ALIYU GADANGA.!

Background color
Font
Font size
Line height

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

_*Daukaka wata abace,Ta dan lokaci in ta Aureka Duniya zata sanka sosai kayi more porpular,and One Time u bcome Cele by Force ohoo😹buh duk lokacin data sakeka kashima yafika Daraja,fans ma zasu daina zencen buk dinka balle akai ga zencenka kazama mar amfani garesu,Shiyasa ka/ki yi Fatan daukaka ko Shahara ita din kamar misalin Duniyace Rigar aroce,in tashiga wanchan gobe zata barkane ta shiga wata,...Shiyasa kazama mai aiki da Hankalinka,kayi komai don Allah sai gaka yama ka sakayyah da kyakyawan sakamako wanda bakayi Tsammani ba✌🤘🙏,...Assalamu Alaikum Janafy Fans*_

          *Chapter 24*

    ""Adaddafe Aliyu ya Fito yana Tafe yana rike maransa,Da Jabir ya cikaro akofar apartment dinshi,yana ganinshi ya isa gareshi yana fadin"Wai captain meyake Faruwa ne? lafiya kake dukewa ko baka da lafiya ne? ina ita Azeemar? yafada yana leka kofar Shiga Falon.

  Ture hannunsa,Aliyu yana fadin"Kasa Ayi bincike acikin barikin nan,Kada abari wani ya Shigo kuma kada wani yafita,da anga wata bakuwar Fuska Juz ku sanar dani.."Yafada yana cije baki saboda azaba Hannunsa Jabir ya riko yana fadin"Look Aliyu nifa ba iya abokinka bane don Allah kafadamin meke Faruwa? Wani Mutum ne ya Shigo,dan Fashi ne,ko ko dai aikoshi akayi ne? Aliyu ya dago kansa idanunsa sunyi jawur,baya Jabir yaja ganin yanayin Aliyun baicemai komai ba ya koma cikin gida,ya Rufo kofar,nan ya sulale yana Rike kansa da hannu daya,Saboda yadda yake saramai,So yake yayi kuka,ammh yakasa zuwa Tunda yazo duniya bayan Abunda ya Faru Ranar Daurin Aurenshi da Ni"ima,bai taba Shiga tashin hankali irin na yau ba,dame ya rage Azeema?wata zuciyar tacemai ammh taya zaka yarda Azeema zata gayyato wani kato,karka manta kai kasameta a burduwa fa? toh ammh in ba hakabane babu wanda keda alhakin Shigo da wani cikin bariki nan sai da wanda yasan wajen? Toh ammh ai ita Azeema batasan ko"ina a barikin nan ba,Toh waye ya Shigo dashi yanunamai gidana? wata zuciyartace waye kuwa banda Azeema babu wanda zai gayyatoshi sama da ita.

Kansa ya Dora bisa Tafin hannunsa yana Kiran Sunan Allah,Yana zaune wajen yasamu kiran Jabir kan yazo Security offoce yanzu,da hanzari ya mike Fuskarsa tayi ja,saboda Bacin rai,koda yaje chan Nan jabir ke mai bayanin bakin Fuskar da"aka samu duk ziyara suka kawoma danginsu nan ya Shiga nunamai mutanen da suka Shigo barikin aranar,ammh baiga Fuskar wanda yake nema ba,da hannu yayima Jabir alamu da a sallamesu kuma abude get kowa ya fita,Jabir ya Shiga damuwa ganin Halin da Aliyu ke ciki,ammh bai bashi Fuskar sanin meke Faruwa ba,don Aliyu yace bazai iya kallon idon Jabir yacemai Azeema yakama da wani acikin gidansa ba,Shiyasa yakasa mai mgana sai dai kawai ya kalleshi yana kada kai.

