ALIYU GADANGA..

Background color
Font
Font size
Line height

*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

*Dedicated to UMAIMA ALIYU...Tanque dear for ur Wonderful Comments*

        *Chapter 17*

   """Washegari da duku duku goggo tagama Shiryama Azeema duka kayanta ta sakata tayi wanka ta shirya cikin wani leshi mai Ruwan Kasa da zanen fulawan brown ajikinsa sai Farin hijabinta data sanya wanda ya wuce gwiwanta da kadan,goggo na cikin Shiryamata Sauran kayan nata cikin babban akwatinta wacce ta siyamata gadanga ya tarar dasu cikin daki Shima cikin Shirinsa na Riga da wando,rigar light blue ne,sai wandon baki ne,kafarsa sanye cikin wani takalmi mai Rufi baki kansa kuwa sanye da hula p-cap sai wata katuwar jakar bayansa,wacce take rataye abayansa kallo daya zakamai ka fahimci ya mallaki dukkan zati da jarumta goggo na ganinshi tace"Badai wai har ka Fito ba gadanga..? rausayar dakai yayi kafin ya tsugguna yana gaisheta amsawa tayi tana fadin"Kwa tsaya ku karya ko gadanga,kuma sai ka biya da ita tayima kakarta sallama,tunda tafiyace ba yau za"a dawo ba,kuma ba gobe,ko saboda halin Rayuwa.

  Mikewa gadanga yayi kafin yace"Goggo na yanke wata shawara,kawai kema ki Shirya naki kayan mutafi tare dake da Baba Aden da ita Azeemar,yanzu nagama ma Baba bayanin Allah barshi in zamu tafi tashiga tayimai sallama koya kika gani? Dan jim goggo tayi tana kallon Azeema wacce ke zaune gefen gado tayi Rau rau dab ido kada kai tayi kafin tace,,"Eh kuma kaima kace wani Abu bai kamata Azeemar takai kanta ita kadai ba,bari na Shirya sai mu biya mu dauki Baba Aden nasan ba mtsala me ko kawunka zaiji dadin ganina kullum mukayi waya sun dingamin dan kida kenan Shida Umaimah.."Mirmishi Gadanga yayi kafin yace",Kema goggo kin nacema gombe nan kamar wani ya kafeki ciki kodai kodai.."Keyarsa ta maka da Rigar dake hannunta tana fadin"Kodai me,Ja"iri Fita falo kajiramu gamunan zuwa Dan kawai.."Dariya yayi yana fadin"Allah baki hakuri goggon Gadanga,ai ni babban burina shine mutafi bariki tare muyi zamanmu mu uku na tabbata Azeemar taki zata fi jin dadin zama sosai.."Kallon Azeema Goggo tayi sukayi mirmishi atare kada kai goggo tayi tana fadin"Allah ya shiryamin kai gadanga.."Take fada tana mirmishi ita kadai.

Cikin lokaci goggo tagama hada nata kayan dama tayi wanka karyawa kadai sukayi suka kulle ko"ina suka Fito Aliyu shiya kwashi akwatun yasaka amota bayan ya Fito da motar daga gareji,goggo da kanta ta tasa Azeema zuwa cikin gidansu,domin tayi bankwana da mahaifinta koda suka Shiga cikin gidan suna sallama,ba wanda ya leko sai mallam lawal,din nan fa yatasa Azeema yana ta mata Nasiha sosai tare da horar da ita hakuri da kuma yin biyayyah ga mijinta daga karshe ya dafa kanta yana fadin"Allah yayi miki albarka Azeema yakuma albarkaci Aurenku keda Aliyu ya kareku da dukkan sharri,Allah ya kade Dukkan Fitina atsakaninku yakuma baku zuru"a dayyaba tashi kuje Allah ya tsare hanya yakuma kaiku lafiya.."Da Amin take amsawa tana kuka sosai hawayenta na shatata wanda ita kanta goggo sai da tayi kwallah Sun mike zasu Fita Azeema ta waiga kofar dakin Inna Ramatu wacce ke tsaye ta Fito ganin Abunda ke faruwa,ganin ta waigo sai tayi Saurin sakar labule ta koma,kada kai tayi sai kuma idonta karaf kan dakin dasuke kwana ida da Azeeza nan ta hango jikin window dakin tana hawaye,Kallon ido cikin ido sukema juna kowacce da Abunda take sakawa Aranta kafin Azeema tajuya tana share kwallah tabi bayan goggo suka fice tana ma gidan wani kallo mai kama dana karshe.

