TeenFic.Net Stories that stay with you ♥

part 17

NUNA SO GABAN KISHIYA❣️

wattpad:UMMIEN2018
whatsapp number:09076427357

*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment and to educate and enlight  our readers)_*

I dedicated this page to MRS ALEEYOU kiyi yadda kike so dashi wannan naki ne ke kadai alllah yabar kauna tsakaninki da oga...               

               page 17

Ruwan jarka dasuka zo dashi wanda zallar ruwan zamzam ne ya dakko wanda already  an riga da an gama topha duk addu'oi a wannan ruwan sbd akoi masu kalar matsalar da akan samu un-espected shi ya dakko ya tsiyaya cikin kofi kana umarci moha daya matso kusa...

bismillah yayi mallam sani ya zuba masa ruwan a tafin hannunsa yace ya shafa ma mimi ruwan a fuska... aykuwa ana shafa mata taja wani dogon ajiyar zcy ...

fes ta bude idanunta batare da mallam yabata zarafin magana baa yabawa moha ruwan yakafa mata a baki batayi musu ba tas ta shanye wannan ruwan...

tun kamin ya karasa ajiye kofin tafara babbankarewa  tana nurkususu a wajen take wani amai mai shegen wari ya barke mata a wajen...

yi takeyi kamar wacce zata amayar da hanjin cikinta saida tashafe 10mins tanayi kana aman ya tsaya kowa tausayinta yakeyi...ummi kam kuka takeyi sosai tausayin yartata na kara bin jijiyoyin jikinta...

yaraf ta ta kara zubewa tana maida numfashi saida ta huta na sawon minti 5 ta dawo saiti kamar ba itace ke iface iface dazu ba...

rarraba ido kawai takeyi tsakanin iyayennata da duk wayanda suke parlon domin kou ita pha batasan abinda ke faruwa ba tsakani daa allah...abinda tasani sun kwanta bacci tare da ummie a daki amma gata a parlo kuma yanxu...

idanunta ne ya sauka akan ameer sannan kuma ummie saiga anii a kwane shame shame a tsakar parlon...

mikewa take sonyi domin zuwa inda suke amma takasa sbd jikinta duk yamata sanyi...Alhmdlh mallam sani  ya ambata sbd ya gama nazarinta yanxu komai normal babu wani matsala...

muhammad kamata tamike ka kaita wajen mahaifiyarta...!babu musu moha yakamo ta yakaita kan kujerar da ummi take ya zaunar da mimi ta kwanto jikin ummin tayi lamo tanajin dumin jikin mahaifiyarta ko minti uku ba rufe ba taji kuzarinta yadawo...

Hakan baisa ta tashi ba inda mallam sani yakara umartar moha yakawo ummie ma...

bayyi kasa a gwiwa ba ya kinkimota kasancewarta itama bawata mai auki bace... d same itama wannan ruwan ta siyaya a kofi moha yashafa mata a fuska da kuma gashinta bisa umarnin mallam...

take ta farfado a wajen inda yakafa mata ruwan a baki itama batyi musu ba tashanye tas atake bacci yayi gaba da ita...

kan 3seater aka shimfidar da ita……

abba,daddy,goggo da ammy sun zama yan kallo domin ko kallon abin suke kamar a shirin film...

baby da maryama suna zaune sai kuma mami wato yar maryama dake ta sheka baccinta tunda suka shigo……

Mikewa mallam yayi ganin haka wayanda yazi dasu dasuke zaune tun dazu suma suka mike...!

inda ameer yake ya tunkara suma suka rufa masa baya...ciccibarsa sukayi dakyar sbd wani bahagon nauyi daya kara...  wanda tsaf suka fuskanci mai hakan ke nufi...!

tsakar parlon suka shimfide shi kana mallam yace moha ya karo masu garwashi sbd wannan da aka kawo da farko har ya mutu...allah yasa akoi a wajen baba mai gadi dan haka babu bata lokaci yaje ya kawo masu...

wani kullin farin laida dan karami yafito dashi inda yamikawa wannan dattijon yakarba ya fiti da wani karamin kwalba da wani abu fari tas yake ciki ya diga a cikin wannan garin farin laidan...

yamikawa mallam sani shi kuma ya fara tofa addu'oi wjen minti shabiyar tukunna ya dakata... yatsarsa yasaka yaa lakato wannan abin yamikawa dayan dattijon dake wajen kan ameer sauran...

Hmmm shima lakatowa yayi inda ya tusa cikin hanci ameer sannan ya karo wani ya mursuka a hannunsa kamin yafara shafawa ameer akansa,wajensu kunnensa,wuyansa tas ya shafe kuma har lokacin ameer bayyi motsi ba...!

hakan kuma ba karamin mmk yabama mutumin ba...!

mallam sani kuma wajen kafafun ameer tsakanin yatsunsa ya shashshafa masa sai ya dakko wannan kaskon ya lakato mai dan yawa ya jefa kan garwashin...

Take wani dan banzan hayaki ya turnuke cikin parlon...take ameer yafara wani kalar tari na fitar hankali wanda haka yayi sanadiyar farkawar ummie daga bacci...

kallon kowa tayi inda tasauke idanunta akan mimi datake tarin itama ga kuma turtsetsen cikinta dan wata bakwai da sati amma a haka idan ka gani kamar na wata tara...

mikewa tayi daga kwace datake btr da tayiwa kowa mgn ba taje gefen ummi tazauna itama ta kwanto jikin ummie tayi mata side hug ta zubawa sarautar allah ido...

ameer kam tari yame tayi duk idanunsa sun fito waje tsabagen wahala jijiyoyin kansa rado rado duk ya fice a hayyacinsa amma tsabagen garda baxai bude baki ba...

wannan ruwan daya daga cikin samarin yazuba akofi ya watsawa ameer a fuska aykuwa take ya challara wani kalar ihu wanda ya razana duk wani mahalukin dayake cikin parlon...

wani ruwan yakara watsa masa wannan karan kam a razane yamike jikinsa na bari zai gudu...aykuwa matasa biyunnan sukayi wuf suka kamosa amma a  hakan ma so yake ya zubarsu...

ganin haka da mallam yayi ne yasa shi cema moha y tashi shima ya tayasu...abin mmk moha ma yana kamasa sun zama su uku kenan... Ameer yy wani kukan kura gaba dayansu sai gasu a kasa warwas!

tashin hankali kenan mimi,ummie,baby,ammy,ummi goggo da maryama duk kuka suke wurjanjan sun takure jikinsu waje daya ganin yadda ameer ya zubar dasu moha abin ya matukar birkita masu lissafi...

daddy da abba ma mikewa sukayi suka tunkari ameer din inda suma wayanda suke kasa suka mike tare suka kamo ameer dake kokarin guduwa yanata ihu yana fisgewa shida lallai abarsa yafita waje .....

saida suka tabbatar da sun masa riko mai kyau ta yadda bazai iya fecewa ba kana suka maida shi kan cafet dake malale tsakiyar parlon duk suna tofa masa addu'oin dayazo bakinsu...

vote
comment
share
follow@ummien2018

You are reading stories on: TeenFic.Net

Tags: