ALIYU GADANGA..!

Background color
Font
Font size
Line height

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

        *Chapter 33..*

"Abinci mai Rai da lafiya suka girka,suka zuzzuba amanyan kololi,suka kai kowani Shashe,bayan sun Hada da lemuka da Ruwan gora,Su maimarta suna dai barayin gadanda suna cin nasu,ayayinda su gadanga suka hade Shida manyan Aminan nashi,Azeema ko dasu Zafira,sai su Anty mardiya da ita da Anty madina,goggo kuwa kunya takeji takasa ci,ummah mai babban daki ita kadai takecin nata,Ummah kuma ita da gimbiya Razeenah,Fasilatu kuwa babu wanda yabi ta kanta don Tunda ta Shiga ciki bata Fito ba,bayi da Fadawa ma ankai musu nasu barayinsu.

Ko kafin yammah tayi lbri ya Mamaye gari tako"ina mutane sai Shigowa suke suna ma goggo barka tare da Murna lokaci daya,wasu gulma ke kawosu,na ganin sarki da ake fadi,don wasu gani suke duk zence ne,aikuwa Maimartaba bai hana kowa ganinshi ba, yace abarsu suyi ta Shigowa yama Fi son hakan,da dare yayi maimartaba Sarkin gombe yaso Sarki Abdulnaseer yakoma masarauta,ammh yanunamai yafiso zamanshi anan,ko banza inda Suwaiba tayi rayuwa ne,ita da gudan jininsa,Shiko Aliyu yaso kebewa da Azeema ammh babu dama,yadda gidan yacika ne yasa sukayi musu sallama suka koma hotel din da suka kama ma Umar daki da safe suka kwana da Safe koda sukadawo suna cikin Shirinsu ne,don Maimartaba yace ayau din zasu kaduna sukuma biya zaria duk atare.

Inna Ramatu kunya da Nadama duk sun kamata,yau dai ga goggo data ke zagi tazama matar sarki,yau ga Aliyu datake yawon Fadin baida Asali Ashe dane,ga Sarki,da mallam lawal yadawo ya isketa tana kuka,ko kallo bata iaheshi ba,saima gyara kwanciya dayayi,yanaji tana kuka tana rokonsa wai ya roki Aliyu don Allah yasa baki Asaki Azeema wlh tayimai alqawarin bazata kara barinta ta aikata wani Abu makamancin Abunda ta aikata ba yana jinta yayi mata banza,saima Juyamata baya dayayi,Aransa yana Fadin bai yarda da Nadamar Ramatu ba haryanzu.

Koda su Aliyu suka dawo sun iske kowa ya Shirya, Nan suka iske Baba Ade tazo, yima goggo barka da kuma taya Aliyu Farincikin Saduwa da mahaifinsa,Hatta da goggo ba"a barta abaya ba ta Shirya tsab da ita,akwatun kayansu aka saka amota ita Azeema tunda zasu dan kwana biyu inji kawu,Su Aliyu ne zasu yi Tafiyar mota zuwa kaduna,su kuma sauran Jirgin maimartaba zasu bi,Gabadaya gidan aka Fito domin Tafiya su Aliyu tuni sun mika hanya Su maimartaba ne tsaye suna bankawana da su mallam lawal,sai ga inna Ramatu ta Fito daga gida da gudu ta zube gaban maimartaba tana kuka,mallam lawal kuwa yana ganinta yafara hararaart maimartaba ne ke tambayanta Meyake Faruwa tana kuka tana Fadamai kamun da Aliyu ya sanya akama Azeeza,Jinjina kai maimarta yayi kafin yace"Ash Abu baiyi kyau ba tashi tashi insha Allahu zan shashi yasa asake yau din nan.."Yake Fada yana kallon Kawu kafin yace"Bala don Allah kiramin Aliyu.."Kawu baiyi gaddama ba ya ciro waya ya kira Aliyu wanda ke gefen Jabir yana driving,Umar da Haisam suna bayan mota,da Azama ya daga kiran kawu yana Fadin"Hello kawu.."Bai yi mgana ba ya mikama Maimartaba wanda yace"Aliyu..."Yafada cikin dattako da mulki,saurin gyara zama yayi yana Fadin"Na"am Abbah,kun taho ne..? Bai bashi amsa ba yace"Yarinyar nan daka sa akama kanwar matarka kakira waya yanzu ka saka asaketa Umarni na baka ba Shawara.."gyada kai Aliyu yayi kafin yace"Angama Ranka ya dade.."Yana fada yana katse kiran,nan take yakira DSP MALEEK KABIR KUMO,sukayi mgana kafin ya bada Umarnin sakin Azeeza,nan sukayi mganar cewa bayan ya dawo yazo nan headquater su,akwai File din da zai cike nan sukayi sallama,jabir ne kawai yasan Abunda Ke Faruwa baiyi mgana ba,ko banza ai Ta horu Shegiyan.