Suna Fitowa ko ganin Azeema tana kuka baisa gadanga ya tambayi ba"asi ba,suka Shiga mota suka nufi gidan Baba Ade,ko da suka shiga cikin gida Goggo ta koramata jawabi,baba Ade guda ta saki tana korama gadanga Albarka tare da Fatan Nasara bata ta bata wani lokaci ba tashiga ciki ta gyara jikinta ta dauko yan kayanta kala biyu ta rufo dakinta tama matar datasa haya agidan makulli suka fito suka Shiga mota,Dakyar Azeema ta yarda ta shiga gaba sai da goggo tamata ta jan ido kana,Shiko Aliyu kalloma Azeemar bata isheshi ba,don mganar gaskiya haushinta haryanzu bai gama sakinsa ba,sakamakon goggo na motar gadanga bai samu damar shararan gudu kamar yadda ya saba basu iso kaduna ba sai after 3:00pm na Rana,kai tsaye anguwan Rimi ya isa dasu wato gidan kawu bala kenan,wani makeken gida mai kama da aljanar Duniya ga security nan tako"ina agidan yadda kukasan gidan wani gwamna ko mataimaki,motoci kuwa baka iya kirga iyakarsu aharabar gidan,bazata ka taba kallon goggo da gadanga kayi Tunanin suna da dan"uwa mai tarin dukiya da mtsayin irin haka ba,duba da inda ita kanta goggo ke rayuwa ammh ko ajikinta donta Fi son gombe Fiye da shigowarta kaduna,don ko banza tanajin kamshi zaria in ta shigota Shiyasa bata kaunar nesa da gombe don koba komai goggo tace garin Shiya Rufamata asirin lokaci da garin na zaria suka nemi su tona mata.

  Hajiya Umaima Sai dai kawai taga baki daga sama,ai bakinta yaki Rufuwa saboda murna a babban Falon gidan aka saukesu,nan da nan masu aiki suka cika gabansu da kayan ciye ciye dana Shaye shaye,Awaya Ummah takira kawu tana Sanar dashi zuwan goggo,farinciki dayake ciki ne yasa bai dau wani lokaci ba yataho gidan,koda yazo bai tarar da gadanga ba,don na yabar su goggo yashiga barrak saboda major na chan na jiransa.

  Kawu yana Shigo falon sanye da shadda riga da wando harda babban Riga,Bakinsa saboda murna yaki Rufuwa,Hannu ya warema Suwaiba yana Fadin"Taho Taho Suwaiba so nake na tabbatar da ba mafarki nake ba.."Dariya goggo take itada Ummah,Tashi tayi ta isa gareshi ya rumgumeta yana dariyan Farinciki yake fadin",Ashe dai da gaske ne,Suwaiba rabon ki da gidan nan Tun Bikin su madina fa..",Ummah tayi karaf tace,",YAu din ma ta rako surukarta ne da kila bazata zoba sai wani lbri mara dadi ya isheta.."Dariya kawai goggo keyi kan tace"ni bazan ce miki komai ba Umaimah dama kin saba min Sharri,ai yaya yasan komai...",gabadayansu dariya sukayi kafin sukarisa cikin Falon tare,nan ya duka yana gaida baba Ade,Azeema ta gaisheshi ya amsa yana ta saka mata albarka,basu samu zama sai da yaje yayi wanka yaci abinci sukuma aka kaisu masauki sukaci abinci suka huta kana Kawu yanemi ganawar Sirri da Goggo,nan take karantamai Duk Abunda yafaru Ummah na wajen sai da ta rike baki tana fadin"Goggo ita wannan yarinyar? koda yake fa ana tsontson bala"i a nono,don Ramatu ba kanwar lasa bane,ammh goggo inagani  mikama Gadanga Azeema yatafi da ita bariki,Ba masalaha bace,tunda yarinyar bata iya komai ba,kinsa fa bariki baruwan kowa da kowa kuma shi gadanga Namiji ne ba lalle bane yasan Abunda yadace da ita ba,kuma goggo a mikata hakanan babu wani gyaran mata.."Tafada tana yar dariya,girgiza kai kawai Kawu yayi yana fadin"Allah Shiryeki Umaimah sam baki da girma sai najikin ki.."Dariya tayi tana kallonasa tace,"Haba Ranka yadade ina girman yake,haryanzu ina cin lokaci na,banda kowani da agabana saboda haka yanzu zankira madina in fadamata kana na tura direba yakai ita Azeemar chan ko sati daya tayimata insha Allahu nasan kafin lokaci komai zai daidaita.."Jinjina kai goggo tayi tana fadin"Mungode Umaimah hakika kin bada gudummuwa wanda yakamata uwa taba yarta Allah yayi miki sakayyah da gidan Aljannah,ammh zaki kira shu gadangan ki fadamai ko? Ummah tace"Eh zamu mgana dashi,yanzu dai bari na fara kiran Madina,goggo ke kije ki sanar da Baba Ade da Azeema yanzu direba zai karisa da ita.."Tana gama fadar haka ta haura sama tana Faman latsa wayar hannunta,da kallo kawu yabita Yana yar dariya,sam umaimah ba ruwanta ko da ya'yanta haka take,ta dauki kanta tamkar wata yayarsu ba uwaba,ballatana Haisam,wanda tamkar kaninta,saboda shakuwar da yaranta,duk duniya basu iya sharing damuwarsu da kowa sai da ita,saboda macece datasan rayuwa tana da ilimin Addini da na bokon duka gabadaya shiyasata take amfani dashi wajen mu'amalarta tayau da kullum,ajiyar zuciya ya sauke kan yadawo da ganinsa kan talabijin yana kallon Tashar aljazeera,domin itama goggo Tuni ta tashi ta barshi nan zaune.

