Page 33

Background color
Font
Font size
Line height

*INUWAR ZUCIYATA❤*
           _{Zarah ko Jeedah}_

*Na: Raheenat Mamoudou*

*Story by: Mamuh geee*

*ViaWattpd Raheenatmamoudou*

*Da Sunan Allah mai rahma mai jin kai*
______________________________________

*<<Page 33>>*

Daddy ya ce "Ai aure nufi ne na Allah, idan Allah yayi sai ka auri Fauxiya Jeedah ta isa ta hana ne?  Ni da Jeedah da Fauxiya  duk daya ne a wurina ba zan ki Fauxiya saboda ita ba. Ni da tun farko ka gaya Mini da yanzu na kashe rigimar.
      Zan je nasa a aura maka Fauxiya din, idan tana zama ta zauna idan bata zama ta yi abun da za ta yi tunda an riga an daura auran ai ba ta isa ta warware ba. "
        Cikin kuka Jeedah ta ce "Ni d'ama Dady ai h'aka na ce ya aure ta, ni ban ga abin tashin hankali ba. Amma ni ya sawake mini. " Daddy ya daka mata tsawa ya ce "Tashi ki bani wuri ko yanzu nan jikinki yai tsami, ina Dallin wannan fitina? Yarinya duk kin bi kin tayas ma da mutane hankali, tun yanzu kike wannan, jarrabar kishin, to idan kin girma wa ya san irin rigimar da za ki rikito. "
     Jeedah  Ta tashi cike da fushi tana share hawaye ta bar wurin. Ramadan Ya ce "Wallahi Daddy ni ban ce zan auri Fauxiya ba, idan ita  Fauxiya tayi hakuri ta kwantar da hankalinta ma a hankali za ta samu miji tayi aure ne, idan ta gaji da naci zata kyale ni. " Daddy ya girgiza kansa ya ce "Ba zai yiwu ba, mu zuri'armu ba za ta taba wulakanta ba, saboda Jeedah ba zaka banzatar da Fauxiya ba, ka je nima ina zuwa zan zo har Diffa na daidaita komai. " jikin Ramadan yayi sanyi sosai, ba wani tsananin so yake yi ma Fauxiya ba, wani bai ma san meye tsakaninsu da ita ba. Amma dubi yadda Jeedah ta sa kowa yake ganin wani so yake yi mata .
    Ya ce "Dady ni fa ba wani so nake yi ma Fauxiya ba, kawai dai rigimar Jeedah ne haka take ganin kamar ina son Fauxiya ". Daddy yayi murmushi ya ce "Yaro-yaro ne to ai idan kai baka son Fauxiya a yadda ka bani labarin Fauxiya daga frko har karshe ni na gano tana sonka, don haka tunda tana sonka ba za a tauye mata hakki a shiga rayuwarta ba, dole a san abun da za ayi. Uwar Fauxiya ba za ta ji dadi ba a ce diyarta tana fama da sonka, an hanaku aure saboda Jeedah ba ". Ramadan ya sake sanyaya murya ya ce "Daddy da aka bar wannan zancen ko don na kubuta daga zargin da Jeedah take yi min na ina son Fauxiya. " Daddy ya ce "Kai yaro ne, tashi ka bani wuri. Amma abu daya nake so ka yi mini alkawari ". Ya ce "Daddy mene ne? " Daddy ya ce "Ina so duk umarnin da na gindaya a kanka ka bishi ka ji ko? " kansa a sunkuye ya ce "Insha Allah Daddy zan bi ". Daddy ya kalle shi ya ce "To ka zamo jarumi, musamman a kan mace, Idan ka zama jarumi babu macen da ba za ta bi umarninka ba. Kai fa mijin mace hudu ne, bai kamata ka tsorata da daya ba. Ka jira ka ga matakin da zan dauka, a sannan nake son jarumtar ka. Ka daure kar ka yi wasa kaji ko? " A hankali Ramadan ya amsa "Insha Allah Daddy ". Mmy ma natsiha take yi mashi . Abida kam sai ta hada mishi tea ta ajiye a gabanshi, ta cika filet da kayan soye-soye ta ajiye mashi ta mike ta bar wurin.  