UWAR MIJINAH...

Background color
Font
Font size
Line height

*UWAR MIJINA...!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_

       *Mallakar:JANAF*
       *Wattpad:Janafnancy12*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*Intelligent writer's Asso*✏

_Hakika jiya naga Tarin masoya wanda ni MAMI JANAF Bantaba tsammanin haka UWAR MIJINA YA SAMU KARBUWA BA..bansan dawani kalma zanyi Amfani da ita ba wajen godiyata ga Allah(SWA) ba Ammh duk da haka ina mika godiyata garesa taredaku gabadaya, Allah ya saka da alkhairi yabar kuma so da kauna na har abada_

_*Attention:zan danyi tsokacine, gameda masu cewa wai sakin da mu"azzam yayi ma Zahirah wai bata saku ba,who told u ehe?to malamanmu sun fadama mana ko acikin maye ,mutum ya saki matarsa ta saku,balle wanda yayi cikin hankalinsa,mahaukaci ne kadai akace inda ya saki matarsa to bata saku ba,kuma masu cewa saki ukun dayayi mata amtsayin guda daya ne? waya fada muku,malamai sunce indai akayi saki uku lokaci daya to abarshi a Saki daya ne,ammh duk sakin da"akayishi A rarrabe ma"ana mutum yace ya saki matarsa saki daya,na sakeki saki biyu,na sakeki saki uku,to Aurensu ya haramta har sai in Wani ya doramata idda,to da hakan nakeso na fadamuku Auren Hirah Da mu"azzam ya haramta harsai wani ya doramata idda,Allah shiyafi kowa sanin Daidai*_

          *NO 24*

        ""Gaskiya direban wanda yasan hanya ne,sosai don Karfe Hudu na Asuba suka shiga babbar tashar na maiduguri,lokacin wasu duk sunyi barci saboda gajiyan mota ammh banda zahirah wacce ciwo yake mukurkusa,taci kuka kamar ba gobe,ga maranta dayake kartamata lokaci bayan lokaci,idanunta biyu ko alamar barci babu har suka iso cikin tashan ta maiduguri.

   Ana zuwa kowa ya sauka,lokacin data saukane taji Tsausayin kanta ya dirarmata to yanzu ita ina Ta nufa,gidan Baffa ko gidan Bahna,agaskiyan batu bazata iya zuwa gida awannan Halin data ke ciiiki ba,saboda batason hakalin iyayanta ya tashi,ta inda aka hau dole ta nan za"a Sauka,batare da wani Tunani ba,ta tari mai Napep tace ya kaita Famfamari,dayake cikin tasha ne sai hada hada akeyi kamar rana kai bakace lokacin karfe hudu bane na Asuba.

   Suna tafiya ciwo ya dawo mata zanga zanga abun ba wasa tun tana dauka na yadda yake zuwa yabari ne,sai kuma taga abun ya girmema Tunaninta tun tana salati aboye har ya fito sarari,ganin yadda take juye juye yasa mai keken yakara gudu babu bata lokaci suka iso kofar gidan baffa shettima wanda dama yana bakin Titine.

  Zahirah dakyar ta sauko daga cikin keke saboda azaba ko takan mai keken bata bi ba, yana fadin Hajiya kudin fa,ina hankalinta baya jikinta cikin Fitan hayyaci ta karisa ga kofar gidan datake kulle ta shiga bugawa da karfin gaske hawaye na wankemata ido,ganin halin datake ciki ne yasa mai keken kada kai yayi gaba.

Shettima dake zaune afalo yana lazimi kamar amafarki yaji anata dukan kofa bana hankali ba,da hanzari ya mike ya dauki tocilarsa mai haske ya fice yana cema yakura,ana buga gida bari yaje ya gani,lokacin kuma yakura tashinta kenan,Ficewa yayi ya isa ga kofar yana fadin"Waye..? yafada cikin dan Tsoro kadan,zahirah data gama jigata ta furta cikin wata murya mai kama da na mutum na cikin mawuyacin hali'"Nine baffa,.."Tafada lokaci daya dataji wani abu yana binta akafa.

