RUWAN DAFA KAI 91~95
Na SUMAYYA DANZABUWA
"Banason kukan nan yana damuna"shine abinda yayita yiwa Abu yawo aka tanata nanatawa,"haka baban Amin ya damu da ita dama?to ya akayi ma yasan tayi kuka dazu,ko yasan halinda take ciki ayanzu?meyasa zai damu da ita??haka dai tadinga tunane tunane duk tabi tashiga wani hali don ta ma kasa fuskantar yanayin dakuma abinda ke shirin faruwa,ta bangaren yusuf shima yanacen yanata kallon wayar yana jiran reply dinta amma shiru,"ko tayi baccine bata gani ba,ko kuwa dai dagaske bata iya karatun ba bare rubutun yadda yake tunani?"kai Allah yasa dai bahaka ba,don zanso mudan zanta a darennan konayi bacci mai dadi"yace aranshi tardeda saddaqarwa tunda ankusa minti goma aha biyar da tura sakon nashi amma shiru hakan ne yasashi tunanin duk yadda akayi tayi bacci,yana shirin ajiye wayar ya kwanta ne yaga message yashigo"Nagode sosai Allah ya saka da alkhairi"wani mugun dadi yaji aranshi tabbas yayi underestimating yarinyar nan,bai zata takai haka ba,dubada yadda ta tsaro rubutun babu ko kuskure aciki,spelling da komai daidai,tabbas hakan ya matukar birgeshi,ita kuwa Abu saboda rashin sabo dakyar ta rubuto message din saboda wayace dabata saba da ita ba kuma karonta ne nafarko shiyasa ta wahala,amma dole a sannu zata saba komai lokacine,"Amin,saida safe kiyi bacci Allah yatashemu lafiya"ya tura mata,itadai kasa reply tayi duk wani iri take ganin abin,saboda abune dabata taba tsammani ba ace mutum mai ilimi dan gayu,mai kudi kyakkyawan namiji irin yusuf yana nuna mata wannan kulawar a matsayinta na maiaikinsu shida iyalinshi itada ba yar kowan kowa ba,tasan dai mutumin kirki ne a iyakar zaman datayi agidan saboda ita kanta tasan yadda yake shanye wulakanci da rashin mutumci irin na farida duk hakurinta(Abun)wani lokacin gani take inda itace shi saita dinga maida martani amma inaa baya taba daukan mataki kamar wanda aka asirce,hasalima idan tana masifar baya biye mata,sau dayawa saidai ya girgiza kai yace Allah ya kyauta,duk tana lura dahakan ita,to wannan halayyar ita tasa take mishi kallon kamilin mutum mai mutumci da hakuri,gashida rikon ibada,bakuma yataba nunawa ita maiaiki ce sabanin yadda farida take nuna mata kamar ma ita din wata halitta ce ta daban.
Yusuf yanacen yana jiran reply,ya juya ya kalli farida da ta dade da shanya hakora sai minshari take,harda yawun bacci,murmushi yayi dabaima san dalilin yin hakan ba kawai dai yasan ya tsinshi kanshi cikin wani sabon yanayi,cigaba yayi da latsa wayarshi,"Allah yabamu Allhairi ya tashemu lafiya"yaga Abu ta turo,murmushi yayi a fili harda washe hakora kamar tana gabanshi yana ganinta,sai yanzu kwakwalwarshi ta nusantar dashi dalilin dadewar yarinyar wajen yimishi reply nacewar bata saba da waya bane shiyasa,"Allah sarki dasannu dai,"yasha alwashin zai dinga yawan mata message yadda zata koyi typing dasauri,yakuma wayar da ita ahankali,dahaka ya ajiye wayar ya kwanta yayi baccin dadi cikeda farinciki da nishadi.
Har mafarki yayi wai sunyi aure suna shan soyayya.
Haka lamura suka dinga kasancewa kullum idan yusuf baya gida yakan kira Abu sau ba adadi kafin yadawo acewar wai yana kira ne yaji idan komai lafiya,musamman Amin,tun bata iya sakin jiki suyi hira harsuka fara sabawa yau da gobe sai Allah,itama kuma idan taga bai kira ba kamar yadda yasaba sai ta fara damuwa to amma ko meyasa oho?wannan tambayace datasha tambayar kanta amma dai har yanzu takasa samun ansa.
