Page 31

Background color
Font
Font size
Line height

*INUWAR ZUCIYATA❤*
           _{Zarah ko Jeedah}_

*Na: Raheenat Mamoudou*

*Story by: Mamuh geee*

*ViaWattpd Raheenatmamoudou*

*Da Sunan Allah mai rahma mai jin kai*
___________________________________
🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂
🎂🎂🎂🎂🎂🎂
🎂🎂🎂🎂🎂
🎂🎂🎂🎂
🎂🎂🎂
🎂🎂
🎂👄 *Happy Birthday Mamuh gee*
*A wanni Sun shud'e, lokaci yana ta tafiya gashi har Allah ya k'ara nuna mana zagayowar ranar haihuwarki, Allah ubangiji yasa wanga sabuwar shekarar ya zo miki da abubuwan alheri ya zo miki na ni'ima da kwanciyar hankali ameen ya Rabbi ni Raheenat ina alfahari dake tawan Allah ya bar so da kauna ya kara muku donk'on soyayya k'eda oga ya raya mana Ayman da Afrat ya nuna mana auren Afrat nazo har Nigeria domin tayaki murna Allah ubangiji ya ara mana sawan kwana da lafiya da kwanciyar hankali aneen.*
🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂
🎂🎂🎂🎂🎂👄
🎂🎂🎂🎂👄
🎂🎂🎂👄
🎂🎂👄
🎂👄
👄 *Happy Birthday dear Mamuh gee Allah ya karo shekaru masu albarka ameen👄*
____________________________________

*<<Page 31>>*

*LABARIN FAUZIYA*

fauziya fara ce doguwa mai siririyar kira, tana da hips sosai, shi ne ya baiwa shape din damar fita. Mai kyau ce ainun ba kowane namiji ne zai ki yi ma kansa sha'awar Fauziya ba.
       Babu abun da Jeedah za ta gwada mata a fannin kyau sai gashi, tana da gashi dai-dai azanci. Fauziya mace ce mai son wasa da dariya, haka nan tana da saurin sabo.
      A fannin Ilimi Fauziya ba'a isa a kushe ta ba, ita ce Babba a cikin 'yammatan familin Alhaji Babba, uwarsu daya ubansu daya da uwarta da Uban Ramadan, mahaifiyarta ce kanwar uban Ramadan.
      Sun taso gida d'aya da Ramadan, Sun shaku sosai da shi da ita, kusan tun bai ce yana son Jeedah ba Fauziya take sonshi, tun yana sakandire suka shaku sosai, tun Ramadan yana yaro Hajiya ta yaye shi a bakin nono, gidan Alhaji Babba yayi wayonsa.
      Haka aka yayo Fauziya suka taso tare, ba abin da yake rabasu Sai barci, haka nan Alhaji yana matukar son jikokin nan nasa guda biyu, tamkar babu jikoki a gidan sai su.
    Dalili kenan da shakuwar Ramadan da Fauziya ta yi tsanani ,lokacin da ya kammala sakandire a lokacin Fauziya ajinta hudu a primary.
     Alhaji Mubarak mahaifin Jeedah shine yazo ya kai shi kashashen turai (Maroc)  domin karanto likita. Babu Wanda yayi baki'n cikin tafiyarsa irin Fauziya da suka shaku tare, makaranta tare suke tafiya, tare suke dawowa.
     Haka nan Hajiyar Ramadan wato Bilkisu ta takura rayuwar Fauziya, don hajiyar har rubutun dangana ta sanya aka yi mata.
     Lokacin Ramadan ya tashi zuwa hutu Sai ya iske har Fauziya ta shiga sakandire aji biyu, a lokacin Jeedah ta kammala primary suka zo Diffa aure ita da Inna, idon Ramadan kir akan Jeedah, ya ce Inna nayi kamun diyarki, ki ajiye min ita zan dawo na aure ta.
    Ta ce "Jeka ka hada karatu ka dawo ko kuda bana bari ya taba maka Jeedah." A lokacin Fauziya tana yarinya taji haushin yadda Ramadan ya ce yana son Jeedah bayan gata.
    Har ta iske shi yana kallon fim din india ta ce "Lallai Ya Ramadan, ka kyauta ka ce Kana son Jikar Inna bayan gani ina sonka ". Ya ce "Ki yi hakuri kema zaki samu miji mai sonki. " ta ce "To ni fa Ya Ramadan baka sona? " yayi shiru yana kallonta ya ma rasa amsar da zai bata. Ya ce "Kiyi hakuri Fauziya ina sonki kin ji. " tayi dariya. Ya ce "Kar ki damu aure nufin Allah ne, haka nan matar mutum kabarinsa, wani baya auran matar wani sai dai tasa. " ta ce "Haka ne Ya Ramadan ,ni dai kar ka kini kaji ko? "
     Ya kalli Fauziya yayi dariya, yarinya ce karama bata san ma meye so ba yake tunani a ransa. Ashe sabanin ne yake shirin faruwa (SABANIN KAUNA).
     Dalili kenan da Fauziya ta girma da son Ramadan a ranta, abun kamar wasa ya dauke shi, bai taba baiwa abun muhimmanci ba sai yanzu da ya lura abubuwa suna son rikicewa SABANI yana shirin faruwa, dole yayi hanzari farkawa a barci da yake saboda tun dawowarsa karatu ya matsu ya ga wani girma da jikar Inna tayi? Da  Ya ganta ,to amma kuma ya aka yi har Yanzu Fauziya taki fita cikin shirginsa?
     Tattali irin na rayuwa ba irin wadda bata yi mishi ba, kauna ba irin wadda bata nuna mishi, tunda ya dawo Niger ya kyalla idonsa a kan 'Jikar Inna bai samu sukuni ba kamar yadda Fauziya ta rasa kwanciyar hankali da nutsuwa.
     Sai yau da ta samu damar Mayas da abun da yake faman damun zuciyarta. Rauyuwa kenan, yau da gobe har ya kai Fauziya tayi aman abun da yake zuciyarta, a gaban Jeedah 'Jikar Inna SABANIN ya afku, SABANIN mai girma sabani mai ban mamaki mai ban tsoro.

