan na ɗauki matakin daya dace akanta?? " Boka ya ce, " Daga ni har sauran matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da yarinyar domin ita ɗin FILSIFI ce, abinda muke kira da FILSIFI kuwa aharkar bokan ci, tarraya ko haɗakar shuɗaɗɗun ruhika mabanbanta daga jinsi Mabanbanta, zo ki duba nan " ya ƙarasa faɗa yana buɗe mata wannan jan littafin da ke gefensa. Zanen wasu matasan mata ta gani guda uku sai dai duk cikinsu babu wacce zanen fuskarta ya fito sosai daga ƙasan kowacce anrubuta wani irin gwamammen rubutu, ta farko ya fara nuna mata yace, " Wannan da kike gani ita ce Muhaibish ita ta rayu ne tsawon dubbannin shekarun da suka gabata, Ƴar Sarkin jinsin Fararen Aljanun ƙarƙashin ƙasa ce, tunda take bata taɓa taka doron ƙasa ba " Zaro idanu Fulani Maryama tayi tana mamakin abinda ya faɗa, ta biyu ya nuna mata ya cigaba da cewa, " Wannan kuma sunan ta Kalimsiyat Ƴar sarkin fararen Aljanu ce amma ta nan doron ƙasa itama ta rayu atsawon dubbanin shekaru, acikin wani littafin bincike na karanta cewar ta yi rayuwa ne tun bayan zuwan Annabi Yusuf (A.S) ita kuma tunda ta ke bata taɓa nutsawa ƙarƙashin ƙasa ba a matsayinta na jinsin aljanu, kuma ita Kalimsiyat mace ce mara haƙuri mai faɗan gaske, kuma abinciken da nayi dukkan su biyun kashe su akayi bisa doron zalinci, kuma abinda zai baki mamaki kusan duka ruhinsu guda ne, sai dai banbancin nahiya da zamani. Sai ta Ukun su ita ce aka ce zata xo aƙarshen zamanin nan, sunanta Rayzuta ita ta haɗa dukkan abubuwan da waɗancen suke dashi harma da wanda suka rasa, ƴar baiwa ce me ɗauke da ɓoyayyun al'amura, ita kanta batasan da wannan baiwa tata ba."…

SHAFAFFU DA MAI

SHAFAFFU DA MAI

237 24 5

LITTAFIN GASA NE NA MATASAN MARUBUTA DAN ALLAH MASOYA KU NUNA MUN ƘAUNA AKWAI RANAR DA ZASU BAMU LINK MU BAKU ZAKU DANGWALA MANA VOTE, INA FATAN ZAKU BANI HAƊIN KAI.…

WANDA BAI JI BARI BA....

WANDA BAI JI BARI BA....

3,638 272 22

Iska ce ta fara kaɗawa ahankali ta fara hango waɗansu irin manyan ƙwari masu kama a fasalin maguna sai dai kowanne su maƙale yake da fukafuki a gadon bayansa, sautin tafiyar Dokin ce ta ƙara kusantota hakan ne yasa ta maida kallonta ga inda tafi jin sautin na matsowa. Kamar yanda ya bayyanar mata a karan farko wannan karan ma wata zabgegiyar Abaya ta hango baƙa, tsawon abayar ya kece tsawon bishiyoyin dake cikin dokar Dajin sai da ta ɗaga kanta sama sosai sannan ta hango dai-dai kansa sai dai kansa ne amma babu alamar fuska ajikinsa. Ƙarasowa yayi gabanta ya tsugunna cikin murya mara daɗin sauraro ya fara magana, " Bingirsima baguar kinbasu wakisfatminar, kisasu biragu kilbasu tattarakimbas wajihagar, farafafus bintigad gurmanas YUSRA? harbaskila mindadu bar washbasbismas shizas kima bu warsa? " ( A karo na biyu ina ƙara miki barka da zuwa cikin daularmu nida ahalina, da sannu zan gabatar da ke ga sauran iyalaina domin kusan juna keda su ina fatan kina jina YUSRA? Ga ƴaƴana nan sun fara zuwa gaisheki ina fatan zaki basu kulawa ? ) Wannan zabgegen Aljanin ya ƙarasa maganar yana nuna mata waɗannan hallittun masu fasalin Maguna da fukafukai. Yusra da tuni hawaye yake wankewa fuska ta ƙara durƙushewa ƙasa cikin sigar magiya tana faɗin, " Ka dubi girman Allah da Annabi ba dan ni ba, ba dan halina ba kayi haƙuri ka maidani cikin mutane dan Allah, wallahi bazan iya rayuwa cikinku ba na tuba dan Allah kamun rai " Miƙewa tsaye yayi sannan yayi taku biyu zuwa uku sannan ya waigo ya ce mata, " Hargigas markusa bayas tinga " ( Tashi tsaye kije jikin waccen bishiyar kukar ) Yusra har tuntuɓe take da sauri ta miƙe tsaye saura kaɗan Abayar jikinta ta kayar da ita, jikin bishiyar taje ta tsaya tana sauraron abinda zai sake faɗa, batayi aune ba ta tsinkayi muryarsa yana faɗin. " YUSRA Lilbas faragaras binsafa walgibas zalzulfat kinari " ( YUSRA kalli Abayar jikinki da kyau, idan har kin iya cireta daga jikinki…

