RUWAN DAFA KAI 61~65
Na SUMAYYA DANZABUWA
Tabbas Farida tasha wahala matuka,don ta dade tana labour har an fara tunanin ko zaa mata cs Allah ya taimaka ta haifo dan kyakkyawan yaro,bandai san wa yayo ba acikinsu tukunna domin kuwa dai indai kyau ne daga ita har yusuf din babu baya.
Yusuf kuwa yana waje an hanashi shiga,hankalinshi ya kai koluluwa wajen tashi inbanda adduoi babu abinda ya dukufa dayi ganin anshafe awowi kusan nawa ana abu daya lallai abinnan (haihuwar)ya shallake hankalinshi ya zarce tunaninshi shi dayayi zaton ana shiga da ita zaa cemishi ta haihu amma gashi awanni kusan nawa shiru?,gashi yama kasa sanarda kowa,da yayi tunanin kiran mama ko hajiya sai kuma ya tuna halinda zasu shiga don yasan duk macenda taji labarin yaruwarta tana labour wani hali take shiga na rashin kwanciyar hankali,yana cikin wannan yanayin ne likitan tazo mishi da albishir na cewar farida tasauka lafiya an samu namiji,sujjada ya farayi,cikeda godiyar Allah,murnar dayayi a lokacin nan bazata fadu ba don abinda ya dade yana fatane yasamu Allah ya rabasu lafiya(Farida da dan),babu wani bata lokaci akace zai iya shiga ganinsu,kasancewar dukanninsu nacikin koshin lafiya.
Saida yashiga yagansun tukun hankalinshi ya kara kwanciya,sannan yasamu damar kiransu Hajiya dasu mama da bash ya sanar dasu labarin mai dadi,kafin kuce meye wannan kowa yafara garzayowa.
Gida mama tace ya koma don kwaso musu kaya dukda dai bawani zama zasuyi ba tunda Allah yasa lafiya ta haihu saidai dan abinda baa rasa ba.
ko daya karasa ya shiga palon,da Abu yafara cin karo rikeda qurani alamun ta dade tana karatu,tunda ga abin sallah cen ma ya hango,(bai san tunda suka fita take abu aya ba ga dukufa datayi tanata adduoi duk dan akan farida ta haihu lafiya don yadda taganta dazun nan ta tsorata dayawa),"Ya Auntyn"ta tambaya cikeda damuwa,bayan ta ansa sallamar tashi,ganin murmushin da yusuf yasaki ne yasa zuciyarta dan nutsuwa "tana nan kalau ansamu da namiji"kawai yace, tareda karasawa saman cikin dan sassarfa,"Alhamdulillah Allah nagode maka"tace tareda ci gaba dajin dadi don Allahn dayayi ta tana masifar son yara,shikenan yanzu kullum tasan zata kasance tareda yaron nan,tunda tasan duka ragamar kula dashi hannunta zata dawo yadda ta fuskanci uwar dakin nata batason aiki ko da wasa,wayyo dadi,ko don yaron nan zata ma daina tunanin tafiya don tasan zai dinga debe mata kewa,jikinta ne yayi sanyi kuma,tunowa da halin uwardakin nata,kar tazo kuma tace batasan zance ba ma'ana tace babu mai taba mata da,don zata aikata.
Koda yusuf ya karasa dakin farida don kwaso kaya rasa ta inda zai fara ma yayi don kuwa babu abinda ta hada,babu wani shiri,bayan babu yadda baiyi da ita ba akan ta hada kayanta yadda kowace mace take hadawa idan haihuwa ta kusa saboda gudun mantuwa dasauransu, mama ma saida ta tambayeta rannan ko ta hada tace zadai ta hada ashe kuwa bata hada dinba,wayanda idanunshi suka hango su kawai ya dauko itama ya zabo mata.
