Page7

Background color
Font
Font size
Line height

*INUWAR ZUCIYATA❤*
        _{Zarah ko Jeedah}_

*Na Raheenat.. Mamoudou.*

*Story by: Mamuh geee*

*Wattpd@Raheenatmamoudou*

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
           ☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* [email protected]

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1

_____________________________

*<<Page 7>>*

_Jaheed ne ya shigo da hanzarinsa ya d'aga Jeddah, ya yin da ta kai kafa tana dukan Zarah. Alhaji ya ce, "Ke Jeedah ki bari mana". Ta kuwa fashewa da kuka ta ce, "Ba Ita ce Ina zaune take duka na ba, wai bana shiga kicin". Yayi dariya ya ce, "Ke Zarah ke ce fa babba Ina ruwanki da Ita zaki ce wai Sai ta shiga kicin ta yi me? Ko Mariyam da Iya Larai meye amfaninsu a kicin din? Ba biyansu nake yi ba? Bana son fitina da son tayas da zaune tsaye wannan ai son rigima ne". Shi Kam Jaheed kamewa yayi a wuri daya numfashinsa na nemi ficewa gaba daya yadda ya ga surar Jeedah a bayyane , da kyar yayi ma kansa linzami duk yadda ya kai ya mai da son Jeedah Sirri a ransa abin ya faskara. Mmy ta ce, "Ni bana son daurin gindi ke Jeedah Zarah ba ta girme ki ba, ko Dan kinji Alhaji yana goya miki baya? Kin kama ta kin danne Sai jibagar ta kike ,sannan an goya miki baya". Alhaji ya ce, "A'a Hajiya bana son rigima, Ita Jeedah ba shiga hakar Ku take yi a gidan nan ,Amma kun bi duk kun takura mata, Ina dalilin? Cikin kuka ta ce, "Ai ni Daddy gobe za'ayi mana Hutu ma nayi tafitata Dan issa nayi zamana na huta da jarabar Zarah". Mmy ta ce, "Allah ya raka taki gona , ki huta da jarabar Zarah ko mu huta da jarabar ki?" Alhaji ya ringa goge mata hawaye da babbar rigarsa ya ce, "Bari a yi Hutu ki rakani Egypt, idan na kamala abin da nake yi Sai  mu shiga saudiya mu isar da umuararmu mu dawo kin ji yar gidan Inna?" Ta ce, "Daddy tare da Inna zamu je ko?" Ya ce, "Idan zata Sai mu wuce tare ba matsala". Hajiya Aisha tayi dariya ta ce, "Sai kun dawo, Allah ya kiyaye". Jaheed ya ce, "Ameen, idan ba ta je ta tsokano 'ya'yan larabawa su yi mata dukan tsiya". Ya kama hannun Jeedah suka wuce suka wuce abinsu sama._

*Washe-gari*

_Allah-Allah take yi ta je ta karbo jarabawarta ta zo direba ya kaita garinsu wurin Innarta, ta barma Zarah gidansu , don ta gaji da zaman boranci.A can gidansu Ita ce Mowar 'ya'ya Amma a nan idan ba Jaheed da Alhaji suna gidan ba shikenan ta zama borar Zarah, ko wata boyi-boyi, komai ta yi Mmy gwale ta take yi, ta ce bata iya ba. Sassafe suka tafi karbar results, sannan aka bayas da Hutu kasancewar Jaheed bai je makarantar yau Hussaini direba ne ya kaita ya dauko ta.Jaheed ya je Diffa da sassafe Alhaji ya aike shi._

