*SIRRINA...!!*
*K _ S H I T U*
*_SHAFI NA ASHIRIN DA UKU DA NA ASHIRIN DA HU'DU._*
*P 23-24*
Wani mugun zufi na gaske ramin yake dashi, tun da suka faɗa basu jisu ƙasa ba, sai da suka ja kusan mintuna ukku. Da ƙarasowa macizzan basu yi wata-wata ba suma suka faɗo ramin, Wani wuri mai manya manyan bishiyu, gurin babu komai sai korayen shuke masu tsayi, faɗowa sukai a wani uba mai kama da rijiya, suna faɗawa murfin abun ya rufe kansa. Gudu sahash ke yi na fitar hankali, har ta ƙaraso kogon da ta saba zuwa.
Cikin ƙasƙas da kai ta sunkuyawa ƙaton halitar dake zaune alamar girmamawa, ɗaga gabjejen ɗan yatsansa ya yi, alamar amsawa. "A Halin yanzu na aikata duk kan abun da ka umarce ni, na zuba jinina a kabarin Nazaan, amma izuwa yanzu ban ga wani chanji ba..." wata dariya ya fara yi mai ban tsoro da firgitarwa, "Hahhaha! dole zak je JAZAL Ki ɗauko makullin sirrin daga kin yi haka dukkansu zasi dawo ƙarƙashinki, ayi yaƙi kiyi nasara masarautu ukkun su zama naki..." "Amma a ina tekun yake?." "Babu wanda ya san duniyar da tekun yake, amma akwai wata sarƙar sirri da zarar an same ta, zata yi jagora da farin tsun-tsun har zuwa wannan tekun, zaki haɗu da hatsarori masu ban tsoro da waɗan da baki taɓa cin karo dasu ba ko'a tarihi." cikin nuna jarumta ta ce "Zan jure zan yi ƙoƙari zan jure duk wuya da tsanani na..." dariya fashe da ita "Yaro man kaza! zaki fara bincike ta inda jiniknki zai miko amfani." Dogayen yatsu ya chaka mata a tsakiyar tafin hannunta, jini ya fara zuba wani ƙoƙo yasa ya tarbe, ya miƙo mata. Amsa tayi ta fiddo wani ƙaramin ganye ta saka jinin, "Tashi ki tafi ki aikata komai cikin zafin maita..."
NAHAAR Mahaifiyar Karan ta dubeshi tana faɗin "Karan! ka aikata abun da ya dace kuwa? har yanzu shiru nake ji babu wani matsi ko bayani." Numfashi ya ja ya ce "Kiyi haƙuri ranki ya daɗe ina ƙoƙarin na dai-daita kom...", "dakata! kar layi kuskuren faɗa man Aliya ce a zuciyarka. na faɗa maka a karo na ba adadi ka rabu da ita amma da yake ban isa na faɗa maka zance ka aminta ba ka kasa haka ko?." "Haba saauniyar nahaar ba hakan nake nufi ba in son na dai-daita yanda komai zai kasance dan gane da yanda masarautun ukku zasu cure gu ɗaya su zama mallakinmu." "Zaka iya ni na sani karan." "Ko mai zai faru ba zan taɓa baro Arman ka auri Zulmah ba, suna burin kanai-naiye mu don samun damar ɗanɗanar mulki ne kawai." Duban ta ya yi cikin damuwa ya ce "Mai martaba ya riga da ya furta dole na aureta, ni na tsaneta tsana mai muni ina jin tamkar na shayar da dabbobi jininta, Kimin alfarma dan girman abin bauta, ki dakatar da hakan". "Kar ka damu Arman hakan ba zata taɓa faruwa ba". tana gama faɗar hakan ta fice zuwa gun mai martaba fuuu. Bar bayyana ko'ina ba sai gaba mai martaba, cikin huci take duabnshi tana faɗin "Naji kana wani furuci akan Arman! to a gaskiya ba zan taɓa iya bari ɗana ya Zulmah ba koda hakan na nufin zan bar nahaar ke nan na har abada." Zama ya yi ya ce "Tabbas! dole ne ya aure ta koda zai rasa rayuwarsa nayi wannan alƙawarin. ke kuma zaki iya barin nahaar a duk sanda kika so." "haka kace?." "haka na ce, ko akwai abun da zaki iya yimin." Wani shu'umin kallo ta bishi dashi, kawai a ɓace ba tare da ta tanka ɓasa ba. HIZAAR Sarki ahal ne ke ta kai kawo zuciyarshi babu daɗi komai ya chunkushe masa, ita kuma sarauniya halsha ta hakimce bisa kujera ta zubo masa idanuwa tana sauraron tambayar da ya ce zai mata. "Halsha wai yaushe ne komai zai wuce? ina son naga na ɗauko muhimmiyar fansa, Amma cikin gogaggun hatsabiban sheɗanun nan babu wanda ya tashi cikinsu. hakan na nifin gwagwarmayar da muka sha shekaru bila'adadin ta tafi a banza." murmushi ta saki ta wani kanne idanuwa cikin izza ta ce "Haba sarkin hizaar ya zaka kasya cikin sanyi haka? Tsohuwa ta tafi duniya sihiri tana mana muhimmin bincike inda zamu samu wani tsun-tsun da zai kai mu tekun jazal." "Amma kina tunanin za'a yi nasara...." Dariya kawai ta fara bata bashi amsa ba. "Sanaam ki dakata! kar kiyi wannan kuskuren A rayuwarki, hatsarin sarauniya Rahash ya fi ƙarfin tunanin ki, chutar mata da ɗanta karan da kike ƙoƙarin yi zai iya yin silar ki....."
*K_shitu.*
09117440993