page 15

Background color
Font
Font size
Line height

👩‍❤️‍💋‍👨 *Zab'ina*👩‍❤️‍💋‍👨
*ko*
💔 *na Mahaifiya ta Sabuwar Rayuwa*💔

*ciga bane*
*** *** *** *** *** *** *** *** *** *** *****

*Daga alkalamin🖊️🖊️ Habiba Ahmad wanda akafi sani da princess*

*~kirkirarren labari ne kuma bashi da tsayi~*

*Dedicated* *to* *sis Khareema ~(my dangin kuma tu~*


*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*




https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Talbiyyar mai Harama da Hajji ko Umra:*

لَبَّيْكَ اللَّهُمَّ لَبَّيْكَ، لَبَّيْكَ لاَ شَرِيكَ لَكَ لَبَّيْكَ، إِنَّ الْحَمْدَ والنِّعْمَةِ، لَكَ والمُلْكُ، لاَ شَرِيكَ لَكَ.

Labbaykal-lahumma labbayk, labbayka la shareeka laka labbayk, innal-hamda wanni'imata laka walmulk, la shareeka lak.

Amsawarka ya Allah! Amsawarka. Amsawarka! Babu abokin tarayya gare Ka, amsawarka! Hakika yabo, da ni'ima da mulki naka ne (Kai kadai); babu abokin tarayya gare Ka.

*Bismillahir rahmanin rahim*

*Page 70~75*

Murmushi kawai ta sakar musu taku cikin nutsuwa ta k'arasa gurin Don ya manta da kanshi dan ya luluk'a duniyar tunani.

Tana murmushi tace" Allah ya kare, Allah ya bada sa'a Daddy sai ka dawo.

Ganin yadda take bashi duk wani girma yasa shi yin hawaye murmushi yayi yace" Khareema in mutum ya baka kyauta kana bashi tukuici ko?

Cewa tayi ehh cikin nutsuwa yasa hannu a aljihu ya ciro kud'i ba tare da ya ƙirga ba ya mik'a mata.

Sunkuyar da kai tayi tare da cewa" Daddy nafi buk'atar addu'ar ka da wad'annan kud'in dan haka keep it.

Bata kula Don ba, juyawa ta sake yi gun Sabeer tace" bro Sabeer a dawo lafiya tana gama fad'a ta juya ta nufi d'aki Don fa ta tafi da hankalin sa dan ya kasa komai bushewa yayi a gurin sai da Sabeer ya buge shi kafin ya tuna office zaije.

Daddy sosai yaji dad'in yadda ya ganta yau da kuma irin kallon da Don yake mata yasan cewa akwai wata a k'asa,

Har ya isa office yana ganin kallon da Don yake yi wa Khareema shawara ya yanke ya basu wata hud'u su fara san juna kafin ayi wani motsi.

Koda ya shiga office zama yayi yana murmushi yadda ya ganta but abu d'aya shine tana fushi dashi bata kulashi.

Hibba da Saddika dad'i sukaji sosai dan sunyi nasarar na farko saura plan B.

Suna shiga d'aki Zahra ta bata Chacolate kamar yadda ta mata alk'awari,

Zahra tana cikin bata labari ta ga ta suma ihu tasa kowa ya shigo amma mazan gidan sunje office waya Hibba ta d'auka ta k'ira Don ta sanar dashi halin da ake ciki.

Cikin k'an k'anin lokaci yashigo ya d'auke ta zuwa asibiti Zahra da Mummy ne suka bisu su Hibba kuma don yace suje office akwai aiki daya wa.


Bayan likitan ya gama duba ta ya mata allura san nan yafara bayanin meyasa ta suma nan yake cewa ta fad'i saboda tayi stressing brain d'in ta daya wa ne due to yin hakan yanzu ta tuna ta girma bayan haka ba abunda zata iya tuna wa watakila ma har abada baza ta tuna komai ba.

Jikin Don sanyi yayi sosai zuciyar sa kuwa kuka take cike da tausayin ta.

Kwanan ta biyar a asibiti kafin ta dawo gida ta zauna dasu na gurin sati kafin tafara surutu duk abunda take in taga Don sai taji duk a tsarge take amma duk da haka bata nuna masa Hibba kuwa tatafi gidan mijin ta,

Yanzu su Sabeer sosai suke plan dan su samu Don da Khareema su fara san juna amma ina in sukayi wani motsi da yawa sai hakan yayi leading d'insu to fad'a ko ka d'an Khareema bata san kula Don bare shiga har karsa in kuma baya kusa da ita gaba d'aya ji take she's not comfortable.