  Azeema kuwa tunda tabaje akasa take kuka kamar Ranta zai Fita data Runtse ido Mutumin take gani da maganganun dayayimata,da sanda Aliyu ya dakamata tsawa,dataTuna haka sai ta toshe kunni tana sakin kuka,Tana nan kwance tana kuka har sai da muryanta ta Shide dakyar ta Tatashi ta Koma tiolet tayi alwala tazo tayi sallar la"asar tanayi tana kuka,Tana idarwa taji Shigowar yaya captain da hanzari ta mike ta Fito,tsakiyar Falon ta ganshi zaune ya dafe kai,Tunda daga kofar bedroom dinta ta durkushe tana kuka,Matsowa take idanuwanta na tsiyayar hawaye yana jin gunjin kukanta ammh yakasa dagowa ya kalleta saboda yadda zuciyarsa ke tafarfasa,Zumbur ya mike yana juyamata baya da wani irin karfi da Tsawa yace,"Kada ki kuskura kizo kusa dani..Azeema kin cuceni kin ha"inceni,kin kuma cucu aurenki da Yardan da mahaifinki da mahaifiyata sukayimiki,Dame na rage?,meye bana miki,?na baki abinci na baki lokacina nabaki kulawata kai hatta da soyayyata na baki Azeema why"!Why Azeema meyasa kika zabi ki cutar da zuciyata da Abunda zai kasheni har lahira.ehe..Why..? yafada muryansa Tafara rawa.

Juyowa yayi yana kallonta,Yake fadin"Sai dai, kuma bani kadai kika cuta ba Azeema harda kanki domin bazan cigaba da zama dake ba,domin zamanki tare dani watarana zan iya shakeki ki mutu saboda bakinciki gwara na tattaraki na maidama mahaifinki ke,ngda da sakayyah Azeema ngd da yardan dana baki kika cutar da zuciyata Allah nagani bantaba zina ba,kuma...Kuma Ni banta sha'awarta ba,Sai dai in shegentakan da"ake kirana dashi,shine yake bibiyar Rayuwata.."Yafada yana Runtse ido,Dakyar da sodin goshi sililin hawaye ya zubomai guda daya,Azeema da gabadaya hijabinta ya jike da hawaye ta rarrafa da gudu zuwa kafan yaya Captain takama da hannun bibbiyu tana fadin"A"a..A"a kada kayi haka..Wlh tallahi banda masaniya Akan komai,wlh ban..Ban san komai ba don Allah ka tsaya ka bincika don Darajan ma'aiki.."Take fada tana wani Gunjin kuka.

Tsaye yayi yana jin yadda zuciyarsa na Tafasa,Kafa yasa ya shureta tatafi ta bugu da kujera,center table din dake gabansa ya Saka kafa ya buga sai da ya rabe gida biyu,kallonta yayi yana fadin"Saboda haka ki tashi yanzu ki hada duka kayanki,duka nace banison ganin ko Silin gashinki agidan nan,Gobe zan maidake gombe domin Zuciyata bata da karfin gwiwan Sake zama dake.."Daga haka ya shuru kafa yafada daya bedroom din yana huci.

Hannu Azeema ta dora akai tana kuka tana fadin"Innlillahi...Na shiga uku,waye yayimin wannan kazafin,wlh kowaye bazan taba yafemai ba Har Duniya ta nade.."Take Fada tana kuka,kafin tatashi da gudu tashige daki,tafada bisa gado tana ihu tana buga kanta jikin katifa babu mai lallashinta,Shiko Aliyu tunda ya Shiga bedroom din yafada Tiolet ya sakarma kanshi Shower yana sakin ajiyar zuciya.

________________

   Dai dai wajen anguwan Rimi bus stop ta saukeshi Ta damkamai wani Abu abakar leda tana Fadin"Mungode,in wani aikin yataso zamu nemeka,and don't forget ka lura Sosai inajin tsoron ganin Fuskarka dayayi.."Mirmishi yayi yana rike ledan dakyau yace"Bafa ki da mtsala Hajiya aikina ne nasaba.."Kada kai kawai tayi kafin taja motarta tayi cikin Anguwan Rimi.

