part 20

Background color
Font
Font size
Line height

*INUWAR ZUCIYATA❤*
           _{Zarah ko Jeedah}_

*Na: Raheenat Mamoudou*

*Story by: Mamuh geee*

*ViaWattpd Raheenatmamoudou*

*Da Sunan Allah mai rahma mai jin kai*
_________________________________

*<< Page 20 >>*

Mami ce ta shigo dakin jaheed a cikin bacin rai.
Jikin Jaheed yayi sanyi sosai, ya tsorata sosai da yanayin da yaga mahaifiyarsa, dole ya sauko daga gado ya zube a gabanta ya zura mata ido cike da tambayoyi masu firgici, ya ce "Mami me ya faru? "
    Ai kawai ta fashe da kuka sakamakon ta rasa me zata ce don takaici. Jikin Jaheed tamkar an zuba masa kankara don tsananin sanyi, yaji gaba d'aya duniya  ta fice a kansa.
    Ya ce, "Don Allah Mami ki yi shiru, me ya faru? Dan Allah ki yi mini afuwa?". Ta ce,  "Jaheed me kake shirin nuna mana? Bamu isa da kai ba ko me? So hauka ne? Saboda kana son zuciyarka za ka bar mana abin gori abin Magana."
    Ya ce,  "Dan Allah Mami kiyi hakuri, me aka ce na yi?" Ta ce "Me ye ya hanaka tafiya dinner party? Saboda me ka fada mini? " Ya ce "Wallahi ba komai, kawai dai daga Allah ne, don ba abin da zan iya ce miki. Kiyi hakuri gobe Idan Allah ya kaimu za ayi party,akwai abokaina masu zuwa daga kasashen turai koma miye gobe zan halarta, Don Allah Mami kiyi hakuri".
    Mami fateema ta kakkabe hijabinta, saboda ita duk tausayin Zarah ne ya rikita mata zuciya. Ta mike ta bar dakin. Ta girgiza  kanta, tabas Zarah so take yi ta rabata da danta, yarinyar ta cika korafi, Bayan ta tilasta an raba danta da abin da yake so ta zo tana koke-koke don ta tayar mata da hankali, ina dalili.
      Shi kam Jaheed kansa ya rike cike da damuwa, ba shi da yadda zai yi. Mutum daya yake jin zai tunkara da maganar nan ya fahimce shi, mudin shima ya goyi bayan su daddy tabbas dole ya hakura ya rugumi kadara.
     Inna Hadjara ma tana neman ta la'ance shi, zuciyarsa ta ringa bugawa, bai yi zaton Jeedah za ta yi mishi haka a gaban Inna ba, Ya kwanta shiru, shi kam ta faru ta kare an yiwa mai dami daya sata.
     Tunani ya tsananta bai har karfe biyu da rabi na dare, amma bai daina hayaniya ba da jama'a. Ya shiga falon duk mutane a kwance sun yi shimfida, wasu sun yi barci wasu kuma idonsu biyu.
      Ya so wuce ba hanya, ya koma corridor din falon ya kira wayar Zarah a kashe, ta Jeedah ma a kashe. Sai ya kira ta Abida ,ringing biyu ta dauka. Ya ce "Ina Jeedah?" ta ce, "Gata nan tana game a T. V". Ya ce "To ina Zarah?" ta ce, "Tana dakin Mmy ina ganin kamar ma bata da lafiya yanzu suka dawo daga asibiti".
    Ya ce "Me ya sane ta?" Abida ta ce "Kamar dai na ji wai an ce hawan jini ko zuciyarta ta yi me? Oho dai!Amma sun dawo yanzu" ya ce "Ki yi dabara ku fito nan corridor  falon Daddy ke da Jeedah ina son ganin ku". Ta ce "To ba matsala".
      Da kyar ta fito da Jeedah a corridor, yana tsaye daga shi sai jallabiya ,ya ce "Abida dan jirata ku koma".