Farida nashigowa gida yau ta hango Su Abu akan tabarma itada Amin,gawani mutum akan kujera azaune,da alamun dai karatu sukeyi,tunda ga Quranai nan ahannayensu,kwafa tayi cikeda rashin fahimtar abinda ke faruwa ma,parking tayi ta fito cikeda masifa da balai a tattare da ita tacika ta batse nema take kawai ta fashe,yusuf yanajin shigowarta yayi saurin fitowa don yasan yanzu saita iya aikata abinda bashikenan ba ta tapka rashin mutumci,"Baby"yadan kirata tajiyo ta zabga mshi wata harara don tabbas da saninshi ake wannan lamarin,"meye?"ta bashi ansa"bismillah shigo daga ciki"yace tareda wangame mata kofar, ganin harta nufi inda suke karatun,"kamarya inshigo daga ciki meke faruwa ne,waye wannan din?"tace fuskar nan cikeda iko da mulki,"kishigo mana don Allah zan miki bayani"yusuf din yace cikin kasa kasa da murya kamar mai munafurci wai don Kar malam din yajisu,tsaki taja cikeda takaici,kafin ta ankara sai ganin yusuf tayi yakamo hannunta yashige da ita ya rufo kofar,binshi kawai tadingayi da ido cikeda mamaki,"sakeni mana meye haka zaka wani kamoni kamar wata yarinya agaban yara"tace a hasale,"toh nasakeki"yace bayan ya saki hannun nata,jakarta ta wurgar akan kujera hadeda key din"kayimin bayanin abinda ke faruwa acen"tace cikin masifa tareda nuni da inda su Abu suke karatun ta window tunda ana hangosu,"karatu sukeyi mana"yabata ansar a takaice bayan yanemi waje yazauna,"wat?kamarya karatu islamiyyar kuma fa?ko tafi karfin taje islamiyyar tunda ta shahara,?"takara cikeda rashin fahimta,"babu laifin yarinyar nan,laifina ne,amma kinsandai koba komai yarinyar nan amana ce agaremu ko?gani nayi masu gadin unguwarnan dawasu en iska na daban,suna neman su sa mata ido kowa fa yasakata agaba"saboda ga Aishwarya Rai ko?wannan harwani kyau ne da ita dazaawani sakata agaba?meye wani abin birgewa a tattare da ita dagar zai wani ja hankalin namiji?kodayake duk meye dama daidai dasu suka gani shiyasa"tayi maganar cikeda izgili,yusuf baiji dadin zancen ba amma dai ya dake saboda bashida ikon nuna bacin ranshi a yanzu,"duk abar wannan,zancen ai ba sai mace tanada kyau maza suke binta ba,farin jini ma ai is something,to cut it short dai saboda gudun kada sani abu yazo yafaru mara dadi,shiaysa kawai naga gwara in samo mata mai mata karatun agida tunda baa hanata karatu ba sharadin mama ne,"kallonshi kawai take tunda yafara maganar har yakai aya,wata yar dariya tayi wadda duk wanda yagani yasan tarainin hankali ce,"wannan ne kawai dalilin?nace wannan ne kawai silly reason din?wai kai me kake nufi ne da lamarin yarinyar nan?yusuf the rate at which kafara zakewa akan mai aikin nan kuma yana nenan yafara bani haushi fa,ina ruwanka da sabgarta ko kana mantawa ne da kalamanka na baya?kuma ma ni danake da iko da ita shikenan ban isa kafadamin abu ba saidai kawai inga ka aikata?ko kana mantawa nima gidan nan nawa ne?ta inda take shiga bata nan take fita ba ta mugun fusata taji haushi,yusuf yasan bai kyauta ba wannan karon tunda da gaskiyarta ko ba komai itama ai tanada iko bai kamata kawai ace taga abuba bazata to amma kuma me?tsakani da Allah yasan halinta babu yadda zaayi yafada mata kudirinshi akan hakan ta yarda shiyasa yanke hukuncin shine kawai mafita,kuma Ahalin daake ciki yadda ya zurfafa da soyayyar yarinyar,Fitar datakeyi da kulata dakowane gaja yakeyi yana sosa mishi rai,yarinyar nan aurenta yake shirinyi yazama dole ya killaceta"Au wato ga banza tana magana,shine kanajina zaka min shir....","kiyi hakuri nasan ban kyauta ba,"ya katseta,"wallahi amana kawai nake kokar....."haka akayi akan wayar nan fa rannan,yarinyar nan ko kai ka haifeta sai haka,"tacigaba da masifa,"kiyi hakuri karatun qurani ne muma fa zamu samu lada"tsaki taja cikeda takaici,tayi hayewarta sama,don ta fuskanci yana neman ya raina mata hankali,dama ba zancen daukan mayafi da jakar data ajiye wannan aikin Abu ne ita take kwashewa ta kaisu.