Mmy ma ta tashi ta shiga kicin, shi kam Ramadan hira suke da Daddy amma hamkalinshi yana ga maganganun da Daddy yayi, don haka ya ringa cin abincin tamkar ba ya so. Suna zaune Jeedah ta fito da shirin tafiya makaranta, hannunta da litattafai ta wuce gefen Daddy ta dauki makulin mota. Kamshin turarenta ya lullube Ramadan, da kyar ya iya dubanta ya sunkunyar da kansa. To wace irin jarumta zai yi ma zuciyarsa a kan son Jeedah, ba zai iya ba in dai sai ya nuna jarumta shi din zai zamo namiji, sai dai har abada ya zamo ba namiji ba. Kalli fa wata irin sha'awar ta ce take bashi wahala. Ya sanyaya murya ya ce "Sai ina ". Ko waigowa Jeedah ba ta yi ba ta wuce shi. Dady yayi dariya ya ce "Ka kyaleta Ramadan, ka fita harkarta kwata-kwata tana daina wani share ka kana manne mata. Ka barni da ita zan yi maganinta, duk jarabarta zata kyale auren nan tunda nine ubanta, idan taga an Aura maka wata sannan zata gane bata da wayo. " Ramadan yana so yayi magana amma ba ya so daddy ya ce mishi yayi mishi gardama, haka ya ringa shan shayi tamkar ba ya so.
      Daddy aka mishi waya, motar da t'ake kai shi zirga-zirga ta iso. Ya mike yana kallon Ramadan ya ce "Yaya babba ko zamu je? " ya girgiza Kanshi ya ce "Aa Daddy a dawo lafiya. " Daddy yana fita kwaram sai shi ma Ramadan ya tare tasi ya nufi makarantar su Jeedah. Bai sha wahalar ganota ba, dalili 'yan Africa basu da yawa sosai. Jeedah tana can cikin wasu furani karkashin bishiyar, wurin akwai sanyi sosai, ga wata irin ni'ima da take shakar ta mai tsananin sanyi da kwantar da hankali ,tunani ne take yi sosai idonta yana zubar da hawaye, tana zaune ta juya ma hanya baya sai ji tayi an sumbaci bayanta. Ta runtse idonta jin kamshin Ramadan ya sa ba ta motsa ba, ya gewayo gabanta ya zauna, ya ce "Don Allah ki taimake ni kiyi hakuri meye abun kuka?  Komai fa ya wuce ". Hawaye ya zubo a idonta ta ce "Ba kana biye ma maganar Daddy ba ?" ya ce "Eh, to ya zan ki maganr Daddy mai sona, kin san shi da zafi zai ga kamar naki mishi biyayya ne. Amma ni wallahi har ga Allah babu wata mace a gabana idan bake ba, Fauxiya fa gida daya aka goye mu da ina sonta sai dai kiga har na aure ta. So babu irin wanda ba ta nuna mini ba, amma ni dai bana sonta wallahi ko kallo ba ta ishe ni ba. Ina so ki gane, ni mutum ne mai magana daya, Allah idan na ce yes, wallahi ba zan cewa no ba. Ba zan taba auran Fauxiya ba, ki amince dani don Allah. " ya matsa a gabanta yana share mata hawaye, ya ce "To meye ma na tashin hankali (Mai sona, kece fa INUWAR ZUCIYATA), ki sanya ma zuciya hskuri mu biyu zamu yi rayuwarmu kin ji ko". Ina gefe na ce Anya ko da gaske kake Ramadan hhhhhh muje zuwa dai.
     Ya rungume ta a jikinshi, ita kam kuka take yi. Ya ce "Ki taimake ni ki sanyayya mani raina, ki tsaya mu fahimci juna. Cike da shagwabarta ta ce "Bayan ka share ni wata da watanni ba waya ba sako, ina fa jin haushi ". Ya saki ajiyar zuciya ya ce "To ya zan yi abin sona? Kinyi mini fushi kin guje ni, ba kya daga wayata, kallona kike yi kamar ba namiji ba, ko don kinga na kyale ki, kin danne mini hakki na kyale ki :. Dago ido tayi ta kalle shi, gaba daya ya kashe mata jiki da wata irin sha'awarshi. Ta dan janye ya rike ta gam! Yana mata kallonsa mai tsoratar da 'ya'ya mata ta ce "Ai ni ba wannan maganar nake so mu yi ni da kai ba, ni maganar yadda ka basar dani a gaban Fauxiya yafi yi mini ciwo. " ya ringa magana cikin kunnenta, ya ce "Ke ma kin san ke zan zaba abun sona ,to amma idan na zabe ki na ce nabi abun da kike nufi, Fauxiya kulatarki zata yi a ranta, taga saboda ke na wulakantata. Don Allah kiyi mini hakuri. Ta dan janye jikinshi ta ce mishi "Lallai, to idan ma ta kini ta kullace ni meye? " ya girgiza kansa ya ce "Aa, ni ba zan so ta ki ki ba, na fi so kowa ya ke sonki a danginmu. Don idan Sun ce basa sonki zan bata da jama'a da yawa ". Ta ce "Lallai kam kana da babban aiki, ai ni ba farin wata ba, ba yadda