page 25

Background color
Font
Font size
Line height

👩‍❤️‍💋‍👨 *Zab'ina*👩‍❤️‍💋‍👨
                   *ko*
                        💔 *na Mahaifiya ta Sabuwar Rayuwa*💔

   *ci gaba ne*
*** *** *** *** *** *** *** *** *** *** *****

      *Daga alkalamin🖊️🖊️ Habiba Ahmad wacce aka fi sani da princess*

       *~kirkirarren labari ne kuma bashi da tsayi~*

*Dedicated* *to*  *sis Khareema ~(my dangin kuma tu~*

  
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

          


https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Bismillahir rahmanin rahim*

     *Page 120~125*


        K'arar fad'uwar da suka ji a parlour ne yasa suka fito da gudu ganin mahaifiyar ta su a k'asa suka tsorata suka rungume juna suna kuka.

      Jin yadda wayar ta yanke yasa shi k'ara k'ira

    Rayaan ne ya d'aga yana kuka yace Daddy Mummy fall down.

     Kashe wayar yayi yayo gida.

      Cikin mint kad'an ya iso bai bi takan su ba Khareema ya d'aga ya fita binsa suka yi da gudu yana sata a mota suma suka shiga ya nufi asibiti.

      Zahra ya k'ira yace " ta same shi a asibiti.

      Emergency aka yi da ita aka bata pain reliever saboda juyin ciwon ciki da tafara ga bleeding da hannunta ya yanke da glass d'in center table yaji mata ciwo sosai.

      A gefe guda suka takure kamar basa nan don kam mantawa yayi da suna nan Zahra ma wuce su tayi ta nufi gurin d'an uwan nata tana tambaya ko lafiya bai iya cewa komai ba sai ma rungume ta da yayi yana hawaye tare da cewa wallahi I love her Zahra bana san ganin ta in pain I can't bear it,  it hurt I swear.

     Itama hawaye idon ta yafara dan tama kasa magana.

       Yasa shi tayi yazauna ita ma ta zauna ji sukayi muryar mummy na tambaya where have you been?

    
       Tare suka juya sai lokacin ya tuna yazo dasu ransa b'aci yayi tashi yayi ya nufi gurin cikin b'acin rai ya d'aga hanu zai dake su ji yayi an rik'e hanun sa ta baya.

     Juya wa yayi ganin Khareema ne ya rungume ta sai da mum tayi gyaran murya san nan yasake ta, murmushi tayi kai a k'asa

   Tace" bai kamata ka dake su ba basu fi 6 years ba yara ne har yanzu zan musu magana ta yaren da zasu fi ganewa.

      Tsuguna wa tayi gaban su ta b'ata rai tare da cewa some ppl Wanna see my angry 😡 face.

     Rungumeta sukayi suna mummy sorry we won't repeat it again.

    Murmushi Khareema tayi tace" OK tunda fad'a kuke I ve to punish u guys  daga yau zuwa sati biyu baza ku sake zuwa play grown ba, bazaku sake zuwa gidan mummy ba for 2 weeks so don't even beg me later cos bazan bari ba, haka su Harisa ma das their punishment mummy.

     Murmushi mummy tayi tace " Khareema you are the best kuma zan iya fadan haka a ko ina.

    Murmushi tayi tace muje gida sai mu k'arasa maganar I ve surprise for u all.

       Had'uwa sukayi duka suka tafi.

       A filin gidan sukayi parking san nan suka sauk'a suka shiga a parlour suka zauna ganin wata budurwa a gidan ya bawa Khareema mamaki tambayar ta tafara me take yi a gidan ta?

     Rik'e ta Don yayi yace " ki nutsu tuna fuskar suby tafara jikin ta na rawa tafara ganin suby da mijin ta ture shi tayi a jikin ta tana cewa you are cheating on me with her go away fad'uwa tayi a jikin sa dukan su kasa magana sukayi su Rani kuma kuka suka sa dan basu tab'a ganin ta haka ba.

     D'aga ta yayi ya kaita d'aki ya kwantar tare da k'iran likitan ta.

