17

Background color
Font
Font size
Line height

KARAMCI WRITER'S ASSOCIATION
(Karamci Writer's Association)

    SAKAMAKON KAUNA

NA

KHAIRAT UP

      Vote @wattpadkhairi_muhd.

                     17.

*FANCIABLE CREATION*
_sun zo muku da hajar zannuwan gado domin gyaran gadon ki._ _Ina Uwargida ina Amarya? Wannan damar taki ce a ajiye tsoffin zanin gado a siyo sabo domin burge maigida ga kyau ga laushi , Hajju za ki samu duk wannan ne a rahusa mai sauk'i._ _Sai an gwada a kan san na k'warai_
*Domin Samun wayanan kayan adon.*
👇👇👇👇👇👇
Quilt(duvet)*
*Plain bedsheets* *( 2pillowcase & 4pillow case)*
*Half set*

*Throw pillows*
*Curtains*
E.t.c
_Za ki iya tuntubar wannan layin._
👇👇👇👇👇👇.
08031534014.

Tausayinta yake ji hakan nan bayan abin da ya faru tsakaninsu ya ji wata iriyar girma da ganin darajar yarinyar ya dirar masa a cikin rayuwarshi amma bai ji wai yana sonta ba but ta samu babban gurbi a cikin rayuwar ta shi yana ganin girmanta da mutuncin ta.

Ita kuwa zazzabi ne ma ya rufe ta kwantawa tayi kan gado tana fitar da numfashi dai-dai.

Shigowarshi kenan ya ce bari ya lek'a ta ganinta a kwance tana makyarkyata ya k'arya mishi zuciya da sauri ya k'arasa kusa da ita ya tallafo ta yaji jikin nan zafi zau kamar garwashi ya ce "Ya salam." A hankali ya tashi ya koma kitchen ya samu wata karamar roba mai zurfi ya dibo ruwa a ciki da sauri ya shiga cikin dakin ya samu wani dankwali mai tsafta ya tsoma a ciki, rigar da ke jikinta ya cire mata aiko ya yi kyakyawan gamo ya hadiyi yawu makwat ya dauke kai da sauri ya matse dankwalin ya dinga goga mata a jikinta ko ta ji sanyi. Kasa bude idanuwanta ta yi sabo da tsabar kunyar abin da yake yi mata wani iri take ji tsakanin jiya da yau abubuwan da suke faruwa kara daure mata kai suke yi daman haka yake?.

    Tashi ya yi ya ce "Sannu kin ji bari na je na siyo miki magani ban ce ki sauko daga kan gadon nan ba."

Kai kawai ta gyad'a masa ba ta iya ce masa komai ba.

Bai samu magani nan kusa ba saboda safiya ce sai wellcare yaje ta hadeja road ya samo magungunan zazzabi da na ciwon jiki ya yi mata yan siyayyar su chakulet da biskit da alawa harda biredi ya biya ya fito.

Ko da ya dawo ya tarar ta yi barci duk da haka sai da ya tashe ta ya bata maganin bayan ta sha ruwan tea da bread din ya bata magungunan sannan ya gyara mata kwanciya ya yi mata sannu da jiki ya fita daga dakin. Cikin sa'a kuwa Gwagwo bata nan sun fita da Innar cikin gida.ita ma Gwagwon da gayya ta k'i shiga gun Amirar dan kar ta ji kunyarta shi sa ta yi ficewarta.

*

Cikin kwanaki biyun da Aliyu ya yi kowa zai san ya sauya ko in ce ya samu sauyin yanayi da sauyin rayuwa , ya yi kiba abin shi har wani haske ya k'ara fuskar nan cike da annuri da zati sai aikin walwala. Amira ta samu sassauci daga wurin shi ko da basa hira sosai amma ai ya fi da yana cin girkinta yana sa ta aiki yana bata kudin kashewa wani bin ma har makaranta yana kaita duk da baya nuna mata wannan kiliyar irin ta da amma baya daga mata kafa ko kadan in dai yaji yana jin yin abin to fa sai ya yayin ko bata nan zai yi mata sak'o ta yi sauri yana jiranta ita kuma baiwar Allah tsoronshi take ji da azama take dawowa ta yi mishi abin da yake so.

Sai da ya fara shirin komawa ne kuma ya ji hankalinshi ya tashi saboda yanzu ya saba da abin ya saba da aikinta a gareshi ya saba da sanyinta sai ya yi tunanin komawa da ita Lagos da wannan shawarar ya samu Gwagwo a d'aninta tare da Amira suna hira kamar ko yaushe tana gyara mata goro.

