Ouummey
1,502 104 16
Rayuwa cike take da kaddarori da dama, dan Adam baze ce tayi imani ba kuma Allah ya kyale shi kawai, dan yadda da wannan imanin se Allah ya rubuto series of jarrabawowi din tabbatar da ingancin imanin namu.Se dai san rai da son zuciya na jagorantar dan Adam ga munanan ayyuka, wanda daga karshe suke jinginawa Ζaddara, akwai Ζaddara, amma kuma a boye cikin kaddarar nan akwai jagorancin wasu munanan halaye, son kai, hassada, bakin ciki, da ire iren su.Akwai wani karin magana da Bahaushe ke amafani da shi,musamman a tsakanin mu mata, wanda nake da ja akan shi, da kwarin gwiwa ta, da dukkan zuciya ta, haka da dukkan murya ta nake faΙin CIWON Ζ³A MACE BE TAΖA ZAMA NA Ζ³A MACE BA!.Ban yarda da karin maganar wai CIWON Ζ³A MACE NA Ζ³A MACE bane, ban kuma aminta ba, shiyasa tun tasowa ta nayi watsi da shi, bangarori da dama da na duba na rayuwar mu mata ya karya ta shi.Ina tunanin bahaushe be fahimci rayuwar mu ba, be karanci mata ba, da na tabbata baze fadi wannan zancen ba balle har ya shiga jadawalin karin maganar mu na Hausa masu tushe da dimbin tarihi.Bari kuji, mace ita ce matsalar mace yar uwar ta, dukkan kukan mace in kun yi duba daga tushe zaku ga daga mace yake, kyashi, bakin ciki, hassada, son kai, munafunci da wasu sauran mugayen halaye da dabi'u sun tare a wajen mata ne.Ba zan ce duka ba dan ko a cikin gidan karuwai akan haifi malami, sedai da yawan mu haka muke, bana tunanin akwai macen da in aka binciki rayuwar ta ba za'a samu tabon yar uwar ta mace ba, in one way or the other, se kuma da na fara fahimtar rayuwa na fahimci DOLE ACE MATA SUN FI YAWA A WUTA.!Ban tsani mace ba dan nima itace, mahaifiya ta ma itace, akwai kuma tarin yayye da kanne, sedai na tsani munanan halayen mu, na kyamaci gurbatattun mata na daga cikin mu, dan sun taka rawar gani cikin KADDARAR RAYUWA TA!.Dan Allah kar ku yanke min hukunci batare da kun saurare ni ba, ina rokon ku ku bani aron lokaci da hankalin ku, ku biyo ni dan jin muguwar rawar da mace ta taka cikin raβ¦