ALIYU GADANGA..!

Background color
Font
Font size
Line height

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

       *Chapter..34*

"Koda suka isa Cikin babbar Masarautar ta Tambari buzu,ai sai su Aliyu dasu kawu suka saki baki harda hanci suna kallon Abun mamaki,domin Fadar irin girma dakuma Fadi,tareda kyau da tsari irin na masarautar *TAMBARI BUZU* Bata lokaci ne,domin wata Duniyace guda mai tattare da Al"umma masu ban mamaki da al"ajabi domin dukkansu Farare,masu tsawo da karfi da zati kuma dukkansu yawancinsu kammaninsu daya.

Dayake isar dare sukayi,gabadaya masarautar ya gauraye da Hasken kwai mai kyau da tsari,bayan ya kawatu da wasu Glob masu haske suna Fitar da wani kyalkyali na maraba bayan kidan algaitu,da Tambaru bakajin komai,gabadaya ancika masarautar da kade kade, da raye raye,na barka da zuwa maimartaba,Su Waziri ne kan gaba,dasu jakadiya wajen Tarban maimartaban,Bayi kuwa da Fadawa haka suka suba layi,suna kirarin barka da Zuwan Amalen Sarkinsu.

  Ai su Aliyu basu tsinke da al"amarin ba,sai da suka Shiga cikin Asalin gidan Sarautar nan fa kallo ya fara,don su ko ahoto basu taba Ganin kyau da tsari irin na Masarautar Tambari buzu ba,mazan gabadayansu Shashen Umar aka saukesu,nan ma wani aljannar Duniyance,sai kawu Shikadai aka warema wani Shashe mai kyau da birgewa sai Goggo wacce aka Sauketa awani Katon Shashe mai kyau da yarari,wanda maimartaba Sarki Abdulnaseer ya Sanar dasu Ummah cewa nan ne Shashen goggo na Har Abada,lalle wani kaya sai Amale,kunga barayin Wlh tsaayawa Fadema bata baki ne,domin an narka Dukiya tare da Hikima wajen Tsara Shashen mai dauke da dukkan ababen more rayuwa,kuma shashenshi yana kusa da Shashenshi mai martaba Sarki Abdulnaseer,Gimbiya Fasilatu suma ne kawai batayi ba lokacin da Ummah mai babban daki take bada Umarnin Wucewa da Goggo wannan Shashin,wanda duk wanda ke Fadin masarautar yasan Tsaruwan wajen da yadda Sarki yasa aka kawata Shi,sai gashi Farat daya goggo tazo Ta shige cikin Ruwan sanyi.

   Suko su Azeema dasu Anty mardiya Shashensu Zafira suka yada gajiyansu,ayayinda aka bar Ummah da Baba Ade Ashashen Goggo suna taya ta zama nan suka kwana suna santi da yaba Daular Duniyr da goggo ta Shigo,gimbiya Razeenah itama shashenta ta isa agajiye, hakama Ummah mai babban daki,sakamakom darene shiyasa maimartaba bai Fita Fada ba,sai dai da safe,Tuni bayi sukayita Shige da Fice da manyan farantai da Kwanuka na abinncin alfarma,tare da farantai na kayan marmari,da langa na kayan ciki,kowani Shashe sai da suka cikasu da Abinci da Abunsha sai wanda ya gani,su Jabir cire riganunsu sukayi Shida Hashim suka sauka bisa Capet suna Fadin!Allahu akabar Allah mai yadda yaso.."Suke Fada suna bude kowani kwano dake gabansu Haisam ko na gefe yana daukan Hoto,Aliyu kallonsu kawai yake yana yar dariya,Shi barinsuma yayi ya Shige wani daki ya Fada wanka,shidama Umar yana Shigowa wanka yafarayi,suko Su jabir banda kalle babu Abunda sukeyi,Sufa Abun mamaki yake basu wai suna cikin wannan tafkekiyar masarautar.