Ummah tana kiran Madina awaya ta labarta mata komai tace"ga Azeemar nan Direba zai kawota,komai suke bukata kawai tayi mata waya,kuma karta sake ya fadama Captain ga Abunda suka shirya ko yakirata tacemai Taje mata kwana biyu"Cikin jin dadi Madina ta amsa ma Ummah suka rabu akan sai Azeemar tazo,suna gama wayar ta sauko ta shiga dakin da'a ka sauke su Azeema ta tarar da ita tsaye goggo na musu bayani,ganin haka yasa tace"Na shirya..? goggo tace "Eh.."Shiga dakin Ummah tayi ta dauko akwatin Azeema tana fadin"Wannan ne akwatun ta ko? amsa goggo ta bata,hanyar Ficewa tayi kafin ta riko hannu Azeema tana Fadin"Zo muje diyata direba na jiranki awaje.."albarka baba Ade tayi ta sakama Ummah,itako Azeema bata wani damu ba saboda jin ance gidan Anty madina,tana santa tana da kirki gashi tana matukar son yaranta yan biyu mata,Hibba da Hidaya,Yarane masu Shiga rai,in suka zo gidan goggo ta dinga hidima dasu kenan,kusan mai da wawa,nan da nan Azeema ta shiga ranta sosai,har alhere suna mata ita da Anty mardiya.

  Ummah ita tafita da Azeema har haraban gidan indan Direba ke jiranta,bata tare da bata lokaci ba,ta bude gidan baya na motar Venza2k19,tare da kayanta tana fadin"Toh diyata ki natsu kinji,ki kuma maida hankali wajen koyon Duk Abunda madina zata koya miki kinji ko? kai Azeema tagyada tana fadin,"Insha Allahu Ummah.."Rufe mata murfin motan Ummah Tayi tana fadin"Allah yayi miki albarka Sai munyi waya kenan ko? kai Azeema ta gyada mata kan Direba yaja mota su danna hon megadi ya wangale get suka Fice da gudu,Azeema tabi gidan da kallo tana jinjina kyau da tsari irin na gidan kawu bala.