INDO SARƘA COMPLETE

INDO SARƘA COMPLETE

72,799 5,513 57

Cikin dare lokacin ƙafa duk ta ɗauke banda kukan tsuntsaye ba abunda yake tashi, alokacin ta farka daga bacci kayan wajen Goggo tasa ta ɗauko zumbulelen farin hijabin tasa, kwandon kayan kwalliyarta da shafe sati bata buɗeshi ba, ta buɗe ta ɗauko hoda ta zazzaga ta shafe fuskarta, hannu da ƙafafuwa Ludayin miyar Baba Huwaila da tun rana ta ɓoyeshi ta ɗauka ta sa a hijabi, ƴar fitilarta ta ɗauka ta fito daga ɗaki saɗaf-saɗaf ta je wajen bakin ƙofa ahankali ta zare sakata ta fice, kamar Aljana ita kaɗai ce a waje haka ta samu ta ƙarasa bayan katangar gidan Mai Gari ( _Dake gida huɗu ne tsakanin gidana Baba Huwaila da na Mai Gari_) ta kamata ta ɗane ta dirga. A hankali ta ɗaga labulen ɗakin Mai Gari ta shiga ta same shi a kwance baccinsa yake hankali kwance, toshe bakinta tayi tana dariya ƙasa-ƙasa musamman da ta tuna irin muguntar da zata yiwa Mai Gari, sai da tayi ta gama ta koma saitin kan Mai Gari ta zaro ludayin miyar ta dai-dai ci kan sa ta bashi ƙwaaal, azabure Mai Gari ya tashi yana susar gurin baya yaja ganin mutum tsaye cikin fararen kaya. Indo canja murya tayi shigen ta Goggo sannan ta fara magana, " Ni ce Goggo Kakar Indo Sarƙa nazo tafiya kai cen makwancina tunda cin Amana zakayi " Mai Gari cikinsa ne ya juya baiyi aune ba sai ji yayi ɗumi na bin wandonsa, Indo na ganin Fitsari na bin ƙafar Mai Gari ta gimtse Dariyarta ta kuma cewa.....🥱…

