9/10

Background color
Font
Font size
Line height

___________________

Su Hajiya Binta da sauran matan manyan jahar sun tattauna sosai akan samu voters card ɗin mutanen da ke ƙauyukan jahar, sun kai kusan 40mnts suna abu ɗaya kiran auta Rahma  ne ya sa Mommy tashi tana faɗin " to ni zan koma duk yanda mukayi da su Ladidin zan sanar da ku"  sannan ta amsa kiran, tun kafin Mommy tayi magana Rahma ta ce" wai kina ina har yanzu baki dawo ba, banason su  Farrah su zo bakya nan" ta ƙarasa a shagwaɓe.
Mommy ta ce"to auta ina   hanya bani minti 5 kacal, ina Yayanku i hope dai babu wani abu ko?" Rahma ta ce " nothing Mommy suna sama tare da Ya Musty" okay Mommy ta faɗa tana isowa  bakin parking space mota driver Mus'ab ya buɗe da sauri ta shiga suka nufi gida.

Mommy na fita sauran Hajiyoyin ma suka yi sallama da  Hajiya Rashida suka tafi.

Ihsan ce taga yanda masu aiki suke ta kai kawo tsakanin kitchen da kuma dinning area, ganin Rahma na zaune tana ta faman kiran waya tana faɗin ina jiranku fa, Fatima wacce ake kira da (Ihsan) dan sunan Mommy aka sa mata ta ce" wai suwaye za su zo ne  kike ta wannan abu?" Rahma ta ce "kai Ihsan yanzu baki san su Farrah ne za su zo ba, tun fa last week suka faɗa"
Ihsan ta ce "wow Allah ya sa da my life za su zo" Rahma ta taɓe baki ta ce "mtsww ni wallahi bansan me  zakiyi da wannan yaron ba, ba shi da wani abunyi sai shan shisha har a class ma ba sa shayin kowa amma ke  wai sonsa kike wannan ai abun kunya ne, to ni banyi invited ɗin team ɗin Sameer ba" ta na hararar yayarta ta gami da ɗauke kanta, Ihsan ta ce "okay kin kyauta ba dai su Farrah ne zasu zo ba, wallahi sai na wulaƙanta su a gidan nan indai suka zo" da sauri Rahma ta dawo  ta ce "haba sis ni fa da wasa nake miki har su zasu zo  ai" batare da Ihsan ta furta komai ba ta wuce sama.

Da sauri Rahma ta fara neman contact ɗin Sameer a cikin group ɗin su na Hamdan Academy samun number Sameer tayi ta ɗauka hannunta har rawa yake tayi dialing number ɗin.

Zaune yake a garden ɗin gidansu shi da su Rashid da Al_amin abokansa su na  gambling (caca), gaba ɗayansu under-eigh ne babu wanda ya haura eighteen years, ganin sunan Rahma G.G ne ya sa ya ɗauka dan yana using true-caller, cikin sauri Rahma ta ce "hello Sameer" Sameer ya ce " yeah G.G ykk?" Rahma ta ce " ina inviting ɗinka gidanmu yau please dan Allah kar ka ce ba za ka zo ba" Sameer ya saki murmushi ya ce " zan zo ai dan Farrah ta sanar da ni ma, ina my life?" sanin Ihsan yake nufi ta ce "ta na nan tana ta faman yi maka suprise" dariya suka sheƙe da ita shi da su Shahid suna tafawa ya ce " i miss her alot" ya faɗa ya na lumshe ido dan da gaske yayi missed ɗin.
Rahma ta ce " zan isar da saƙonka yanzu" kashe wayar tayi tana jan tsaki haɗi da hararar wayan kamar Sameer ɗin ta ke gani.