Daganan Fadar maimartaba Sarkin gombe Suka wuce sai da sukayi sallama kafin su isa Airport,dama jirginsu na nan,Suka Shiga suka Lula sararin samaniya,Akaduna suka yada zango Tunkafin su iso mai girma gwanna Jahar kaduna * MALLAM NASIRU AHMED YAR RUFA'I yazo da kanshi ya ya tarbeshi Shida tawaganshi,Sai da sukaje gidan gwannati kafin su wuce gidan kawu,wanda ya kasance Aljannar Duniya nan kowa ya baje,don mamaken gida ne,mai Shashe har guda uku,kowanne ya gaji da haduwa,sai lokacin su Aliyu suka kariso suma,kafin isowasu Aliyu ya amsa waya tafi dari na yan"uwa da abokan Arzuka suna tambayanshi Shin Abunda suka gani gaskiya ne,da eh kadai yake amsawa,sai Barka mutane kemai da tayashi murna,daya gajima kashe wayaryi,Ko!ina na garin gombe jaridu suna ta yawo banda gidajen talabijin din da"akayita watsawa ana nuna Hoton Aliyun dana Maimartaba Sarki Abdulnaseer,Wanda jama"a dadama sunyi matukar mamaki,ciki harda da Ni"ima da iyayanta,mami tana hawaye tana kallon Cp Ahmed Sidi na Iya,wanda yayi Tsuru duk kunya ta kamasa,itako Ni"ima daki tayi dagudu Sauri tana kokarin kiran Muneera dataga ta kirata.

Kunya duk takama Kwamishana,sai zare ido yake,Mirmishi Mami tayi tana Fadin"Ka gani ko? wannan Ranar nake jiyemaka yallabai,kabiyema Sharrin shedan da hudubar dan"uwanka gashi yau kaine,akunya yanzu duk amtsayin kaje kayi gaba da gaba da Sarki,wlh ko haka Allah yabarmu munga sakayyah,Tunda diyar tamu nan harynzu agabanmu kuma tace inba Aliyu bata ba Aure har Abada.."Tana gama Fadin haka tatashi Tafice ta barshi nan yana zufa,lalle al"amarin Allah Kenan,ashe yaron ma yawuce duk Tunaninsu ashe shi din Da ne ga Sarki yanzu haka Shidin yarima ne,Lalle ya tafka kuskure babba ma kuwa.
  

***************

  Azeema ce Tunda yammah tayi take kwance Zuciyarta da gangar jikinta babu wanda suke bukata sai Mijinta gashi kuma gidan yana cike da jama"a,ita yanzu ya zatayi kwance take tarasa mafita,Duk wanda yazo ya ganta kwance sai tace batajin dadi ne,Rasa mafita tayi shiyasa ta aika hibba data aro mata wayar Anty madina,tunda ita tata ta barta Akaduna Tun Sanda Abun nan ya faru,ana kawo mata wayar ta Shige tiolet ta kulle ta lalubo lambar Captain takira wanda suke chan Wani Shashe shida su Jabir yanaganin kiran ya daga ammh kuma sai yaji Shuru anki mgana,sake duba mai kiran yayi kai Tsaye ya Furta.."Pretty..."Yafada yana Tashi saboda su Jabir da suka Tsuramai ido,Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta shagwabe Fuska tace"Bawani pretty,Bayan Tun ranar baka kara nemana ba.."Kanshi yashafa,jin yadda ta kashemai jiki,yace"Ba haka bane pretty kema kinsan dalili aie,ammh koda yaushe kina Raina abar Farincikina.."Mirmishi ta saki tana Fadin"Da gaske..."Tafada tana dariya basar da tambayan yayi yana Fadin"Meke damunki ne,? kowani Abu kike bukatane pretty..? yafada yana Danne dariyansa,Hararan wayan tayi kafin tace"Ni bana bukatar komai..Kai..Kai ne nake son gani.."Tafada tana Rufe fuska,yar dariya yayi yana fadin"Yanzu kuwa zanzo Tunda Service yatashi yanzu an neme ni aie..."Yafada yana rike dariyansa jin ya ganota yasa tayi Saurin katse katse kiran tana dafe kirji kunya duk ya kamata.

