Hally tana cen tashiga wani hali banda kuka ba abinda take don ita kadai tasan metake ji aranta, sanarwa da cigiya dai babu inda baa kai ba,neman duniya babu wanda basuyi ba amma shiru,gashi shi daniskan (bilal)shima an nemeshi an rasa,babu shi bare labarinshi,tayi imanin dauke mata yaran yayi ya kaiwa karuwarshi saboda ya bakanta mata,aikuwa zaisan yayi da gwana don hakika saita koya mai hankali idonta idonshi.
Lallabata iyayen nata suketa aikinyi suna bata baki ana kwantar mata da hankali saboda dare yariga yayi babanta ne ya tabbatar mata dacewar da ikon Allah zaa ga yaranta kuma babu abinda zai samesu inshaallah don zaa tashi tsaye da addua babu ji babu gani.
Bata farka ba sai asubah kodata bude idanu bata ganshi ba motsi dai taji cikin bandakin da alamun yarigata tashi kenan,bakin cikine ya tokare mata zuciya amma tayi kokarin dannewa don ta fuskanci dole tadinga tsiyayawa zuciyarta ruwan sanyi wasu abubuwan saita hakura dole ta kauda kai,to wai da nawa rayuwar take ma dazata dinga musgunawa kanta haka?tunda dai mahaifinta yace bashi ba ita ya yi watsi da lamarinta kuma agaban wannan bawan Allah akaci mata mutumci to bataga kuma dalilin dazaisa tacigaba da shiga kunci ba,tunda mahaifinta yamata wulakanci waye zai sassauta mata aduniya?babu abinda yadace tayi yanzu kamar tasawa zuciyarta hakuri takuma yarda da irin kaddarar da Allah ya dora mata zata dage da addua don tasan koba dade ko ba jima sai Allah ya saka mata tunda ita aka zalumta babu laifin datayiwa kowa,kuma ahalin daake ciki tasha alwashin daina jin haushi ko bakincikin halin datake ciki inshaallah zata rungumi kaddararta hannu bibbiyu hakika Allah baya dorawa bawanshi abinda yafi karfinshi zata zauna da mutumin nan a matsayin mijinta tunda ya nuna shi mai kaunarta ne,idan kuma karya yake yanada wata mummunar manufa Allah bazai bashi ikon aiwatar da sharrinshi akanta ba.
Tana ta tunane tunane tana sake sake yafito,"aa gimbiyata,subhanallahi ya daga tashi kuma sai kuka?"Yace arikice tareda karasowa inda take,wai ashe hawaye take batama sani ba,"kiyi hakuri don Allah kidaina asarar hawayenki wallahi namiki alkawarin zama dake tsakani da Allah bazan cutar dake ba,nasan labarinki kaf komai da komai,nakuma san ahalin daake ciki tsakaninki da mahifin..."ai bai karasa ba tafashe ta matsanancin kuka mai ban tausayi,"kiyi hakuri don Allah,Allah yana tareda ke ki kasance mace mai yarda da kaddara,kinji Aminatu,"yace tareda dan tallabota cikin siga irinta rarrashi ga mamkinshi bata janye jikinta ba bare tamishi masifa,hakan ne yasashi jin dadi tareda kara janyota jikin nashi,itama kara shigewa jikin nashi tayi tana rusa kukan takaici don babu abinda take bukata kamar rarrashi ahalin daake ciki.
Saida tayi mai isarta sannan ta janye ta shiga don yo alwala.
Saida ya idar tafito,suna hada ido yawashe baki kamar koda yaushe tareda mikewa daga abin sallar ya kara gyara mata,batace komai ba saima murmushi datayi karfin halin mayar mishi akaro na farko,wani irin farinciki yaji mara misaltuwa don farin cikine dazai iya cewa tunda yake bai tabajin irinshi ba,Aminatu ta murmusa mai,abin sallar ta haye ta tada salla don dama da hijabinta ta kwana.
Aifa haka yafito don nemo mata abinci farincikin shi ya kasa boyuwa sai washe baki yake don badai faraa ba hakika yatabbata yafara nasara hakan shi yafara cimma ruwa inshaallahu sai ta soshi yadda yake sonta koma fiye suma sun zama kamar sauran masoya.