  Wani Mamaken gida naga tazuba hon megadi yazo ya budemata get ta Sulala ciki,aparking space ta faka motar kafin ta Fito ta nufi cikin gidan,tana Tafe tana cilla key din motar sama cike da Nishadi,ababban Falom gidan ta cikaro da Kanwar mom din nata ita da yaranta,da gudu suka tashi suna mata oyoyo,itama ta rumgumesu tana dariya,dakyar sula barta ta kariso Falon,tana fadin"Mommy kinga Ya"yana zasu kada ni ko? wacce aka kira da mommy na kallah yar matashiyace,wacce bazata wuce Shekara 40 ba,Kallonta tayi kafin tace"Wai ina kika je ne muneera..? Juya idonta tayi kafin tace"Anguwan Sarki naje,gidan wata Friend dina Seeyama,wacce mukayi Sch tare da ita.."Gyada kai kawai matar tayi kafin ta juya ta Nufi hanyar kichen tana fadin"Allah yasa da gaske ne..."Rantsuwar karya Muneera tafara jeromata da hanzari ta dakatar da ita tana fadin"Nifa ba Rantsuwa na tambayeki ba,kawai cewa nayi Allah sa da gaske ne.."Da kallo muneera ta bita tana Tura baki,kafin taja jakarta ta haura sama,tana kunkuni.

Tana Shiga dakin,wayarta ta dauki kara,sai da tazauna bakin gadon ne,ta cirota cikin jaka ta duba ganin mai kiran ne yasa tayi mirmishi ta daga tana Fadin"Sweetheart komai ya tafi kan Tsari harma na sallame gayen.."Dariyan jin dadi Ni"ima tayi kafin tace"Job weldon Sweetheart..Yanzu yaushe zaki dawo mukoma wajen yarinyar...? ajiyar zuciya Muneera ta sauke tana fadin"Gobe insha Allahu,buh wani hanzari ba gudu ba,ita yarinya bafa musan inda zamu sameta ba,kuma bazamu yi Saurin zuwa mujira ko nan da Sati dayane,muga shin aikinmu yayi duk da ina da tabbacin ko ta kwana Akaduna yau,toh ina tabbatar miki gobe a gidan Ubanta zata kwana..."Dariya Ni"ima tayi kafin tace"Kema mganarki Abar dubawa ce,Shikenan sai kin dawon,mganar yarinyar kuma ai bamu da mtsala tafadamama Sunanta,na tabbata in anan area take zamu sameta.."Muneera tace"Ok sai munyi waya.."Daga haka suka yanke kiran zuciyarsu cike da samun Nasara.

   *******************

   ""Koda garin Allah ya waye yadda Aliyu yaga Rana haka yaga dare,Ballatana Azeema data kwana kuka durkushe bisa sujjadarta tana kaima Allah kukanta,ada bata taba Tsorata da al"amarin Azeeza ba koda Abunda yafaru abaya,bata tsorata da Abun ba,sai da Abunda yafaru jiya ya Faru,nan ta yarda duk wanda yayi mata wannan sharhi ta tabbata baya kaunarta,kuma bazai taba Sonta,ba ta yarda ta amince bata da wata mafita domin Anrigaya da ansha Shiryamata Ta yarda bata da yadda zata Fidda kanta.

Kokafin Gare ya waye Fuskarta ta kumbura saboda kuka,idanuwanta kuwa sunchanza kala saboda kuka da Tashin hankali,Shiko Aliyu Tunda ya Shiga dayan bedroom din nan ko motsinshi bataji ba,ta nan zaune bisa darduma bayan ta idar da sallar Asuba,tana addu"a tana kuka,karfe bakwai na safe taji bude kofar bedroom din da Aliyu ke ciki,bata fargaba taji Shigowarshi dakin bai ko kalli inda take ba,ya Furta cikin kakkausan murya.."Ki Fito mu tafi malama.."Yafada kafin ya juya zai Fita,jin ta Fashe da kuka ne,yasa ya dakata yana jin wani Abu na mai daci aransa,Kallonta yayi ta gefen ido kafin yace"Bake ya kamata kiyi kuka ba,nine yakamata na koka,don ni kika zalunta,ammh wannan kukan dakike sai ki dinga nuna Cewa ke aka zalunta.."Daga Haka yafice daga dakin yana jin kamar ya kwanta akasa yayi ta kuka.