Washegari ne masarautar tambari buzu ta bunkasa da Jama"a domin Tun Adaren jiya maimartaba yabada Sanarwan ayi Sheda tako"ina acikin yankin Agadez cewa kowa da kowa yazo Fada yau,akwao Abunda maimartaba yakeson sanar da mutane,shiyasa Tun safe Fada ta cika da al"ummah kama daga bayi mata da maza Fadawa da masu Fada aji,yan cikkakun Masarauta da yan waje sai Shigowa suke,don ganin Abunda mai martaba keson Nunawa don dai masarautar batataba Tara Taro irin wannan karon ba,achan cikin Fada kuwa Maimartaba ya umarci da Ashirya Goggo cikin Shiga ta gidan Saurata hakama Aliyu ya shiryasa cikin Shiga irinta yarima Umar,hakama Azeema itama ashiryata cikin shiga itrinta Sarauniya,Jakadiya ita ta Shirya goggo,cikin Riga da zani na kayan Sarauta sai Wani katon mayafi mai Adon Fulawa ajikinsa suka yanemata jiki dashi,sai takalmin kafanta Shima irin na gidan Sarauta,In kuka ga goggo kallo daya bazai saka ku ganeta ba hakama Aliyu Shigar riga da wando irin na gidan Sarauta da takalmi,kaya iri daya suka sanya da Umar,itama Azeema haka jakadiya ta Shiryata,Wow Abun fa sai wanda yagani Don haka su Zafira suka hau kodata da Fadin"princess Azeema..!"Su Anty madina Abun fa ya burgesu kuma yabasu Sha"awa matuka.

Karfe 10:00am na Safe Maimartaba Ya fito Fada bayanshi kuma matansa ne Gimbiya Fasilatu da gimbiya Razeenah wadanda suka yi Shigan keta raini kowacce da alkayyabata na alfarma,sai su Zafira da Safaru da yarima Umar,koda suka Shiga Fada wacce ta cika da mutane,aka mike ana kai gaisuwa ga maimartaba Fadawa suna kakkarewa har suka isa mazauninsu inda aka Tanadar musu,bayan addu"a Bude waje,Maimartaba dake kan karaga mulki yayi mgana ga mutane Bayan gaisuwa dakuma Fatan alheri ya sanar da mutane cewa yana so ya bayyana da wani Abu zuwa garesu,Waziri yayi ma mgana akunnne sai naga yatashi da Sauri ya isa wajen jakadiya yayi mata mgana da hanzari ta mike ta Fice daga Fadan,chan ba dadewa sai gata dawo,bayi ne mata suka Faro Shigowa kafin Ummah mai babban daki tashigo hannunta rike dana goggo,su Ummah da Baba Ade na marasu musu baya bakinsu yaki Rufuwa,Shiko kawu dama yana cikin Fadar yana kallon Abun mamaki,dagasu sai Azeema wacce kanta ke duke,wasu bayi na biye da ita abaya,sai su Captain Aliyu wanda ke tafe shida Jabir Haisam,sai sarkin gida dake take musu baya,lokacin da suka Shigo ba wanda idon mutane yakoma mawa sai Gadanga saboda ganin tsananin kamarsu da Umar,Abunda yabama mutane mamaki shine ganin Umar zaune gefen maimartaba,to inba Umar bane waye?

