P 19-20.

Background color
Font
Font size
Line height


*SIRRINA...!!*

*K_SHITU.*

*SHAFI NA SHA TARA DA NA ASHIRIN*
*_P 19-20_*

Sun jima suna tafiya cikin gajimare, kafin Tsun-tsun Gimbiya Aliyaa ya sauko ƙasa, gurin wani baƙin daji kwata-kwata ko hannunka baka iya gani, wani farin haske ne, ya fito daga idanun gimbiya Aliya ya ɗan haska jejin, kallo ɗaya da zaka yiwa dajin zuciyar ka tayi kyakykyawan bugu mai razanarwa, dan kwata-kwata jejin yafi shige da wata maƙabarta-maƙabarta ko kuma wani kurkuku ko'ina kukan halittu ne mai tsoratarwa ke tashi ga hayaƙi na fitoea fari wanda sai ka natsu zaka fahimci Hayaƙin da sauri da sauri yake fitowa wata jar ƙasa ce shimfiɗe jajir a ƙasa, sai korayen ciyayi da sun wani yi kaco-kaco ba kyan gani. Ba tare da tsoro ko firgici da fargaba, ba Aliyaa ta fara nutsawa cikin dajin, wasu ƙananan dodanni ne baƙaƙe suka fara yo mata caa tamkar sun ga nama, Sama ta tashi a mamakinta suka saman suka tashi, hakan yasa ta furzo da wata hoda ja daga bakinta duk suka fara faɗowa ƙasa. Cikin azama ta ci gaba da tafiya a sama, wasu korayen halittu ne masu kama da shaho, suka zagaye ta suna wani kuka da ƙarfi sosai, marar daɗin sauraro, jiri ta fara gani ahankali cikin jarumta ta ɓace, a maimakon ta bayyana gaba sai ta komo farko, tunowa da zanchen macijiya da tsoho arar ya mata ne ya saka ta duƙewa ta sunkuyar da kanta ta zama macijiya, ta fara tafiya sili-sili har ta kai gaɓar shiga kusan farkon dajin wani ƙaton icce ya ɓallo zai faɗo mata, cikin firgici tama rasa yanda zata yi kawai ta runtse idanuwanta, duk da macijiyar ƙarama ce sosai amma mai kyau, yarima Aliyu haydar da ya tare ƙaton iccen iya ƙarfinsa ya yi nasarar tunkuɗa shi gefe gudun kar ya faɗo. Hannunshi ya kalla daya ke fitar da jini, bai bi takan hannun ba ya ci gabaa nutsawa cikin dajin, ganin ba wani hatsari kuma ya aliya bayyana a suffarta ta mutum, da sauri ta ci gaba da tafiya duk da ƙayoyin da take tajawa, tana jim raɗaɗi hakan bai sa ta daina tafiyar ba. Cikin hanzari take tafiyar har ta wuce sa kamar walƙiya, duk da irin zafin naman da yasa, ko da yake ita tana da ƙarfin sihiri. Tafiyar ce taƙi ƙarewa gashi ko kwatan dajin basu fara hangowa ba. Chak suka dakata da tafiyar da suke yi,sakamakon ƙafafuwansu da suka ji wasu abubuwa sun kanannaɗe kamar majizzai kamar wata igiyar ƙarfe. kamar kuma tsutsotsi masu kauri, abun sai nannaɗowa yake yana yin sama-masa, wani farin haske ya fito daga tafukan hannayenta ta haske dai dai ƙafar, abun ya zagwanye yai zube ƙasa ɗauri ya warware. Cikin dakiya da kamewa ta tafa tafiya, yarima kam ganin ta samu kuɓta ya saka shima ya fara iya ƙoƙarin shi amma abun yaci tura, sai sama yake yi, har ya kawo gurin guiwar ƙafarsa. Chak ta tsaya daga tafiyar ta juya kanta a sunkuye, ta saka hannun shima abun ya warware, da hanzari ta ci gaba da tafiyar ta, tamkar ya bita amma izza da jin kai ya hana shi cikin basarwa ya ci gaba da tafiya da kuma zafin nama. Sun jima suna tafiya Dare ya raba sosai baka jin komai sai koke-koken tsintsaye da gurnanin namun dawa masu haɗari. Aliyaa na cikin tafiya, kawai wani tsun-tsu mai kama da shaho ƙaton gaske da fuka-fukai, ya damƙe mayafin da ta yane fuskarta, zuwa gashinta, ya fara kiciniyar tafiya da ita sama. Lafiya lau kan shahon irin na mutane amma jikinsa daban, wasu zaƙo-zaƙon akaifu ya saka ya shaƙo wuyanta ya fara janta ƙasa. Sarƙewa numfashinta ke yi fuskarta ta yi wani tsanwa-tsanwa tsabar fari duk da ba sosai ake ganin ita kanta Aliyar ba amma Yarima haydar ya hango abun da ke wakana. Sai a sannan Yarima ya rarumo wani abu ba tare da ya san ko miye ba, ya wulla ma shahon a kai, sakin gimbiya aliyaa ya yi, ita kuma ta fara wani irin tari, yayin da kan shahon ya ara zubar da wani ɗorowan ruwan mai kauri da yauƙi. Ɗan yatsa ɗaya yasa ya shafe gurin, ruwan ya tsaya gurin ya shafe, tamkar yanda yake da. Tari sosai Aliya ke yi zuciyarta, tana zafi wuyanta na fitar da jini inda ya huda mata. Ɗaga hannuwansa shahon ya yi, sama ya fara ɗago da su biyun sama, ba tare da ya taɓa su ba, sama-sama ya dinga ya dasu sai da yazo ssu gab shi, ya matse su guri guda da hannunshi ɗaya, yana ƙare musu kallo a yellow ɗin idanuwansa. Dogon halshensa ya fiddo mai wani irin wari da ƙarni, ya nufo fuskokinsu dashi......

ACCOUNT NUMBER:

*9117440993 PALMPAY BANK, KHADIJA MUHAMMAD SHITU, EVIDENCE VIA 09060584800*

_YA KUKE TUNANIN ZATA KAYA? KU BIYO NI CIKIN LITTAFIN *SIRRINA!* MAI RIKITACCEN SALO, KI BIYA KUƊI KI SHA KARATU ƳAR UWA WANNAN BOOK ƊIN NA KUƊI NE, KAR WATA TA SA KI KARANTA BAKI BIYA BA, GA MASU BUƘATAR ZAFAFAN LITTATTAFAINA SU MIN MAGANA_ _09060584800_


You are reading the story above: TeenFic.Net