Abu na cikin yan tunane tunanenta Taga yusuf yasake saukowa da yar jaka wannan karon ma fuskarshi cikeda jin dadi da faraa,yazo ya wuceta ya fice kamar ta tambayeshi yaushe zasu dawo,ko ta roki atafi da ita tagano yaron,don ta kagu,amma kafin tagama shawara da zuciyarta har maganar ta fito ya fice,"lallai mutumin nan yanaji da matarshi,ji yadda ya dauketan nan dazu duk yabi ya rikice,oh ni Allah sarki taji dadi tayi saar miji,"tace afili tareda shiga harkarta don soyayyarshi ga matarshi ai ba abinda ya shafeta bane.
Saida Farida ta kwana a asibitin sannansuka yo gida da hantsi duk tawani bi ta nutsu kamar ba ita ba (taji ajikinta),don batayi ma tunanin zata kawo iyanzu ba.
Tun a Asibitin Aunty Rasheeda tazo don haka tare suka dawo gidan babu bata lokaci kuw tafara bata duk wata kulawa data kamata itada jaririn,Don Abu saida tazama yar kallo ma saidai abinda baa rasa ba don Aunty Rasheedan irin matan nanne masu hidima dason aiki,irin marasa son jikin nan,lura da Son yin harkar jaririn da Abu takeyi ne yasa Aunty Rasheedan take bata rikonshi lokaci lokaci gudun masifa irinta farida,to kuma abin mamaki sai taga akan yaron dai faridan bata wani daga hankali don Abun ta daukeshi,hasalima indai ba nono zata bashi ba bata fiya daukanshi ba tunda kullum yana wajen Auntyn.
Su mama dakowa har yusuf din anso ayi gagarumin taron suna Farida tace bataso,don tunda ta haihun take nuna wasu halaye na daban da da batadasu,kamar yadda take nuna halin ko in kula ga yaron,da kuka datake yawanyi,babu yadda baayi ba ta dage dole suka hakura.
Ranar suna aka sawa yaro Muhammadul Amin, sunan Abban faridan,tabbas kowa yayi farinciki da hakan,don dama Hajiya tasan yusuf dai bazai sakawa danshi sunan nashi mahaifin ba,Itama faridan taji dadi kwarai don bata taba zata ba,shima Abban dayaji saida yaji kunya,jikinshi kuma yayi sanyi don gashi dai yusuf din dayake yiwa kallon mara nutsuwa mara kunya mara mutumci yabashi mamaki wannan abinne ma yasa yarage jin haushin yusuf din dayake amma har yanzu yana kule dashi saboda duka da zagi da farida tace yana mata.
Wannan chanji na farida yafara damunsu kuma musamman ma yusuf,dole yasa Aunty Rasheeda tamata magana akan suje suga likita don shi har yayi yagaji,tace babu inda zata lafiyarta kalau kawai yanaso ya fara raina mata hankaline yadda yasaba,itama Auntyn Abin yaso yafi karfinta don itama tayi harta gaji faridan tace babu fa inda zataje mai sukeso su maidata ita lafiyarta kalau,hakance tasa Yusuf kiran likitar tazo gida don shidai yasan yadda take abubuwan nan ba lafiyarta kalau ba,"Ba wani abin daga hankali bane "Baby Blues" ne(postpartum depression)mata dayawa suna kamuwa da irin hakan bayan haihuwa amma na dan lokaci ne,kuyi kokari dai kawai kudan dinga yin nesa da yaron daga gareta karta mishi wani abin,sai kuma idan zata shayar dashi a tabbata akwai mai saka mata ido,"cewar likitan"nidai nasan dama abinnan ba haka kawai ba,ko magana fa bata fiya yi ba wanda hakan kuwa ba halinta bane,amma dai zaa kiyaye inshaallah zata iya kaiwa kamar yaushe kenan kafin ta dawo daidai?"yusuf yasake tambaya cikeda kaguwa da damuwa,"karka wani tada hankalinka na dan lokacine ahankali zata daina,babu wani abu inshallah"to shikenan nagode yace sukayi sallama.