Azeema na kuka,ta mike daga ita sai Rigar barci wata doguwa Fara mai Ratsin pink ajikinta,Wani dogon hijabinta ke jikinta wanda take sallah dashi,Akwatunanta dake kan gado ta Shiga saukewa akasa tana kuka,dama tun jiya tahada komai nata,Daukan akwatunan tayi daya bayan daya tana kaisu Falo,harda da kayan kwalliyanta babu abunda tabari,ta kwashe komai nata kamar yadda yace,Dan kit din dake hannunta Shine na karshe ta juya tana ma dakin kallon karshe kafin ta kada kai Tafito tana zubar kwallah,koda Tafito babu Aliyu afalon,kamar da Farko data ganshi tsaye,sabanin yanzu sai wani Soja tagani yanata jiddan akwatunanta zuwa waje,kasake tayi tana share kwallah kafin tabi bayanshi zuwa waje.

    Tana Fitowa ta iske shi Shida Jabir suna Tsaye suna mgana,ammh dukkanasu Fuskokinsu ba Annuri,balle walwala,baya Taja ta Tsaya tana sadda kanta kasa,Jabir yana ganin ta Fito yatako zuwa gabanta yafadin"Azeema ki taimakeni ki Fadamin Abunda ke Faruwa,tunda shi yaki fadamin,Tun jiya na lura wani abu na Faruwa ammh yamin Shuru yanzu kuma gashi kina kwashe kaya don Allah meya Faru..?"Dago idonta tayi dasuka chanza kala tana kallonsa,hawaye suna kwaranyomata,Wani Tsausayin Aliyu ya Tsirgamata,tana kallonsa tana Jin koba komai yayi mata karamci Tunda ya iya boye wannan Sirri,kasa mgana tayi sama jan kafanta datayi da gudu zuwa wajen motar ta bude gidan gaba Tashiga tana kuka mai cin rai,da ido Jabir ke kallonta yana mamakin wannan al"amari,yana kallo Aliyu yazo ya Rufe gidan kafin ya dawo har zai gotashi sai yadawo da baya ya dafa Jabir yana fadin'Am Srry Dude,bafa wani Abu bane wajen goggo zata koma ta Rubuta jarabawarsu ta candy,shine fa kaga munshiga damuwa,ammh babu wani abu ka kwantar da hankalinka yau insha Allahu zan dawo dazarar na kaita bazan tsaya ba.."Juyowa Jabir yayi yana Kallon Aliyu Shiko yaki yarda su hada ido,Girgiza kai kawai Jabir yayi kafin yace"Allah ya kiyaye hanya..." Daga haka kawai yakada kai ya Wuce,don kwata kwata bai yarda da kalaman Aliyu ba,ammh Tunda yana boyemai bazai kara neman yaji ba.

  Da Hanzari Aliyu ya isa ga motar ya Shiga bayan Sojan ya gama Dura kayan Azeema abayan motar,ganinta Zaune agidan gaba ta saka kanta tsakanin Cinyoyinta tana kuka yasa yayi gaggawar Fitowa yana fadin"Plz ki koma baya don Allah,i don"t want to see u in my Side again.."Tana jinsa tayi Saurin danne kukanta ta Fito da Sauri ta bude gidan baya tashiga tana boye Fuskarta cikin hijabi,Sai da ya bata lokaci kafin ya Shigo motar tana jnsa yana karanto addu''ar matafiya ya Daura Belt suka Sulala,basu bata lokaci ba Suka Fita daga cikin barikin kafin su dauki hanyar Gombe.