  Bisa hanya haka Azeema ta saki baki da hanci tana karema Kaduna kallo,ashe haka take kyau da tsari,gidaje kerarru sai wanda yagani,Nan da nan Abun ya Shiga burgeta ko"ina suka wuce sai wasu classic mata take gani kowacce na harkan gabanta,wasu su suke tuka kansu cike da ilimi da wayewa,wasu kuma Direba ke tukasu suma din cike da wayewa,lokaci daya Azeema tagane Kaduna ba na zaman irinsu bane,don in baka da wayewa tuni za"ayi baka,nam da nan ta kudirta aranta zata cire komai takoyo duk Abunda aka koyamata domin nan Duniya bata wanda yafiyemata Yaya captain da goggo da Ahalinta,babanta kadai gareta,shikuma baida wani iko akanta inna Ramatu kuma bata da wacce ta tsana sama da ita,ga yar"uwanta kwaya daya datake kallo taji Sanyi Azeeza da bakinta ta Furta bata da wata makiyiya kamarta,Tundaga lokacin ta farka daga Nanannauyan barcin daya kwasheta Ta fahimci mutanen datake kokarin yima butulci sune nata ba wasu ba.

  Gidan Madina yana anguwar Sarki ne,mijinta Controller ne,yana lagos yana aiki,Suna zuwa mamaken get din gidan suka zuba hon maigadi ya budemusu,suka rankaya cikin gidan,Madina na haraban gidan da kanta tazo taran Azeema,tunda ummah ta sake kiranta ta Fadamata Azeemar na bisa hanya,tana sanye da wani leshi mai Ruwan hot,ta karya daurin Zahra buhari,fuskarta dauke da simple makeup kallo daya zakamata kasan yes ta amsa sunanta na mace,domin madina macece mai wayewa da sanin duniya,shiyasa Mijinta Ahmed kallo Sauran mata yake matsayin basu san komai ba

  Da hanzari ta karisa ta budema Azeemar murfin motan Tana fadin"Maraba da Antyn Hibba da hidaya,yau in suka dawo mkranta zasuyi ihun murna in suka ganki.."Take fada tana mata dariya,Fitowa daga motan Azeema tayi,tana kokarin dukawa tagaisheta,tayi Saurin rikota tana fadin"Sannu da zuwa Azeema,kona ce matar yaya ko? Sunne kai Azeema tayi tana mirmishi Rikota tayi tana kwalama yar aikinta kira,tana fadamata tazo ta dauko akwatin Azeema,takai mata dakin dake kallon nasu hidaya.

   Suna Shiga babban Falon gidan sai Azeema tazama yar kauye balle da kafarta ta nutse cikin lallausan Chinese capet din dake malale afalon,Haka ta saki baki tana bin Falon da kallo,kan daya daga cikin Royal chairs din dake falon ta zaunar da ita,da kanta ta kawomata Ruwa da drinks,tasha kafin ta rakata dakin da"aka kai akwatinta,shima dakine nagani na Fada,gado da wardrope sai madubi da tiolet,shikanshi gyare tsaf,Madina ta Shiga toilet ta hadama Azeema Ruwan wanka ta fito tana fadin"Matar yaya,shiga Tiolet ki watsa Ruwa,kizo kici abinci ki kwanta ki warware gajiya kafin anjuma mu fara Aikin namu ko?"Mirmishi Azeema tayi kafin tace"Ngd Anty madina..."Itama mirmishin tamaida mata tana fadin"Ah bakomai,yayana fa zan gyaramawa,to meye namin godiya hop dai u are ready..? kunya takama Azeema sai ta Rufe fuska Ficewa madina tayi tana fadin"Wai kunyata kikeji,dankari,toh kinga kima daina Tun Wuri,don kunni zaki bude ki kwashi lacra yarinya.."Ta fice tare ds jawo mata kofa,Hijabinta ta cire tana bin dakin da kallo,kafin ta fada tiolet din,chan ma bakauya ta zama ashe bayin gidan goggo bakomai bane,akan wannam,dakyar dai Azeema tayi,wanka,ammh kusan Rabin wanka duk takareshine wajen kallon kanta amadubi,kafin ta fito,tana Fitowa daga Anty madina adakin tana Bude mata wani lotion tana ganinta tace"Yauwa kinfito,ga mai kishafa,bari na dauko miki wasu kayan ki chanza,ki Fara daukan karatunmu Tun yanzu kowani wanka to danashi sabon salon Dreesing din,kinji ko?gyada kai Azeema tayi kafin ta karisa Fitowa,jikinta dauke da kayan jikinta data Shiga dasu,Akwatinta dora bisa gado ta bude ta zazzage kayan ciki,tsaki taja tana daga kayan tace"Gaskiya muna bukatar kudi,domin chanjin kayanki,Lalle ne su goggo nan toh da Nufinsu da wannan kayan da zaki gidan miji,bari na kira Ummah yanzu sakawanan kila anjuma mu fita kasuwa ki zabi kayansawa,daganan mu biya ki wanke kanki ko? gyada mata kai Azeema tayi tana ansam doguwar rigar abayar da Anty madina ke mikamata,ficewa tayi da hanzari Dakinta takoma ta dauki waya ta kira Ummah.

