page 13

Background color
Font
Font size
Line height

👩‍❤️‍💋‍👨 *Zab'ina*👩‍❤️‍💋‍👨
*ko*
💔 *na Mahaifiya ta Sabuwar Rayuwa*💔

*ciga bane*
*** *** *** *** *** *** *** *** *** *** *****

*Daga alkalamin🖊️🖊️ Habiba Ahmad wanda akafi sani da princess*

*~kirkirarren labari ne kuma bashi da tsayi~*

*Dedicated* *to* *sis Khareema ~(my dangin kuma tu~*


*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*




https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Bismillahir rahmanin rahim*

*Page 60~65*

Don ya kasa komai sai tunanin Khareema dan ya jima yana mafarkin ta yana cikin tunanin bacci ya d'auke shi.

Next day da Asuba Zahra ta tashe ta sukayi sallah tare tasa ta tayi karatu abun yabawa Zahra mamaki duk gurin da ta bud'e mata tana iya karanta wa,

Bayan sun gama karatu tasa ta koma bacci ita ma Zahran ta kwanta.

Har tafara bacci tafara jin ishi ruwa tashi tayi ta fita bata san ko ina ba a cikin gidan tafiya kawai take tana ganin k'ofa ta bud'e ta shiga mutum ta gani a bargo har zata fita sai ta koma ta bud'e bargon Don ne a ciki yana bacci cikin kwanciyar hankali har zata tashe shi sai taga ruwa a kan bedside drawer d'auka tayi tasha ta ajiye har zata fita sai tayi murmushin mugun ta takoma ta d'au ruwan nan ta bud'e ta zuba masa,

A razane ya tashi dan ba'a tab'a zuba masa ruwa ba ransa b'aci yayi to d extend ganin ita ne yasa shi tsarewa mik'e wa yayi cikin b'akin rai yace" how dare you do that.

Kuka tafara wai ya mata tsawa,

Sanyi jikin sa yayi lumshe ido yayi san nan yafara bata hakuri ganin kukan yak'i k'arewa yajata ya rungume ta yana shafa kanta yace " am sorry I won't repeat it again I promise.

Murmushi tayi tace" OK we are friends now.

Tsuguna wa yayi a gabanta yace " rashin ji is bad manners please karki sake tashi na a bacci kinga kaina yana ciwo.

Murmushi tayi tace" OK bazan sake ba juya wa tayi har sai da taje bakin k'ofa ta juya tayi murmushi irin wanda kullum yake gani a mafarki tace billu sai ta fita da gudu.

Kifa kai yayi a bakin gado yana ganin murmushin a idon sa ji yayi an tab'a shi a baya d'aga kai yayi da sauri ganin Sabeer ne yasa yayi tsaki ya tashi tsaye tare da cewa " meye damuwar ka?"

Kan Sabeer a k'asa yace" don wallahi kana santa tunda ga ganin ta da kayi a asibiti naga san da kake mata a idon ka tun ranar and I wish zaka sake tunani kaga gaskiya on your own yana gama fad'a ya fita ya barshi.

Hmmm ajiyar zuci yayi ya kwanta.

Koma wa tayi d'aki ta kasa bacci hakan yasa tafara wasa da toys .

**** *** *** *** *** *** *** *** *** *** ***

Alhmd jikin Asad yayi sauk'i sosai har yafara fita yana zaga anguwa, kullum shida Ahlum suke fita kullum hakan ne yasa shakuwa tafara shiga tsakanin su.


Umma tunani fitowa ta fad'a wa Asad rasuwar Aqsa take amma kuma tsoro takeji dan tunda ya dawo kullum hiran sa Aqsa ne lumshe ido tayi taci gaba da shafa kan autan ta.

Dama idan da shak'uwa watarana so yana shiga zuciya ya zauna yawan zama da Asad yaja Ahlum tafara sanshi amma duk da haka ta kasa nuna wa saboda gani take kamar cin amanar Aqsa ne duk da sun sami labarin Aqsan ta rasu damuwa ta shiga sosai dan bata san make mata dad'i ba memories d'insu da Aqsa tafara tunawa hakan ya sa ta kuka,

Ta jima tana kuka tare da kallon duk wani crazy pics d'in su da videos d'in da sukayi.

