Page 35

Background color
Font
Font size
Line height

*INUWAR ZUCIYATA❤*
      (Zarah ko Jeedah)

*Na Raheenat Mamoudou*

*Story by Mamuh gee*

*Via Wattpd@Raheenatmamoudou*

*Da Sunan Allah mai rahma mai jinkai*
______________________________________

*<<Page 35>>*

Muryar Jeedah ta ringa rawa don tausayawa 'yar'uwarta Zarah , sai kuma hawaye ya zubo mata. Ta jima tana kuka Ramadan ya ringa lallashin ta ya ce "Kiyi hakuri ki daina kuka, meye abun kuka? Sai dai addu'a ai ". Jikin Ramadan yayi sanyi, bai taba ganin aure irin na Jaheed da Zarah ba, ya ce "To shi wai me yake damun sa? Nawa aka yi aure irin haka kuma aka zauna lafiya? " Jeedah ta share hawayenta, ita dukansu biyun tausayi suke bata, d'aga Jaheed har Zarah. Ta ce "Ni da Mmy naga Tana yawan korafin halin da Zarah take ciki haka na ce, a raba auren kowa ya huta. " Ramadan ya harareta ya ce "Kar ki Kuma wannan tunanin ma, idan an raba auren ba zai taba barinki ki zauna dani ba, dama-dama da Sun haihu, ma'ana Sun kusanci juna, to ya haramta a gare ki bani da kaico Amma idan an raba auren yanzu ni zai jefa a matsala. " Jeedah ta kawas da kai ta ce "Ai sai dai yayi biyu babu, amma ni na barshi har abada. Haba don Allah Yaya Ramadan, ai ni da kai wallahi har abada mutu ka raba takalmin kaza, ba gudu ba ja da baya. "
      Ya ce "To ai nafi son hakan, domin an hanani nayi yadda nake so ". Jeedah ta ce "Ai na gaya maka ka jira ayi bikinmu, wannan ba matsala bane, ni tsoron ciki nake ji kana gani fa har an fara gulma wai ina da ciki, ana tsegumi. " ya ce "Ai ke din ce kin ganki kuwa?  Ya fada yana kai hannun shi bisa nonon ta. Da gudu ta fito ya biyo ta, kicibis da Abida yasa ya saurara mata m
      Tana huci ta boye a bayan Abida. Abida din ta ce "Daddy ne yake kiran ku, ku zo yanzu. "
    Jikin Jeedah yayi sanyi, ta ce "Lafiya? " Abida ta ce "Lafiyar kenan, ku zo dai nima ban san dalili ba ". Jeedah ta kalli Ramadan ta ce "Yaya Ramadan, kar fa Jaheed ya kawo karar mu ne? " Ramadan ya ce "Muje mana, idan ma ya kawo kara ai kansa ya tonawa asiri, ni na fi so ma ayita ta kare a gaban manya. "
     Dukk'ansu a gaban Daddy, Mmy tana mishi lissafi, cikin satin nan Dubai za ta je, suka nemi wuri suka zauna. Daddy ya ce "Ina so zan je Niger a cikin satin nan, Sun aiko mini 'yan Scotland Sun kammala karatunsu, an kuma yanke bikin su. Don haka nake so naje a hada bikinku ayi kowa ya huta. Kai Ramadan ka shirya da kai zamu tafi, ku kuma ku raka Mmy Dubai. Ke Jeedah ki zabi kayan da kike so, ku sayi duk kayan da zaku yi biki ke da 'yan'uwanki amare, amare uku kenan, Mufeedah, Fareedah sai kuma naki,don haka ki kiyaye kin ji ko? " Jeedah ta "To Daddy". Tun a ranar suka fara shirye -shiryen tafiya, ita kam Jeedah duk abun da ta saya sai ta saya ma Zarah, kwanan su Goma a Dubai suka diro Niger, birnin Niamey. Kwanan su uku ana biki sannan aka dunguma zuwa Diffa. Duk Yadda Zarah ta so ta nuna kanta a wurin bikin abun ya faskara, saboda irin ramewar da ta yi. Tausayin kanta ne ya ishe ta, ta rasa yadda za ta yi. A haka ta bisu Diffa.
     Jaheed kam yana Diffa , amma bai leka wurin Bikin ba. Hotel ya wuce Nicon ya kama daki ya shiga juyayin abin da yake damun sa.
     Wani lokacin yayi kuka, wani lokacin yayi sallar nafila, wani lokacin Kuma sai dai ya tashi da azumi, Dan raguwar harkokin business da yake gida Niger sai dai ya gabatar ta waya ko ta internet, idan ya zamo dole sai ya halarta zai tura daya daga cikin yan office dinsu.