Gabansa ne yayanke yafadi cikin Rawan murya yace"Kece wa.."? tafara Fitama daga hayyacinta tace"Za..Hi..rah ce ...."Tafada tana jingina da kofan dajin zata fadi,Cikin wani irin Rudewa baffa yace"Zahirah wata zahirah kuma,innalillahi wa"ina Alaihirraju"un..'yafada yana zare sakatar gidan Rigigaf kawai yaji mutum yafadomai Cikin tashin hankali baffa ya riketa yana fadin"Ke dawaye kukazo da tsohon darenan,ina mu"azzam din.."? yafada cikin Tashin hankali.

  Zahirah tabata cikin hayyacinta fadi kawai take"ya Sakeni baffa,Baffa Ummi tasa ya mu"azzam ya sakeni,ku taimakeni zan mutu..."Lokaci daya tanajan wani dogon salati kan taja Numfashi ta sulale ajikinsa,Baffa cikin wani irin tashin hankali yahau kwalama yakura kira..."Yakura.!Yakura..!Yafada da karfi.

  Yakura dake daki ta fito asukwane tana fadin"Gani mallam lafiya kuwa wannan kiran.."? tafada tana karisowa ganinsa rike da mutum yana jiggawa yana kiran sunan zahirah yasa yakura karisawa da sauri tana haskata take fadin"Mallam yahna ce,ina kasamota ne,munbani mun lalace.."Tafada tana tallafota sai taji ta tallafi ciki ,cikin tashin hankali ta kalli kasanta kafin tace"Mallam ciki ne ma da ita,Nakuda ma takeyi,kuma har faya ta fashe,kamamin ita muje cikin gida.."

  cikin Tashin hankali Baffa yace"A"a kudai zamuje asibiti ne.."girgiza kai yakura tayi tana fadin'Ba lokaci mallam haihuwar tazo gadan gadan ne.."Tafada tana rikota shima yakama mata suka tallafeta domin jikinta gabadaya ya saki Numfashima dakyar takeyi saboda azaba cikin daki yakura ta shiga da ita tana salati,tsakar dakin ta kwantar da ita tana kwayemata doguwar rigar dake jikinta sama take fadi"Zahirah kiyi Nishi da karfi kan da ya fito,taimakeni don Allah..'Tafada tana waremata kafa cikin azaba Zahirah ke sakin Nishi da karfi Yakura na fadin ta kara kamkameta tayi tanaa salati da karfi hawaye na zubomata,baffa kuwa yana falo yana safa da marwa duk addu"ar datazo bakinsa yake karantawa cikin tashin hankali.

Cikin dan lokaci Zahirah tasaki wani nishi mai karfi sai ga da yafito yakura ta jawosa yana canyara kuka tana kokarin nadesa da zani taga alamar sabuwar nakudace takara tasoma zahirah cikin murna ta jiye yaron bisa gado tazo ta riketa tana cemata tayi nishi,cikin galabaita take Nishin karfinta duk yagama karewa cikin ikon Allah sai ga yarinya ta fado Yakura ta chabeta tana fadin"Alhamdulillah."

Baffa dake falo shima Alhamdulillah ya furta yana karama Allah godiya don ga kukan jarirai nan ya karade gidan saboda tsausayin zahirah baisan sadda hawaye suka zubomai ba,Allah sarki Allah yaga niyyarsa,hakan yatabbatar da cewa bawa bai isa ya gujema kaddararsa ba,wannan kaddaran zahirah ce, Allah bata ikon cinyewa.