    Ita kam Jeedah kallon sa take yi cike da kosawa da al'amarin da ta kira da saninsa.ya ce "Wai Jeedah wane irin mataki kika dauka?Rabamu fa ake shirin yi?Jeedah rabuwa ta har abada, ban ga kin dauki mataki ba, ban ji kin ce komai ba, duk hanyar da na biyo don ki ceto soyayyarmu ban ji kin ce komai  ba, kina nufin hakan dai-dai kike yi? Please Jeedah ki dauki mataki don ke ce kawai za ki iya hanawa a gidan nan a hanu a dalilin Inna."
     Idonta ya cicciko da hawaye, a sanyaye ta ce "To yaya me zan yi? Ya kuke so na yi? Ka ga kuwa yadda Zarah ta koma a dalilin sonka? Duk ta rame fa ta yi wani irin ta fita a hayyacinta, ta ce mini muddin bata aure ka ba rayuwarta ta lalace. To ya zan yi? Saboda ina son ka sai na bari rayuwaar 'yar'uwata ta lalace saboda son zuciya irin nawa? Ka  duba fa ka gani, so kake na bari yar uwata ta halaka saboda me?"
    Jaheed ya Kalle ta a tsakiyar idonta ya ce "Saboda (SONA)". Ta girgiza kanta hawaye yana zubo mata ta ce "Ba zai yiwu ba". Ya ce "Ni kenan son naki ya kashe ni ko Jeedah?"
    Ta dauke kai gefe ta ce "Baka ga abin da suke mini a kan auran nan, Don Allah ka yi hakuri ka manta ma ka taba son wata Jeedah a rayuwarka don Allah?"
   Wani makoko ne ya tokare shi a makoshi ya ce "Duk wanna abu Zarah ce ta yi mini wallahi son zuciya ne irin nata, daga taga mun yi aure Allah hakura zata yi, ai ke kin sani idan na rasaki ya Rayuwata zata koma?"
    Jeedah ta jinjina da bango ya yin da shi din ma ya matso daf da ita, numfashinsu na bugun na juna  ya ce "Ke dai Jeedah ba kya sona kawai ki ce mini". Ta girgiza kanta ta ce "Kuma Don ina sonka sai na batawa yar uwata rai? Ko duma don ina sonka sai mu nuna rashin tarbiyya a kan namiji da idan daya ta mallake shi cikin mu ya zamo haramiyar dayarmu?" Ta fada tana share hawaye. Dukkansu tausayin juna ne ya kama su,  ya fada muryarsa a sarkake tamkar zai yi kuka, ya ce "Idan da wata daga cikin dangi ne zan hakura na aure ta Jeedah, amma ba zan iya hakura da ke ba.
    Ita kuma Zarah idan na aure ta ke din kin haramta a gareni har abada, ki taimake ni don Allah Jeedah ki samu Babba FaruQ ki zayyana mishi don Allah, zai San yadda zai yi yayi maganin komai, amma ni ke nake so, ki taimaki raguwata Jeedah, idan na rasaki raguwata tagayyara zata yi. Wani hali zan shiga ki rufa mini asiri don Allah ki ceto rayuwata, ta yaya zan iya auran Zarah ke kuma ya zan yi da sonki?"
    Jeedah ta juya masa baya tana wata irin shessheka ta saki kuka mai karfi, abun da take boyewa dole ya bayyana, ta ringa kuka tana karawa, ya matso gabanta sosai ya dafe bango ya ce, "Ba kuka ba, wallahi kiyi komai ta fanjama -fanjam! Ai kin sani ba za ki iya daurewa ba kiyi rayuwa ba tare dani ba".
     Yayi shiru yana kallon ta, ita kam jin zafin maganganunsa take yi da wani irin tashin hankali da ya lullubeta, ta ce "To meye?  Ai kaine ka yi kuskure, kuskuren da ba zai taba gyaruwa ba.  Ta yaya zaka hada son Ya da kanwa a lokaci daya? Ai ni banga laifin Zarah, tun farko a wurinka ta samu damar da ta sanya sonka a zuciyarta, dole kuma ta shiga wani hali. Baka ga yadda ta koma ba idan ka ganta tilas kaima ka tausaya mata, daga ni har kai bamu kaita shiga takura ba, baka ga yadda ta koma ba, idan na aure ka mun yi aure mun barta ta shiga wani hali meye burinmu?"