Mommy na shigowa ta ga su Yusuf da Musty a zaune a parlour sun ɗau wanka cikin farar riga da farin jeans hakama cambus ɗin sa fari ne sai wata bandana mai alamar good ya ɗora a goshinsa gashin nan nasa ya ƙara rina shi hakama beard(gemu) zobunan sun cika yatsunsa, ba ƙaramin kyau Yusuf yayi ba.(a wajen gays)
Musty kuwa daman da shigarsa ya zo.
Ganin Mommy ta dawo yasa suka ce "welcome mah" Mommy ta ce "welcome my kids ko kufa kunyi kyau fa" murmushi Yusuf yayi ya na gyara zaman sarƙar da ke wuyansa ya ce "thank you mommy"

Rahma ce ta sauko da gudu ta na faɗin "sun zo" cikin farinciki tayi compond dan tarar su Farrah, Ihsan  ce ta fito sanye cikin riga pink da wandon jeans blue sai wani blue veil siriri da ta sa a kanta fuskarta ta sha make-up sosai tayi kyau tsaye Musty ya tashi yana kafe ta da ido ganin shigar da tayi ta fitar da shape ɗin jikinta, duk motsin da tayi sai jikinta yayi rawa.
Mommy ta washe baki ta na faɗin " wow my beautiful daughter, sun zo ko"  ta ce "yeah" ita ma ta fita da sauri dan ganin Sameer ɗin ya zo ko ba su sanar da shi ba ta  yi kutumar uba kowa ya watse..........

************

Kuka sosai Jawahir take na rabuwa da ƴar'uwa kuma abokiyar sirrinta Zainab, muryarta har ta dishe Umma ce ta shiga ɗakin sanin ba fitowa zatayi ba, jin an shigo ne ya sa Jawahir rufe idanunta kamar mai bacci, Umma ta ajiye furar da ta kawo mata ta ce" nasan ba bacci kike ba, ke da kika auri kuka, tashi ki sha" Jawahir ta yi shiru dan babu abinda take so a yanzu sai kaɗaici, Umma ta ce "ba da ke nake ba?" cikin mutuwar jiki ta tashi kanta na mata ciwo idanunta sunyi jajir Umma ta miƙa mata fura mai sanyi cikin cup, "na...na...ƙoshi" ta faɗa cikin rawar murya tausayinta ne ya kama Umma zama tayi bakin ƙaramin gadonsu Jawahir ɗin ta ce "Jawahir ki yi haƙuri daman fa dole watarana sai kun rabu da Zainab, aure tayi ai ba wai mutuwa ba ke da za ki mata fatan alkhairi sai ki zauna kuka haba autar Baba, karɓi ki sha kinji Allah ya yi miki albarka ya nuna min ranar da zan aurar da ke kema"

Wani ƙunci ne ya ƙara ziyartar zuciyar Jawahir cikin fitar da hawaye ta ƙarɓi furar ta kafa a baki,tamkar maɗaci haka take shan furar, Umma na kallonta sai da ta sha fin rabi sannan ta ajiye, Umma ta ce "yanzu ki samu kiyi wanka sai ki kwanta kinji zan turo miki su Salma ku kwanta tare"
Jawahir ta ɗaga kai, lokan da ke ɗakin Umma ta buɗe ta ɗauko paracetamol guda biyu ta ba ta tare da pure water'n da ta gani a ɗakin, ba musu Jawahir ta sha, sannan ta ce "nagode Umma" murmushi Umma tayi ta fita tana mai share ƙwalla dan ta tuno, yanda ƴan unguwar suke zunɓe da ƙifcen Jawahir suna nuna ta ga waɗanda ba su san abinda ya faru da ita ba.
Ba su san ce wa zai iya faruwa ga tasu zuri'ar ba,

Zuwan su Amina ne ya katse mata tunanin da take yi, "kun dawo Amina?" ƙanwar Baba Hajiya Maryam ta faɗa ta na musu sannu, sallama suka yi musu suka nufi gidansu kuma dan biki ya ƙare, sai fatan Allah ya ba da zaman lafiya.

"hmmm Umma kenan, banji za ki ga wannan ranar, waye zai aure ni, bayan an cuci rayuwata, Allah ya isa Hafiz ba zan yafe maka ba har abada kuma wata shari'ar sai a lahira"ta ƙara fashewa da kuka, kamannin Hafiz na dawo mata, da lokacin da ta farka ta ganshi cikin furgici mutane sun rirriƙe shi, za'a yi masa duka wasu na faɗin, a kira hukuma tukun na, wasu na faɗin  asa masa taya a ƙona shi, a haka su Salma suka  same ta, nan suka hau rarrashi duk tunaninsu kukan rabuwa da Zainab ne,nan kuwa biyu ce ta haɗu......