"Salamu alaikum Inna!."

"Wa'alaikum salam Baba na na kaina ya dai?."

"Lafiya kalau Gwagwo na sai dai zan yi k'ewar ki sosai da sosai."

Murmushi ta yi ta ce "Aifa dai mutanen ikko kenan ai duk inda ka ke ina tare da kai , addu'ata tana tare da kai bazasu ga bayan ka ba sai dai ka ga nasu in sha Allah."

Murmushi ya yi kafin ya na sosa k'eyarsa ya ce "Gwagwo dama zan gaya miki zan wuce da ita ne?."

Sai da dak'in ya yi dan dum saboda shiru da ya ratsa shiru bata ce masa komai ba har sai da ta kusan mintina uku zuwa hudu kan ta ce da shi "wa Kenan Baba? Ko Su'ad?."

Dan bata rai ya yi jin tace Su'ad kamar bazai yi magana ba kuma sai ya ce "Amira dai."

Amiran ma wani iri taji wai da ita zai tafi to makarantar fa?.

"Wasa kenan Baba."

"Wasa kuma Gwagwo?."

"Eh! Wasa. Taya yarinya na zuwa makaranta kawai dan kai ne oga kwata-kwata sai ka ce ta ajiye karatun da ka tsinceta da shi ta bika wata uwa duniya ai bazai yuwu ba abin ma babu dadin sauraro ai."

"Haba Gwagwo karatun ai bai fi mijinta ba kawai ina da mata sai na zama kamar gauro?."

"Yau naga ikon Allah Aliyu nace bazata bika ba ina nufin ba zata bika ba sai dai in an yi musu hutu tazo tayi ma kwana amma ban da yanzu."

"Dan Allah Gwagwo ki bar ta ta bi ni."

"Baba bazan bari ba ka yi tafiyar ka kai kadai ka barta daman can ba da ita ka tafi ba,kai yanzu ya dace ka datse mata karatu?."

"Gwagwo zan nema mata transfer ta koma can."

"Aliyu!."

Jin ta ambaci sunan shi kai tsaye cike da dakiya da umarni ya sa ya yi shiru sai dai ba haka ya so ba haushin yarinyar ma ya ji ya kama shi ganin tayi shiru kamar ma ba da ita ake yi ba tsaki ya yi a ransa na bakin cikin kansa da kansa na ma damuwa da ita har yake wannan dagiyar don ya tafi da ita. Tashi ya yi ya ce "Allah Ya huci zuciyar Hajiya sai na dawo."

"A dawo lafiya."  Ita ma a dawo lafiyar ta yi mishi sai dai bai amsa ba ya yi ficewar shi.

Kasuwa ya je ya yo mata yan siyayyar kayan abinci da suttura ya karo mata hijabai ganin tana yawan sa wa sosai bai taba ganinta da mayafi ba kuma zai so ya ganta dashi amma yanzu gwara ya bi ra'ayin ta.

Aliyu bai koma gida ba sai bayan isha'i suna ta yawo a gari shi da Alameen har gidansu budurwar Alameen sai da suka je nan suka ma dade inda ya dinga ganin love tsababa a gunsu har yaji ina ma shi ne ake ma wannan tarairayar shi mutum ne mai son kulawa da tarairaya gun mace sai dai kila ba zai samu wannan damar ba a rayuwar shi.

    Tsaki ya yi ganin bai sameta a gidan ba sai dai ko ina tsab ga kamshi ta ko ina kayan ya adana a kitchen in ta zo ta gyara abin ta sai da ya yi wanka ya saka jallabiya tukuna ya dauki na Gwagwo ya fita kai mata a tsakar gida ya tarar dasu harda wata kawar Gwagwo suna ta yi.

"Maraba da Baban Gwagwonshi."

Murmushi ya yi kawai ya gaidata.

"Bazan amsa ba idon ka kenan?."

"Afuwa Ammi zan zo kan na tafi in Sha Allah."

"Shi kenan ya kake?."

"Alhamdulilahi."

"Ma Sha Allah."

Cikin uward'aka ya kai wa Gwagwo kayan abincin sannan ya ajiyewa Ammi dubu daya yace 'ki sai goro."

"To Allah Ya yi albarka."

"Ameen."

