part 17

Background color
Font
Font size
Line height

*INUWAR ZUCIYATA❤*
           _{Zarah ko Jeedah}_

*Na: Raheenat Mamoudou*

*Story by: Mamuh geee*

*ViaWattpd Raheenatmamoudou*

*Da Sunan Allah mai rahma mai jin kai*
_________________________________

*<<Page 17>>*

          Madam Sabirina malama ce a makarantar da su Jeedah suka yi primary suka yi  secondary, Ita ce ta yi musu lesson tana da ilimi sosai a harkar koyarwa, akwai method of teaching, don haka Daddy yake son ta koyar ma yaranshi, don ko su Mmy Ita ce malanarsu. Sun samu ilimi sosai ya fi na wanda ya kamala diploma wurin madam Sabirina,don zuwan sukasar turai basu da ilimi da ya wuce na primary.
         Ita ta kaisu suka yi karatun shekara uku suka gama secondary. Itace tayi musu hanyar da suka yi diploma,komawar Mmy Egypt a can tayi digiri dinta, Fateema mahaifiyar Jaheed Ita ma tayi , madam Sabirina ta daure masu gindi sun samu ilimi sosai ta hanyar ta, don ko Ita yanzu tana aikinta na koyarwa a primary kasancewar tana jin dadin aikin ta sosai, kusan kusan koyarwa a cikin jininta yake. Tayi musu sallama ta wuce gidanta.
     A ranar har karfe biyu na dare suna hira, don Mmy ta dade da kwanciya ba ta San ya zo ba, Sai da safe ta ganshi. Da safen ma a kicin ta iskeshi shi da Jeedah suna kwamacalar su. Ta rike baki ta ce "Me ake yi a nan?"
      Ta sa kai kicin din,sai kuma tayi arba da Jaheed sanye cikin kayan barci, ta ce "Au!" Dama kai ne ka tayar da Jeedah ta shiga kicin da sassafen nan? Saukar yaushe?"
       Yayi murmushi,ya ce "Wurin Sha biyun dare jiya na shigo, Sai kuma na iske madam Sabirina da Jikar Inna a falo suna faman lesson suna fada". Mmy ta ce "Ai fa aikin kenan,babanku yayi ma Inna wayo ya ce ta zo ta yi Hutu a nan sati uku na rakota, Sai kuma ya kaita makaranta, don ko ni ban yi shirin zaman nan ba, yanzu tilas ta sani Sai Na sake shekara biyu a garin nan bana son sa, saboda yanayin sanyin shi".
      Jaheed yayi dariya ya ce, "Haba dai Mmy shekara shida za ki yi, har Sai Jeedah ta kammala digiri". Ta rike baki ta ce , "Ka soma shirmen naka ko? Ta ma kammala Sakandire din ai an rage, ni ban fiye son hayaniya ba, ka San kuwa zama da Jikar Inna hayaniya kullum ne bakina ba ya hutawa, idan ba ta yi fada da madam Sabirina ba za ta yi da masu aiki, kullum ni ke nan bakina ba rufuwa".
     Yayi dariya domin dai ya san gaskiya ta fada. Ya kalli Jeedah tana faman soya kwai ya ce, "Ni fa Mmy sai na ga kamar tayi hankali yanzu, Allah ta rage". Ta kalli Jeedah ta ce "Yanzu dai da sauki, don ni Ina mamakin natsuwar Jeedah, wani lokaci kuma Sai ka ga ta yini a daki". Jaheed yace "Gskiya Kam".
     Jeedah Kam ko ta kansu bata biyo ba, ta ci gaba da sabgarta don itace ta shirya tebur ranar, har mamaki Jaheed ya ringa yi lokacin da yayi wanka ya fito diening room.
      Jeedah Kam da ta yi wanka Sai ta sanya wata irin riga yar fit ko cibinta bata rufe ba, Sai dogon wando wani baki haka mai fadi. Ya juya ya kalle ta tsigar jikinsa ta yi yarrrr! Ya kau da kai. Ta iso gabanshi ta daure gashinta da ribon, ya ga dai za ta iya ba shi kunya a gaban Mmy, don ba zai iya dauke idonsa d'aga kallon ta ba.
        Ta ja kujera a gabansa ta zauna ,ya lumshe idonsa da kyar dai yayi ta Maza ya ce "Jeedah meye haka? Ki koma ki canza shiga wannan ai shirme ne zama a cikin shigar turawa". Mmy ta ce "Wannan fa sai ka tsawatar kana ganinta wannan ba jin magana take yi ba, Sai ta yini a tsakar gida d'aga Ita short nica Sai best".