_Jeedah ta shigo falon ba kowa ta nemi wuri ta zauna da ambulan dinta a hannu, Sai wani shan kamshi take yi, Hussaini direba ya wuce Kicin ya ce, "Hajiya mun dawo". Ta ce, "Ah! Hussaini har anyi hutun?" Ya ce, "Gata can a falo". Ta ce, "To" ta fito tana fara'a da murnarta ,ta ce "Jikar Inna an dawo?" Jeedah ta kara daure fuska Kar ma a duba mata result, Mmy ta ce "Anya Hussaini anyi abin arziki a jarabawar nan kuwa? Na ga ba'a dariya". Ya ce, "To dai ga ta nan hajiya na ga kawayenta sun rako ta har mota". Mmy ta ce, "Ai fa abin da ta iya kenan shegen muliki da iko a aji, 'yar gidan hajiya Rahmat ta ce group ne da Ita a ajinsu Sai yadda tayi da dasu ba ko'kari ne da Ita ba, Amma ta zama kamar uwarsu Sai yadda tayi dasu, daman idan ka ga 'yan fadanci sun yi ma mutum yawa a makaranta bai San komai ba". Ita dai Jaheed Sai ma ta sake daure fuska, ta aha mur sosai, Malam Hussaini ya ce, "Na ga dai tana bude na kawayenta tana gani, Amma ban ga an bude nata ba" Hajiya Aisha tana dariya ta karasa gabanta ta ce, "Mu gani Jeedah yar gidan Inna?" Tayi kicin-kicin ta ce, "Don Allah Mmy ki bari  Sai Daddy ya fito a dakinshi Sai ki gani" Zarah ce ta wani fado a falon tana fadin "Eye , sister let me see" Jeedah ta ce, "Bana son wulakanci Zarah bana bada wa din" ta kai hannu za ta zara ya yin da Jeedah ta sake kankamewa. Mmy ta kwashe da dariya Ita da Hussaini direba, Jeedah Kam Sai ta fashe da kuka, ya yin da dariyar ta Karu, dai-dai lokacin shigowar Jaheed d'aga garin diffa, ya nemi wuri ya zauna yana dariya ya ce, "Mmy me ya faru" Mmy ta nemi wuri ta zauna ta ce, "A'a , Tambayi Hussaini direba kila shi ya sani Sai ya gaya maka ko?" Hussaini direba ya ce, "A'a ,ranka shi dade ba komai bane jarabawar ta zasu gani ta ce ba ta badawa to fa shi ne kuka ya zo ya shiga cikin tsarin ya bata lamari". Jaheed ya ce, "To ba mai gani, kawo Jeedah na duba". Ta ce, "Ni gaskiya babu mai gani idan ba Daddy ne ya zo ba mai budewa". Alhaji Mubarak ya ringa taka matatakalar bene yana saukowa a hankali . Senye yake cikin shadda 'yar ciki da babbar riga, dinkin yayi kyau an zuba surfani a gaban babbar rigar .Sai kamshi yake yi, ya tako cike da nutsuwa ya karaso gaban Jeedah ya zauna ya ce, "Kai Jaheed me ka yi mata?" Yayi dariya ya ce "Daddy bani bane Ita da Zarah ne". Zarah ta ce, "A'a Daddy ba dani bane Sai dai Mmy". Ya kalli Mmy ya ce, "Hajiya me Jeedah ta yi miki?" Ita ma dariya take yi , ta ce "Me ta yi min kuwa? Results aka ce ta kawo a gani ta hana" Alhaji ya amshi ambulan din yana fada ya ce, "To Dom me za'a ce Sai an gani?wannan ai son ganin asirin mutum ne, me kuma za'a ga a jarabawar ta?" Ya bude ya duba yadda ya ga result din nata shi ne ya sa shi saurin maidawa ya mikawa Jaheed ,ya amsa da sauri ya duba, ya ce "Ni na San dole Sai haka, kin yi kokari". Daddy ya ce, " Ba sosai ba dai idan ta yi kokarin". Zarah ta yi wuf! Ta zara, Jaheed ya bita tana dubawa ya ce, "Wallahi idan kika duba zan mareki" .Ai kuwa Sai da ta gani ta yarda kasa Jaheed ya dauka , ta yi tsalle  ta yi inda Mmy take ta ce, "Mmy mutum biyu ta fi ko'kari a ajinsu". Mmy ta ce, "Daman idan mutum ya fiya baki'n iko ba abin da yake samu a jarabawarsa Sai shirme. Jeedah ta sake fashewa da kuka ta ce, "Daddy ka ga Zarah ko?" Ya ce, "Eh! Lallai Kam na ganta, yanzu  Na gane abin da suke nufi, Ina laifi ma da kika fi mutum biyu kokari? Ai kinfi wanda yayi na karshe fa, shi ya zai ji ? Ni haka ma na gode Allah yayi albarka". Ta amsa da "Ameen Daddy, Amma dai yau zan tafi maradi wurin Inna ko?" Ya ce, "Yau zaki tafi, kai Jaheed a fitar da duk abin da ya kamata a sanya a but, ka fitar da kudi kayi musu shipping kayan tea da sauransu". Ya ce "To Daddy". Ya sake cewa "Hajiya a yi ma Inna miyar kaji a tafi mata da Ita". Ta Dan rusuna ta ce, "Ai na kammala masu tun jiya, ga dambun naman rago can ma Mariyam ta yi musu ba matsala". Ya ce da Jeedah "Ki shirya sosai idan an Sako d'aga matsalaci Sai Jaheed ya kai ki, ni Sai vusarmu ta fito za ki ganni nan da kwana goma." Ta ce, "To Daddy". Ya ce "Ke kuma Zarah burinki ya cika yau dai Jikar Inna za ta bar muku gidanku, duk wanda yayi miki laifi Kar ki gaya ma Inna ki tara su idan an  samu ama Sai ki gaya min ko?" Ta ce, "Yo Daddy". Ya kama hanyar fita suka ringa a dawo lafiya Daddy, yana amsa Amin Allah yasa.amma 'Yar gidan Inna ko Tari ba ta yi ba._

_Tafe suke a titi Sai fella gudu yake yi._

You are reading the story above: TeenFic.Net

#page