  Abunda ke Ran mutane kenan harsuka samu wajen da"aka tanadar musu suka zauna,Fada tayi Tsit,Maimartaba ne yayima Waziri magana,shikuma yayima Shamaki mgana Wanda ya mike da hanzari yafara bada Shelan kowa ya Saurara maimartaba zai yi mgana mai muhammaci,Aiko Fada tayi tsit kowa na Sauraran maimartaba wanda Saboda muhimmanci Mganar da zaiyi har saida ya mike kafin ya fara jawabi,Yayi narrating lbrin ne saboda lokaci bazai barshi ya sanar dasu duka ba,Nan take ya sanar dasu Lbrin matarshi Suwaiba da kuma Da'n sa Aliyu fada gabadaya ta dauki kabbara da Son barka,nan take Jakadiya ta riko hannun goggo tazo da ita gaban maimartaba,wanda ummah mai babban daki ta mikamai wata Alkayabba mai ruwan Zuma wacce take tashin kyalli,Su Ummah na bayanta,maimartaba da kanshi ya mike ya sakama Goggo wannan alkayyaban bisa kanta fada ta dau kabbara nan da nan kade kade da bushe bushe na tashi,nan da nan akafara Shela tare da kirari"Agaida mai gayyah mai aiki..A gaida Giwar mata,agaida GIMBIYA SUWAIBA,Shugaban matan Adalin Sarkin Allah ya taimakeki Allah baki yawan Rai..",Suke Fada, Ummah kuwa har saida tayi guda da juyi jin Goggo tazama gimbiya kuma shugaban matansa gabadaya,Nan da nan aka Zabarmata bayi da Fadawan da zasu dinga kula da Shashenta nan take,Wuri fa ya hautsine Guda kawai ke tashi,Gimbiya Razeenah ita ta riko hannu goggo suka dagama mutane hannu suna dariya goggo ko hawaye ke zubomata na Farinciki,da kanta ta karisa da ita,kan wata kujeran alfarma dake kusa da maimartaba ta zaunar da ita,maimartaba ya dago yana kallonta yana mata mirmishi,su madina da su Jabir banda hasken camera baka ganin komai,domin Daukan hotuna kadai suke da video,daga Goggo sai Gadanga wanda Sarki da kanshi ya nadamai Rawanin YARIMA ALIYU..,Nan fa waje ya kaure da bushe da bushe da Kidan Tambarin Sarakai,Aliyu yaji Abun bambarankwai shiyasa ya Rumgume maimartaba yana so ya boye kwallansa,Gabadaya Fadawa suka Dauka "Allah ya taimake Magajin Sarki Wato Yarima Aliyu,angaida maimartaba uban Mazaje,kaine Uban Aliyu kaine kuma baban Umar,uba kake ga Zafira Da Safaratu kuma,gwarzo kake ga Gimbiya Suwaiba,kuma bango kake ga Gimbiya Fasilatu,kuma Miji kake ga Gimbiya Razeenah,Allah ya taimaki sarkin Agadez,Allah ya kareka Sarkinmu nayau kuma sarkinmu agobenmu in Allah ya yarda.."Waje ya dauki Surutun mutane da Yabo ga Sarki ga iyalansa,Nan take maimartaba ya gabatar da Azeema amtsayin Surukarsa,kuma Awajen gimbiya Razeenah ta sakamata Alkaybban Zama Sarauniya Kwaya daya tak amasarautar Tambari buzu kai Abun fa kayatar,sai wanda yagani,Su jabir da Haisam Abun fa ya matukar burgesu haka suka faka gefe suna bama idonsu Abinci,naga jama"a dadama wanda basan sanda suka zo ba Naga yan TEAM AZEEMAR GADANGA,sun Kame agefe,wasu na kokarin Ture mutane su adole sai sun karisa sun dauki Selfie da Gaganda da Azeema,wasu kuwa sunce su ko goggo ce zasu dauka da ita,ALIYU GADANGA FANS1,2,3,4 Duka sun hallarta wajen,sai yan BENEFICIAL WRITERS,da yan JANAF NOVELL1,2 yan Gidan ZUMUNTA ma ba"a barsu abaya ba,harda yan gidanmu na Amana wato *INTELLIGENT WRITER'S* Su our boss Anty meero,harda jika gaban hijabi saboda kallo,su sahiba ko saboda tsabar son kallo,cikin bayi ta shige tsudum😜my Anty na Najata,da Kanwata leema,sai My Sharifiyyah kuwa chan naga Fadawan sarki sun iza keyarsu sun kamasu suna kokarin kutsawa inda goggo take,wai su dole sai goggo ta gansu tasan da zuwansu😂Tawan kuwa da Dota ta mom kausar Batakowa sukeba illah ta Raguna da"aka bankare,kowa na yanka yadda yakeso,shinagani kowacce data yanke sai tasa ajaka sunayi suna sude hannu,suna waige waige saboda kada Agansu😹Umme Abden,da Uwar dakina,dasu Aisha zubair,da Special,da real mom Afra,kowacce da kudin kayanta,sufa sunce sunzo kenan,don wannan daular ta masarauta toh dasu za"a damashi wai suko abayin Princess Azeema ce suna so Abasu,kowacce idonta cike taf da hawaye suna kukan kada ace bazasu zauna ba ayo Nageria dasu😛😹,Suma fa yan INTELLIGENT FANS 1,2 ba"a barsu abaya ba,sun hallarta,kai naga mutane dadama wanda Bakina bazai iya Furtawa ba,Maimartaba da iyalansa basu tsaya sauran shagulgulan ba,suka koma cikin masarauta suka cigaba da nasu bikin don a kayattacen Falon mai mairtaba aka baje ana cin abinci,komai kake bukata akwai awajen,duk kwadayinka sai dai ka hakura,daga waje kuwa bayi da Al"umarr dake masarauta,suke Rakashewa domin suma wajen babu Abunda babu,domin Maimartaba yace kowa yaci yasha saboda yau Ranarta musamman ne.