ASEELA COMPLETE

ASEELA COMPLETE

20,552 1,692 52

Ƙwarangwal ɗin suna tafe wani irin ruwa mai yauƙi na fita daga gaɓɓan jikinsu tamkar waɗanda aka kunna fanfo ajikinsu, daga kowanne ɓangaren hallita akwai shugabansu wanda shi ne yake kan gaba su kuma suna biye dashi abaya, hannu kowanne shugaba ɗauke yake da wani farin ƙyale da jikinsa yake da ɗishi-dishin jini, ahankali ta fara ɗaga ƙafarta tana ƙoƙarin ja da baya da niyyar guduwa sai dai nauyin jikinta shi ya hana ta gudu har suka ƙaraso inda take, mararta ce ta ɗan karta mata bayanta ya riƙe sannu ahankali ta tsugunna ta duƙa agurin wani irin azababben ciwo na cinta, jeruwa suka yi sahu-sahu sannan suka fara zagaye ta suna faɗin wasu kalmomi da sam bata fahimtar mai suke faɗa, " YAMDUMISA! YAMDUMISA!! YAMDUMISA BISRATIK KUZAR!!!, KIMBASA MIN! KIMBASA MIN!! KIMBASA MIN MAR FAZKINBAT!!! " ( BARKA! BARKA!! BARKA DAI SHUGABA!!!, DAWOWARKU NASARA CE! DAWOWARKU NASARA CE!! DAWOWARKU NASARA CE TARE DA FANSA!!! ) haka suka dinga zagayeta suna maimaita kalmomin bakinsu shugaban ɓangarori biyun masu ɗauke da farin ƙyallen nan suna zazzaga mata wannan kyalen akanta, ciwon da take ji ƙara tsananta yake banda ihu ba abinda takeyi sai kiran sunan KABEER take tana maimaitawa, idan abun ya kuma tsananta ta kuma kiran Kabeer ko Habeebee amma ko gezau basu fasa wannan surutan nasu ba kuma basu fasa zagayeta ba suna yarfa mata wannan farin ƙyallen ba, wani lokacin ma wannan ruwan mai yauƙi na ɗiga ajikinta, ita bata ma san suna yi ba saboda azabar ciwo fatanta kabeer ya kawo mata ɗauki. Ta ɗan ɗauki lokaci ahaka kamar minti talatin ahaka sai ji sukayi kukan jariri alokacin ta galabaita sosai amma ahaka take yunƙurin ɗaukar abinda ta haifa dan neman tsira daga garesu, sai dai kafin tayi wani yunƙuri tuni shugaban ƙwarangwal ɗin nan ya kai hannu yayin da shima shugaban mai mummunar hallitar shima ya kai hannunsa, atare suka suka ɗago jaririyar kowanne ya riƙe hannunta ɗaya yana faɗin, " KAGARSIN BIDA, KAGARSIN BIDA LANBISMA GIRUS " ( KA…

MARWAN COMPLETE

MARWAN COMPLETE

19,789 2,354 35

Safwan yace, " dama inasan ganin Nazir akwai muhimmiyar maganar dana zo da ita nake san mu tattauna " yana gama faɗa mahaifiyar su Nazir ta rushe da kuka sannan tace, " Nazir baya magana hasalima baya cikin hayyacinsa baisan waye ma akansa, kallan yayan Nazir tayi ta ce, " kai je kaxo mai da Nazir " nan take ya tashi ya fice sai gashi da wheel chair da Nazir aciki sai kallan mutane yake yana zubda hawu hannuwansa da ƙafafu gaba ɗaya sun shanye, Safwan na ganinsa cikin tashin hankali yace, " Wannan ne Nazir ɗin mai ya sameshi? " wani sabon kukan mahaifiyar su Nazir ta ƙara sawa, cikin ƙarfin hali yayan Nazir ya fara magana, " aranar da mahaifinmu ya rasu Nazir yace mana zaije gidansu Maryam, to bayan y dawo muna zaune sai gani mukayi ya zabura yana ihu yana cewa bazai kuma ba, sai kuma muka ga yana ta surutai daga haka kawai sai gani mukayi ya yanke jiki ya faɗi, shikenan har yau ka ganshi ahaka kullin magani ake bashi amma ba sauƙi kullin ciwon gaba yake yi. " gaba ɗaya jikin Safwan ne yayi sanyi cikin sumutar baki Safwan yace, " tabbas Marwan ne " karaf yayan Nazir yace, " wai waye Marwan ɗin nan naji lokacin da yake ta sumbatu yana cewa Marwan kayi haƙuri, ko kuma abokin aikinsu ne dan wannan ciwon ba tantama sihiri ne. " Safwan gaba ɗaya tausayi da tsoron halin da Nazir ke ciki ya kama shi.…

GIMBIYA FADEELA

GIMBIYA FADEELA

623 26 2

labari ne akan wata yar sarki da Wasu Manyan Aljanu guda biyu da suke rayuwa acikin masarautar batare da ansani ba, ƙawata labarin baxai bayyanu anan ba ku biyoni ciki dan jin mai labarin ya ƙunsa.…