     Gaban Jaheed ya buga da karfi! Wace irin rayuwa Jeedah za ta yi cikin turawa da wannan halitta? Sai kuma ya shiga addu'a a ransa, ya Allah ya bashi ikon gaya mata gaskiya, ya all ya bashi ikon ganar da Ita hadarin da yake tare da turawa.
      Ya ce "Ai dole Mmy na tsawatar ba zan yadda da wannan shirman ba, bari dai na samu zama zan dan kwana biyu daku. Daddy ba ya nan ko?" Ta ce "Ya je Maroc Amma cikin satin nan zai shigo".
     Suna hira sama-sama su kai breakfast din, Jeedah Kam ba ta fito ba har suka gama, don haka bai biyo ta kanta ba ya fice harkokinsa.
       Sai gab da magarib ya shigo , Mmy ce kawai a falo, ya durkusa ya gaishe ta, ya nemi wuri ya zauna. Natalie ce ta shigo tana son ta yi 'yan goge-gogen yamma, wato mai aikin Mmy ce. Ta gaishe da Jaheed ya amsa ya ce "Wai Mmy har yanzu Natalie bata yi aure ba?" Mmy ta yi dariya tana kallon Natalie din, tsohuwar mai aikinsu ce ta ce , "Natalie bata yi aure ba, su ka sani idan har ba suyi suna twenty years ba suna iya kaiwa fifty years ma ba tare da sunyi auren ba, kuma basu damu ba". Ya ringa tunanin gida Niger.
       Inna kullum maganar ta ayi mishi aure ayi ma Zarah aure, idan ta rasa miji ne a hadasu ayi musu auren gida.
    Tambaya d'aga can cikin zuciyarshi ta ce mishi "To ko ire-iren wannan maganar ne ya sa Zarah ta sanya ma ZUCIYATA son auren shi?"
    Kuma dai Sai ya Kawas da wannan tunanin, ya ce "Mmy Ina Jeedah ne ban ji motsinta ba?" Ta ce mishi ,"Ina jin fadan da ka yi mata da safe shi ne ta kule ,ka San Jikar Inna rigimar duniya, shi ya riga yasan ba shi kadai ba, kowa ma ya kalli surorin Jeedah a bayyane dole ne ta taba maka ZUCIYA, balle shi da yake da rauni a kanta, muryarta ma rikita shi take yi, to balle ya ganta a bayyane, Lallai 6arna za ta afku, Allah ya kiyaye . In dai ba ta daina ba Sai dai ya bar garin da zarar ya kammala abun da ya kawo shi.
      Ya ce, "Natalie kawo mini abinci". Ya fada cikin yarenta. Da hanzarin ta ta kawo center table ta ajiye ,ta je ta shiya abinci ta dora a kansa, ta janyo shi gabansa.
      Yayi murmushi ya fara cin abincin, bai yi rabi ba Sai kuma ga Jeedah ta bayyana cikin shigarta dai da yake fada a kanta. Sanye take cikin best da short nica farare Sol.ta baya ta shigo falon, suna hada ido ta juya da gudu.
    Ya ja tsuki a hankali tare da sunkuyar da kai ya dau cup da lemon juice ya kora mai sanyi , d'aga haka bai sake cin abincin ba, zuciyarshi na yi mishi fada,me ma yasa ya biyo Jeedah ne? Maimakon a samu sauki Sai rashin sauki, bege ya tsananta ga rayuwarshi . Daga sama yaji Mmy tana cewa, "Ka ga irin abin nata, idan har baka yi mata magana ba bata da niyyar dainawa, ni tsorona daya 'ya'yan turawa nan kar su bata mata tarbiyya".
    Sai kuma jikin Jaheed yayi sanyi , da hanzarinsa ya Mike ya bi bayan Jeedah, har cikin dakinsu . Jin kamshinsa ya sa ta juyo ,ai kuwa Sai ta kasa hada ido dashi, don tsoron kallon da yake dauke dashi. Ya ringa binta tana matsawa,har dai ta zube a gaban dressing mirrow. A yanzu sanye take da doguwar riga blue mai adon dawisu, ta yi mata kyau sosai. Bai yi magana ba Sai ya ja stol din da yake gabanta ya zauna, ya tsare ta sosai ba ta da yadda za ta yi ta gudu, cikin muryar sa mai kaifi mai tsananin tasiri a gangar jikinta ya kirata , 'JEEDAH!'