Haka aka kwana Shagali da Murna,kowa yasan Sarki na cikin Farinciki kuma kowa ya Fahimci Gimbiya Suwaiba tana muhimmaci ga maimartaba sosai,saboda anyi Abunda ba"a tabayi ba Tunda ake a masarautar Tambari buzu,duk da Sarki na kwantantawa,Su jabir kuwa Suka sabe suka bar Aliyu da iyayanshi suna shan hira,suka tasa yanmatansu Zafira da Safaru,da zuwansu yawata dasu masarauta su gani,toh da wannan damar kowa yasamu ya fallasa sirrin zuciyarsa Shi Jabir Zafira ya dauka,shikuma Haisam ya Dauki Safaratu,kuma ga duk alamun Kowacce tayi na"am da samun gwarzo kamarsu,achan suka ci karo da su Madina kowacce da mazajensu suma suna yawata masarautan cike da sha"awa da burgewa ji suke dama ace anan zasu dauwama har Abada ai da sunji dadi😂Itako Gimbiya Suwaiba tana Shashenta su Ummah na kara gyarata,domin yau zata Turakar maimartaba,wanda goggo taso tayi gaddama Ummah taje ta fadoma kawu yazo da kanshi yayimata Fada,wai ita kunyar yara,da anbari baki sun Tafi ko😂Allah sarki goggonmu ta gargajiya,shiko Aliyu yana Shashensu wanda aka waremishi Shida gimbiyar tashi suna makale da juna ana Famshe bashin da"aka dauka,Aliyu har mamakin Azeema yake itako gajiya batayi,fahimtar dayayi cikinsa ne yazo da haka,shiyasa yayi bakam yana amfana tunda dama ta samu.

Jakadiya tazo da kanta tatafi da goggo Turakar Sarki,wacce gimbiya Fasilatu taga wucewarsu,harsaida tayi kwallah saboda bakinciki da kishi,Goggo duk kunya yakamata wai kada wani ya ganta tsofai tsofai dazuwa Turakar miji,batasan kowacce cikinsu tana makale da mijinta marasa miji suna makale da yanmatansu,Lokacin da jakadiya takai goggo shashen maimartaba bai Shigo ba yana babban Falonsa,tukun Saida safe jakadiya tayi mata ta Fice,Maimartaba dama yana kagare,jakadiya tana sanar dashi takai Goggo Turakarsa,da hanzari ya Shigo cikin Turakan ya Fitar da Annurin mirmishi,koda ya Shigo goggo na durkushe kasa cikin alkayyabanta,Tsaye yake yana kallonta yana kara godema Allah,Kiranta yayi cikin Natsuwa kafin ya karisa gareta ganin taki dagowane yasa ya zura hannu ya Riko hannunta yana fadin!"Tashi Suwaiba tashi muje isa ga Allah mu nuna godiyarsa daya kara mallakamana juna akaro na biyu.."shi ya tada ita,da hannunsa kuma ya ciremata akayyaban yana kallonta,goggo ko sai wani Sunne kai,take kunya amaren nan😂

Sallah suka gabatar raka"a hudu kafin maimartaba ya Shiga kwararo musu Addu"a mai tsayi,daganan kan Dardumar bai barta tatashi ba,sai da ya Shayar da ita daga wata madara mai kyau da gardi domin koyi da sunnar ma"akinmu Annabi muhammadu sallallahu alaihi wasallam,goggo Tuntanajin kunya dole ta cire,domin dai taga alaman cewa maimartaba ya Shirya kara'i,sai gashi da kanshi ya dauketa zuwa mamaken gadonshi wanda yaji shimfidun alfarma,Nidai daganan nayo waje don Wannan karon Abun na manyane babu Ruwana kada Dota tace nayi Rashin kunya😜

