RUWAN DAFA KAI

Background color
Font
Font size
Line height

RUWAN DAFA KAI 81~85
Na SUMAYYA DANZABUWA

"Wato shikenan kuma basabanba tunda kayi da kamanta da jamaa"cewar Bash bayan yazo gidan yusuf,hakika sun dan jima basu hadu ba,amma dai sukanyi waya lokaci zuwa lokaci sakamakon ayyuka da lamura na yau da kullum dasuka sha musu kai,"ah to ya son ranka,ai tukunna ma bakaga komai ba tunda kullum kai burinka sa ido"yusuf yabashi ansa yana dariya,nan suka shiga gaisawa na an dade baa hadu ba ido da ido,sannan suka fara taba hira,"ya mutuniyar tana nan kuwa?naga banga mota ba,kuma ina fatan dai yanzu komai daidai,norms"hmm Bash kenan don kaji nayi shiru kwana biyu wato?babu abinda ya chanja fa,mungode Allah dai kawai shine Abinda zan iya cewa amma kasan mai hali baya fasa halinshi halinta ne ahaka babu ranar chanji,bata dawo daga aiki ba,tukun"yace "biyar fa ta wuce ko dama haka suke dadewa?"bash yace tareda kallon agogon dake hannunshi,"eh to bayan laasar dai take tashi,watakila ta biya wani wajen ne kasan gimbiya bata bukatar tambaya,(sararta ce idan ta fita aiki tayi ta biye biye tana yawo,babu zancen tambaya dama tun yusuf din yana fada,har ya gaji,hakan nema yasa idan yaga bata dawo dawuri ba bai fiya damun kanshi ba)"bakomai acigaba da hakuri dai,abinda hakuri bai bayarba rashinshi kuwa kaga ai bazai bayarba ko?adaure,"hakurin nan kam ai anayinshi"cewar yusuf"to yaron fa ya akeyi dashi ko dashi take tafiya?"inafa,agida ake barinshi Akwai yarinya datake kula dashi,"kardai kace min mutuniyar nan taka ce mai rainon?(Gloria)"kyalkyalewa da dariya yusuf yayi,"kaima kasan bazan yarda ba ai ko me zaayi kuwa"banda dai kuri wancen lokacin ma me kayi?ai kawai zuba ido zakayi kamar koda yaushe ni danasan hali"Inji Bash,dariya kawai yusuf din yayi,"nima fa banida mutumci dakake ganina nan na iya tsiya idan aka taboni"hmm abaki ba,kafadawa wanda baisanka ba,to ita wannan din,wacece?a ina kuma aka samota?kuma har hankalinku ya kwanta da ita ne haka sosai dahar kuke fita kubarta agida da yaro?kasan mutane yanzu abin tsoro ne babu wanda zaka ce zaka yar...."to wane zancen yarda kuma,inda wani abu zai faru ai datuni aikin gama yagama,wannan yarinyar haifar yaron nanne kawai batayi ba,amma duk abinda kasani na raino itace tun daga haihuwarshi zuwa zancen danake maka yanzu"Yusuf ya katseshi,"kai,Amma dai farida bata kyautaba bata ko tsoron yadinga ma mata kyuya ko yana yarda da ita?"kai daka sani,ya zaayi ya yarda da ita bai saba da ita ba bayan ba ganinta ma yake ba"yusuf ya kara,"bawai zuga ba amma yusuf abubuwan dake faruwa tsakaninka da matarka sunyi yawa,lamuran gidan nan kullum da sababbi,ni nakasa ganewa,gaka nan kullum jiya i yau har gwara ma yau akan kwanaki naga kadan ciko","hmm to ya zaayi rayuwarce sai hakuri kawai kuma waikai ina ruwanka da kibata ne kafa samin ido",yusuf yace.