Ganin Amira bata tashi ba Ammi ta ce "Aa fa Amiran Gwagwo bana son kauyanci ke sai an ce miki kije mijinki ya dawo? Aiko za ki rasa shi kuwa dan shi namiji ba a yi masa haka ki rike abin ki ta hanyar bashi kulawa yadda ya kamata kul na kuma ganin ga dawo ba ki bishi ba sakarci ne mace mijinta ya dawo taki tashi taje ta yi lalenshi ki kiyaye."

Kai kawai ra gyada cikin kunya kan ta yi musu sai da safe ta mike.

Tana ji tana yi wa Gwagwo fad'an bata koya mata dabarun kama miji a hannu bata karasa ji ba ta shige part din nasu.

  Kan kujera ta same shi ya kwanta sai dai ba barci yake yi ba , kitchen ta shiga dan kawo mishi sanwa taga abin arziki sai da ta yi musu adani mai kyau kafin ta fita kai masa abincin.

     Tana ajiyewa ya yi maza ya ce "Kwashe kayan ki."

Da sauri ta d'aga kai ta ce "Me ya sa?."

Harara ya fara yanka mata kafin ya ce "Haka na ga dama ba na so ! ba na so ko dole ne?."

"Idan laifi na yi maka ka yi hak'uri dan Allah, ka gaya min sai in gyara amma kar ka ki cin abinci ."

Be ce mata komai ba ya tashi ya shige d'aki abin sa.

Abin ya yi mata ba dad'i sosai bata son a dinga yi mata irin wannan disgin amma haka ta tashi ta bi shi d'akin.

   Ruf da ciki ta same shi ya yi da sauri ta ce masa "Babu kyau irin wannan kwanciyar ka gyara."

Bai ce komai ba amma ya gyara kwanciyar ta shi ya na cije lebbensa shi kan shi bai san dalilin hsushin nata da yake ji din ba.

Haka suka kwana sukuku ba wani walwala ya saba ko bai mata komai ba zai dan sa ta a jikin shi sai dai yau ya haramtawa kan shi so ya yi ta ce zata bi shi a gaban Gwagwo amma sai ta yi shiru ta nuna ma bata san yana yi ba kenan shi ne ma ya damu da ita me yasa ma ya yi maganar mtsew.

Washe gari ta shirya tsaf sabida suna jarabawar semister ne yau zasu fara ko girkin bata yi ba. Doguwar rigar atampa ta saka ta bi jikinta ta kwanta ta yi mata masifar kyau ta shafa farar powder ta saka lipblam ta yafa mayafi a kanta ta saka mayafin ta dauki jakar ta, fita ta yi daga d'akin ta shiga d'akin da ya kwana shi ma cikin shiri ta sameshi kusan karo ma suka yi da juna sabida zai fita zata shiga da sauri ta yi baya ta ce "Yi hak'uri ta dan russauna ta ce Ina kwana?."

"Lafiya" kawai ya fad'a. Ya wuce ta da sauri ta sha gaban shi ta ce "Dan Allah Yaya ka daina fushin nan haka ka bari mu gama jarrabawar wannan semester din sai na biyo ka can din yanzu....."

   "Kin ga kar fa ki sa tunanin sabida ke ne nake fushi aa wani abun ne daban ni bana fushi da ke, in fact ki cire ma wai na damu da ke ne kawai ina son ki zama kina can za ki na yi min girki,wanki da gyaran gida haka sai kuma ki dinga dauken larurata amma bayan haka ba wai damuwar na yi da ke ne ba ai abin da ka ke son shi ka ke damuwa da shi ni kuma kin sani na sani bana son ki wannan auren Gwagwona ce ta had'a shi haka zata gaji ta sa a kunce shi."

    Maganganun shi basu taba bata mata rai ba irin na yau wato ma amfaninta kenan ta yi mishi gyaran gida da girki da kums gyara masa shimfida? Me ta rage shi da shi? Me laifin ta dan tana son shi? Mai laifin ta don tana son kasancewa da shi? In dai son nan wahala ne zata yi kokarin raba kanta da wahalar zata yi kokarin dauke kanta daga gareshi haka ya sa ta sauke ajiyar zuciya ta juya ta fita daga falon ta bar shi a tsaye.

Baki ya saki yana kallon tafiyarta "Shi ta tafi ta bari a tsaye yana magana?." Abin ya yi mugun daure masa kai ,ya ba shi mamaki, lallai dole ta yi masa haka mana tunda ta ga wurin kwwnansa ta ga girman sa zan yi maganinki.