Ko sati biyun baa cika ba kamar yadda likitar tagayawa yusuf farida tafara nuna halayenta na da,don ita kanta Auntyn saida tayi mamaki "wato yarinyar nan ashe aure bai nutsar da ita ba tana nan da wayannan mugayen bakaken halayen nata kenan na rashin kunya?"wannan dalilin shine yasata tun farko tazo tazauna da ita din don idan ba ita ba babu wanda zai iya zaman sanin halinsu(faridan da sauran yanuwanta)dakowa yayi,to amma me?ita Auntyn tayi tunanin ko tunda tayi aure yakamata ace ta chanja amma ashe babu wani chnaji saima iskancinta daya karu,babu abinda yafi daurewa Auntyn kai kamar yadda taga faridan ta raina mijinta,shikuma yana lallabta,don iyaka zaman datayi dasu ko sau daya bataga yayiwa matar tashi kallon banza ba bare yace zai mayar mata da martani,ko ya auki mataki,duba da irin kalamai marasa dadi datake gaya mishi.
Ganin wannan abu ba mai karewa bane yasa Auntyn zaunar da yusuf din don ta tabbatar da abinda take tunani,"yusuf wai meyake faruwa ne"a ina?me kika gani Aunty"yace cikeda ladabi,don babu abinda yake kara birgeta dashi sama da irin biyayyar shi bayan kyautatawa,shikuwa yanayin hakan ne saboda a ganinshi bakowa bane zai iya zuwa yazauna da matarka yadinga kula da ita da danka kyauta,duk wanda zai maka haka kuwa yamaka komai kuma ya cancanci ka kyautata mishi,"matarka farida,meke faruwa ne ko har yanzu bata warke din bane?"Cewar Auntyn,yar dariya kawai yayi,"lafiyarta kalau Aunty Haka take ai"kawai yace,duba datayi da idan ta matsa da tambaya babu abinda zai fada mata hakan ne yasata hakura,da tambayar,"ka kara hakuri yusuf nasan kanayi amma dai ka kara kaji nayi tunanin ko ta chanja ashe har yanzu hakan take"tace,sannan tacigaba dayimishi yan nasihohi masu kwantar da hankali,"wato dai albasa batayi halin ruwa ba duk yanuwan mahaifiyar farida da ita kanta mahaifiyartata dukkansu babu masu irin hali nata duk sunada kirki a iyaka saninshi,kenan dai mahaifin nasu ne silar zamar dasu hakan kenan?lamari yana kara gasgatuwa,Allah ya kyauta.
Cen kuma Bash ne da matarshi Amina suke fafatawa don tace bazatazo barka ba,tayiwa farida na Allah da Annabi kuma,tunda suke basu taba kace nace ba shida ita sai wannan karon,"matar nan tanuna batasona karara kaima wayasan me take cewa akanka?dolene sai nayi harka da ita?ai ba yusuf kadai bane mai mata cikin abokannanka ko kaga ina yiwa sauran haka?kabarni kawai basai naje ba kai tunda kaje ai shikenan Allah ya raya yaro"yanzu akan matsalar wasu kika fusata haka har kike neman kimin rashin kunya Amina?"Ba rashin kunya nakeso namaka ba kafi kowa sanin halina tunda muke dakai ka taba jan layi na tsallaka?to mezai hana wannan karon tunda kaga na dage ka hakura kawai ka barni?ni so nake kawai ka fuskanci gaskiyar lamarin nan,abinnan fa guda dayand farida bata sona bakuma taso tayi harka dani to don me zan dinga nace mata,?nasan yusuf amininka ne tare naganku kadamj dashi to....."kufa mata matsalarku kenan daukaka zance,yanzu meya na girmama zancen nan haka?"ya katseta"nasha gayamiki kidaina biyewa abubuwa irin waynannan ke fa mai hankalice da nutsuwa Amina,babu kyau kace wai duk abinda aka maka saika rama meye aciki don kinje ai ba don ita zaki ba sai don yaron dakuma babanshi haba Aminata"yace cikin kwantar da murya bata musu da mijinta amma gashi akan farida sunayi gaskiya taji rashin son matar nan ya karu aranta,gashi ta dalilinta tana neman tabata ran mijinta,"zanje amma wannan ne karo na karshe"bakomai kishirya ina jiranki"yace.