*** *** *** *** *** *** *** *** *** *** *** ***

Bayan kowa yaci abinci a ka zauna hira a dining kafin su fita office Don de hankalin sa yana kan Khareema da Zahra dan ji yake kamar zata fad'i yadda suke ta wasan gudu a parlour juya wa yayi zaiyi magana yaji k'arar fad'uwa da sauri suka juyo Khareema ne tafad'i a fusace ya taso ya d'aga ta tana kuka tsawa ya mata akan gudun da suke da Zahra saboda ya hanasu tun da suka fara amma basu daina ba,

Hanu ya d'aga zai mare ta Daddy ya rik'e hanun sa tare da girgiza masa kai,

Tsorata tayi sosai rungume Hibba tayi kamar zata shiga cikin ta tausayi ta basu ganin yadda ya tsorata da marin da yakai mata,

A fusace yabar gurin ya tafi d'aki.

Rarrashin ta sukayi har sai da tayi shuru suka raka ta d'aki ta kwanta.

Saddika ne tace " Zahra kinsan yadda yake please take care of her and kina nuna mata abu me kyau da mara kyau yanzu shi take buk'ata ita a gurin ta komai ma dai dai ne kuma me kyau ne so ki kiyaye kinsan b'acin ransa.

Zama Zahra tayi a gefen ta.

Binsa Sabeer yayi har d'akin yace" you can't bear to see her crying am I right? das why ka d'aga hanu zaka dake ta kace bakayi believing love ba right ?

But am sure you will believe in love after you fall in love lokacin kuma da kayi realizing zaka fad'a min na tafi office see u later ficewar sa yayi ya barshi a gurin.

Tsaki Don yaja yafara duba files d'in da zai fita dashi.

Tunda yayi kamar zai dake ta tagama tsorata dan yau ko parlour tak'i fitowa tunda abun yafaru tayi fushi da kowa wai yanzu Zahra ce kawai friend d'in ta a gidan Zahra kawai zata na kulawa ko abinci sai Zahra ne ya d'ebo musu ta kawo d'akin suka ci bayan sun gama sukayi wasa da yamma Zahra tasa ta sake wanka tasa riga da wando wanda Don ya aiko bayan ya fita ya mata kyau sosai Zahra ta wanke mata gashi ta mata drying ta gyara mata sosai a kwana biyun nan suka shak'u da Zahra bata da k'awa sai Zahra bata kula kowa sai ita...

Dare na yi suka dawo daga office bayan anyi Sallah aka zauna cin abinci kasa hak'uri don yayi sai da ya tambaya ina Khareema da Zahra?

Kallon sa Mummy tayi tace"d'azu da ka d'aga hanu zaka dake ta ai baka tuna da bata da lafiya ba tunda kai baka san yadda zaka kula da yaro ba yanzu tace Zahra kawai zata na kulawa dan ita ce friend d'inta. "

Kallon sa Hibba tayi yadda yasa emotional face tab'a Saddika tayi suka had'a ido nan mummy taga me sukayi amma bata ce komai ba.

Key ya d'auka yafita da gudu dake kana nan kaya ne jikin sa kuma abun sauri ka k'arfi agurin sa ba abu me wahala bane.

Dukan su kallo suka bishi dashi, Sabeer kuwa tab'e baki yayi yaci gaba da cin abincin sa.

Bai d'au lokaci ba ya dawo da manyan leda a hanun sa bai tsaya ko ina ba har d'akin su Zahra yana shiga yasamu suna tsalle a kan gado ya jima yana kallon su bai kula su ba,

Ta bayan sa Saddika, Hibba, Sabeer suka tsaya yana kallon su suna kallon sa da irin murmushin dake fuskar sa suma murmushin suke kamar wasu wawaye.

K'afar ta ne ya zame ta fad'o zata sa kuka ta ganshi a bakin k'ofa gudu tayi ta rungume Zahra tana cewa "please send him away tell him to go away bamuje parlour ba kuma bamuyi gudu ba tell him dat you are my only friend.

Ganin Don d'in yasa Zahra ta kasa magana dan ita ma fushi take dashi saboda ya d'aga hanu zai daki Khareema duk da bata da lafiya Zahran ma rungume ta tayi tace" nima I don't want to see him let's close our eyes.

Duk abunda suke yana kallon su bai ce komai ba ya shiga d'akin ya zauna a bakin gadon ya bud'e ledan farko kayan zak'i ne aciki bai kulasu ba yafara k'iran su Hibba duka suka amsa yafara raba musu chocolate wai ko zasu kulashi sai ma k'ara rungume juna da sukayi duk abunda zaiyi su kulashi yayi sun k'i kallon sa tashi yayi yafita ya bar ledan a gurin kallon kallo su Hibba sukayi sai suka ce meeting time tare suka fita su ukun suka barsu a gurin yadda suke


You are reading the story above: TeenFic.Net

#yerp