*

Bayan mun gama exams din a k'asan wata bishiya na zauna ina tunanin rayuwata kawo yanzu ni mutum ce marar son hayaniya da tashin hankali babu ruwa na da ababen duniya buri na kawai na yi ilimi mai zurfi ta yadda zan tallafi Inna ta , ina da kyau amma kyawuna bai rinjayeni na yi wani mumunan abu ba a rayuwata, ina da samari amma ban taba jin wani a cikin raina ba kamar yadda na ke jin Yaya Ali ba tun tasowata a unguwarmu nake ganin shi kuma yake burgeni shi kuma bai da abar k'i sama da ni na sani amma dake an ce so hana ganin laifi ko kuma so ba ya ji ba ya gani na kafe na nace na kasa yakice shi daga cikin rayuwata, ba shi da wani kudin a zo a gani hasali ma bai da wani shahararren kyau gashi nan dai dan daidai kawai za a ce amma na kasa cire shi daga raina babu kalar wulakancin da ba ya yi min amma na kafe na ji na gani duk wanda ya kwana ya tashi da mu ya san ni da Ya Ali ba ma jituwa ko in ce bana burge shi ban taba tsintar kaina a cikin farin ciki ba irin lokacin da Inna ta sanar min da aure na da Ya Ali ji na yi kamar an yi min bushara da kujerar makka sai dai ba haka ba ne a wurin shi karshe ma tafiyar shi ya yi ya bar ni yanzu kuma yake morata saboda ni din mace ce zuwa sannan kwallar da ya cika a idanuwana suka yi nasarar zubowa sai yanzu nake ganin wautata da yarinta da na dinga zubar da aji na saboda shi haushin kaina nake ji sosai da sosai .....dafa ni na ji anyi haka ya sa na daga kaina na yi saurin share hawayen fuskata.

        "Salamu alaikum baiwar Allah lafiya?.''

''uhm! Lafiya abu ne ya fad'a min a cikin ido na."

"Hmm! Ki yi hak'uri dan Allah kar ki ga kamar na shiga cikin rayuwar ki , na sani kin sani babu abin da ya fad'a miki a idanuwanki wani abun ne amma na sani bazaki gaya min ba nima bana son na sani sirrinki ne saidai in ce kiyi hak'uri komai na rayuwar nan hak'uri ake yi. Na cika ki da surutu sunana Amina Aliyu Sabo department din mu daya da ke sai dai bamu taba yin magana ba nutsuwar ki ta burge ni kullum ina son na yi miki magana Allah bai taba bani iko ba ina da aure ina da yara biyu yan biyu Farha da Farhan ina zaune a Sabon titi na Dorayi. "

Murmushi na yi lokacin da ta kai aya a bayanin kanta sai na ga ta burgeni ina son mutum mai saukin kai Wallahi.

   Sunana Khadija Aliyu Wakili nima ina da aure ina zaune a unguwar yakasai sai dai ni ba ni da ya'ya tukuna.

Hala amarya ce?.

Dariya na yi na ce aa na fi amaraya kawai dai yaran ne babu.

To Allah Ya kawo masu albarka sai dai har a yanzu sunan ki amarya tunda ba ki kawo mana boy ko girl ba.

Nan muka yi musayar numbobin juna muka kula sabuwar alaka da junanmu.

*

Washe gari Yaya Ali ya tattara ya koma garin ikko ya bar ni da kewa duk da har ya tafi wata kwakwarar magana bata taba shiga tsakaninmu ba bama magana na dai yi mishi sallama na yi mishi miya na yi mishi cake da cincin na sa a kayan shi bai ma sani ba dan na san in ya sani ba zai karba ba.

Da daddare ina kallo a tv dita da Yayana ya sai min second hand yar karama da dvd ina kallo naji sak'o ya shigo min wayata na dauka na duba.

"Nagode! Na iso lafiya kuma ki kula min da Gwagwo."

Murmushi kawai na yi da kyar na daure na tura mishi sak'on nima cikin halin ko in kula na ce "ok". Kawai.

Ya jima yana duba amsar da ta bashi "ok" kwafa kawai ya yi ya ajiye wayar .

Haka rayuwa ta dinga tafiyar mana jefi-jefi ya kan yi min text in na ga dama in amsa in na ga dama in ki amsawa.  Haka muka kare hutunmu muka koma makaranta ni da Amina shakuwar mu ta kai shakuwa mun saba sosai da sosai sau biyu ma mijinta ya kawo ta gidana ta yini muka sha hira sosai, ma fi yawancin lokuta yanayin raywuwar auren Amina da Mijinta Mubarak na burge ni sosai so simple, kulawa,da mutuntawa a kalla a rana zai kirata ya fi sau biyar bini-bini my life ya kira suyi ta soyewarsu abin sha'awa.