  Shiko daganan cikin gidan ya Shigo su goggo suna Falo ya gaishesu Rasa inda Azeema take yasa ya kira hibban madina ya tambayeta akunne,Nuna masa sama tayi alamar Tana Upstairs,Sosa kai ya Shiga yi kafin ya mike rike da hibba ya fara Taka Steps,dukkansu nuna sukayi basu gansa ba,kowcce ta dauke kanta,su Zafira suna ankare da yayan nasu,suna danne dariya,Sai da yakawo kofar dakin kana yace ma hibba"Toh maza koma wajen goggo yanzu zan dawo.."Jin haka yasa takoma da gudu tana murna,murda kofar dakin yayi ya Shiga da sallama,tana zaune kan gado,kanta babu dankwali tayi tagumi don bata zata zai zo ba,ganin ya Shigo yasa tadawo natsuwarta harda wani juya baya,Ganin haka yasa yayi Saurin karisawa gareta ya rikota yana Fadin"Am Srry pretty... ba gani ba.."Yafada yana Shinshinar wuyanta,Jin yafara chanzamata yanayi yasa ta saki jikinta itama ta rumgumeshi tana Shakan kamshinsa harda su lumshe,Matseta yayi yana Fadin! I miss u pretty.."Miss u more and more Yayana.."Kamkame juna sukayi kafin sufara sumbatar juna kamar wasu mayunwata,Azeema fa ba dama,domin Ture Captain tayi ya fada gefe tabishi ta danne tana wani kallonsa ta gefen ido,idonsa ta sa hannu ta rufe kafin ta hau zare kayan jikinta bata barshi ya bude ido ba,sai da yaji tana zaremai Rigar Shirt din dake jikinsa,Bai yi gaddama ba ya taimaka mata suka cire duka kayansu blanket ya jamusu suka Shige,Yau Azeema da zafinta take kai Farmaki Shiko yana Neman kare kansa,kafin kace kwabo an lulu barnin da bakowa ke zuwa ba Sai me rabo,.

Tsawon minti talatin kafin su samu Natsuwa Rumgumeta captain yayi yana saka mata albarka domin Duk sanda zai kusanci Azeema ji yake babu bambamci da daren Farko,abunka da mai Shigar ciki tare sukayi wanka kafin yayi wanka tsarki ya fito ya barta itama tayi,kayan jikinsa ya maida,sai lokacin kunya Abunda suka aikata ya Shigeshi yanzu taya zai iya Ratsa mutanen falon ya Fita haka dai ya kukan Kuran Fita,domin alokacin anata kira kiranyen sallar mangariba,Yana Fitowa yaci sa"a babu kowa afalo,sai su hibba suna wasa,Da hanzari ya sauko ya Fice,yana Fitowa yaci karo da su Haisam suma sun Fito zasu masallaci,suna ganinshi suka tsaya suna kallonsa yake yayi musu yana Fadin"Muje mana,ba sallah zaku ba.."Haisam ne yace ahankali"Kayi wanka kuwa..? zaro ido yayi kafin yace",Wankan me? Jabir ne ya duke yana kallon Umar kafin yace"Wankan Janaba mana.."wani dogon tsaki Aliyu yaja yana fadin"Janaban Ubanka,kudai yan iskane idonku na kan Sunnah kuna saka ido,kuka sani ni banda lokacinku kunga tafiyata. "Yafada yanayin gaba,suko suna mai dariya,Umar dake gefe yana dariyan yadda yaya Captain din ya hade rai,wai shi dole tsare gida har sukaje masallaci bai kulasu ba wai shi adole bayasaon Raini,cikinsu maimartaba dasu Kawu ya Shige dasuka mai mgana yace"Gaskiya ya lura zaman dayake acikinsu ma zubar dakaine,a mtsayinshi na magidanci mai mata harda ciki,sukuma amatsayinsu na yara kaskancine,kawai su kama kansu shima yanzu zai chanza taku ne,gwara yafara zama cikin manya Shine mutumcinsa"baki Haisam ya rike yana fadin"Kut..Kai wai ban girmeka ba..?"Wani banzan kallo Gadanga ya jefamai kafin yace"Koda ka girmeni ai baka halliceni ba.."Yafada yana wucewa ya barsu suna zaginsa shida jabir,Aransa yace",Na bar kara zama cikin yara daga yau.."yafada yana yar dariya😜😹