      A fusace Mum tace" yaushe ka sanja Don yaushe kafara harka da mata bansani ba dama ka d'akko ta kundawo gida dan kana cutar da ita ne wan nan shine tarbiyar dana baka Zahraddin?

     Shock d'in magan ganun Mum ne yasa ko motsi ya kasa bare yayi depending kansa akan zargin da take masa.

     Sallama likitan yayi Don ya masa jagora zuwa d'akin da take ya gama dube duben sa yace" pass dinta ne yafara hunting d'inta in sha Allah   takusa tuna komai amma sai ana hakuri dan ita gani zata nayi kamar yanzu abun yake faruwa har zuwa lokacin da zata tuna komai.

       Godiya Don ya masa yayi rakiyar sa zuwa bakin k'ofa.

     Wani iri mum taji na abunda tafada masa lumshe ido tayi tazauna sai kuma take k'are ma Khareeman kallo  hanu takai zata tab'a cikin ta sai Don yayi sallama dawo da hankalin ta kansa tayi tana bashi hakuri murmushi yayi tare da cewa Mum baki hurting d'ina ko kad'an ba fa manta kawai ya d'an jata da surutu  sai suka ji kukan Rani wai Rayaan ya dake ta dukan su parlour suka koma suka barta tana bacci.

     Suna zaune mum ta d'aga kai zatayi magana sai taga Don sai murmushi yake shi kadai hakan ya bata mamaki gyaran murya tayi tace me kakeyi wa dariya yanzu kuma?

    Shafa kai yayi yace" mummy yanzu mutum yana da mata kamar Khareema meyasa zai nemi wata mum kinsan.....

     Tarar maganar tayi da nikam yi min shuru mara kunya kawai a gaban yaran naka zaka fara zarar zance je ka duba matar ka..

      Har yafara tafiya sai mum d'in ta kara cewa lover boy ba romance na aike ka yi ba hope kajini.

    Shafa kai yayi sai da ya tafi Zahra tace " mum wallahi ke da Don kunya kuke ban baya kunyar fad'a miki magana ko me cece 😔kuma a gabana kukeyi kubarni da kunya.

    Murmushi mum d'in tayi tare da kallon Zahra bata ce mata komai ba.

     Da alamu bacci su Rani suke ji Zahra ta raka su d'akin su suka kwanta bacci.

     Ko da ya shiga d'akin yi yayi kamar bazai tab'a ta ba sai kuma ya tab'a ta aikuwa ta tashi ido ya zaro dan yasan yanzu mummy zata wanke shi.

     Ruwa ya bata tasha ya rik'e ta kafin ta tashi suka nufi parlour kallon Khareema ya kasa isan mummy dan da alamu tasanja lokaci guda tayi k'iba ta kuma k'ara haske har sai da ta zauna kafin mummy tace" hope de yanzu ba damuwa murmushi tayi tare da cewa ehh.

     K'ira mummy tayi na yen aiki guda biyu d'aya Laraba d'aya kuma namiji ne Sadiq namiji zaina girki ita kuma macen gyaran gida murmushi Khareema tayi tace " mummy kina sakalta ni daya wa fah.

     Fad'a mummyn tashiga mata akan stress ta kuma ce tana yawan huta wa akai akai shima Don ya kiyaye zama a gurin da Laraba zata bi saboda gudun yawan fad'uwar nan.

     Sai da ta gama musu fad'a tace zata tafi gida amma Zahra ta musu sati  biyu saboda su Rani suna gidan rakiya sukayi wa mum har zata shiga mota sai tace "Khareema kinyi gwadin ciki a asibiti? Ko kuma bakya ganin change a jikin ki ne?

     Kai a k'asa tace " mummy kawai dai yanzu bana komai a gida ne hutu yamin yawa sai yasa.

     Hmmm Allah yasa hakan ne mummy tafad'a tare da shiga mota.

      Basu koma cikin gidan ba sai da ta tafi d'aki Zahra ta tafi dan huta wa shikuma sarkin san mata ya jata jikin sa a parlour suna zaune, fitowa Zahra tayi dan tambayar Khareema abu tagansu juya wa tayi ta rufe ido da sauri Khareeman ma ta tashi a jikin sa shikuwa mara kunya cewa yayi Zahra wallahi kinkai aure,  aurar dake zanyi dan kin iya zuwa a wrong time.