Karfe goma da wasu mintina Motar Aluyu tayi Parking akofar gidan na goggo,dayake lokacin yayi safe dayawa,shiyasa layin babu kowa,tsit kowa yatafi neman Halali,mataye kuma suna cikin gida,suna Dafa Abun sawa abaka,idonta biyu suka iso,don tunda Suka Fito daga kaduna take kuka,har suka iso gombe,da hanzari Ta bude murfin mota dauke da karamin kit dinta ta Fada gidan goggo da gudu tana kuka,shiko dama bai yi niyyar Shiga ba,waige waige yafarayi kafin ya Hango wani almajiri da hannu yayafitoshi yako zo da Sauri,Yana zuwa ya zura hannu a aljihu ya zaro dari biyar ya mikamai kafin yace"Don Allah kaya zaka Shiganmu dashi Cikin gidan nan..!Yafada yana numa mishi gidan,washe baki almajirin yashigayi yana godiya booth din Aliyu ya budemai yana Fito da akwatunan,shikuma ya fara dauka yana Shiga dashi cikin gidan.

  Goggo na zaune abakin Fomfo tana dauraye yan kayanta taji Fadowar mutum jikinta Ana kuka,ta tsorata ta Waigo da Hamzari tana fadin"Subhannallah waye haka.."?Tafada Tana Rikota Da Hanzari Azeema ta jaye hijabinta kanta tana kallon goggo,Baya goggo taja tana Fadin"Azeema...Azeema,mezan gani haka? keda waye kuka zo?Azeema na kuka tace"Goggo sunyi Nasaran Rabani da yaya captain,Sun rabamu goggo,sunyi Nasara akaina,wayyo Allah na Shiga uku.."Mikewa da hanzari goggo tayi tana Rawan jiki,bata kai ga yin mgana ba,almajiri yayi sallama yana Shigowa da kayan Azeema,da kallo Goggo ke binshi tana kallon Azeema lokaci daya kafin tace"Kedawa kikazo? Runtse ido Azeema tayi kafin tace"Shi ya kawoni yana waje.."Ai goggo ko mayafi bata sanya ba tayi waje da gudu,sai dai tana zuwa Motar Aliyu na barin wajen da hanzari goggo ta Kwalamai kira Tana fadin"Gadanga.."Kai Gadanga.."Ammh ina har Ya kule daga layin.
 

  Baya goggo taja tana dafe kai,Kafin takoma cikin gida,tana bin akwatun nan da almajirin yagama Shigowa dashi da ido,gefe daya kuma tana bin Azeema da kallo wacce tayi zaune akasa hannunta bisa kai tana kuka,duk kammaninta ya chanza bakin goggo na Nauyi tace"Wai Shin Azeema Abunda bangane ba gadanga ya sakeki ne ko yaya,nifa kunsani a cikin duhu don Allah bar kukan nan yimin bayani,naga gabadaya kayanki gasunan meya faru ne? Majina Azeema taja kafin tace"Bai Furta saki gareni ba goggo,ammh yace bazai iya cigaba da zama dani ba..?"

  kusa da ita goggo ta kariso tana fadin"Kam wani dalili..? nace kan wani dalili ko ya dauka aure Shiga jeji ne koko harbin bindigane..?Goggo tafada cikin bacin rai,bakinta Azeema ta dafe tana fadin"Wlh ban aikata ba goggo,Sharri ne,kuma bansan wanda ya aikatamin haka ba,kuma bansan dalilin kowaye ba."Kuri goggo tamata da ido kafin ta sanya hannu ta rikota tana Fadin"Daina kuka Azeema,taso mu shiga daki,ki warwaremin komai,insha Allahu ina tare dake.."Tafada tana rikota suka Shiga daki,Kan kujera goggo ta zaunar da ita,kafin takoma ta rika jido akwatunan Azeema tana Shigowa dashi,gefe daya na zuciyarta tana cike da takaichin wulakancin da gadanga ya yayi mata,ai ko miye Azeema tayimai ya kirata awaya su tattauna ammh dayake wulakanci ya Shirya harda kawota da kanshi,kuma yajuya yayi Tafiyarshi,wlh zai zo ya sameta zai ya gane ita ba"a mata iskanci Ja'irin yaro kawai.




*Intelligent writer"S Asso*
*Janafty..*

You are reading the story above: TeenFic.Net