Ummah na tare da kawu bala,kiran Madina ya Shigo mata cike da zumudi ta dauka tana Fadin"Makka da madina ya akayi ne? Tura baki Madina tayi kafin tace"Toh ku Ummah kuna nufin haka zaku kai diyar taku babu kayan kirki,yanzu na bude akwatinta wlh babu kayan kwalliya na mata ko kadan.."Ummah tace"Topha to yanzu yaza'ayi Hajiya madina.."Madina tace"Kudi muke bukata Ummah,da zan Shiga kasuwa nayi mata siyayyah,sai sauran kayan gyaran da zan Hada mata,da wanda zatayi amfani dashi anan harda wanda zata tafi dashi"Ummah ta jinjina kai tace"Ok tom ba damuwa bari nayi miki Transfer din 2 hundred Thousand yanzu ai zasu isa ko? Madina tace"In ma basu isa ba,Ummah zan yi ciko,ai Matar yaya ne,so antytin for him aie.."Tafada tana dariya,kashe wayar Ummah tayi tana fadin'"Allah ya Shiryeki Madina.."Kawu na gefe yace"Harda uwar Madinar itama Allah ya Shiryata.."Dariya Ummah ta kece dashi batayi mgana ba.

  Kawu yace"Naji ana mganar kudi ne,babu bukatar taimako na.."girgiza kai Ummah tayi tana Fadin"Babu bukatar Taimakon yallabai anan,kai kagama naka,Tunda ka biya sadaki kuma ka karbo Auren,barmu da Sauran mu makarisa Abunmu.."Gyada kai yayi yana fadin'Hakane.."Tace"Eh mana.."Maida kansa yayi kan kujera yayi yana fadin"Allah bada sa"a ammh a sassautama Dana don Allah.."Wani kallo Ummah tayi kafin tace"Toh yallabai..."Tafada tana dariya Shima yar dariya yakeyi,nan take tama Madina Tranafer din kudin datace,kawu bai damu ba domin yasan halin Umaima indai tana dashi toh babu Abunda bazata iyayimai ba,balle ma ita Aliyu tamkar uwa da Danta ne.

  Shiko Aliyu tunda ya Shiga bariki abubuwa suka mai yawa,sai zuwa darene,ya samu kiran Ummah tana Shaidamai Azeema tana wajen Madina zatayi sati awajenta kafin Su kawota nan Barrak din,Ummah ta fake ne da cewa akwai wani dan gyare gyare da sukeyene,bai damu ba yace Bakomai,dayake Aliyu Namiji ne,kuma Soja,so kwakwalwarsa bata kawomai wani gyara akema Azeema ba,yafi bada kila lalle za"ayi mata da kitso,kowani Abu dabam😂Shiyasa bai damu ba,bai samu komawa gidan kawu ba yabari sai dai da safe,in jabir ya dawo suzo tare dashi Tunda shi bai samu dawowa Aranar ba sai washegari.

Suko Su Azeema basu tafi kasuwa Aranar ba saboda yammah tayi,gashi su hibba sun dawo daga sch nan fa suna cin karo da Azeema sukayita ihun murna kamar su maidata ciki sun hanata sakat,itako tana biye musu Ranar ko Maminsu basu bi ta kanta ba,hatta cire musu uniform da saka musu kaya na Azeema sukace suna so tayi musu,wanu homework ne,harda yar goye goye duk ita kadai,dayake kuma ta saba da yaran,kuma kunsan Aduniya babu aikin da zai gagari Azeema sai dai in ba"a kirkiroshi ba,Karshenta dai Ranar dakinta suka tattara sukace wlh chan zasu kwana har jan madina tayi musu suka makale su Tare Anty Azeema zasu kwana,Azeemar ta roki,Anty madinar kafin ta kyalesu su kwana,aiko sun kai wajen 11 suna hira,kafin su kwanta,ta Shege tsakiyarsu kaunarsu na Ratsata tana fatan kada Allah ya Dau Ranta sai ta haifi mace ta sakamata Suna FATEEMA..,Niko nace karki damu Azeema very soon Aliyu zai baki kwan haihuwa🙈🙈