Kafin gari ya waye yakura ta gyare mai jego tsaf ita da jariranta sun kame bisa gado suna barcin gajiya,tunda zahirah tashiga ruwan zafi,yakura ta gasa mata jiki tana dawowa daki barci ya dauketa saboda wahala,suko jariran Duka ruwan zamzam yakura ta basu kan ta daukesu takaima Shettima,wanda ya rikesu duka biyun yana kallonsu yakura yace"Me aka samu.? tana mirmishi tace"Mace da Namiji ne,ga Namijin nan kamar kayi kaki,itako macen,tamkar suhaima ce.."kallonsu Shettima yake yana mai Farinciki aransa koba komai yana mai Farinciki da wannan albarka da aka samu,wato rabon ya'yane yasa ka shi matsawa sai anyi auren kenan,hawayen dayake makalewa ne suka zubomai cikin mamaki yakura ke kallonsa tana fadin"Mallam yau ba ranar kuka bane ranar Farinciki ne,ina shi mu"azzam din ko ba tare suka zo ba?

Dukar dakai baffa yayi yana fadin"da tare suka zo da baki ganshi ba yakura,itakadai tazo nan kuma tafadamin cewa Suhaima ta saka danta ya saketa a daren jiya kuma takorota.."yafada cikin karaya dafe kirji yakura tayi tana fadin"Na shiga uku na lalace,da tsohon cikin tasa aka saketa,ashe Suhaima bata da imani koda ta saka yasaketa bazata iya mata lamunun kwana gobe da safe ta kamo hanya ba,ammh saboda rashin imani da tsausayi ki saka asaki yarinya da tsohon dare ga tsohon ciki,wlh abunda na guda kenan,nasani dole watarana haka zata Faru.."Takareshe fadan haka tana fashewa da kuka,bai hanata ba don shima hawayen yake saboda bai da hurumun hana kansa kuka,domin duk shine silan komai.

yakura taci kuka kamar mene bama kamar in takalli ya"yan sai taji tsausayinsu ya tsirgamata,zahirah bata dade da barci ba ta farka tunda tatashi take kuka,kamar ta zare ko yayan data haifa bata ko kallesu ba,yakura bata hanata ba ta barta ta koka domin dole ne,yaran sunata kuka yakura tayi tayi da itama ta karbesu taki kallonta tayi tace"Kibar kuka yahna Haka Allah yaso,in kikai hakuri sai kiga kinci ribar Abun,inkuma da rabon sake zama tsakaninku sai kiga kun sake komawa karkashin inuwa guda.."dagowa zahirah tana kallonta tace"Bazamu mu taba komawa guda ba yakura,saki uku Ummi tasa yayi min kuma duk a rarrabe..."Salatin da yakura ta yankane sai da baffa ya shigo dakin cikin rudewa yana tambayan lafiya,cikin kuka yakura kefadamai Abunda zahirah tace mata takara da cewa"Ammh ko Suhaima tacika babbar jahila mara takwwakali,kuma insha Allahu da sannu zata ga sakayyah..."Shettima bai iya mgana ba illa kadai kai dayayi ya fice yana jin zuciyarsa na kuna.

Dakyar Yakura talallabata tasha kunun kanwar data dama mata,sai dumamanman Tuwon data zubomata duka ta sharesu don ba laifi taji yunwa,yaran kuma zamzam aka cigaba da basu dayake basu da rigima kafin Ruwan Nonon yazo.

********

Mu"azzam kuwa Tun ficewar Zahirah yarasa control dinsa,kuka yake kamar wani karamin yaro,Ummi na zaune tana kallonsa ko ajikinta,mikewa yayi yana tangadi ya nufi shashensa ganin yana layi yasa ummi mikewa tana kwalamai kira,ammh yayi mata banza ya shige shashensa ya rufe kofa,Ummi ta zata abun nashi wasa ne shiyasa tayi komawarta ta zauna tana fadin"Ka ma dawo dai dai ne yaro.."