"Ni ko khadija in tambayeki mana?."

"Allah sa na sani."

"Kin sani ma sai dai ki k'i  gaya min ko ki boye min."

"In sha Allah kawata bazan boye miki ba ni me ki ke boye min naki? Komai kina gaya min kina shawara da ni Allah ne Ya had'a mu ni da ke jinina da naki ya had'u."

"Nagode da matsayin da ki ka ba ni naji dadi da yadda kika d'auke ni tamkar yadda na d'auke ki. Abu na lura da ke ko in ce gyara zan yi miki a alamarin rayuwar auren ki."

Dauke kai Amira ta yi kawai tuni hawaye suka taru a idanuwanta suka ciciko ji tayi kamar wani nauyayyen dutse aka dora mata a kai wanda ya danneta ya hanata kwakwaran numfashi tamkar wani lik'i ne aka famo mata haka taji.

"Kiyi hak'uri in maganata bata miki rai..."

"Ko daya maman biyu ni kaina abin yana damuna ba na jin dadin yadda muke rayuwa ni da Ya Ali Allah ne ya dora min son sa na sani ke ma in kika ji labarin mu za ki ji haushi na a matsayina na mace ba ni da aji amma ki yarda da ni nima yanzu abin ya ishe ni kuma na d'auki matakin da nake ganin shi zai bille min."

"Ina sauraron ki."

Tiryan-Tiryan ta kwashe komai ta gaya mata bata boye mata komai ba. Shiru Amina ta yi kawai tana kallon Amira kamar bazata yi magana ba sai kuma ta ce "Amira kina da laifi laifin ki kuma daya ne kin riga da kin nuna mishi kina mugun son shi kin fi son shi da shi, a yadda kika gaya min yanzu na sani duk inda yake baya da sukuni yana tunanin ki kawai bazai iya fitowa fili ya gaya miki ba ne sabida miskilanci tunda kin ce yana yawan yi miki sak'o ta waya ko bai kiraki ba kin ga alama ce ta Kulawa, kin ce ya so ya tafi da ke amma aka hana shi kin ga kenan yasan amafanin ki yanzu yasan muhimmancin ki yana son kasancewa da ke wanna ma wani nau'i ne na soyayyya sai dai bai sani ba ko in ce yana hana kanshi fad'awa cikin soyayyar musamaman wa ke da ya gama nunawa k'iyayya kawai borin kunya ce ya ke yi miki amma yana son ki. Na ji dadi da ki ka dauke mishi wuta kika share shi wannan zai sa ki kara tabbatar da cewa yana azabtuwa da tunaninki duk inda yake bai da sukuni amma babu yadda zai yi. Amma ni nan zan tsuma ki zan gyara ki sai ya dawo yana yi miki kamar kwar-kwar a tafin hannunki za ki na juya shi dan har na gano lagon shi kedai kawai ki saki jiki ki dau darasi yadda ya kamata ke ma mace ce ji kyau,ji diri,ji kyan hali,amma kin wani maida kan ki wata bakauya" ta fad'a tana hararta suka sa dariya tare.

"Da gaske ni ma Ya Ali zai so ni? Zai ba ni kulawa?."

Dariya sosai Amina ta yi harda tafawa kan ta ce "In sha Allah za ki yi mamaki kuwa ki maida hankalin ki kawai kawata."

"Nagode."

"Yaushe kike ganin zai dawo?."

"Wallahi ban sani ba bama waya."

"Mtsw! Wallahi gara ce ke ai cusa kai za ki dinga yi a gareshi ki koya mishi kewarkk ta karfi da yaji ki koya mishi son kasancewa da ke ko ta halin k'ak'a kin wani tsaya sanyi a Lagos fa yake garin da mata basu da kunya kina nan ayi miki wuff da shi tun kan ki kafa taki gwamnatin da kyau."

Kwalalo idanuwa tayi waje sosai kamar zata yi kuka sai kuma ta ce "Yanzu to ya za ayi?."

"Ki yi kokari ki san lokacin da zai zo daga nan ne aikin mu zai fara."

"To amma taya zan sani?."

"Komai sai na koya miki?."

"To ya zan yi?."

"Ki dinga yi mishi text na safe daban na rana daban na dare daban ki dinga kiransa ko bazai ce komai ba kina bashi Kulawa har ku saba."

"To."

Da wannan shawarar Amira suka rabu da khadija.


You are reading the story above: TeenFic.Net