ƊAN BA ƘARA COMPLETE

ƊAN BA ƘARA COMPLETE

6,965 747 15

Salati goggo ta rafka tana ja da baya cikin tsoro take Fad'in, " me nake gani ni hansatu kamar danyen kifi ke mejidda zo ki tayani gani " mejidda atunaninta rikicin Goggo ne tana daga zaune ta cewa Goggo, " tunda kifin Kika gani ay shi d'in ne, kema Goggo Banda abinki kifin k'afa garshi da zai shigo cikin gida bama nan, idan nace kinfiye rigima kice zan gaya miki magana " ganin kifin na yi Mata murmushi yasa Goggo ta K'ara rafka wani salatin tana sakin tunkunyar tana yowa gaba, mejidda dariya takewa Goggo harda rik'e ciki tace, " Goggo wai me yake faruwa ne Dan Allah ko kunyar gudu bakiji ba? gudu kikeyi amma kamar me rawar Etigee" Goggo Bata bi ta Kan mejidda ba ta rabe ajikin katanga tana leken tunkunyar data jefar ,wani Kan kifi ta hango suna had'a ido ya K'ara kashe Mata ido daya😉 sannan ya washe Mata baki😃, daskarewa Goggo tayi cikin tashin hankali ta mik'a hannu tana nunawa Mejidda kifin, da saurinta Mejidda ta K'arasa gurin ba shiri ta dakata musamman yanda taga Kan kifin Yana wangale Mata baki, k'ank'ame Goggo tayi tana ihu cikin tashin hankali Take Fad'in, " wayyo Goggo Kan kifi Yana wangalen Baki zai cinyeni, ki taimake ni Goggo na yi gamo da Aljanin kifi ". Ita kanta Goggo abun tsoro yake Bata Amma sai ta D'an dake ta K'ara lek'awa Amma ga mamakinta sai taga tukunyar wayam, ko irin alamun jinin kifin babu. Goggo ta Jima tana kallan tukunyar Amma ko d'ishin kifi Bata gani ba, zame mejidda take Shirin yi daga jikinta caraf ta Kara k'ank'ame Goggo kamar za'a k'wace Mata ita, itama goggo Bata gama sake wa ba suna cikin Haka ba zato wani almajiri ya rafka ba ra, " Waaahiiideeeeeee " Me jidda ce ta Fad'a aguje cikin d'aki tabar goggo jikinta sai rawa yake ta Mara Mata baya, kafarta D'aya d'ingisa ta takeyi Amma alokacin Nan tuni ta take ta bata sani ba, Almajirin shi dariya ma abin ya bashi yi yake yana k'yak'yatawa, goggo dake d'aki ta cika fam Dan Jin yanda Almajiri ke b'ab'b'aka dariya, lek'awa tayi Dan tayi Masa magana…

TSANTSAR BUTULCI COMPLETE

TSANTSAR BUTULCI COMPLETE

21,906 1,720 47

Ko daga jin sunan littafin basai na baku labarin irin BUTULCIN da za'a tafka acikinsa ba, labari ne me tab'a zuciyar me karatu ya kunshi darasi acikinsa, Kuma izna ne ga azzaluman mutane, kubiyo zasu fahimci abinda nake nufi.…