  shiko cikin wannan halin ya lalubo Dr Abduljabar awaya yana rokonsa ya taimakeshi yazo unguwarsu ya duba masa zahirah,yana ma tambayasa lafiya ammh yakasa mai mgana saboda yadda Saitin zuciyarsa ke bugawa,Dr.Abduljabar yazo har maitama yagama karadeta babu Zahirah babu dalilinta,mu"azzam yakara rokonsa yaje masa har tashan mota nan ma lbrin daya ne bata ba mai kama da ita,sai gashi dalilin dalilai yasa Dr.Abduljabar yaje har gidan minister Alhaji gaddabi Nura neman Zahirah,Sakamakon mu"azzam ko mikewa yayi jire ke neman gadasa shi,shiyasa ya wakilta Dr ammh shima lbrin daya bata zo ba.
  

  Asma"u da mamanta sun shiga tashin hankali don babu shakka Ummi ta samu lbrin cikinan koma miye to abun bamai dadi bane,gashi tana ta kiran wayanta akashe balle taji meyafaru kuma bata da wanda zata kira yafadamata abunda ke faruwa.

Lokacin da Dr.Abduljabar kefadama Mu"azzam bai ga zahirah ba kashe wayar kawai yayi ya sulale bisa kafet hawaye suna kwaranyo masa,yasani Shikenan Ummi ta saka Almakashi ta datse Farincikin Rayuwarsa harda cigabansa,yanajinta tazo da safe tana bugamai kofa yayi banza da ita,yanzu ko sha'awar kallon Ummi bayaso saboda yadda yaji lokaci daya Ummi taficemai daga rai duk da tana mtsayin mahaifiyarsa,Wuni yayi adaki ko fitowa baiyi ba,yana kwance babu ci babu sha,sallah kawai ke tadashi,itama din azaune yake yinta,cikin kwana daya kawai ya zabge ya rame kamar wanda ya shekara yana ciwo,ga saitin zuciyarsa dake zafi ga jirin dayake fama dashi saboda yunwa ammh bakinsa bazai iya koda saka kwaran abinci ba,saboda yadda ya yankema Rayuwarsa jindadinsa ya kare har abada tunda Ummi ta rabasa da Matarsa uwar ya'yansa,yana son kiran maiduguri yaji ko zahirah ta isa,ammh ina yakasa bakinciki da kunya sun kasa barinsa yakira,mai zaicema mahaifinta,bayan ya tozarta musu ya" ya sakota da tsohon dare ga kuma ciki,wanda yana kyautata zaton koda ta fita yakusa zuwa Duniya.

****-*****

Lokacin da bukar yazo gaida baffa yaci karo da wani lbri mai tada hankali da bakinciki,haka ya zauna dirshan yana kallon zahirah da ya"yan data haifa idanunsa sunyi jawur,baitaba kawowa ransa haka zata iya faruwa ba,baitaba tsammanin rashin imanin mahaifiyar mu"azzam yakai haka ba,bai samu zarafin mgana ba saboda yadda tsausayi yaran,ya shigesa lokaci daya amaka saki uku,gata yarinya ga kuma rabon ya"ya innalillahi wa"inna Alaihirraju"u.."kawai yake nanatawa ficewa kawai yayi daga gidan,da kanshi yaje kasuwa yajido kaya nata dana yaran,harda su kayan tea  duk abunda zata bukata yakawo,yanaji aransa wannan karon bazai bar kowa yamasa iko da diyarsa ba wacce yake matukar so,gida yakoma yace ma mahgana tagyara tsohon dakin zahirah zai dawo da ita gabansa ne,lokacin da magahna taji lbrin itama fashewa tayi da kuka tana tsinema Ummi.

 
Lokacin da bukar yakoma shida mahgana da niyyar daukan zahirah takoma gunsa tayi jegonta,daga yakura har shettima babu wanda ya musa,domin yanzu basu da iko kan zahirah in abaya shettima yayi iko da ita,yanzu kam Bukar yahau dokin zuciya zai bama yarsa kariya da kuma farinciki insha Allah,sunaji suna gani suka sakata a mota ita da ya"yan tare da rakiyan yakura suka tafi,shettima sai da ya zubar da kwallah,ammh duk da haka yana godema Allah,koba komai zuru"ar da"ake neman hadawa ta haduwa,haduwa ta har abada.