     Khareema dai kasa magana tayi dan abunnasa yafi k'arfin ta,

      Bata ma iya yin tambayar ba ta tashi tare da cewa Anty in an gama abinci flash me dan ko su  Rayaan bazasu fito ba saboda karku lalata min yara tun now baku da aiki daga kiss sai romance wan nan ko ciki kikayi tun daga ciki zaku b'ata baby gwalo tamusu ta tashi da gudu.

     Tana tashi don yace " yawwa bamuyi kiss ba fa yau nima sai yanzu na tuna tashi tayi zata gudu ya rik'e ta ya kuma b'ata rai san nan yace"kin manta da baby na ko be careful banson irin haka.

      Dawo wa tayi ta kwanta a jikin sa.

       Zahra da yaran ta ana kiran sallah sukayi suka fara karatu har zuwa 8:30 kafin suka fito cin abinci ganin Khareema da lemon tsami tana sawa a hanci yaba wa Zahra mamaki dan ta tuna yana hana tashin zuciya ne kasa hakuri tayi tace " Khareema anya babu ciki a jikin ki?

    Don ne ya Karb'i maganar da ke kika mata?

     Juya ido Zahra tayi dan abunsu yana bata mamaki wanda aka tambaya daban me amsa daban har aka gama cin abinci dai ba wanda ya sake magana saboda su Rayaan.

      Bayan sunci abinci ne Rayaan yayi irin tashin da k'anin Aqsa keyi aiko tafara ganin wasan da take dashi suta gudu yanzu kam ta iya tuna Aayan da gudu ta tashi tana cewa Aayan katsaya karka ji ciwo Aayan katsaya or else zan dake ka tana gudu tana tuna yadda take dashi rik'e ta Don yayi gam ajikin sa yana shafa kanta na wasu lokuta kafin ya zaunar da ita yana kallon idon ta yace "waye Aayan mirmushi tayi tace " Aayan is my favorite bani da brother sai shi kad'ai Aayan karamin yaro ne wanda kullum  muke wasa yana ina ?

      Murmushi don yayi yace "Aayan ya tafi abroad karatu yana dawo wa zankawo miki shi domin ya girma yanzu yaran ki ma sunfi 6yrs bare shi.

     Murmushi tayi tace yaushe zan ganshi shuru Don yayi Zahra tace soon.

     Badon yana so ba amma dole ya mata k'arya saboda lafiyar ta.

        Tana murna tace "Aayan ya girma.

    Yaude cikin farin ciki take haka akayi bacci.

      A kwana a tashi yau tsawon wata biyu da yamma tafita Evelyn Garden da niyar huta wa dan cikin ta girma yake dad'a yi sai tana ji ta gaji da gidan gurin wasa ta ajiye Rani da Rayaan ita kuma taje cin suya.

      Sunjima a gurin kafin suka tafo su hud'u da gudu Rani ne tace "mummy munyi new friends shafa kansu khareema tayi tace yaya sunan ku amsawa macen tayi da sunana Mabaruka shikuma Mabruk.

      Ji tayi yaran sun shiga ranta tana murmushi tace " to shikkenan duk Thursday kuzo nan zaku same su sai kuna wasa tare koh.

     Kai yaran suka d'aga mata sai tace "suje suci gaba da wasa su kuma su Rani suzo su tafi haka ko sukayi hanyar fita tayi karo da saurayi da bai wuce shekara sha takwas ba yana fito wa a mota ita kuma tasa su Rani zata shiga kallon ta ya tsaya yi har tashiga ta tafi amma yana ji yasan fuskar nan.

       Ciki ya k'arasa ya d'ebo yaran da suke k'iran sa da uncle har zasu shiga mota sai Mabruka tace " Uncle Aayan munyi friends nan suka fad'a masa abunda Khareema ta fad'a ya yadda zaina kaisu duk Thursday suka shiga mota.


     Tofah sabuwar zance yaya za'a kaya


You are reading the story above: TeenFic.Net

#yerp