Murmushin jin dadi yayi afili tareda komawa bakin windown yana hangosu suna karatun,dama wani dattijon malami yasamo,donma kar ya samo wani dan saurayi matashi yace yanasonta azo ana samun matsala musamman idan yasan aiki take agidan don mutane akwai rainin hankali,shiayasa ma bai fadawa malamin ba shima don kar asamu matsala ya zata zai iya rainata yamata gani gani, shiyasa ma yace kanwarshi ce.
Farida na zaune tana danne dannenta a computer,saiga kira yana shigowa taga an saka shegiya 2,mamakine ya isheta,idan zaku iya tunawa masu karatu a baya akwai numbobi data kwaffa daga wayar yusuf wayanda suke turo mishi da sakonnin soyayya to numbobin guda hudu ne haka tabi tayi saving dinsu shegiya 1-4,kin daukan wayar tayi tabarta tanata ringin,ganindai kiran bazai kare bane yasa ta dauka a fusace daniyyar taci mutumcin kowacece,batayi magana ba tana jiran taji muryar shegiyar,"au bazakiyi magana ba,farida kenan,"take tagano mai maganar,"ko kinyi magana ko bakiyi ba hakan bazai hanani fadar abinda nayi niyya ba,nakirane in shaida miki soyayyar danakewa mijinki yusuf h......"dakikiyar banza kawai kinyi kadan wallahi munafuka algunguma",tuntsurewa akayi da dariya daga dayan bangaren,"wallahi farida tunda Nayi ido hudu da yusuf mijinki naji duk duniya babu namijin dazan iya rayuwa dashi inba shi ba ki tambayeshi kiji ai yasan....."idan kika sake kirana sainaci ubanki gloria wallahi Allah kinji ma na rantse mara mutumci yariska,mara kunya wallahi inda nasan haka kike t....."ko ke inci naki ubanba shegiya,bakida wani sauran mutumci a idona farida kidaina mantawa Nawanke miki pant,to wane raini kuma?,gargadi daya zan miki idan baki bar azabtar min da masoyi ba yadda kika saba saina"...."mtswwww"farida taja dogon tsaki tareda kashe wayar a fusace,tayi blocking number,tana huci,wasu hawayene zafafa suka zubo mata,wannan wane irin raini ne? lallai tayi sakaci da lamarin yarinyar nan tun filazal,itama mai yakaita bawa mai aiki undies dinta ta wanke,tabbas lokaci yayi dazata daina bawa Abu wankinsu itama tunda abin raini yake jawowa,"ki tambayeshi kiji ai yasani"shine abinda yadinga mata yawo aka.
Ai bata tashi daga wajen computer ba kuwa yashigo da Amin a hannu sun dan fita,Abu kuma na kitchen tana girkin dare,"aa aikin ne dai ake tatayi harmunje mundawo kina nan ?"yace da ita cikeda tsokana,"meaysa zaka boyemin?"tayi maganar a fusace batare da ta kalleshi bama,"boye miki me?wani abin ne yafaru?"yace cikeda rashin fahimtar lamarin,"dama kasan gloria ce take turo maka wayannan sakonnin shirmen soyayyar amma kacemin bakasan ko waye ba meyasa zakamin karya?"tace afusace,don dabatayi niyyar magana ba amma jin glorian tace wai ai yasani shine yasa ta harzuka,kuma bayan data tambayeshi lokacin dataga message din a wayarshi cewa yayi baisan kowacece ba to meyake nufi,yar dariya yayi,"wace gloriar wai?""bangane wace gloria ba da gloriar har dubu nawa kasani,?"ta hayayyako,"girgiza kai yayi kawai,ya kwalawa Abu kira,"karbeshi ya mikamata Amin "muje sama muyi maganar acen"kawai yace tareda tafiya tunda ya tafi dai tasan ba yadda zatayi dolene tabishi indai har tanason ayi balain,shikuma yayi hakan ne don karbAbu tagani bare taji abinda zaace,wanda hakan kuwa ita farida bawai damuwarta bane,agaban kowa tapka rashin mutumci take,batasan hakan ne ummulaba isin janyo raini ba magana agaban koma waye.