     Ita kanta Umminsa rabon da ta ga Zarah an dade, da ta ganta a Diffa hankalinta tashi yayi, ta ringa mamakin irin ranewar da tayi. Jama'a har basa gane ta don tsananin rama. Ummi ta ce "Meye haka Zarah? Ko  baki da lafiya ne?  Ko duk cikin ne? " idon Zarah ya cicciko da hawaye, kafin ta budi baki tayi magana hawaye ya barko. Ita kanta Ummi yarinyar tausayi ta ba ta. Ta ce "tashi ki raka ni, tashi muje ". Suka ratsa jama'a suka fito. A harabar gidan ana ta kwasar yammata zuwa wurin (Sister Day), amare sunyi kyau, kowace sheki take yi.
     Ummi ta bude mota ta ce "Zarah shigo muje ". Ta shiga ita ma Ummi ta shiga. Asbiti suka je aka duba ta, suka ce ba ta da ciki
Tun a asbitin take faman tambayar ta "To me yake damun ki Zarah? Menene?  Idan baki gaya min ba wa za ki gaya mawa? Me ya miki Jaheed din? " ta ci gaba da share hawaye, Mmy kam tuki take yi bata san inda take sa motar ba, da kyar da addu'a suka iso gida lafiya.
      A lokacin babu jama'a sosai, sai yan tsiraru. Ta nemi wuri tayi parking ta ce "To Zarah me kike so muje mu cewa Allah, an baiwa dana amana ina gani ya kasa rikewa ko me?  Ki gaya mini dalilin wannan ramewar da kika yi in dai kina so hankalina ya Kwanta ". Zarah tayi shiru tana tunani, to ita meye burinta idan ta tona ma Jaheed asiri?  Da can ma yana yi mata wulakanci balle yanzu da ta fadi laifinsa. Ta share hawayenta ta ce "Ummi ba abin da yake mini, wallahi bani da lafiya ne kuma na samu sauki ". Mmy ce ta shigo dakin da ya zamto su biyu suka kebe kansu, ta ce "Wallahi Yaya ko ni nan Nayi nayi ta gaya min abin da yake damunta wallahi taki, amma kin ga wai ciwon zuciya ne yake damunta ". Ummi ta dafe kirji da karfi ta ce "Ciwon zuciya? " sai a lokacin Zarah ta ci gaba da sheshekar kuka, Ummi din ma kuka take yi, gaba daya hankalinsu a tashe yake. Mmy kam mahaifiyar Zarah  sai abun ya motsa, fulatanci, sai ma ta mike ta bar wurin. Ummi ta ce "Kada ki tafi Aisha,zo muyi zancen mu san yadda zamu bullowa al'amarin." Mmy ta ce "To ni me zan ce?  Ai Sun fi kusa ". Kusan har aka gama bikin nan Zarah bata da lafiya, saboda wani bacin ran ma ta mance dashi, amma a dalilin tambayoyin da iyayenta suke yi mata.
    Da safe tana shirin komawa gida sai kuma suka biya ta gidan amare, suka yi musu Allah ya sanya alkhairi. Jeedah kam sai a lokacin suka kebe da Zarah ta ce "Wai yaya Zarah meye sai ramewa kike yi?  Yaushe za kije ganin likita a Landon?  Ko kizo nan Ramadan ya baki tretment tunda matsalarki ya karanta, kin zauna ciwo sai damunki yake yi, shi kuma Jaheed don zalunci ya zo ya sanya miki ciwo yana wani gudun ki. Auren dole ne kike zaune yake gallaza miki a kan me? " Zarah ta share hawaye ta ce "To ya zan yi Jeedah? idan naje na fada babu mai kulani tunda tun farko ni na ce ina son shi, ke kam kin yi Sa'a jeedah, mijinki yana sonki, kiyi mishi biyayya. Amma ni ki barni akwai abin da Allah yake nufi da wannan rayuwa da ya nufe ni na shiga cikin ta. Ki ringa yi mini addu'a." Jeedah ta ce "A kirawo Inna nan mu gaya mata ko? " Zarah ta girgiza kai ta ce "Ki kyale Inna a zo ana yin rigima, ni bana so dan Allah. " ita kam Jeedah dole ta bar zancen ba don tana so ba.

Muje zuwa.

You are reading the story above: TeenFic.Net

#page