     A hankali ta amsa "Na'am" . Ya sanya manyan sexy eyes dinshi ya ringa kallonta , ya yin da ta gama mutuwa a zaune, shi ya san dole majm Jeedah ta yi sanyi saboda ko Ita ce ta kalle shi kashe masa jiki take yi, balle kuma shi da ya Lura tana da rauni sosai idan ya kalle ta, Sai ya ringa hukuntata da idonsa.
       Ya ce, "Me yasa ba kya jin maganar Mmy?" Idonta ya cicciko da kwalla ta kara matsawa jikin Madubin ta ce "Ni wallahi Ina Jin maganarta". Ya ce "Jeedah ba kya ji ,da kina ji ya Mmy za ta yi miki magana ki ki jin maganarta   Sai fa kun bi Iyayenku 'ya'yanku za su biku. Kiyi amfani da wannan ayar da Allah ya fada cikin suratul Abzab. To balle ma Mmy tana miki fada ne don ki gyara kiyanarki ,ki kyautata kwanciyarki kabarinki, ki taimaki kanki, ki taimaki rayuwarki nima ki taimake ni, ki yi tattalin komai da Allah yayi miki baiwarsa ki 6oye surorinki ,ki taimaka Jeedah ki ku6ata d'aga sharin nasara da take tattare da garin nan ,ki 6oye min kanki kin ji my love?"
    Kunya ce ta kamata sosai, ta ce "Ni wani namiji ne ma ya isa ya kama mini hannu balle ya nemi nuna mini wani sharrinsa?" Ai kuma shi Sai yaji kunya , Lallai duk mace sunanta mace.
       Sai ya ce "Yauwa Jeedah ashe kin gane, ki ci gaba da 6oye kanki ba Sai  Na gaya miki ba, kin sani kina da sura mai daukar hankali, ki kiyaye kin ji ko?" A hankali ta amsa . Ya ce "Tashi muje ki ci abibci kin ji ko? Mmy ta ce mini wai baki ci komai ba". Ta ce "Na ci mana, abin da Mmy din gidan kawarta ta tafi bata nan".
     A nan cikin hikima da dabarunsa na da namiji ya fahimtar da Ita abin da yake so ta ringa yi ta kuma amince. Don haka washe gari ya saya mata himar da after dress sun fi kala goma, dukkansu Turkey ne masu asalin kyau da tsada , idan ta yi shigarsu tamkar balarabiyar indonosia.
     Shi kansa mamaki yake yi yadda weather din wurin ta karbi jikin Jeedah, don har wani fari take yi fatarta tamkar ta jarirai don laushi ,kafarta kuwa tamkar ka 6ula jini ya fita, don surorin Jeedah Sai yanzu ne ma suka fara bayyana da wani irin santsi da kyau da aheki, balle kuma da a yanzu ta kara wanin irin gogewa.
      Kullum da safe idan ta fito da shirin tafiya makaranta cikin uniform lalacewa yake yi wajen kallon ta, wani lokacin kuma kishi ya lullube shi . Sai da yawa Sai ya kai ta har gindin school bus, idan ta dawo gida kuma yini suke yi tare ba shiga ba fita, yana koya mata home work.
      Da karfe uku ta yi ta wuce evening lesson a can makarantarsu Sai biyar. Tana dawowa kuma ta wuce babban matsalacin unguwar su ta dauki karantun al'kur'ani, gida kuma Sai goma da Rabi take dawowa. A nan kuma Jaheed ya dawo d'aga wurin harkokinshi , Sai ya tare ta da hirarsa mai zafi.
     Daddy yana zuwa ya ce , "To kai Jaheed yaushe zaka koma? Akwai mutanen mu na nan da suke so su iske ka can Niger, ka tura sabon injinan?" Ya ce "Eh ,na tura su ta jirgin ruwa Sai son 12 kayan za su isa . Don haka nima sai on 10 zan tafi".
     Daddy ya kalli agogon hannunsa ya ce, "Yau 5 ga wata". Ya ce "Eh bai fi sauran kwana biyar ba zan   tafi". Daddy ya ce "To  ni ban ga abin da kake yi ba, dukiyarmu ta tafi kai kana nan". Ya ce "To ni ya zan yi Daddy? Jira nake na ga results din su Jeedah ran alhamis za a rufe makarantar za a'yi Hutu, Ina son kuma zan Sai mata kayan happy holiday" Daddy yayi dariya jin Ana wani kambama Jikar Inna ya ce "Kai ma dai zaku da Inna tunda kake kula mata da yarta' ya ce "haka ne kam Daddy".
