RUWAN DAFA KAI

Background color
Font
Font size
Line height

RUWAN DAFA KAI 26~30
Na SUMAYYA DANZABUWA

Kodata karasa gida,akwatinta taja tashige ciki inda ta tarar da mahaifiyarta (Asiya) wadda suke kira da mama da mahaifinsu Abba,sai kanwarta sauda da yayarta Safina suna zaune suna kallo ana dan taba hira cikeda jin dadi,kukan data shigo tanayi shiyasa dukkaninsu maida hankalinsu gareta,cikeda rashin fahimta da shiga wani hali,"aa lafiya dai ko?"mama ta fara tambayarta,fashewa tayi da wani sabon kukan,jin antabo mata inda yake mata kaikayi,batace komai ba sai karasawa datayi inda suke zaunen,ta rukunkume maman,hakan ne yasa hankalin maman kara tashi,inda tacigaba da tambayarta ko lafiya,amma ba abinda take sai aikin kuka,"meya farune?ko wani abune yasami yusuf din?"cewar Abba cikeda kulawa,jin ya fadi hakan ne yasa tasake fashewa dawani sabon kukan,"ke banason shashanci zaki nutsu kiyi bayanin abinda yake faruwa ko kuwa saina bata miki rai yazaki samu agaba k...?","aa ai abin bana fada bane abita ahankali zata fada"Abba,ya katse mama,shiru kawai mama tayi cikeda takaici,saida farida tayi mai isarta sannan ta gyara zama tafara"wallahi nagama zaman aurennan nagama,nagaji da bakin halin yusuf,h..."ke kinsan mekike cewa kuwa?mama ta katseta,"wallahi mama munafuki ne wannan dakuke ganinshi kowa yana mishi kallon mutumin kirki amma tsantsan mugune kawai n... "shine nace mai akayi?mama tasake cewa,nan farida ta kwashe duk labaran abubuwan dasuka faru da wayanda basu faruba,na karya da gaskiya sannan ta kakkara abubuwa hardasu wai yana dukanta ga zagi baacewa komai,"hmm lokacin daake fada miki ai kinji kikayi,kika dage saishi, kika zake gashinan tun baaje ko ina ba ai yanuna miki hali,ni dama kowa yasani ban taba son wannan mijin naki ba saboda kalar munafurci ce dashi,dama irin way..."rufewa mutane baki babbar kawai ko kunya ma bakyaji"mama ta katse safina wadda dama ita tun cen da bata taba son yusuf ba kuma shima yasani,don babu yadda batayi ba wajen ganin ta gamsar da yaruwar tata wajen ganin ta fasa auren amma ta dage,"kina nufin shi yusuf dinne duk ya aikata wayannan abubuwan?amma kuwa yabani mamaki tabbas abinda bazan laminta bane wannan ace zaa dinga zagi har ana duka"cewar Abba cikeda bacin rai don Allah yayi shi da tsananin son yayanshi,shiyasa ma duk abinda zasuyi a duniya basa laifi,kuma baa isa a tabasu ba,wannan dalilin ne yasa suka taso a sangarce don ma mama na bakin kokarinta wajen tsawatar musu,itama safeenan haka tadinga zabga rashin mutumci da rashin kunya anata gidan mijin tun yana iya hakuri har ya gaji,daga karshe dai abubuwa sukaki dadi,saboda tsananin rashin kunyarta da yawo,haka tadinga tadawa mijinta hankali duk hakurin dayakeyi da ita kuwa, tace saiya saketa babu yadda baiyi da ita ba akan tayi hakuri tadage,tareda goyon bayan mahaifinta dai aka raba auren,saboda shi mutum ne dabaya lamuntar ganin yayanshi cikin kunci,abinda yake faranta musu rai shi kawai sukeyi shiyasa dukkaninsu basuda kunya suke ganin sunada ikon taka kowa su kwana lafiya saboda sunsan mahaifinsu ya tsaya musu,shekaru kusan takwas kenan da kashe auren tana gida,gashi dama bata taba haihuwa ba kuma har yanzu Allah baisa tasake wani auren ba.
"Hmm wai sai kadinga magana kamar bakasan halin yarinyar nan ba,ko ka manta da rashin kunyar farida ne?dason kanta d...."ko me zatayi dai bai kamata ace an daketa ba dai ko?"ya ce cikeda fada,"nifa bacewa nayi ina goyon bayan dukan nan ba amma fa ni nasan halinta itama bataji m....."wallahi babu wanda zaice zai takurawa yarana auren ai ba hauka bane?Yana wani simi simi ashe bashida nutsuwa,..."banaso ka bata ranka akan lamarin nan har kace zaka yanke hukunci ni ina ganin zaifi kyau ace an kirashi shima aji ta bakins...."me zaaji daga gareshin? laifine fa ya riga ya aikata kuma do..."yarinyar nan fa yaji tayo bawai sakinta yayi ba b..."ai da sakin nata yayi ma dahakan yafi don yadda nake ganin abubuwa sakin shine zai zama mafita don bazai yiwuba takoma yacigaba da zalumtarta,"Abba yacigaba da fada sannan ya tashi ya shige ciki,farida kuma tayi kus agefe don ita kanta bata dauka zai dauki abin haka dazafi ba tasan hakika mahaifinsu yana sonsu matuka dahar baya ganin laifinsu amma kuma shin hakan yayi daidai kuwa?yakamata kuwa ace tayiwa yusuf haka ta shafa mishi bakin fenti a idon duniya?meya mata?masoyin kwarai,hmm Ita fa a tsarinta babu zancen rabuwa da yusuf kawai dai tayi hakan ne saboda tadan tsoratar dashi yakara darajata amma wai taji Abba yana zancen saki?to daga kawo kara kuma sau daya?itadai tasan tanason mijinta don bazataso itama akashe mata aureba tadawo gida sucigaba dazama itada safeena har sudinga fada,shikenan kuma gidansu yakoma gidan zaurawa kenan,tunda indai haka lamura zasu cigaba da wakana tofa tabbas autarsu ma zata biyo sahu.
"ki fadamin tsakaninki da Allah yaya abinnan yake kinsan dai babu wanda zai gayamin halayenki ko? Ni nasan zalumtar yaron nan kike,dawannan kazantar taki da rashin kunya"mama tatsareta,"wallahi yadda nagayamuku haka abin yake,kuma na chanja fa(zancen kazantar)"tace batereda ta kalli maman ba,"nidai kunsan bazai yiwu ba in zauna ina ganin ana abinda bai kamata ba inyi shiru ko?Kuma kunsandai bazaa dinga rashin mutumci ba indinga kauda kai ba inaganin ana shashanci, yanzu meye amfanin hakan? ke kin kaso naki auren(safeena)kema gashi kin dawo kuma dukkaninku bakuda wasu kwararen dalilai naazo agani, kawai saboda kunga anbarku kuna abinda kuka ga dama wato?to rayuwace dai,wanda yayi dakyau ma ya yakare bare wanda yace zaibi son zuciya,tunda haka kuka zaba ai shikenan kuyi abinda kukeso zaman gida kuma dai gaku gashi ai"mama tace,tareda shigewarta ciki.
Su akullum gani suke kamar mama batasonsu saboda bazata goyi bayan shirme ba,don kuwa indai zaayi ba daidai ba sai tayi magana ta tsawatar wanda sukuma suke ganin hakan a matsayin takura,sau dayawa ma sukanyi tunanin ma wai ko ita ta haifesu (don iskanci),saboda kwata kwata halayyarta data mahaifinsu tasha banban.