  
Ko washegari maimartaba ko zaman Fada bai Fito ba,itakanta goggo ko kuda bai gitta Shashen maimartaba ba,abarsu su murji amarcinsu son Ransu,su Jabir kuwa sai da suka kwana su kadai,don Aliyu Rabonshi dasu tun jiya,yana chan makale da Matarsa shima yasamu dama yana ta damawa Abunshi hakama Ummah tana tare da kawu,baba Ade kadai ke Shashen Ummah mai babban daki hatta su madina kowacce na tare da mijinta da ya"yanta,Su Zafira kuwa Tun safe aka dau wanka,suka saka bayi suka fara isa da kayan kari zuwa shashensu Jabir,wadanda suna ganinsu kowanne yafara jifan tashi da wani mirmishi mai tsayawa aran masoya,Shidai Umar ciki ya Shige saboda kannensa nasa suma su sake da samarin nasu.

___________________

Sati daya cur suka kwashe amasarauta kafin suyi haraman komawa domin Kiran gaggawa tasamu su Aliyu kan Ana nemansu abariki,domin an Fara posting dinsu zuwa wajen da zasuyi aikinsu,shiyasa duk hankalinsu yakoma gida,dukkansu sukayi Shirin komawa harda su kawu da su Ummah,Goggo ce ta roki alfarmar abarmata Baba Ade su zauna tare,nan take maimartaba ya saka baki,Ya roki Baba Ade don Allah ta zauna tare dasu,toh bataki ba,domin ba wanda yaki jin dadi da hutu,balle yanzu gimbiya Suwaiba keda Fada aji awajen sarki,maimartaba baya isa tsallake Abunda takeso saboda so yake yacike gurbin Kuncin daya sata abaya da Farinci ayanzu,shiyasa yake nunamata soyayyah kamar ya lasheta,hatta gimbiya Razeenah wani lokacin ta kanji kishi,balle ya yadda Ummah mai babban daki take nuna kulawanta kara kara ga goggo,balle gimbiya Fasilatu,da ko Fitowa daga Shashensa batayi saboda kishi da bakinciki,domin yanzu duk cika bakinta babu tadawo baya,Gimbiya Suwaiba tazo dole ta nannade kayanta tabama mai waje wajenshi.

Su jabir basu jira Aliyu ba,suka sanar da kawu sunga iri,Kawu kuma baiyi Nauyin baki ba,ya sanar da Maimartaba wanda yaji Farinciki sosai,kuma nan take ya basu yace kuma ko yaushe sukeson Adaura Auren suzo za"a Daura,Farincikin wajensu Jabir ba"a mgana harda yi ma Aliyu gwalo,shiko yana musu dariyan ko yanzu kasuwa tatashi yasan shike da riba😂Azeema kuwa anan Goggo tace abarta Tunda in sun koma ba zama zasuyi ba za"ayi posting din su ne zuwa wani yanki da"ake tashin hankali,kuma gata da ciki ta zauna ita kadai babu Abu bane mai kyau,da hanzari maimartaba ya amince yace abar Azeema anan har suje su dawo,Azeema dataji lbri tashiga halin damuwa duba da irin halin datake ciki,yanzu ma Abun yayi Sauki ba kamar da ba,Bata da yarda zatayi suna ji suna gani su Kawu da Ummah dasu Anty madina da Aliyu da Umar da jabir da Haisam da Umar suka koma kasar Nageria bayan sunyi Rabuwar bankwana da gida domin awannan Tafiya basu ta tabbacin zasu dawo Da rai ko akasin haka,kuka kuwa Azeema dasu zafira sunshashi kuka gimbiya Fasilatu kuwa sai da maimartaba ya riketa yadda ta kamkame Umar tana kuka,shiko maimartaba ya bisu da addu"ar samun Nasara ko babu komai yana alfahari da duka zaratan ya"yan nasa,haka dai suka shiga jirgi suka koma Nageria zuciyoyinsu babu Dadi.



*JANAFTY*

You are reading the story above: TeenFic.Net