Yan wajen aikinsu farida ma duk sun zazzo,harda sammy,don ba irin mutanen nan bane masu riko,an riga an wuce wajen amanta dakomai,rayuwar kenan.
Kasa shiru Da irin abubuwan dake faruwa agidan Aunty tayi,abubuwa ne kamar a film,yusuf din kamar tsoron faridan yake,sai abinda tace zaiyi yana gudun bata mata rai,lallai dole tazauna da faridan don jin dalilinta na raina miji datayi,"nifa ba rainashi nayi ba kawai dai ina kwatarwa kaina yanci ne da mutumci kinsan mazan nan na yanzu idan sukaga ka fiya musu biyayya sai su rainaka"tace cikeda rashin mutumci,"ke ni kike gayawa haka?"Cewar Aunty a fusace don dama faridan ta kwana biyu tana bata mata rai takuma lura da tsantsan rainin datake nuna mata sharewa kawai take,don tanayin komai ne saboda yaruwarta,dakuma yusuf din,"to meye aciki menace?yanzu fa sai kice rashin kunya namiki ko?"tasake cewa,tareda cigaba da taunar chewing gum dinta,"lallai farida wato baki chanja ba,ni kike gayawa wannan maganar,to kuwa kibi ahankali miji kike wulakantawa ba saurayi ba,ni nazata ko kyautata mikin da yakeyi yaci ace yaci darajar hakan,tunda nazo gidannan yaron nan yake fadi tashi dake,h...."da yaushe kikazo gidan dahar zaki bada shaidarshi?mijinki ne ko mijina?"tasake hayayyakowa, wannan karon harda daga murya,"too,har kik kai nan?lallai zaki iya nada min duka kenan?wato ni kike gayawa haka saboda bakida mutumci?wannan rashin tarbiyyar dai kinsan daga inda kika gadoshi, don yaruwata da danginmu baki daya bahaka muke ba,mara kunya fitsarrarriya,"To agaskiya nagaji da irin bakaken maganganun dakike fadamin agidannan kullum,kina zagina ni ina ganin gwara kawai ki tafi,don bzai yiwu ba kice zakizo har cikin gidana k....wani wawan mari Auntyn ta tsinketa dashi wanda yasata gigicewa,tunda ta sakankance bata zata ba,kasa kuka ma tayi tsananin gigicewa,don tunda take ma ita baa taba marinta ba,,"kinyi kadan wallahi,kuma dai kinsan ai ko kince ko bakice ba dama nagama zaman gidan nan yau tunda ke bakisan mutumci nikuma da abin kirki bai karbeni ba,ai na dade da lura da take takenki kyaleki kawai nake kuma wallahi kikace zaki sake fadar wata magana anan ta rashin tarbiyya saina miki shegen duka, bawai kina ganin kina iskanci kina cin bulus ba,sai Allah yasakawa bawan Allah,shashasha kawai"cewar Auntyn tareda tashi tashige tahado kayanta,don taga idan takara wani dan lokaci agidan zata iya yiwa farida dukan tsiya,Kuka Abu tasaka ganin dai dagaske Auntyn tafiya zatayi dukda dai batasan meya faru ba amma ta lura kamar ranta a abace yake don tunda tazo gidan inbanda mutumci da girmamawa babu abinda yake shiga tsakaninsu,bayadda ta iya dole sukayi sallama ta jaddadmata kara hakuri da uwar dakin nata.
You are reading the story above: TeenFic.Net