za ayi na hada da duniya da haske, balle ma ni ba yadda za ayi na yi Hulda da wata Fauxiya tunda ta nuna bata kaunata. Wace kauna zaka siyo min a wurinta? Bayan duk abin da kayi ji tayi don Kana sonta NE kayi. " ya ce "To kiyi hakuri idan don ni wallahi ba za a kuma ba kin ji ko ?" ta dan zunkuda kafada ta ce "Wallahi a kuma, don ni idan na barka ko? Wallahi na barka har abada, ka kulla wata Fauxiya  ko a waya na gani. Kai ni ba ma Fauxiya ba, wallahi kar ka bari na kama ka da hulda da mata, ba za ka ji dadi ba wurina, don ni idan ina son abu wallahi ban son ayi mini kishiya. GA misali, ko jaka na rataya na ga mai irinta zan kyautas da ita. Haka ana ina da special tailor Wanda idan zai yi mini dinki ba tayi ma kowa irin nawa. Haka nan bana bayas da aron dinki, idan kinga dinki a jikina kin ce ya miki zan cire har kayan na baki kyauta, ba maganar wai ki ara ayi miki irin nawa. Haka nan na tsara rayuwata, daga ni sai mijina, idan kuma ka hadani da wata, ma'ana kayi mini KISHIYA, to wallahi mun samu sabani dani da kai har abada, ka kiyayeni. "
     Ramadan yayi bakan yana jinta, ya ce "Haba don Allah abun sona?  Bani da kamar ki, ke ce fa rayuwata, ki kalli irin ramar da na yi bayan kin yi mini fushi, wallahi ba wata matsala ki kwantas da hankalinki, zan tattala sonki da kaunarki a raina, tamkar yadda zan kula da lafiyata. Abun sona ki kwantar da hankalinki idon Dan matsalar Fauxiya wallahi komai ya wuce. Ke ba ma Fauxiya ba, ko wace mace ni Ramadan na rufe shafinta, ni naki ne ke kadai mai sona. Don Allah kar ki kuma yi mini fushi kin ji ko? "
     Jeedah ba ta amsa ba. Ya kamo hannunta ya rike ya ce "Ina rokon alfarma mai sona kar ki kalluce ni kin ji ko? " ta kwantar da kanta a kafadarsa ta ce "Ya wuce, a da din ma ni na barwa Fauxiya ne da ka ga wannan fushin nawa, amma a yanzu shi kenan na yafe maka. " ya saki ajiyar zuciya ya ce "Jeedah duk wannan sabanin da muke samu ni da ke ba komai ne yasa kika ga ina binki ina tsananin son rayuwa da ke ba, sai yadda kika damu da fushina. Ki kalli abun da ya hadamu a can baya, har gida kika bini kika bani hakuri. Jeedah ta ce "To ai ban burge ka ba, don na ga har gori kayi mini ". Ya ce "No, ba gori bane kawai dai na san kin girmamani, amma na fada ne ki gane har abada mata sune a kasa da namiji, dole kiyi biyayya dani. " ta ce "Na yi biyayyar da kai, ya zamo dole ba sai ka fada ba. Amma har haka ka ce mini wai kai mijin mace hudu ne, ni wasu maganganun ma bana son tuna su don Sun barazana ga fasa mini kwanya. " Ramadan ya rungumeta ya ce "Wallahi duk karfin hali nake yi Jeedah, kece kawai farin cikina abun sona ina ta shirin daidaita komai shine kika wani gudu ". Ta ce "Ah! Ai kai din ne tun komai bai daidaita ba naga kana son wulakantani saboda wata Fauxiya ". Ya ce "Aa, ke ce don ban sanya ki laulayi ba shine kika wani fushi, don Babba ma haka yace, wai nine na sake, da kin san karfina baki isa ki raina ni ba, na tsaya tsoronki ban sanya miki ciki ba. " Jeedah ta rufe idonta, wata irin kunya ce ta kamata. Ta ce "Kai ma dai da wani zance, don Allah ka bari ". Ya ce "Aa, ba zan bari ba ,bana barci fa kullum sai na kusance ki ki ya fi hawa a Raina.
    Ki bani dama abun sona na kashe kishirwarki dake damuna ". Jeedah ba tayi magana ba sai ta Mike tayi tafiya nisa daga inda yake. Ta ce "Don Allah ka Bari". Ya ce "Gaskiya ba zan bari ba sai dai kiyi alkawarin daidaita komai a yau sai zance ya wuce. "

*Muje zuwa*

You are reading the story above: TeenFic.Net

#page