   Tun Adaren Aliyu ya samu kiran Ni"ima Tana mai murna,bayan itama harda mahaifiyarta tabamawa mami,wacce ketayashi murna itama amsa musu yayi kafin yayi musu godiya suka yanke kiran,Shuru yayi yana Nazarin wani Abu kafin ya saki ajiyar zuciya yana ayyana Abubuwa dadama.

Washegari suka wuce birnin zaria,A Fadar maimartaba suka yada zango,Maimartaba sarkin zazzau yaji dadin wannan ziyarar ta Sarkin Agadez maimartaba Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,yace dama yaji lbrin zuwansa bai zaci zai zo har Yankinsa ba,An gaisa cikin mutimci sosai kafin wasu jawaban su biyo baya,Maimartaba sarkin zazzau yayi mamaki wai sarki guda ya zauna agarin zaria abaya,lalle Allah mai hikima da kari,su jabir kam sai zagaye masarauta suke,suna fadin"daliin kaza gadangare kansha Ruwan kasko,yau gashi dalilin gadanga sun shiga masarautu dadama,haka su madina ke Fadi,ummah ko baki yaki Rufuwa godema Allah kadai take,domin dalilin goggo sun taka in ba basuyi tsammani ba,daganan Fadar tare da rakiyar Adalin Sarkin zazzazu suka iso anguwan dasu Goggo suka zauna,Allahu akabar Asalin gidansu nan nan kawu ya gyarashi yasaka wasu mutane suna zauna don Allah,saboda su kula da gidan karya lalace,zuwansu gidan yasa Sarki da Suwaiba suka tuna wasu al"amura da suka gabata inda dakinshi yake awanchan karon yanzu wajen ne aka kafa famfo,Maimartaba ya kurama wajen ido,hawaye suna taruwa a idonsa hakama Goggo,mutane anguwa kuwa da lbri ya samesu sunyi matukar mamaki,akwai dattawa dake da rai haryanzu,sai kuma wadanda suka samu lbrin bayan abun ya Faru,basu jima ba suka koma masaurata Tunda Allah ya wanke suwaiba da Da'nta,daganan kaduna suka dawo saboda Shirye Shiryen Tafiya chan Masarautar Tambari buzu ammh bayan An maida Auren goggo.

Kawu da Maimartaba basuyi Shawara dakowa ba,washegari bayan sallaar Jumma"a aka maida Auren goggo da Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,akan sadaki dubu Dari biyar,wanda awajen Daurin harda Maigirma gwannan jahar kaduna,Wanda aka daura amsallacin Sultan bello,Yan mazan ne kadai suke da masaniya sai da suka dawo gida suke Fada,goggo jitayi Abun yayimata wani banbamrakwai daki ta Shige tarufe kanta ganin yaran sun Faramata shakiyanci da Amarsu😛,Gimbiya Fasilatu kam dataji lbri kamar ta mutu takeji ga Danta Shima gabadaya taga baya tsaginta yana manne da dan'uwansa kamar wani zai rabasu,ga gimbiya Razeenah itama ko ajikinta harda ita cikin masu cewa agyara musu goggo,don so suke maimartaba ya rude fa😿Ummah mai babban daki kuwa wani lokacin tafi zama cikin Su Jabir kodon yadda take sakasu dariya,suko su Zafira basu iya saakewa ciikinsu saboda yadda su Haisam da jabir ke damunsu da kallo,Umar ne ya lura har ya shafama Aliyu,dariya takamasa yana fadin"Daz great,karabu dasu lalle wasu yara zasu dawo cemin babban yaya"Yafada yana dariya har ga Allah Abun yayi mishi dadi ko banza zai samu hanyar sakamusu da Abunda sukayi mishi,kuma zumuncinsu zai kara karfi fiye da Da.