Lokacin da dangin Bukar suka samu lbrin sunso bore don akwai wa"inda sukayi damaran zuwa har abuja suci mutumcin Ummi wasu kuwa mu"azzam din suka ga laifi,wasu kuma shettima saboda sunce shine yaso kansa dayawa, yadauki yarinya ya bada, inda yasan cewa daman Tuni an tsaneshi to in ba zalunci ba meyasa yayi haka,babu yarda zasuyi illa hakuri domin bukar ya fadamusu cewa yarinya dai itace tasu kuma sunkarba,yara kuma suma nasune, saboda haka zasu cigaba da kulawa dasu duka indai itane basu so to har abada bai fata zahirah ta sake komama mu"azzam har abada.
  

*Bayan kwana uku*

Tuni aka cigaba da bama zahira da yaranta kulawa, kanwar babanta Ashe ,ita da yakura suke kula da ita,komai kuwa na bukatar rayuwa bahna dinta ya ijiyemata don dai duk yasata Farinciki,yara kuwa tuni rafara basu nono in tana kallonsu bata sanin sadda take fashewa da kuka,intana kallon macen yadda hatta yatsunta irin na Ummi ne,sai ta kamkameta tana kuka tana fadin"Wayyo Ummi da kinsan haka da baki aikata ba,Shi Allah ba"a mai dabara kalli cikin dakika tsana na haifo mai kama dake,wayyo ya mu"azzam kana ina nasani dakana nan Allah kadai yasan Farincikin dazakayi,ammh kamin Nisa,nisa na abada,.."haka zatayi ta fada tana kuka,wani lokaci aboye takeyi bata bari su yakura su sani kada sufadama bahna dinta ya shiga damuwa,ammh tabbas gangar jikinta ne ke maiduguri ammh zahirin batu Ruhinta da zuciyarta na Abuja tana son sanin wani hali ya mu'azzam ke ciki koma wani hali ne ta tabbata bamai dadi bane.



***********

*ABUJA*

    Yau kimanin kwana uku ko kofar daki Mu"azzam bai Fito ba,yana cikin daki duk ya zabge ya rame ya lalace,baya zuwa office,duk wani abu najin dadin rayuwa ya dakatar,ko wanka bayayi sallah ce tazama dole yakeyi itama azaune,yunwa kuwa takusa mai illah sai yaji kamar zai mutu ne sai yasha ruwa,ko yadan ci Fruit haka,yakoma ya kwanta saboda baya da karfin jiki,ga ciwon kai mai tsanani dayake fama dashi,ga jiri wanda shiyama fi damunsa,wayoyinsa kuwa har an gaji da kira baya dauka,kullum kwana yake kuka,kukan bakinciki da tunanin wani hali hiransa ke ciki,? ta haihu ko bata haihu ba? taje gida ko wani abu ya sameta a hanya? duk baya da wanda zai bashi wannan amsar.

  Ummi kuwa kwana daya ta shareshi ita azatonta yana gama fushinsa zai fito ya warware ammh sai mai har aka kwana biyu ba mu"azzam ba dalilinsa ba ita kadai ba kaffa ma'aikatan sun shiga damuwa sosai,Ai ummi dakanta ta isa kofar dakin nasa tahau bugawa tana rokonsa ya bude ammh yaki budemata tayi magiyan duniyan ammh shuru kakeji,shiko yana jinta ammh bazai ma iya tashi bane har ya bude kuma shi yanzu yafiso,Ummi ta kyalesa yayi rayuwarsa shikadai Tunda burinta kenan kullum ta dinga nakasa mai Farincikinsa.