A irin yar Rumfar nan suka zauna a compound din gidan basu shiga ciki ba,suna tsaka da hira kuwa sai ga Abu nan ta nufosu hannunta rikeda tray shake da kayan ciye ciye,da kayan sha,tasha hijabinta kamar kullum,cikeda nutsuwa takaraso ta tsugunna sannan ta gaidasu ta ajiye(yana daga cikin sharudan farida agareta na duk sanda akayi baki takawo musu abin motsa baki,aikinta ne shiyasa ma tasaba daga taji anzo zata aiwatar gudun aikata laifi da batawa matar gida rai),"Ina Amin din ko baccin yake"yusuf ya tambaya,"eh har yanzu bai tashi ba"tace kanta a kasa,don bata fiyason abinda zai hadata magana dashi ba saboda tsoron farida,"ai kuwa dai naso ganinshi,saidai wani lokacin idan Allah yakaimu"Bash yace,"jeki shikenan"yusuf yasaameta,a nutse ta tayi hanyar shiga ciki,yusuf yabita da kallo,duk bash din na lura dashi,tundaga fitowar yarinyar har tafiyarta yadda yusuf yake mata mayataccen kallo.

"Baka bani labari ba to,ya akayi ne da waccen mutuniyar taka,Gloria take ko wa,"bash yace cikin tsokana,nan yusuf ya kwashe duk yadda komai yafaru har zuwa korar daya mata,"kace fatattakarta kayi,?ah lallai na yarda kafara iya rashin mutumci,ashe dai zaka iya tabuka tsiya kaima?"hm wannan yarinyar abinda yafi dacewa da ita kenan ai don inda na kyaleta na sakar mata bansan mezatayi ba,har yau fa farida batasan dalilin korar ba,har ynzu nasan kallon mugu takemun dana korar mata mai aiki,don batasan cin amanar da yarinyar tayi ba,"haba dai amma meyasa?ai da ka fad......"sanin hali mana,ni nasan halin kayata sarai,ba lallai ta yarda ba cewa zatayi dama saboda banason yarinyar nan zanyi hakan,hm bash duk yadda kakae tunanin farida ta wuce nan,ko ka manta mutuniyarta ce ta hannun dama,(gloria),tunda batada aiki sai yabon ta kana gani fa akan yarinyar nan babu irin kuncin da ban shiga ba agidan nan kai shaida ne"hakane kuma gaskiya kasha wahala mutumina"bash din yasake kyalkyalewa da dariya,"yaro mai white blood wato duk inda kayi mata kaunarka suke"mtsw sai kayi tayi"yusuf yazuba musu lemon.
"To wannan din kuma fa how far?ko dai kana cikine don yadda naga ka kakkafeta da ido kamar zaka cinyeta dazu na tsorata,"banason sharri,wai kai komai saika chnaja mai maana ne,kallon ma bazanyi ba kenan saika fassara Allah ya sawwake maka"Amin Amin kafadamin ya ake ciki don karya kake kace wannan kallon na lafiya ne"Bash yasake cewa cikeda kaguwar jin gulma,"well,to kadai ganta ai,nutsuwarta,kamalarta,addininta da hankalinta sune suke birgeni wallahi,"ga kuma rainon danka datake ko?"bash yakatseshi,harararshi yusuf din yayi,"kayi shiru mana in gama"ba bata lokaci ya kwashe mishi labarin Abu kaf," Zainabu Abu mai tagwayen suna wato sabuwar masoyiyya kayi ashe"cewar Bash,"to ya zaayi ita zuciya ai batada kashi,na daure na jure na cije naga dole inso yarinyar nan,kuma sonta nake ni tsakani na da Allah,"kallonshi kawai bash yakeyi tunda yafara maganar har yakai aya,"wata sabuuwa! kullum dai agidannan kunada sabon lamari wato,kullum sai an saki sabon episode,kaidai kaida farida zan iya cewa dama Auren kaddara kukayi don kuwa wannan abinda ke faruwa a zamanku bazan kirashi da auren soyayya ba"kamar ya auren kaddara?yusuf din ya katseshi," ah toh kaimai ka fahimta gameda zamanku da ita(faridan),duk tsahon lokacin nan,nifa am sorry to say but bana tunanin tanasonka gaskiya don kuwa duk abubuwan datake aikatawa basa nuni dakomai sai rashin so karara wannan wace irin rayuwace"bash nima abin yana dauremin kai amma kuma me?kamanta lokacin danake nemanta akwai danuwanta daakaso ahadasu takishi tadage sai ni?to idan ina irin wannan tunanin naceewar ko sonane batayi sai kuma inga rejecting danuwanta fa tayi saboda ta aureni kuma duk tarin manemanta tadage saini, kawai dai tanada wata halayya ne tata ta daban amma rashin so ma bai taso ba nizan bada shaidar