        Ranar Hutu kam Jaheed yayi kayan happy holiday wata school bag aka buga mai hoton Jeedah a jiki, tana sanye da uniform, siket iyakarsa gwiwarta, Sai T.shirt din uniform, tayi mata kyau babu Dan kwali Sai wani dan ribon da aka Dan lullube gaban goshi , safa da takalmi.
     Hoton Jeedah yayi kyau sosai, don jakar kalar pink aka yi, aka manna hoton a jikinta. Ta rabawa calassmate dinta. Gaskiya Jaheed ya kashe kudi sosai,sai dai ta yi kyau na ban mamaki.
    School bus tana ajiye ta Jaheed yana fita da saurinsa ya taryo ta, da kayanta na kawaye da suka yi happy holiday, su irin jakunkunan da a kai mata, su fulas din abinci kala-kala.wasu kuma maficin roba, wasu kuma exercise book da hotunansu a jiki, wasu kuma safa suka raba, wasu kuma handkitch da hotonsu, wasu T.shirt haka nan al'adar bature ta gada, dole ayi hotona kala-kala na calassmate da kayan happy holiday idan Hutu ya zo dole ne su yi shi.
     Jaheed ya amshi ambulan din hannunta yana dariya, ya ce "Kawo mana My baby?" Ta ce "A'a, Yaya ni dai gaskiya ka tsaya Daddy ya duba". Kallon da ya sakar mata ne ya sa dolenta ta sakar masa ambulan din.
   A falo ya bude yana dubawa , gaskiya ta yi kokari sosai, d'aga assignment har test duk ta cinye, haka nan exam mark ma ta yi tray, matsalar dai Ita ce ta zo (Last position) ta karshe.
    Ya duba ya mika ma Daddy yana fadin, "Ta yi kokari". Daddy ya ce "Wanne kokari kuma? Kana ganin comment din (Class master)Dinsu". Jaheed ya ce "Aa Daddy ka duba , comment din principal kaga abin da ya rubuta".
    Daddy ya duba ya ce "Don't consider with position,you have consider with mark and put more eport try again letter" can kasa kuma an sanya mata (Promot to S.S.2) Daddy ya ciko takardar yana dariya ya ce "A nan dai a ka Dan yi Sa'a tunda za a ajin gaba, Amma Ina abin kokari an dauki na karshe, don ma dai an Dan Samar maki Amma ai........."
     Jaheed ya katse Daddy yana dariya ya ce "Aa, Daddy ka sanya mata albarka mana". Yayi shiru. Jeedah jikinta yayi sanyi ,ta ce "Allah kuwa na dage Daddy, har fa bana barci Ina karatun jarabawa, don Allah Daddy ka sanya Albarka".
   Yayi shiru kamar bai ji ba, ta kalli Jeedah ta ce "To shi kenan Yaya Jaheed don Allah ka gaya ma Inna ta sanya mini albarka, an sanya ni a makaranta ka ji ko?"
   Yayi murmushi ya ce "Insha Allahu zan gaya mata" Daddy din ma dariya yayi ya ce "Jeedah nima na sanya Albarka, Amma ki tausaya ma Mmy dinki don ke take zaune a nan Egypt ta Lura da karatun ki, idan kin dage Sai ta ji dadi ta San ba zaman banza take yi ba, kin sani Sarai dai idan ba kya yin kokari ba zata ji dadi ba".
   Ta sake marairaicewa ta kalli inda Mmy take din sannan ta juyo ta ci gaba da kallon Daddy ta ce "Daddy wallahi wannan 'yan ajn namu masu bala'in kokari ne wallahi,karfi ne dasu a ilimi Daddy. Ina ma laifi na samo six hundred marks , wallahi Daddy I am try".
  Ya ce "haka ake yin try din? Maki Dari shida a cikin dubu, kyanki a ce Ai Jeedah kin kai nine hundred". Jaheed Kam dariya yake yi ya ce "Daddy ka ji fa?" Daddy kam haushi ya ishe shi da takaici, ya ce "Kema So nake ki dage ki zama mai bala'in kokari".