Ummi falo takoma tayi tagumi tana hawaye su karime na zaune gefe suma suna cikin halin damuwa,ita lami ko damuwa batayi ba illa fadin datake aranta"Komai yafaru ke kika jawo.."Karime ce ta kalli hajiya tace"Don Allah Hajiya kibar kukanan hakanan kada kema wani ciwo yakamaki.."share majina tayi tana fadin"Dole nayi kuka karime Mutum mai rai ya kwana uku bai sa komai bakinsa ba,ina lafiya kuma wlh nafikowa sanin halin son zai azbtar da kansa da yunwa ne hartazo ta mai illah.."tafada tana share kwallah

Shuru sukamata suna mamakinta kin janyo abu kuma kizo kina kuka,Allah yakara sukayita mata aransu,damuwarsu daya rashin sanin halin da yallabai yake ciki, ammh da ba don haka ba,wlh ko damuwa da ita baza suyi ba,tunda ita batasan Farincikin dan ta ba.

Ranar da"aka kwana hudu Ummi na kuka tana rokon mu"azzam ya bude ammh,yaki budewa,tayi magiyan hartagaji ammh tarinsa bataji ba,sai jikinta yafarawa tafara zargin tabbas babu lafiya,dakinta ta ruga ta dauko wayanta ta kira shureim tana kuka tana  fadin yazo ya taimaketa kada mu"azzam ya mutu ya barta, yana ma tambayanta lafiya takasa mai bayani dole ya yanke wayar yakoma yakira na mu"azzam nan kuma harta katse ba"a dauka,ba cikin rudewa ya Fito daga Asibitin ko gida baije ba,yakamo hanyar Abuja

Mu"azzam na kwance kan kafet baya da riga daga shi sai Wani bakin dogon wando,kallo daya zakamai ka kauda idonka saboda yadda yakoma,ya rame ya lalace kamar wanda ciwon ajali yakama,wayarsa dake gefe dake keta kuka tundazu ya mika hannu cikin karfin hali ya dagota da niyyar ya kasheta gabadaya,Sunan wanda yagani yasashi mikewa yana rike kansa Da hannu daya *BUKAR MAID* ne ke kiransa.

Sai da ta katse yakasa daukan kiran saboda yadda zuciyansa ke amsawa,tuni kansa yayi masa wani Nauyi,wani kiran ne ya sake shigowa cikin karfin hali ya daga kiran batare da yayi mgaba ba don ji yayi bakinsa ya kafe da Wani miyau mai daci,Bukar kuwa yanajin mu"azzam yadaga kiran yace kai tsaye"Zahirah ta dawo gida,Ranar data dawo Allah ya Sauketa lafiya yau kwana hudu Tasamu karuwan yara biyu mace da Namiji,zaka iya zuwa,ko  ka aiko da sakon Sunan da za"a sanya ma Yaran.."daga haka kawai Bukar ya yanke wayar yanajin Haushin mu"azzam har cikin ransa,don harda shi aka taru aka boyemai Halin da yarsa take ciki,wanda daya nada,lbri wlh da dakanshi zaije ya daukota yadawo da ita gida.

Mu"azzam kuwa wani tari ne ya sarkeshi saboda jin yadda bukar din yamai mgana,ga murnan Samun Lbrin Hiransa lbri mai dadi harda lbrin haihuwa ya"ya biyu Allah Abun godiya,Mirmishi yake mai kama da kuka lokaci daya tarin na kara sarkeshi lokaci daya hancinsa yafara zubar da jini,wani abu ya tahomai abaki da yawa yana tara hannu yazubo da jini mai yawa,cikin rudewa yake bin jinin da kallo lokaci daya yana dafe saitin zuciyarsa dake masa ciwo yana cigaba da tarin,kuma hancinsa bai daina zubar jini ba.



*DON"T FORGET TO COMMENT,SHARE AND VOTE...*


*Mami Jamila*

You are reading the story above: TeenFic.Net