hakan,"to ina so anan?yusuf kabude idanunka mana macen datakesonka ce dagaske bazata iya kiyaye abinda zai bata maka rai ba?ko kuwa macen dake sonka dagaske ne baka isa kafada taji ba sai abinda tayi niyya shi zata aikata,yanzu gashi tana nunawa karara dan dakuka haifa ma bataso ni tunda nake nataba ganin abu irin wannan?"nima abinnnan kullum dauremin kai yake,nayi magana tace basonshi bane batayi,kuma wai duk runtsu dole ai ai gane itace uwarshi yadaina gudunta,bama wannan ba,shikenan ni duk wata kula daduk wani namiji yake samun daga wajen matarshi nifa babu ni aciki,kum....hmm kodayake Akwai Allah"yace sannan yayi shiru ganin kamar yasaki baki ne yanata fadawa Bash din sirrinsu"a tsarinmu daga ni harkai babu karin aure,ko ba haka ba,to ni Alhamdulillah Allah ya ceceni,ya hadani da nutsatsiyar mace,wadda take sona take kuma nuna min ladabi da biyayya kaima shaida ne,to zan iya cewa ni na dace,zan baka shawara a matsayina na amininka danuwanka wanda yadamu dakai yusuf indai kanaso kaci ribar aure tun kafin akasheka agidannan,to kanaimi mace kamila ka aura,don wallahi idan kace ahaka zaka cigaba dazama tofa ankusa daukan gawarka,dubeka fa don Allah don Annabi,wai mutum yanayin aure ya murmure yayi kyau amma kai tunda kayi aure kake kanjamewa,wallahi indai zaka cigaba da zama da farida ita kadai burinka najin dadin zaman aure bazai taba cika ba tunda macece dabazata taba canjawa ba saidai kuma wani ikon Allah,"hakane kasan nama fika tsanar karin aure to amma na dade ina wannan tunanin,karin auren nan shine kawai maslaha agareni ahalin daake ciki dai,"yace"yawwa haka nakeso inji ai kayi tolerating farida dayawa,tunda kace ka dade kana tunanin auren haka to kasamo watane?"shiru yusuf din yayi yana murmushi,"babu waddda nasamu"karya kake dan iska,"Bash ya katseshi yana dariya,"kaidai yarinyar nan zainab ita ta kwantamin,nakasa daina tunaninta,dafari nayi kokari wajen ganin nacire abin daga raina to amma inaa kasan yauda gobe tafi karfin wasa kullum ina ganinta,son karuwa yake,saboda yarinyar batada matsala kwata kwata,tanada hankali ga tarbiyya,ga..."ya isheni haka,kafada dazu"bash ya katseshi cikeda tsokana,"saima kajita tana karatun qurani"shege" bash yasake cewa tareda kaiwa yusuf din duka cikin wasa,"wato saima naji kiraarta ko?karya kakeyi bawata kiraarata data birgeka dawani abin dai"bash ya kara,"kaji na rantse maka da Allah wallahi son danakewa yarinyar nan so ne na tsakani da Allah,farida tafita komai,ko kai baka dubeta dakyau bane?babu wani abu dazance wai gashi taka maimai sabodashi nakesonta wallahi aa babu,ita dai ba wani kyau ba na azo agani,ita ba kudi ba,h...."ya isa,na yarda dakai wasa nake maka dama,indai hakane kuwa to akwai masifu fa mutumina,don yanzu zancen nan ma yadda zaka fito dashi ka bayyanar dashi har ka sanar da uwargida tashin hankaline"nima nasha wannan tunanin amma kafin nan abin damuwar shine kada yarinyar kuma ni taki ni,saboda ahalin daake ciki fa ni kadai nake kidana nake rawata,ko kuma tayiwu tana son nawa itama amma tsoron farida bazai bari ta amince ba,"bakomai karka wani damu kanka Komai zaizo dasauki inshaallah Addua kawai zaa cigaba idan Auren akwai alkhairi Allah zai tabbatar idan babu sai kaga ya musanya maka,"hakane Alah dai yasa mudace,"Amin mijin Abu Mijin Abu"bash yacigab da tsokanarshi,"kai wai meye haka,zee zakace"tuntsurewa sukayi da dariya dukansu,"wato zee ko,kacigaba sai boss din gidanga tajika,fatana dai Allah yasa auren yarinyar nan ne zai kawo karshen wahalarka"Amin fa
Dahaka suka cigaba da hira,har dai Bash yabar gidan Bayan Maghrib Farida bata dawo ba,kuma yusuf yanata kira taki dauka,koda tadawo ya tambayeta inda ta tsaya,cewa tayi Gida ta biya kwana biyu bataga Abba ba,kyaleta yayi ya shiga harkarshi,don yanzu ya rage damun kanshi akan lamuranta.