Washegari kawu ya umarci Ummah da Goggo da Azeema da Aliyu su tafi gombe su tattara kayan goggo,tayi sallama da mutane saboda jibi zasu tafi chan masarautar Agadez,Gimbiya Razeenah ma tace zata,nan su Zafira sukace suma wlh sui sunje suna makale da princess dinsu,Mota biyu sukayi daya Aliyu ke driving tare dashi Umar,sai baya kuma Ummah da gimbiya Razeenah sai Goggo,dayan motar kuma Haisam da Jabir sai Azeema da Su zafira,wadanda su Jabir suka dinga jansu da zence,itako Azeema sai dai tayi musu mirmishi,suko yan matan basu saba ba duk kunya sukeji,Aliyu ko bini bini ya kira Jabir awaya yana fadin"Subi mai mata da kanne a hankali in ba hakaba ya hana abasu auren"Shuru sukayi suna Tunanin kashinsu ya bushe Tunda yaji lbrin ai sufa sai Abunda suka gani.

Sun isa gombe lafiya,su ummah suka Shiga gidan suka fara hadama goggo kayanta masu amfani,itakuma goggo tafara Shiga makota sallama,suna sallama tana kuka,sune har gidan Baba Ade,wacce itama tayi damara tace wlh da ita za'a Raka goggo masarauta😜goggo ko taji dadi tace ta Shirya su koma kaduna tare,kai goggo mai jama"a ce haka layi yacika,duk gidan data Shiga sai sunyi kwallah rabuwa da goggo Shekaru wajen talati sai yau kwatsam ace za"a rabu,toh basu da yarda zasuyi Tunda yanzu goggo ta wuce da saninsu matar sarki guda,Anan sukejin lbrin dawowar Azeeza goggo taja hannun Azeema suka Shiga cikin gidansu,Wlh da goggo da Azeema da sukaga Azeeza basu iya ganeta ba,saboda yadda tazama wata kamar kwarangwal duk kiban nan bata yanzu ta rame ta lalace tayi baki sai wasu kuraje afuska,ta kode ta lalace tana kwance kan tabarma daga ita sai daure gaba tana wani numfashi ba dadin ji,dukawa Azeema tayi gaban Azeeza tana kallonta tana hawaye take Fadin"Azeeza..Kice kika koma haka meyafaru dake? Inna ramatu dake gefe ne tace tana hawaye"Haka Aka dawomin da ita Azeema,ashe tun kamata da"akayi take rashin lafiya,ciwo ba"asan daga ina yake ba,tunda dai tadawo take kuka da kirjinta sai kuma ciwon kai mai tsanani,tabari muje asibiti,taki bari bansan me take so amata ba.."Kuka share share Inna Ramatu take tana durkushe gabansu goggo tana fadin"Don Allah Azeema da goggo ku taimaka kumin aikin gafara,wlh harda hakkinku ke bibiyanmu,na kyamaceki na wahalar dake,ke kuma goggo nabata miki suna sosai agari na cewa Aliyu bashi da uba gashi yau Allah ya nunamin iyakata,Ga Azeeza itama wlh harda hakkinki Azeema don Allah ki yafemata.."Tafada tana kuka,kamar zata Shide Azeema kuka take tana rike hannun Azeeza wacce ke miko hannu tana so tayi mgana Rikota Azeema tayi tana fadin"Sannu Azeeza Allah yabaki lafiya na yafemiki Duniya da lahira.."Tafada tana hawaye hakama goggo ta riketa tana jadadda yafiyarta,suna nan durkushe sai ga Mallam lawal sun Shigo Shida su gadanga,Shikanshi Aliyu dayaga Halin da Azeeza ke ciki sai da ya kauda kai,jabir ne yafara Fadan meyasa ba"a kaita Asibiti ba,Mallam lawal ya amsa da fadin"Ba inda zan kaita indai da kudina ne,kubarta tana girban Abunda ta Shuka ne.."Goggo ce ta katseshi da Fadin"A"a mallam,kada kace haka itama ya'ce kamar kowa,kuma tayi nadama don Allah ka yafemata"Jin sun saka baki yasa yace ya yafemata,Azeeza na kwance tana kallon Captain Aliyu tana hawaye,domin duk inna tabata lbrin mahaifinsa da duk Abunda yafaru,hawaye take tare da nadamar Abunda ta aikata,gashi yanzu tana ji ajikinta mutuwa zata yi,ammh kuma zata mutu da soyayyar Aliyu aranta domin ba ita ta dorama kanta ba,Aliyu ya Furta yayafemata,ammh fa Susinshi baijin zai iya badawa,Azeema ce tabata Dubu hamsin,wanda cikin kudin da kawu yake bata in yazo take Tarawa,Haisam da tsausayi,shima 50k yaba Inna Ramatu yace akai Azeeza Asibiti Allah yakara lafiya,Shidai jabir da Aliyu sisi basu bada ba,don aransu ma dadi sukeji ko banza anrage mugun iri,sallama sukayi musu suka Fito,inna ramatu har kofar gida kamar zata kwanta musu saboda godiya,nan nema goggo tace su Mallam lawal su tashi su dawo gidanta da zama ta mallaka musu halak malak,in Kawu sun dawo zai sa azo abuge gidan nasu ahade musu da wannan,Hakika mallam lawal yaga karamci,domin nan take maimartaba dake chan yace asanar da mallam lawal An biya musu kujeran makka,shida matarsa ai inna Ramatu harda Faduwa saboda taji Abun abazata ne,oh Duniya yau ga wanda ta wulakanta,sune gatansu Ashe,godiya sukayi ta zubawa kamar ba gobe,goggo ko tayi rabon kudi sosai,haka mutane suka cika bakin motarsu suna Fatan Allah ya kaddara saduwa gimbiya domin dai sun san,cewa kila sai dai kuma a lahira,koda suka bar anguwan haka goggo ke kuka babu wanda ya nemi hanata domin sabo yawuce komai,shikanshi Aliyu da bai cika zama ba, yau yaji Jikinsa yayi sanyi da barin gombe koba komai cibiyarsa ta haihu tana Gomben,ammh kafin sutafi saida ya biya mkrantarsu Azeema sukayi mgana da principal din,cewa Azeema zatayi tafiya,koza"a samu wacce zata cigaba da rubuta mata jarabawan kan tadawo,da hanzari ya amsa mai da za"a samu,kudi mai yawa Aliyu ya bashi sukayi sallama,bayan ya damka mishi Exam card din Azeema wanda yakarba Ahannunta.