Shikuwa Don abunda yake b'ata masa rai shine wan nan sunan da tasa masa billu gashi duk abunda ya nuna baya so ita kuma shi takeso duk abunda baya so shi take so ko zama yayi yana tunanin ta cikin farin ciki a k'arshe sai yayi tsaki saboda tunda ya nuna mata red is his best colour ta daina sa kaya red duk wani k'ok'ari da su Saddika suke ko sun shirya sai sun k'ara fad'a kamar wuta da aiduga.

**** **** **** **** **** **** **** **** ***

Daure wa yayi yace wa Ahlum yana santa daga lokacin suka fara soyayya sosai , aka saka auren su a wata d'aya dake dama Asad ya shirya auren Aqsa matsalar da aka samu ne.

A kwana a tashi yau ake d'aura auren amma sai dai sunce basa son grand weeding hakan yasa ba'ayi komai ba daga d'aurin aure sai walima suka tare gidan su aka bar Umma da Aayan d'inta.

*** **** **** **** *** **** **** *****

Yau tsawon wata biyar amma ba abunda ke tsakanin Khareema da Don sai fad'a na yau daban na gobe da ban hakan yasa daddy ya k'ira su d'aki ya ajiye su yafara musu fad'a yace su fad'a masa meye matsalar dake tsaka nin su.

Nan Khareema tace"daddy ni bani da matsala dashi shiya ke da matsala kullum shi yake fara argument not me...

Sauri Don yayi yace"hey u me kike nufi wato nine nake neman masifan ki kin ma raina wa kanki wayo....

Cikin b'acin rai tace "excuse me billu me kake nufi magana kake ko wak'a...

Ransa b'aci yayi ya d'aga hanu zai mare ta hakan ba k'aramin b'ata ma Daddy rai yayi ba a fusace ya musu tsawa tare da cewa su tashi su bashi guri tunda gaba d'aya basuda kunya,

A k'arshe ya ke fad'a musu cewa tunda halin da sukeyi kenan in sha Allah zai aurar da su duka biyu a kwana biyar tunda yanzu sun girma basu da kirki...

Duk kasa magana sukayi tare suka fita kowa ya yi hanayar d'akin sa...

A fusace ta shiga d'aki tana huci Zahra ta tambaye ta meya faru nan tafara masifa wai yanzu billu yaja Daddy yace zai aurar da su a kwana biyar a cikin masifan take cewa yanzu kowa daddy zai aurar dani wa oho, wallahi gwara ya aurar dani wa fitinan nan nan da ya aura min wani wanda ban sani ba.

Zahra kuwa tayi recording komai dan dama abunda daddy yake son ji kenan shima kuma haka Sabeer ya sake fusata shi har yakai ga cewa wallahi gwara ya aure masifaffiyar nan da a had'a shi da wata mace.

Jin hakan yasa su dad'i jin dad'i sosai suka yanke shawarar abunyi.

Tunda ga lokacin daddy ya musu tsakanin da kar su kula junan su har lookacin da zai aurar dasu.

Damuwa sosai suka shiga dan fad'an da suke ma wani relief ne tunda suna kula juna but now an musu iya ka.

Yau gurin kwana uku ko ganin juna basuyi bare suyi fad'an ma k'arfe ukun dare ta tafi teras dan having wani strange feelings kamar ta tab'a shiga halin nan before tana tsaye idon ta yakai kan window d'akin billu aiko suka had'a ido kallon juna suke suna jin ya kamata suyi magana amma ina an musu tsakani sun jima suna kallon juna banda ruwa ba abunda idon Khareema suke.

Don d'in ma ji yake zaa rabashi da wani important part najikin sa.

Kuka ne ya kwace mata aiko tasa gudu ta shiga d'aki ta rufe.

Aka wayi gari saura kwana d'aya hankalin su k'ara tashi yayi yadda Mummy take bata magani iri iri gaba d'aya bata jin dad'in jikin ta in kuma tafad'a wa Saddika sai ta mata dariya wai ta tsumu ne ko kuma tace mata gaskiya angon nan zai more.

Hakan kuma ba k'aramin kunya yake bata ba.

Zaune Sabeer yake a office Don ya shigo alamun yanaso yayi magana ya d'au lokaci sai kuma yafita.

Mummy kam hankalin ta kwance take bata magani saboda ko anyi auren kar ego yasa su kasa kusan tar juna.


You are reading the story above: TeenFic.Net

#yerp