~~~~~~~~~~~
(A wannan yammar bayan an daura auren jameel Aliyu kundi da hauwa Husseini Abubakar)
Kowa da kowa farinciki baya misaltuwa
Amarya kuwa da friends d'inta suna Luxury Hotel ana shirin tafiya wajen Dinner,
D'an qaramin towel ne a jikin Raeesah da shower cap a kanta , zaune take sai faman makeup ake a shafa wannan a shafa wancan
Da yake Tafeeda's glamour aka d'auko domin yin kwalliyar tun daga kano .
Asmau ce ta shigo tana taku a hankali domin high hill d'in da tasa a qafarta . Wata qaramar nylon ta bud'e ta d'auko wasu blue nights wears y'an qanana ta jefawa Raeesah wacce ke zaune a gaban mirror
Wallahi ke dai asmee sai a hankali !! Inji Raeesah ,
Toh daga abin arziqi?
Toh bari kiji wannan shine wanda xakisa on your first night
Hmm Raeesah tace Toh nagode, asmau ce tayi wanni wawwan tsalle ta fad'a kan Raeesah tana kyalqata dariya , oh oh asmau ki d'agani dan Allah, koh tausayina bakiyi! Ki luguiguita ni kuma anjima in sha wani!
Hmm wannan batu na manya ne ! Inji ihsan
Harara Raeesah ta galla musu zaku sani ai shegu mugwaye!!
Dariya suka fashe da shi suna kallon Raeesah suna mata waqa! Tareda tsokan , Amarya a gidan jamilulu, ke kikace kinaso, xamu kaiki mu barki π€ͺ.
Qarfe 8:40 aka fara had'uwa a ceremonial canopies dake anguwar rimi kaduna ,
Babban hall ne wanda yake daya daga cikin top 5 greatest event center a kaduna, an kashe kud'i kamar yayi.
Maman hauwa da Abban Raeesah kaya kala d'aya suka sa,
Hmm su maman hauwa uwar Amarya π ansha gwala gwalai a wuya da hannu sai sheqi ake, abban Raeesah kuwa a wannan ranar kyautar kud'i ya dinga yi domin aljihunsa kansa yayi nauyi ,
Abokan ango sunyi shigarsu cikin sky blue da hula , ango da Amarya sunsha kyau Amarya da friends d'inta guda biyu sai sister basma sunsha peach material, amarya kuwa b'a magana domin yau ranarta ce , hmm su Raeesah Amare π€©
Fara event d'in keda wuya ana ta hidima a yanzu haka amarya da ango sunyi cutting cake d'in aurensu wanda aka rubuta HML J&H
Hmm gayyar sod'i Amina ce ta shigo da tawagarta kamar ance suzo wajen su biyar har da ita, Fatima kuwa ta tandi makaman yaqi domin a yau take jin kanta zatayi betraying Amina domin jameel ya kwanta mata a rai, amma babu yadda zatayi saboda haka ba Raeesah zata kashe ba jameel zata kashe kowa ya rasa domin itama ta kamu da sonshi π₯ she can't do without him jameel Aliyu kundi .
A daidai lokacin da Amarya da ango suka koma mazauninsu ne Amina ta dokawa Fatima kira,
Hlo yes mah lady! Inji Amina
Sannan taci gaba da magana, it's time to do your work, make sure no one sees you, idan aka kamaki babu ruwana!
Toh shikenan ta kashe wayar,
A daidai wasu manyan chairs Fatima ta lab'e domin aiwatar da abinda ya kawota, a yau dai tayi alwashin kashe jameel domin kowa ya rasa,
Saboda ita kanta haushin Amina takeji, a hankali ta fitoda bindiga daga hand bag d'inta tana riqeta da kwarewa kamar ta saba,
You are under arrest taji ance mata! da sauri ta juya bayanta don ta firgita , batayi tunanin za,a ganta ba ! Yan sanda ta gani su hudu a bayanta kowanne da bindiga a kanta,
Fashewa tayi da kuka , don Allah kuyi haquri wallahi qawata ce ta sani, dan Allah ku barni in tafi gida, pls
Kuka takeyi kamr ba gobe ,
Amina ce ta tako tana clapping hands d'inta,
Oh oh poor girl, revenge is a dish best served cold,
Wannan kalma tayiwa fatima ciwo
Aminace ta kalli police d'in tace: officers you can go with her, okay ma! Sannan suka tafi da ita.
Ta Zaci zan barta ne batasan na fita iya cin amana ba,
Sauran mutane masu biki kuwa babu wanda yasan abinda ke faruwa har aka game dinner,
11:30 aka kai amarya dukda cewa yayi dare amma abba yace a kaita da haka, maman hauwa ce mai kukan rabuwa da Raeesah amma ita madam kuwa koh irin kukan amaren nan babu,π
Bayan an kai amarya ne su anty salma suka yi mata d'an fad'a wanda ba za,a rasaba sannan suka barta ita kad'ai sai angonta jameel abin qaunarta.
Alhamdullilah yau dai Allah ya nuna mana auren Raeesah da jameel saura naku masu karatu!π€ͺ
Zubeefly π¦
Vote pls π₯°
You are reading the story above: TeenFic.Net