Koda suka dawo kwana daya kadai suka kara suna kamallah Sauran Shirye Shirye,Hatta mazajensu Madina sunce dole suma su nemi Yarda awajen aikinsu suma suzo Awuce dasu domin fa dama daya take zuwa arayuwa,goggo ko Ummah ta isheta da kayan gyara itako goggo kunya tana fadin"Umaima wannan Abun kunyar har ina,tsofai tsofai dani,shima fa Maimartaba din ya tsufa don Allah kubarni haka"Ummah tace"haba goggo Shikenan kuma shi Tsoho bayason jin dadi,shima fa yasan dadi,nidai don Allah koda munje chan kisaki jiki,keda maimartaba ku Famshe Riban soyayyarku wanda baku fanshe ba abaya don Allah.."kallonta kawai goggo keyi tana dariya,su madina ko suna taya Ummah Rokon goggo,,Hatta Azeema ba"a barta abaya ba,ta Shige sawun masu son maimartaba ya samu chanjin yanayi😜😂Dole goggo ta yarda tana amsa komai aka bata tana ci,to ya zatayi Allah ya hadata da yaran zamani.

Takowani bangare Shiri yakamkama,Washegari karfe 10:00am na Safe jirginsu yatashi Abirnin tarrayyah Abuja,tunda sai dasuka Koma Fadar gwannati,maimartaba Sarki Abdulnaaeer yayi godiya da Shugaban kasa,kafin su wuce zuwa kasar Niger cikin babban Jirgin da suka zo dashi daga masarauta,Tafiyar data hada mutane dadama,Maimartaba da iyalansa,wadanda suka zo sai su kawu,Ummah,da Su Anty mardiya kowacce da mijinta da yayansu,sai jabir da haisam da Aliyu da Umar,sai goggo da Azeema da Baba Ade,Sune jirgin ya diba zuwa babbar Masarautar Tambari buzu wanda Tuni Lbri ya iske Masarauta cewa maimartaba na bisa hanya Shida duka iyalansa tare da wani Abun mamaki wanda zai bayyanama Masarauta.

_Ina godiya da Addu'o'inku...Ngd Sosai Allah yabar zumunci da zaman Tare..._

*Janafty*

You are reading the story above: TeenFic.Net