Yau jinshi yake cikin nishadi haka kawai,ko duk soyayyar Abun ce oho,?suna kan gado shida farida ta kwanta kan cinyarshi yan hirar na kanta, tanata bashi labari,amma inaa yana dai jinta ne kawai tana magana,don kwata kwata hankalinshi nacen wajen Abu,"wai tunanin me kake inata magana kamin shiru?" tace afusace don bawannan bane karo na farko tunda suka fara hirar sai tajishi dif,kamar an dauke wuta shi kuwa tunanin Abu kawai yake dayadda zai gabatar mata da soyayyarshi agareta dakuma yadda ita din zata amince dashi,"haba baby meye nafushi haka don na danyi shiru?"yace,"idan hirarce bakaso ai sai in bari tunda inada abubuwan yi,in natafi harkata na kyleka kace nabarka kai kadai,yanzu ina tare dakai kana min banza"tasake cewa,(to in banda abin farida,ai ke lokaci ya fara kure miki,lokacin da yake bukatar hakan baisamu ba,sai yanzu dakikayi niyya?hmm tukunna ai bakiga komai bama)"ni na isa inkison hirar gimbiyata cigaba da gashi inajinki"yace.
KWankwasa kofa aka farayi wanda tabbas Abuce tazo sanar dasu tagama Abinci,wani zabura yusuf yayi,harsaida farida tadan tsorata"lafiya dai?"tace cikeda rashin fahimta,"lafiya sumul fa mekika gani?"yakarasa maganar yana mai sauke kanta daga kan cinyarshi,"muje muci abinci wata irin yunwa nakeji"yace cikeda murmushi batareda ya tsaya jiranta bama bare su sauko tare yayo gaba,"mtsw mutum sai shegen gulma kamar bashi yace ya tsani mai aiki ba yatsani girkin mai aiki amma yanzu yama fini zakewa shiyasa baason mutum yafiya rawar kai"tace sannan ta fito itama.
Duk saurinshi kuwa Abu tariga tashige daki kamar koda yaushe tunda farida tariga ta gindaya mata sharadi,shiyasa kullum saita tabbata tagama shirya musu duk abubuwan dazasu bukata sannan take hawa tace tagama,donma kar sai sunzo sun zauna tadinga kaiwa tana kawowa.