   Ta ce "To wallahi Daddy laifin teacher din namu basa bayas da maki sosai,ka ga fa yadda nake daddagewa Amma Dan maki kadan". Daddy ya ce "Ki sake dagewa wani term din Allah,wallahi Ina jin na sata miki mota cikin Happy holiday" ta ce "Daddy ta nawa kake so na yi?"Jaheed ya ce "Kiyi ta daya mana ki gani, ni har party zan zo shirya miki da dukkan calassmate dinki".
   Ya fada yana kashe mata ido. Ta ce "Ta daya? Allah ba zan iya ba". Ta fada cike da shagwabar, Daddy ya ce "Ai kin ji irin ragwantar taki ,kinga yadda zara ta ringa kwaso gift" ta ce "Ai Daddy iya fa Zarah ba irin ajinmu bane a ajinsu".
   Jaheed yana kallon ta ba ta son hada  ido ido da shi so yake ya bata kunya a gaban Daddy, ya ce "Yes! Irinsu ne mana ke ce dai raguwa" ta Mike ta ce "Daman dole karatu a cikin turawa ya baiwa bakar fata wahala".
     Dadd ya ce "Ita fa Zarah 'yar Africa a cikin turawan ta daya take dauka ko ta biyu" ta ce "Daddy Allah yana gani ba zan iya ta daya ba". Daddy ya ce "To fita ki baiwa mutane wuri".
     Ta wuce Jaheed ya bita da kallo, shi kuma Daddy ya bashi da kallo har Sai da ta bace, sannan Daddy ya ce "Sai ka hada komatsanka gibe ka wuce ko?" Jaheed ya Dan shafa sumarsa tare da lumshe ido ya ce "Allah ya kaimu " Daddy ya ce "Amin".
     Mmy ta ce "Ai ni jinku nake yi , bana shiga shirgin Jeedah, yanzu haka da dani a cikin zancen tayi ma mutane kuka" Jaheed ya ce "Ah! Mmy Wallahi yanzu ba komai Jeedah take yi ma kuka ba, kinga fa ta kara hankali Sosai".
    Ta ce "Lallai Kam na gani" ta kalli kayan happy holiday ta ce "Sai ka tattara kayan happy holiday ka kai ma su Kanan ta ragowar ka kai ma Inna ta baiwa masu so" Daddy ma Dariya yayi yana mamakin wannan kauna ta Inna da jikarta, ya ce "Eh Lallai idan anyi haka Inna za ta yi farin ciki".
     Shi kam Jaheed tashi yayi ya bi Jeedah, ya ce "Ki shirya mu fita waje Ina jiranki". Kallon shi Kawai tayi , ta yi murmushi. Kai kokari da dadi , kalli yadda yayanta Jaheed yayi mata tsadadden murmushi. Gaskiya dole ta dage da ilimi ko ta ringa faranta masa,kalli fa yadda har yake Kare  ta ya hana Daddy ganin laifinta?
   Tana tunani tana sanya kayanta , riga da wando ta sanya irinsu daya, sannan ta sanya after dress. Ta kofar baya ta fice ta same shi yana jiranta, tasi yayi shara zuwa (Zuvena point) a can ya samu karkashin lemu ya sanya kujera ta zauna, shi Kam Sai ya ja tum-tum da suke zube a wurin ya kishingida bisa grass carpet.
   Ya ce "Ki bani labarin samarinki na kauye kinji ko?" Ta harare shi ta ce "Ni waye  ya isa ya ce yana sona kaf kauyenmu?" Wani sanyi yaji har cikin zuciyarshi ya ce "Bana son wayon karya fa" tayi far da idonta ta ce "Kai ma ka San ai ba zan yi karya ba" ya ce "Ah! Lallai Kam manya mu babba gare ki" ire-iren ma'aikatan wurin ne yazo ya tambaya ma za'a kawo? Ya kalli Jeedah ya ce "Ka kyale ni na ringa kallon fuskar preaty ya ishe ni, Amma Ita kawo mata Ice cream ta sanyaya ranta da zuciya da ta tsananta da begena, ko ba haka bane my love?"
      Ta saki ajiyar ZUCIYA tare da yin murmushinta mai burge shi. Ya ce "Ko ba haka ba?" A tsakiyar idonta ya kalle ta,ta kuwa boye idonta, ya ce "Ki daina kunyar nan lokaci ma yayi da za ki daina jin kunya ta,abokiyar rayuwata fa zaki zama, na tambaye ki labarin samarinki kin ki kiyi magana" ta ce "Kai dai Yaya ka San halin Inna, yaushe ta barni fita hira balle har  wani yace yana sona?"