Kodaya tashi dawowa abinci ne niki niki kamar yadda yasaba kawowa,yashigo dasu batareda yajira mezatace bama yazuba mata yatura mata,"maza maza Amarya aci akoshi kar ulcer takamaki don naga kema fa bakyason cin abinci"dan murmushi tayi sama sama don ta fuskanci baya gajiya da magana gashida tsokana da barkaanci burinshi akoda yaushe yaga yasata murmushin farinciki,"banajin yunwa ne kawai"tace batareda ta kalleshi ba,"Safiya ce fa,indai kuma ba a mafarki kikaci kika koshi ba aina kika ci abinci?"yace tareda dauko nashi cokalin,"nima nakin zanci"batareda yajira ansarta ba ya sa cokali yafara ci,"kici fa ko in baki abaki"yasake cewa,"hmm gani yake kamar mun wani saba don na dan mishi murmushi"tace azuciyarta batareda ta dago kanta ba,ganin dai dagaske yake fa yamatso zai batan yasa ta dauki nata cokalin,"zanci shikenan?"murmushi yasakar mata wanda yakara mishi muni.
Baibar dakin ba sai wajen 10 don yace wancen maigadin dayayi aikin dare sai goma zai tafi,zaman dasuka danyi babu yadda baiyi ba wajen ganin tasaki jiki dashi sunsha hira amma kememe takasa.
Sallamar Hally ce tafarkar da ita daga dan baccin daya dauketa,ai cikin tsananin zumudi da farin ciki suka rungume juna suna murna,"hally ina kika shiga,ya akayi kika gano gidan nan?"ta jero mata tambayoyi,"location din da kika turamin ne a watsapp"hakane fa nama manta"takara,"wai meya faru najiki shiru nakira wayoyinki harna gaji har gidanki naje akacemin wai bakwa nan"cewar meena,"hmmmm meena ina cikin tsananin tashin hankali bilal ya cuceni mugu azz...."kuka yaci karfinta,"innalillahi wa inna ilaihi rajiun hally kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki kimin bayani"tace bayan ta rungumeta tana rarrashinta,ai hally bata rage ba bare ta kara ta kwashewa aminiyartata duk yadda abubuwan suka faru,"subhanallah Bilal din?,tace cikin tsananin kidimewa da mamaki,"lallai dan Adam abin tsoro ne hally indai kuwa bilal zai miki haka to banajin akwai macen dazatace wai zata tsira daga takaicin da namiji,yanzu shikenan yakwashe yaran to ina yakaisu?"ta kara,"to wayasanwa mugu,neman duniya ko sama ko kasa babu shi babu labarinshi bare na yaran wallahi idan wani abu yasami yayana bazan taba yafe mishi ba,"tasake fashewa da kuka.
Haka dai meenan tadinga bata baki tana rarrashinta wanda kuwa dayin hakan da rashin yinshi duk dayane wajen hally tadaiji ne kawai amma babu abinda yake mata dadi.
Ganin halinda take ciki ne ma yasa meenan kasa tado da nata zancen domin kuwa ahalin daake ciki hally tafita shiga kunci,yaranta guda uku reras aka kwashe bai kamata ta kara mata bakinciki ba.
"To ya ake ciki ina mutumin ni naga ma sai farinciki kike"?ta katsewa meenan tunani,"hmmm hally nifa jikina yayi sanyi zan hakura kawai incigaba dazama da bawan Allahn nan t...."haba meena,dubeki fa ji yadda kikabi kika zama kowa yaganki yasan kina cikin tsantsar damuwa,kalleki fa a boysquaters kan katifa a matsayin matar maigadi yanzu kina ganin har lokaci yayi dazaki sare ki saddaqar?"cewar hally,"to ya zanyi mutumin nan tunda nazo gidan nan bashida buri banda yaga ya farantamin hally babu rashin mutumcin daban mishi ba duka zagi duk abanza hasalima ban taba ganin ko alamar bacin rai ba a tattare dashi gameda irin
abubuwan danake aikata mishi"meena kwananku nawa dazaki yarda bazai musguna mikiba nifa yanzu nafita harkar maza tunda maciya amana ne Allah ya isa Bilal,"kuka yaci karfinta,"hally wallahi bazan ga laifinki ba don kin dauki tsanar duniya kin dorawa maza kin kuma musu kudin goro,amma kuma yazanyi?"kizo mutafi cen wajensu mama kawai(iyayen hallyn)zasu shige gaba wajen ganin an kwato miki yancinki amma zama cikin kunci anan bazai yiwu ba"
You are reading the story above: TeenFic.Net