SANADIN RAGON LAYYA CMPLT

SANADIN RAGON LAYYA CMPLT

3,083 247 10

Bil hakki mlm kabiru ya dage yake ta karantowa hajara ayatulkursiyyu, ya karanta yafi a irga idan ya karanto wannan aya yana kaiwa karshe zai karanto wata, duk atunaninsa aljanune suka make hajara, mamaki ne ya kara cika shi ganin takalmin hajara wari daya akafarta wari daya kuma igiyar ta tsinke, buta a tuntsire ruwan cikinta ya tsiyaye tas, surutai hajara ta cigaba dayi bakai ba fasali, hakan ne yasa mlm kabiru ya kara daga murya cikin azama yana karanto mata ayoyin kur'ani yana tofa mata. Hajara cikin fusata tace, " mlm wai sai tofeni kake yi ni kabarni inji da abinda yake damuna "Dan dakatawa yayi da karatun yana karewa hajara kallo, tsab muryarta take da alama ba wasu jinnu da suke damunta, zaninta ya janyo ya rufe mata cinyoyinta dasu, yunkurawa hajara tayi ta tashi zaune tana zubda kwallah.Cikin tashin hankali Mlm kabiru yace, " hajara lafiyarki me ya sameki cikin dare kike wannan ihun, nasha gaya miki idan zaki kwanta ki dinga tofe jikinki da addu'a, kuma idan mummunan mafarki kikayi basai ki karanta addu'a ki koma bacci ba, idan baccin ya gagareki sai ki yo alwala ki gabatar da sallah ki fawwalawa Allah lamuranki, to hajara kodai gamo kikayi dan naga buta kusa dake " mlm kabiru ya karasa magana yana kallan hajara da fuska ta hade hawaye da majina.Hajara girgiza kai tayi sannan tace, " babu ko daya malam "Mlm kabiru kuluwa ya farayi cikin fada yace, " amma ba abinda yake damunki kikaxo tsakar gida cikin dare kina wannan haukan salan mak'ota suce wani abun akai miki ko azaci aljanu kika hau, cire makota ma yanxu da yaran nan sun farka suka fito suka ganki da dan kanfai me zaki ce musu, sai ki tashi ki kamwashe tsummokaranki kiyi gaba, ina cikin baccin na me dadi kin tashe ni " Hajara bakin ciki ne ya cikata, zafi biyu ga na rashin rago ga sababin da mlm kabiru yake mata, rushewa tayi da kuka cikin kuka tace, " mlm rago ne, wallahi ragon nan ne " sai kuka yaci karfinta ta kasa karasa maganar. Guntun tsaki yaja sannan yace, " yanxu hajara…

YAWON SALLR HJY IYA Complete

YAWON SALLR HJY IYA Complete

2,569 467 25

Gudu yakeyi iya karfinsa amma saboda yanayin girma ga tsufa lokaci guda suka cin masa.A tsakiya suka saka shi suna kokarin rike hannuwan sa, dan tsoho yayi wani kukan kura cikin karaji irin yanda jariman india sukeyi idan suka fusata, yasa gwiwar hannuwan sa ya kai musu duka yana fadin, " wallahi bansan da makiya nake tafe ba sai yanxu idan kuka maidani cikin motar nan ban yafe muku ba.Ku sake ni na karasa bichi a kafa, idan kuka kaini mota wallahi alhakin mutuwata a wuyanku yake, cikin hanzari suka kara matsowa zasu kama dan tsoho, aykuwa ya yi sauri ya matsa baya hadi da buga kafa daya, ya kara kwalla kara yana fadin, " yeeeeeeeee ku matsaaaaaaaa ko in ma ke kuuuuuuu, ya karasa fada yana dunkule hannuwa har huci yake. Daya daga cikinsu ya kallin dayen yace, " wai kuwa Anya bazamu kyale tsohon nan ba yaje yayi ta tafiyarsa, tunda anasan ceton rayuwarsa yana san yayiwa mutane illa, kana ganin yanda ya kaimun duka a gefen fuska badan na kauce ba da ya gwabjeni yayi mun mahangurba, " kai haba yanxu tsohon nan ne zai gagaremu, idan aka ce mun kasa kamo shi ba muji kunya ba dan Allah rabu dashi bari kaga muma karfi zamu nuna masa, muna zuwa ciccibarsa zamuyi farat daya zamuyi masa. Aykuwa suka tunkari dan tsoho me buhu, yana ganin sunyo kansa gadan-gadan ya fara kai duka ta ko ina, yana yi yana ja baya sai kuma yayo gaba kamar zai doko wani daga cikin su, yan da kasan yana filin danbe.Basu bi ta kansa ba, sukub haka suka sun kuci dan tsoho suka mammakure hannusa a hammatarsu sai wutsul-wutsul yake da kafafuwa, yanayi yana wani karaji shi bai yarda ba dole kwacewa zaiyi daga hannunsu.Bakin motar suka karaso suna kokarin saka dan tsoho sai fisgewa yake yana ciccijewa har suka samu suka tura shi ciki, wani daga gefe ya dan leko su yana fadin, " to ita ma iya ku sata aciki man, kunga kun huta, idan fa kukayi sake tsohon nan ya kubce wallahi dawa zai shiga, dan na lura motar nan ta tsora tasu dayawa, juyawa sukayi zasu dauko hjy iya.…