   Sai ma wani dan gidan Baba Arlit Sau biyu ya zo shi zance wurina, shine ya ce ma Inna wai zai aureni idan na kammala karatu .yanzu yana (Maroc)" Jaheed ya gane wa take nufi , ke nan jikan yayan  Inna ne, shine Babba a gidansu.
      Ya ce "Ai ba Dan Baba Arlit bane jikansa ne, wi Ramadan kike fada?"ta ce "Eh shine, Amma ai bana sonsa bai ma kara dawowa ba, Sai daya munje gidan kakansa gaisuwar mutuwa ya dawo damu a motarshi, Har Inna take fada wai ban gaishe shi ba. A can gidansu a Arlit suke cewa ga Matar Ramadan".
    Jaheed yayi shiru bai yi magana ba,ta kallo shi ta ce "Baka ji?" Ya Dan kalle ta ya Kawas da kai alamun ya shiga damuwa, ta ce "Yaya meye?" Ya saki ajiyar ZUCIYA, tunanin Inna yake matsayin  Ramadan  a wurinta,idan bai yi hanzarin daukar mataki ba tabbas Inna za ta iya ba shi matsala saboda Ramadan.
      Ya mike ya ce "Tashi muje" ta bishi suka jera, ta Lura jikinsa yayi sanyi . Sai kuma bata sake magana ba.
    A kofar wani studio suka tsaya, ya ce "Shiga mu yi hotuna". Ta bishi suka yi ta hotuna kala-kala don yawanci dressing din da suka canza a wurin ya saya mata, don ciki botique ne, Sai da ya amshi hotunan daga nan kasuwa ya shiga ya sayi abin da zai saya, sannan suka wuce gida.
    Duk yadda Jeedah taso ta warware masa damuwarsa abun ya fuskara, tilas hakuri tayi. Amma a ranar ba wanda yayi barci d'aga Ita har shi, Ita tunaninta ya fi raja'a kan me ya same shi, me ya faru da shi? Shi kam damuwarsa daya bai San meye ra'ayin Inna a kan neman auren Ramadan ba, ya za ta karbi al'amarin nan? Balle su Baba Ibrahim da Daddynsa,dole a cikin kwanakin nan zai san yadda zai bullo ma al'amarin.
      Da safe duk suna barci shi ya riga ya shirya baya son yayi missing first flight. Yana saukowa d'aga sama Jeedah ma tana saukowa, rigar barci ce a jikinta don haka ta ringa karasowa a tsorace.
    Yana sanye da rigar shadda fara kal dinkin Lagos jamfa, ya Dora zanna bukar, Karin hularsa tamkar a Diffa yadda ta zauna dinta ya barta. Ya ce "Har kin tashi?" Ta ce "Na idan da sallah ne na sauko na shirya ma breakfast".
    Yadda ya ganta cikin rigar shine ya sanya shi ya juya mata baya, ya ce "Ki barshi na gode, na Sha tea a kicin din sama" ta ce "To bari na kira maka Mmy Ku yi sallama" ya ce "Ina jiranki" da sauri ta shiga ta gayas da Mmy ,tana zaune bisa sallaya, tace "Mmy ya Jaheed ya fito zai wuce".
   Mmy ta ce "To gani nan " ta fito jikinta duk yayi sanyi, A yanzu bai iya dauke idonsa a kanta ba, tamkar wani shiri, da kyar ya saita kansa ya juya ya kalli Mmy tana saukowa, ta ce "Yaya Na ga duk kun yi sanyi ko tafiyar ce ba'a  son rabuwa?"
    Ya Dan yi gyaran murya ya ce "Aa ba haka bane Mmy, ai zan dawo ba da jimawa ba" ta ce "To Ina baban naka?" Ya ce "yana baya wurin mota zan je wurinsa zai kai ni airport".
  Ita Kam Jeedah Sai ta hau sama ta sanyo abaya ta iske su suna shirin shiga mota, Ita ma shiga tayi. Mmy ta ringa d'aga musu hannu, Daddy ne yake tuka motar Sai a lokacin Jaheed ya bashi ATM din Mama ya ce ya kai ma Mmy ya manta ne? Daddy ya ce , "Me za 'a yi da shi?" Yayi mishi bayanin komai ya ce "Ba matsala zan ba ta".
      A airport Daddy ya shiga wurin shige da ficen tafiyar Jaheed, Jeedah tana zaune can gefe jikinta jibegegiyar rigar sanye ne,

You are reading the story above: TeenFic.Net

#page