    Yayi shiru ya ma rasa a wace duniya yake don tsananin tashin hankali.  Ya ce "Ki yadda dani Jeedah, wallahi ke nake so, ban san me Zarah take yi ba sai cikin satin nan. Kar ki jahilceni mu fahimci juna mu malaki junanmu, idan ya so daga baya komai zaki ce ki ce mini".
   Cikin kuka ta ce, "To ni yanzu ya kake so na yi da raina?" ya dan kwantar da murya ya ringa tsara mata yadda za ta yi, har dai ta amince. Ta ce "Zan yi ma Baba FaruQ magana, yadda aka yi zaka ji".
   Sai a lokacin ya samu natsuwa, ya kama hijabinta yana goge mata hawaye. Ya ce "Ni sai yanzu na samu natsuwa, watakila yau na iya barci a cikin kwana biyun nan, Jeedah rashin hadin kanki ba karamin bala'i ne ba a cikin wannan al'amari, kiyi afuwa mai sona".
  Sai lokacin tayi mishi wani irin murmushi, ya yin da hawayen ya ci gaba da zuba, ita kadai take jin ya take ji a ranta da wannan al'amari. Ta kewaye shi ta wuce ya bita da kallo.
   Zuciya ta ringa ayyana mishi tunani kala-kala to meye ma idan sun aura mishi Zarah? Wallahi shekara nawa ne sai dai a warware auren, amma baya son ta, ko a yi duk abin da za ayi, amma da girmansa da shekarunsa ba zai ta6a yadda da auren dole ba.
     Yana kallon su Jeedah har suka shige gida, ya yin da zuciyarsa ta ringa tsorata da yadda jeedah tayi mishi wani irin murmushi mai rikitarwa, ga kuma hawaye da ya biyo idonta, tabbas ya san akwai wata a kasa, amma ko meye a yau kwanan zaune zai yi, shine mafitarsa ya kwana yana addu'a.
******* ******* ******* *******
Jeedah ta bayyana a dakinsu da ya zamo na kwanan su, Zarah ce zaune bisa sallaya, kallo ta watso ma Jeedah tamkar kada ta dauke idonta, ta ce "Meye kuma?". Ai kuma sai Zarah ta fashe da kuka, ta mike ta rungume ta ta ce "Jeedah ya ki ko? Baya sona? Me ya ce miki?"jeedah ta Saki ajiyar zuciya cike da dauriya, ,don ta fara jin tsanar yar uwarta, ta yi maza ta kori shaidan ta ce "Ba wani abu Zarah, zan ce ya riga ya wuce".
   Babu wanda ya sake magana, don Abida gaba daya tausayi suka bata, kowa da irin nazarin da yake yi a ransa har barci ya dauke su.
   Da safe iyayen mata suka hadu a babban falo kowa da irin tunanin da yake ransa, Sun juma suna tattanawa a kan wannan rigimar da ta sako kai a tsakanin 'ya'yansu.
    Alhaji FatuQ yayi kiran yan uwansa da mata da iyayen yaran aka yanke magana kowa da abun da yake fada, a hada Zarah da Jeedah don sune manya, sune masu rike zuri'a a can gaba.
   Jaheed ya nuna amincewar sa, baba FaruQ ya ce "Sai ka fada ya kake so ayi? " ya ce "Ni so nake yi kawai a kira Jeedah ta fada da bakinta, idan ta ce bata sona shi kenan na yadda na hakura".
   A wurin ya kira wayarta, ringing biyu ta daga. Baba FaruQ ya ce "Kizo ke da Zarah ". Ta ce "To baba ".
  Sai gasu Sun shigo wurin Zarah ta baiwa kowa mamaki ganin yadda ta rame ta lalace, ya yin da jeedah ta fada kadan. Sai da suka gayas da kowa sannan suka koma gefe suka nutsu suna jiran abun da zai biyo baya.
   Alhaji faruQ yayi gyaran murya ya ce "Ke Jikar Inna ya kuke da Jaheed? " ta daga kai ta kallo inda Baban yake sannan ta kalli Jaheed din da yayi kicin-kicin yake hararar Zarah, lokaci guda kuma suka kalli juna.