Bayan Abdallah ya dawo daga rakiyar abokansa,nan suka gudanar da sallar nafilar da Annabi (s.a.w) ya koyar tambayoyi ya yi mata game da ibada ta amsa masa da kansa ya je kitchen ma sha Allah abinda ya furta kenan ganin yanda iyayenta suka yi ƙoƙari, plate da cups ya ɗauko ya fito, kaza da fresh milk ɗin da ya shigo da su, ya zuba musu da kansa ya ke ciyar da ita, ganin lokaci-lokaci tana share hawaye ya ce "Zainab ko dai akwai wani abun ne?"
Kai ta girgiza alamar babu komai,  ya ce "ni dai nasan  Zainab ɗina bata ɓoyemin farincikinta ko akasanin haka" kamar wacce ya ƙara turawa aikuwa ta fashe da kuka ta ce "ka kira min ƙanwata nasan tana ta kuka iyanzu" rungumeta yayi ya fara rarrashinta cikin kulawa, da ƙar ya shawo kanta, tayi shiru.

Wanka suka yi suka kwanta Zuciyar Zainab cike  da kewar Jawahir, tun farkon dare Abdallah ya fara neman angoncewa da amaryarsa, abunka ga mai ilimin addini,sai da ya kawar da tsoron da Zainab ta ke sannan suka gudanar da sunnah, duk da cikin nutsuwa ya ke,kuma duk juriyar Zainab sai da ta yi ihu, cizo yakushi kuwa Abdallah ya sha su,  amma tamkar dutse sai da suka zama abu guda a daren. Farinciki kamar Abdallah zai yi hauka.

A daren ya hau ba da haƙuri da lallashi, Zainab kuwa babu abinda take sai kuka da tunanin irin azabar da Jawahir ta sha, ita ma ta ji azaba, bare wacce akayiwa ta ƙarfi cikin rashin imani.
Sai da yayi mata wanka, sannan shima yayi, sai nishaɗi yakeyi yana jin ƙaunar matarsa na ƙara samun muhalli a zuciyarsa, ya na ta sa mata albarka.

A rungume take a ƙirjin Abdallah ta ce "Allah ba zai bar wanda yayiwa ƴar'uwata fyaɗe ba, abun akwai ciwo" Abdallah da yasan taji Maza ne ya ce "sorry baby ki yi shiru hakanan kinga jikinki har yayi zafi, da alamar zazzaɓi".Banza tayi da shi, har bacci ya ɗaukesu a hakan.

Washegari ƴan'uwa suka je aka ƙara gyara mata gida,sai tambayar Jawahir take aka ce sai ta kwana biyu zata zo.
Dangana Zainab tayi dan tasan hukuncin Babansu ne.

**************

Kamal na gama wayar ya ja motar yana kiran Sagir ƙanin Abdallah da ya zo ya dawo da motar dan airport zai wuce, tare da alƙawarin zai dawo domin ya kamu da son Jawahir sosai.

Abokan Abdallah ne suka yi masa rakiya har airport  basu tafi ba sai da sukaga tashin jirginsu Kamal, sannan kowa ya nufi gida cikin farincikin gama taro lafiya.

PRISON

Tara duk fursinonin gidan akayi ana kiran masu ƙananan laifika domin mai girma governor zai kawo ziyara gidan cikin satin, shugaban gidan yarin ne ya ke jawabi, killer da su kure suna kulle Hafiz kaɗai aka fito da shi dan akwai wa'adin da zaiyi a gidan su kuwa sunzo kenan har su mutu.

Shugaban ya ke cewa" mun tara kune domin mu sanar da ku cewar mai girma gwamnan jahar nan His excellency Muhammad Bature zai kawo ziyara cikin wannan sati, muna so ku zama masu ɗa'a da biyayya" ihun murna da harkowa fursinonin suka hauyi dan masu ƙananan laifuka sun san za'a fitar da su,su shaƙi iskar ƴanci, control ɗin su akayi sannan sukayi shiru, nan ya ɗora da nasiha ya yi musu fatan samun nasarar fita lafiya.

Wani matashi ne ya kalli Hafiz ya ce "ustazu Allah ya sa muna daga cikin waɗanda za'a yafewa mu ma mu fita" Hafiz ya y........

opoop

Zinariya ce✍🏻


You are reading the story above: TeenFic.Net