10-15

Background color
Font
Font size
Line height

ABLA💞

By Rasheedah Dalha

Dare
     Umma da safna sunje gida, ita da mama kawai aka bari a asibitin  tana nan zaune akan dadduma sai aikin tunanin mutumin da'azun take ta kasa cire shi a ranta ga wani irin haushin sa da take taji. abba da bai dade da dawo normal ba yace mama na tunanin mai kike haka,
   Da sauri taje gunshi ta rike hannun shi tace abba har baccin ya ishe ka?  murmushi yayi yace eh mamana,
   kanta tasa a kafadan shi tana kuka a hankali yace toh mai abun kuka bagashi na warke bah, gyara zamansa yayi ya dago kanta tana kallon shi yace mamana kidaina kukan nan kinji koh,
   Addu'a zaki min Allah ya bani lafiya tace toh Allah ya baka lafiya yace ameeen. 
     mama data idar da sallar isha tace yanzu daga ya tashi bazaki bar shi ya huta ba yar nan, abba yace ina ruwan ki, nan tace Malam karban bakinta kake kenan, abba yace eh mana ai mamana ce,mama tace toh nima maganina kenan duk suka danyi dariya mama ta tambayi abba ya jikin.
   Wayan abla ce tayi kara Abba yace abla ba wayan ki bane ke kara,abla tace nawa ne tare da daukar wayar murmushi tayi ganin wanda ke kiran, Abba yace wannan murmushin fah, a kunyace ta dukar da kanta mama ta dauke kai hakan yasa Abba fahimtar wani abu amma sai ya waske mama ce tace kifita ki ansa wayar karki dame malam,dasauri ta fice. Abba yayi murmushi,mama ta mika mashi fruits tace gashi kasha inkabi na wannan kam shirmen ta dayawa yake.
  
   Kan tafita ma kiran ta katse tana shirin kiran shi ya sake kiranta daga wayan tayi tasa a kunnen ta yace nisful hayati?uhm ta amsa yace ina kika bar wayan ne tace ina busy ne,  yace to fito wajen asibitin tace toh,
   Bayan ta sanar da mama ta fita sunyi hirar su ta masoya daga karshe dai ya gaida abba ya aje masu leda tarako shi har motan shi yata fi.
    Waye abla?
asalin sunan ta maryam Ahmadu maidoya mamanta umma shuwa ce abba kuma bahaushe ne, mama kishiyar Umma ce kuma suna zaman lafiya. Yayin ta uku mata duk sunyi aure sai kanwarta safna
    Shekaranta ashirin 20 kuma tana 200level Buk,wannan kenan.
  

    Mai martaba sarki Al-hussain shine sarki na 24 a masarautar kano yana da mata uku da ya'ya bakwai rahmatu itace matar sa na farko ya'yanta uku Aisha sai Muhammad sai Abdulrahman. Bayan rasuwar sarki sai aka nada babbar dansa wato Muhammad sarki  shekara biyar yayi yana mulki ya kamu da ciwo lokacin matarsa fulani bingel nada ya'ya biyu zeena mai shekara hudu sai murad mai biyu.
  Anyi maganin asibiti dana gida amma abin ya gagara. Fulani ke jinyar shi hakan yasa murad ya koma gun matar kanin mai martaba hamida (wato Sokoto kenan).
   Sarki yayi jinya kusan shekara uku kafin ya rasu, gashi lokacin murad yayi kankanta shiyasa aka nada Abdulrahman kanin sarki a matsayin sarki da sharadin idan murad ya kai 35 zai hau mulki.
    Hamida tayi murna sosai yanzu tazama bingel sai dai kash mai martaba sarki Abdulrahman yace maman su murad zata cigaba da zama bingel ita hamida an bata fulani Sokoto,ranta baiso ba amma haka ta hakura ta yarda.
   Murad dan shekara biyar kasancewar yasaba da Sokoto yasa ya ki koma gun bingel.
  Itama bingel kyaleshi tayi ganin bai chanchanta ta karbe shiba kuma ai intayi hakan bata kyauta bah.
  Sarki Abdulrahman sarki ne na kwarai mai rike gaskiya baya zalunci sai adalci kuma yana matukar son murad da zeena kaman yayansa musaman murad, yaron ya shiga ransa tun yana karami kuma haryanzu, burin sa yaga ya bashi mulki ya kuma ga yadda zaiyi mulkin dan ya yadda da tarbiyan shi ga kuma basira da wayo.
  Halayan murad sak na babanshi ne killa shiyasa mai martaba na sonshi sosai fiyema da yayansa sai dai yana kokarin boyewa.
   Wannan son dake tsakanin murad da mai martaba na bata ma Sokoto rai sosai Amman take boyewa saidai ma ta nuna tana tsananin sonshi  hankan ma yasa saida tasan yadda tayi tasa aka kaishi karatu a UK yana 10years, bai dawo ba saida ya zama medical doctor mai  martaba yayi murna sosai yasa aka gina mishi hospital dinshi.
     Sokoto ganin intayi da wasa toh fa da gaske murad zai zama sarki bayan gata da yaran maza har hudu baban su yarima adam yama girme murad din yana da mata har biyu amma shi adam din sokone aganinta wai bai damu da sarautar ba yana jiran ta masa komai.
   Hakan yasa taso ta aura ma murad yar autar ta Sakina inma ya zama sarkin su juya shi yadda suke so,  tako yi nasara don soyyaya mai karfi ta shiga tsakanin su har anfara maganan aure wata kawar sakina tazo ta hure mata kunne wai suje karatun masters kasan waje ai in yarima murad na sonta zai jirata tunda shekara uku ne ita kuma sakina ta yarda daman idonta a bude yake.
   Sakina tace ma mai martaba saidai a daga bikin tayi masters ta dawo babu yanda ba'ayi da ita ba taki yarda hakan ba karamin girgiza murad yayi ba har yayi ciwo amma sam taki Sokoto ba karamin haushi taji ba, sarki kuma cewa yayi sakina bata isa ta sashi fasa abinda yayi niyya ba amma fulani bingel tace tunda ga abinda yarinya keso toh ayi hakan kawai kar kuma daga baya aji kunya,
   Dai daga baya sarki yace abarta ta tafi, bata tafi ba saida suka shirya da murad kuma yace zai jirata.
    Farkon tafiyar sakinah London suna soyyayar su daga baya ta daina daukan calls dinshi dan ta bude chaptern siyan tane acan.
   Yanzu dai murad is 31 yrs kuma shine MD din Al-Hussain Murad General Hospital.

   🙏Comments  I wanna hear your views. Bazan sake updating ba sainaga ruwan comments.
   

Not editted

You are reading the story above: TeenFic.Net