"meyasa zaka boyemin meye amfanin hakan?of all mutane ma gloria?bayan kai kadinga k....."wai wannan wane irin zancene kikeyinshi bako dadin ji haka,ni wallahi nama rasa gane inda aka dosa,kimin bayanai filla filla ko na fahimta"yace tareda gyara zama ya fuskaceta alamun ashirye yake yaji duk abinda zata fada,"messages din danagani awayarka kwanaki nayi coping numbers din daakaturo dasu nayi saving dazu sai gashi an kirani da num wai ashe yariskar yarinyar nance gloria,nan ta kwashe duk abinda gloria tafada mata tafada mishi,"to meye abin tada habkali ne a wannan zancen?yarda kikayi ne wai ko me shine abinda ma bangane ba ni?"yace cikeda mamakinta,"to ga abinda tacemin,kuma ko yadda kake nunawa ka tsaneta hakan ai ya isa ya...."enough,ke kanki kinsan cewar ko mata sun kare aduniya babu abinda zanyi da ita,kuma messages din daake turowar nibban ma taba sanin waye ba yarinyar nan bawai numta bace dani,kuma datake rubuto shirmenta bama karantawa nake ba,ni wallahi kinma ban mamaki dawai har wannan yarinyar zata gaya miki wannannrainin hankalin ki yarda"yace tareda dankishingida a kujera,"wallahi na tsani yarinyar nan ta batamin ra...."kyalkyalewa da dariya yusuf yayi,"yau kuma?keda gloriar taki?yadda kika dinga nunawa fa akan yarinyar nan agidan nan b....."ai ba zancen da ake ba wanan zancen yanzu ne,tunda abin hakane raini yafara shigowa tsakani,Yazama dole in karbi wayar yarinyar nan(Abu),don bazai yiwu ba bayan an sallameta itama tazo tana kirana har ta naimi ta rainani"waceyarinyar kenan?"yacce bayan sarai yagane abinda take nufi,"zainab mana,h..."to kekuma banda abinki ta ina zaki hada zainab da gloria,ai ni aganina wannan ko sallamarta akayi bazata taba aikata irin abinda waccen ta aikata ba hankalin da nutsuwar ai ba daya ba,"yace cikin muryar rarrashi don wannan ba lokaci bane na zakewa,"aa bafazan dauki chances ba tunda duk masifar da balain akanka akeyi wayasan metake kullawa ita din?(wai Abu)"banaso kisa komai aranki,baa fatan wani abu yafaru"dahaka dai yusuf yadinga kwantar mata da hankali yana gaya mata kalamai masu dadi da yadda yake tsananin kaunarta ita kadai,dakyar yasamu tabar zancen don yasan halin masifarta idan tace zatayi abu sai tayi,bayaso ya zake yanzu ta kori yarinyar idan ta fuskanci wani abu,ko ta kwace wayar shiyasa yake lallabata.
"Naga kamar idonki yayi ja wai zancen ne yasaki kuka"ya tambaya,(babu yadda yusuf bayayi da ita akan tun farko kada tadinga bawa Wani undies dinta dasunan wanki Ama farida ce kowa yasani bawanda ya isa yahanata abinda tayi niyya,dole ya hakura ya kyaleta,kullum haka zata cire pant da bra,vest,da innerskirt tabayar dasunan wanki,ko abu farkon zuwanta saida taga abin banbarakwai amma daga baya tasaba)"kinmin shiru"ya katse mata tunani,"bakomai abune yashigarmin ido"don bazata iya fada mishi dalili ba tunda ai yasha gargadinta akai amma saboda bai isa yafada taji ba taki kiyayewa,duk wanda baiji bari ba ai zaiji hoho,tukunna ma dai.
Kuyi Hakuri masu karatu,kunjini shiru kwana biyu,Jarrabawa nayi ne shiyasa Atayamu da Addua,nagode da kaunar dakuke nunawa rubutun nan,karku manta kuyi following,voting da commenting.
Nagode
Dr. Danzabuwa
You are reading the story above: TeenFic.Net