Sai wani mutsu mutsu yakeyi duk yabi yakasa sakewa,so yake kawai yaga gifcin yarinyar amma taki fitowa,yanata jujjuya abincin yana yan tunane tunane,"waini yau meyake damunka ne,?naga cikeda yunwa kasauko cin abincin nan batareda ka iya jirana bama kuma ynzu ka kasa ci sai jagwalgwalashi kake kana wasa,ko baiyi dadi bane?tajero mishi tambayoyi,"aa da dadinshi kamar kullum,kawai dai yau dinne nima bansan meke faruwa ba,"ganindai idan yacigaba dazama batareda yaga Abu alokacin ba hakan bazai bada kala ba kuma bazai iya cin abincin ba,ya shiga kwala mata kira"menene?mezata maka?farida ta watso tambayar,"Naam bakomai,Amin,Amin nakeson gani"yace,tabe baki faridan tayi,kadai bari ai kagama kasan dai zuwa zaiyi ya dam...."ai bata karasa ba saiga Abu ta bayyana, ta rissina kamar ko yaushe,"ina Amin din"bacci yake tace,"jeki daukoshi kizo kuzauna anan"yamata nuni da kujerar dake kusa da shi,adan gefe haka,"to"tace tayi hanyar daki"to kabari yatashi mana,"cewar farida don ta rasa azarbabin nameye,"naga lokacin tashin nashi ai ya kusa"tasake cewa,"Aa,ai bai dade da kwanciya ba sai cen Anjima zai tashi Aun..."ke ina magana da mijina kina saka baki saboda bakida kunya?yaushe kika zama haka?kada ki kuskura kisake kinjiko ?"ta dakawa yarinyar tsawa take jikinta yafara rawa,yusuf har ranshi yaji abin,amma ba damar nunawa,dakewa yayi kawai"Allah yabaki hakuri"Abu tace sai ga hawaye sharshar,wayyo Allah wani zafi yusuf yadingaji aranshi hawayen Abu suna zuba agabanshi yanaji yana gani bazai iya komai ba,sauri yayi ya juya don bazai iya jurar ganin kukan nata ba,yariga yaga rabonshi,"au kuka ma kike wato,saboda bakiji ajikinki ba,ke ga shagwababbiya baa isa amiki magana ba saiki kama kuka saboda kinfi kowa arhar hawaye,n..."ya isa haka jeki basai kin kawoshi ba"yusuf yace don abar zancen haka,kar farida tacigaba da magana ya maida martani, har lokacin bai juyo ba don ya ji kukan nata ya kara tsananta harda shesheka.
Jiki a sanyaye ta juya ta tafi dakin koda tashiga wani sabon kukan ta fashe dashi "wato dai duk takatsantsan din datake wajen kiyaye dokokin farida saboda su zauna lafiya bata gani ba,don yau tayi dan kuskure guda daya shine tayi kamar zata cinyeta danya,"haka tazauna tanata tunane tunane tadan kwanta bcci ya dauketa.
"Wai yaushe zaki rage masifa ne,yanzu meakayi kika saka yarinyar nan agaba kina mata ihu?naga dai idan akan yaron nanne babu abinda kika sani game dashi bare kice zaki bada shaida,don tace lokacin tashinshi baiyi ba shine tayi laifi,ko kuwa kina nufin kice kin fita saninshi?"yace duk yadda yaso yaga ya boye bacin ranshi hakan ya gagara,saida yayi magana"taremata kakeso kayi ko me?"ta hayyako,"bakomai mutum zaiyi ba kace zaka dinga mai masifa haka,a..."nace tare mata dai kakeyi kenan?mai aikin?harni zakace zaka fifita mai aiki akaina,?Karka manta fa zamana takeyi kamar yadda kasha fada abaya donhaka bakada hurumin da don inamagana da ita zaka saka mana baki,ko inmata abu kace zakayi magana babu ruwanka yusuf,idan baso kake nidakai....."au yau kuma taki tazama ke kadai kenan saboda son zuciya irin naki,kinsan ai wadda nace takice ke kadai kinsanta sarai(Gloria),Allah ya yafe miki dai"yace harda yar dariya,don bayaso tadago komai bare tazata yanajin wani abu aranshi game da Abun,"mtsww taja tsaki ta yarda cokalin hannunta da karfi ta tashi don ya bata mata rai,"harkin koshi ne?naga yanzu muka faraci fa?" yadinga tsoknarta yana dariya tayi banza dashi tayi tafiyarta daki,"hmm Rashin sani yafi dare duhu,dakinsan abinda ke raina gameda yarinyar nan dakin daina zakewa kin fara lallabata(Abun)ku zauna lafiya,ko ta girmamaki nan gaba,don abinda zai hanani auren yarinyar nan guda dayane saidai idan ita tace bazata aureni ba amma muddin ta aminta dani aurena da ita babu fashi inshaallah,"yacigaba dacin abincinshi.

You are reading the story above: TeenFic.Net