****** ******* ********

*Jeedah*

Kayanta ta hattama wuri daya tayi shirin tafiya gida, to wa za ta gaya ma abun da Ramadan ya yi mata, saboda me ba zai gaya ma Fauziya ba ya sonta ba Sai ya tsaya yana wani kame-kame?  WA zai yaudara cikin su biyu ?
     To wai ma me yake nufi? Ita zai raina ma hankali. To idan yana nufin yana son Fauxiya ne yake wani kame -kame, to tabbas yayi kuskure a a rayuwarshi, babu namijin da ya isa ya hada sonta da wata ta zauna da shi, wallahi karya ne. Tana nan zaune sai ga Ramadan ya shigo dakin, ya zauna a gefen gado kusa da ita ya ce, "Jeedah meye? " Manyan idonunta da suka sauya zuwa jajaye ta lumshe ta juya su kansa ta mishi wani matsiyacin kallo.
     Ta ce "Ai ka gama magana tunda ka bai WA Fauziya correct answer da nake so ka ba ta meya saura? Wallahi bana auranka ko Kai ne autan maza baka isa ka hadani ka soni da wannan Fauziya ba, wallahi karya kuke yi daga kai har ita ,har za ka wani rungume ta a gabana. Ka ce daman gulma ce irin taku ta maza. " Jeedah ta mike a tsaye tare da juya mashi baya, ta ce "Na ga a gaban Fareeda ka ce mu zura ido muga matakin da zaka dauka a kan Fauziya, wannan shine matakin ta zo tana wani sonka a boye ka ba ta dama ta furta maka abun da yake zuciyarta. Kun gama rungumar juna sannan za ka ce wai na yi maka afuwa ta yaya? "
Cikin sanyin murya Ramadan ya ce "Ki tsaya kiji uzurina ". Jeedah ta wani mike a fusace ta ce "Wallahi ba zan ji uzurunka ba, ka sake zance in dai kana son zaman lafiya kana sona sai dai wallahi ka zaba ko ni ko Fauziya. "
      Yayi shiru. Yana kallonta,, yarinya 'yar mitsitsiya sai feshe shi take da kalamai zafafa. Ya ce "Jeedah na zaba  ku Duka biyu ". Jeedah ta juyo ta fuskance shi ta ce "Very good, ka tsaya kana batawa kanka lokaci, kalle ka don Allah? Wallahi ba ka yi kama da mazan da zasu hada mata biyu kyawawa kamar ni da Fauziya ba, dan ni na san yadda na isa na kasaita a fagen kyau h'aka Fauziya ta isa ta kasaita a fagen kyau.
    Ya yin da kai ba irin namijin da mace zata kyale bane, kana da kyau kana da kudi da ilimi, kana da kudi. A tsarina a yadda mafarkin rayuwa ya zo min, na samo miji kamar ka ni k'adai ba tare da wata ta sh'igo cikin rayuwar mu ba. Ka sani ka sake sani, abun da ba zai yiwu bane ka hada sarki biyu a bishiys daya, Sai dai wani ya zamo sarki wani ya zamo galadima . Ba zanyi ma tilas ka rabu da Fauxiya ba, amma ina tabbatar mak'a ni ka rasani, rasawa ta har abada. Kaje na barma Fauziya kai. "
    A fusace Ramadan ya nuna Jeedah da dan yatsa ya ce........

*Muje zuwa*

You are reading the story above: TeenFic.Net

#page