   Ta ce "Ya muke da shi kuwa?" Baba FaruQ ya ce "Maganar aure ne babu wasa a cikinsa, ko ni nan bana so na ja da ikon Allah. A da na yi ikirarin hana maganar nan, ganin ya dage yasa na kira ku ki gaya mini miye a tsakanin ki da shi?"
   Ta girgiza kai tana gyara zama,  ta ce "Gaskiya ni babu komai a tsakanina da shi". Jaheed dan takaici kamar ya mike ya rufe ta da duka. Ta ce "Baba babu komai a tsakanin mu ".
     Baba faruQ ya ce "Kar ki yaudari kanki ki fadi gaskiya ". Ta ce "Gaskiyar maganar ke nan, wallahi tallahi ni babu maganar aure ko wani soyayya a tsakaninmu. Kuma ni ya fita idona da maganar nan, Allah baba kar ya kuma yi mini ita, idan shi bai san darajar zimunci ba ni na sani, matsayin Zarah a wurinmu ta fi karfin wulakanci, dole a san yadda za ayi abi mata hakkinta da Yaya Jaheed yake dannewa.
   Saboda tun farko da Zarah suke soyayya laifi ta yi mishi kawai yake son ramawa......."Jaheed ya katseta cike da fusata, ya ce "Don Allah malama ya isa kar kiyi mana karya tashi jeki".
   Baba FaruQ ya ce "Idan dai fushi ne ai fushin masoya hutu ne".Baba FaruQ dai ya ringa dariya ya ce "To kai Jaheed har mace ma ta fika tunani da sanin darajar zumunci? Mace Jikar Inna da duk gidan nan ake ganin ita ce mara wayo, Allah ka bani kunya".
     Duk kuma mutanen sai suke fadin, "Ita fa Zarah da gaskiyarta, hakuri zaka yi Jaheed komai mai wucewa ne, watarana sai labari". Ya ringa share zufa, Jeedah kam ta shammace shi ,yarinya karama har ta mini irin wannan wayo da kisisina".
   Ya ce "Shi kenan Baba Allah yasa haka shi ya fi alkhairi ". Mami ta ce "Abun da ya kamata kayi kenan tun farko, saboda me?  Saboda kune manya kai da Zarah, kune masu rike baya".
  Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Shi kenan ai Mami zance ya wuce, tunda ta ce bata son maganar". Baba FaruQ yayi musu nasiha sannan aka rufe taro da addu'a suka fice kusan a tare.
     Duk yadda Jaheed ya so ya tare Jeedah abu ya fuskara, har suka shiga babban falo jikinsa sai mazari yake yi, ya bisu har dakinsu. Ganin ya shigo dakin Zarah ta shiga toilet, ya tsare Jeedah ya cika da fusata ya ce "Ni kika yi ma haka ko? Ni kika yi ma haka ko? "
    Jikinsa yana mazari kamar zai doke ta. Ta ce "To....... " ya ce, "Wallahi kika yi mini magana sai na tattakaki zan fice a dakin nan, mara mutunci maras kunya."
   Ita dai Jeedah bata yi magana ba, hasalima tausayi ya bata ganin yadda idonsa ya kada yayi jajir jikinsa sai mazari yake, ta ringa ja da baya yana binta har ta jingina da bango, idonsa yafi komai razana ta.
     Ya take mata kafa da takalminsa ya ce, "Kije idan cin amana riba ne kije kin ci amanata, kuma sai Allah ya saka mini". Ya fada yana murje yatsun kafarta jikin tayal, da wani uban takalminshi.
    Ta kwalla kara ya yin da Zarah ta fito da gudu kada yayiwa yar uwarta fyade, ya bata aurensu.
   Ta ce "Me ta yi maka ". Bai yi mata magana ba ya fice daga dakin.....

*®🌲Real Hausa Fulani Writer's Form 🐄*

You are reading the story above: TeenFic.Net

#page