"Alhaji lokaci yariga yadade dayi fa dazaka fuskantar da yaran nan rayuwa,yanzu shikenan su basa laifi?shikenan su kullum a dole su zaace anyiwa ba daidai ba an kuntata musu?kuma ni nayi imanin yarinyar nan rashin kunya takeyiwa yaron nan h...."dakata Asiya,kome zatayi bazai sa yazama dalilin dazai daga hannu ya daketa ba,shi bai iya hakuri bane?ko kuwa bashi ita nayi yadinga dukanta alhalin ko ni nan mahaifinta"ya fadi hakan yana mai nuni da kanshi,"ban taba sa hannu na daketa ba h..."nifa bahaka nake nufi ba kawai dai abinne yayi yawa,kariga ka bata yaran nan dakanka tunda su tunda suke baka taba musu fada ba ni danakeyi shine har suke tantamar ko inasonsu ko banasonsu,yanzu hakan ya kamata ace anmusu aure amma babu dadewa sun dawo gida suna zaune yanzu dubi safeena fa yau shekaru takwas muke magana kai hakan bana ya damunka?Kafijin dadi ace nida ita muna jerawa agidan nan? Muna goga kafada?tunda yarinyar nan ta kaso aurenta ta dawo daidai da rana daya baka taba nuna mata cewar abinda tayi bai kamata ba saini dana dinga babatu,da wannan halayyar ne har wani namijin zaizo yayi shaawar aurenta?bayan yaji labarin abinda ta aikatawa tsohon mijinta?Yaran nan fa mat...."ke wallahi ni bansan wace irin macece bace ke,yayan naki dakika haifa,?to inda badon da kwararan shedu ba na tabbatar da haihuwarsu ai nima sai ince bake kika haifesun ba,kodayake ma, kin daina bani mamaki"yace tareda juyawa yabar dakin.
Haka rayuwarsu take kasancewa akullum,saboda yadauki son duniya ya dorawa yaranshi babu wanda ya isa yace sunyi ba daidai ba,tun da Asiya tayi haihuwar fari (haihuwar safeena)abubuwan suka fara faruwa,bata isa taje nan da cen ba batareda yarinyar ba atitir yarinyar kuma irin rigimanmun nanne,badama yaji tana kuka sai yace anbarta da yunwa,harsaida suka so su samu sabani saboda shi akullum ikirarin shi ta haifi ya amma batasonta,ni kuwa nace akwai wanda zai taba son da duk duniya sama da uwar data haifeshi ne?.

You are reading the story above: TeenFic.Net