  Sai washegari suka samu Tafiya,bayan yaran Sun tafi mkranta,kasuwa suka Shiga Madina ta darzomata Atamfofi Masu Rai da lafiya super,holland,swices less,codde less,material dogayen Rigana,masu sikat da masu wando,Mini sikat da mini wandunan,bras,pants,kayan kwalliya komai da komai da kayan mata sai da ta siyamata harda takalma masu Tsini da Flat,sai kananun jaka,dan kunne,masu sarka da Fashion Bands,da sauransu kafin su wuce shagon dinkinta,tabada dinkunan kayan,wata in yamurace bosse,ta gwada Azeemar tace jibi ta aiko direba ya karbi dinkunar,bayan madinar ta ijiyemata kudinta cash,suna Fitowa dagana shagon salon takaita aka wankemata kai harda gyaran kafa sukayimata,wajen harda gyaran jiki sunayi,ammh sanin itama madinar sana"arta kenan basu mata tayi ba,domin sun santa tun Tuna budurwa suke gyaramata kai,ta yarda da shagon sun san aikinsu sosai,basu dau lokaci ba,suka kammallamata sai ga gashin Azeema ya mike sosai yayi kyau kamar ba ita,ba kudinsu tayi musu Transfer ta banki suka Fito suka wuce,daganan anguwan Rimi suka biya gidan wata kawarta SALAMATU FODIO SG GUMBI..Ta amshi wasu tsimi ahannunta tare da Wasu garin magani cikin wasu robobi,dayake sana"arta kenan itama,basu wani jima ba,daganan suka koma gida,suna komawa gida,madina ta shiga tiolet ta hadamata Ruwan Turaruka masu tsada hadin yan maiduguri ne,ta umarceta data Shiga tayi wanka,ita kuma ta sanya wani kasko ta kunna Hurashi ta watsa Turare,tana Fitowa da digon Ruwan ta Umarceta data tsugguna hayakin Turaren ya dinga shiganta,ba gaddama Azeema tayi yarda Madina tace,sai da ya sike kana tace tatashi,wani hadin mai shima cike yake da wasu hadin Turaruka tabata tace daga yau yazama man shafawanta,karba tayi ta shafa,kayan da suka siyo ta zazzage pants dinta ciro mata kafin ta miko mata wata kwalba tana fadin"Rike wannan almiski ne,zaki dinga digama wandunan ki kafin ki sanya kinji ko? amsa Azeema tayi tana fadin"Naji Anty.."wani riga da Sikat Madina ta mikamata tana fadin"Karbi ki sanyasu,wadandan Dressing din,duk bayan kin daidaici lokacin dawowar yaya captain ya kusa zakiyisu,ammh bayan kin tabbatar da Dinner dinshi is ready kinji ko.."kai Azeema ta gyada tana Fadin"Naji Anty.."kada kai tayi tana fadin"Shirya bari baje na hada miki Sauran magungunar ga Turaran wankan chan a tiolet sau biyar akowanni Rana,Kowani wanka Murfin jarka Uku zaki sanya,na sati daya ne,bari na kawo miki Sauran na garin akwai na karin Ni"ima kana kuma akwai na mganin infection ma"ana Sanyi..."Gyada mata kai Azeema tayi alamun ta Gane ficewa tayi tana fadin"In mun gama da wadanan kingane sai mu dora da lacran mu,munayi lokaci daya kuma muna Shiga kichen tare,domin kinsan Duk wadananan Abubuwan basu tasiri,sai Mace ta kasance ta iya sarrafa mai gida ta hanyar iya girki,balle nasan Sojiji da son cin Abinci mai dadi.."Tana fada tana yar dariya kan Ta fice daga daki.

Yar Dariya Azeema tayi tana bin Tulin kayan da suka siyo wadanda ke zube bisa gado,kayan da Anty tace ta saka take bi da kallo,Tana mamakin yadda zata sakasu,sai da bazata iya bama Anty madina kunya ba,da hanzari ta sakasu,kayan roba ne sai suka lafe bisa jikinta gashi

You are reading the story above: TeenFic.Net