Chapter 1-5

Background color
Font
Font size
Line height

💝 *MAFARKI NA*💝
   💝                         💝

*_Written by F k Ahmad_*

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's_*

*_Follow me on Wattpad @ Fkahmad

[email protected]
IG PML WRITERS
https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
http://maryamsbello.blogspot.

*_In dedication to Mss Hafsy_*👄
      ( *its me* )
_The whole book is dedicated to you my dear._

A short story from my night mare.

01 - 05

      Pom pom pom pom Horn na motor ce aka danna a cikin harabar wata dankareriyar gida da alama jiran mutum ake ya fito.

       Yarinya ce da bata fi shekaru 17 ba ta fito daga d'aki cikin sauri sanye take da uniform na makarantar islamiya da 'yar jaka k'arama a hannun ta.

        Hajiya Fatima ta d'aga murya tace "Hafsah har yanzu baki fito ba?" Hafsat da ta riga fito wa basu sani ba tace "gani nan Mummy na fito fa".

       Alhaji Ibrahim yace " yauwa 'yata yi sauri Ahmad na jiran ki a waje", murmushi d'auke a fuskar ta tace "toh Daddy, Mummy sai na dawo", ta fita a guje.

       Daddy ya bita da murmushi ya juya yace da matar tasa "yarinyar nan da alama tana enjoying wannan sabon makarantar tasu".

      Mummy ta d'ago tace " sosai fa dubi kwata kwata satin ta d'aya da fara zuwa amma duk ta je ta dawo sai ta bani labarin yadda karatun su ya kasance tare da sauran d'aliban har ma da malaman yadda ta saba da kowa ga kok'arin da take yasa har sun zab'e ta wata musabaka da za suyi next week jiya take fad'a mun".

       Daddy yace "ai tana iya kok'arin ta dole mana, shi yasa take burge ni saboda son karatun ta".

      

        Hafsat da ta fito da sauri ta nufi wajen motar ta bud'e gidan gaba ta shiga tare da cewa " yaya Ahmad dan Allah kayi hak'uri na saka jira na".

       Ahmad da ya juya kallon ta yace "ai dan kinsa ba ajiye driver'n ki Bala yana jiran ki ne", Hafsat ta langwab'e  fuska tace " Allah sarki bana b'ata masa lokaci fa yanzun ma wani littafina da bangani ba shi na nema".

       Baki Ahmad ya tab'e ya fisgi motar suka bar gidan. K'awayen ta na islamiyar su da tagani suna tafiya tana d'aga musu hannu suna maida mata.

       Ahmad da yaganta yace "meye haka sai kace wata bakauyi ya", hak'ora ta washe tace masa " ya Ahmad k'awaye nane fa kuma ina missing d'insu".

        Maida kallon sa ya kuma yi kanta yace "toh da wace gulmar ta kaiki barin islamiyar nasu?" Had'a rai tayi tace "ba na fad'a muku shi wancan makarantar basa zuwa kalan musabakan nan da ake ba amma wannan suna zuwa yi har wasu state fa kuma ni haka nake so, kaga *mafarki na* kenan in zamo musaddiqa".

       Gyad'a kan sa yayi yace " sannu malama Allah ya taimaka". A sannan daidai lokacin yayi parking motar sa a k'ofar islamiyar su *Madrasatu Tarbiyatul Ummah.*

      Hasfah ta bud'e k'ofar motar tare da cewa "bye bye Yaya sai ka dawo anjima". Da sauri ya katse ta " ke akwai inda zani fa anjima bazan samu wa ba" ya ciro naira d'ari biyar ya mik'a mata tare da cewa "gashi inkintashi ki tafi", karb'a tayi tace " OK yaya bye", tayi sauri ta shige cikin makarantar tare da sauran dalib'an.


       Tana iso wa ajinsu kenan ta tarar da d'ayan malamin su da yazo kiran su hud'u da aka zab'a zuwa musabakar. "Yauwa ga Hafsat Ibrahim ta iso" cewar wata dalib'a a cikin su wacce har sun k'ulla kasance da ita".

       Hafsat ta k'araso wajen nata murmushi d'auke a fuskar ta tace "Aisha har kin rigani zuwa ne yau". Malamin yace " oya toh muje d'ayan ajin da babu kowa naji karatun ku". Nan duk kan su suka juya zuwa ajin.

       Bayan kamar awa Malamin ya gama saura ran karatun su masu dad'in sauti da tajweedi nan yake fad'a musu saura kwana ki hud'u zuje fadar sarki domin gudanar da musabakar daga can kuma azab'i mata biyu maza biyu cikin duk kan makarantun garin Borno akai su jihar Jigawa dan cigaban shirin.



       Bayan sun tashi daga islamiyar Hafsat da sauran d'aliban da aka zab'a suka kama hanyar zuwa gida nan Aisha take nuna masu wata makarantar dake kusa da nasu tace "suma zasu je musabakar maza zalla ne acan kuma boarding ne tun yara suna k'anana ake kawo su sannan ko wani shekara sai an samu d'alibin da zai lashe wannan gasar daga makarantar saban karantun su da hazakar su amma makarantar nada takura sosai har sai wasu d'aliban sun baka tausayi a cikin su saban yadda suke koma wa dan musguna musu da malaman keyi".

       Hafsat ta wangale baki tace " Allah sarki amma ai hakan kuma ya koma mugunta". Haka suke shan hirar su har kowa ya iso anguwan sa Hafsat ma ta k'arasa gida da k'afa dan daga can babu nisa da gidan su.



Urs Hannaf😘

You are reading the story above: TeenFic.Net