HALEEMATUS SADEEYA

Background color
Font
Font size
Line height

πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 
πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
Β  πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 
Β  πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
Β  Β Β  πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚

πŸ’„πŸ’„πŸ’„πŸ’„
πŸ’…πŸ’…πŸ’…
πŸ’„πŸ’„πŸ’„



Β  πŸ’„πŸ’… *HALEEMATUS SADEEYA*πŸ’…πŸ’„

Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β 

Written by *HUSBA'AHFAMA*


IG *officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real Husba'ahfama*

Follow me on Wattpad *@ Real Husba'ahfama*




*Bismillahir Rahamanir Rahim*






Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β Β  9-10







Ko da malam yabar wajan matansa Rai abace se zancan zuci yake Yana ta Allah wadai da halin matansa wajan sanaarsa yatafi du Wanda yaganshi aranar yasan ransa abace yake

Malika tin safe tinda ta fita Bata dawoba tanacan wajan gantaliΒ  akwai wata kawarta Yar duniya itace babbar kawarta Kuma itace me zigata Kuma Taki zaman aure kawar Tata yanzu karuwanci take aboye ko malika Bata saniba Amma kusan kawayansu abinda suke Kenna bin maza har da matan auran cikinsu ita wannan kawa Tata sunanta nusaiba ita Kuma nusaiba burinta aduniya taga ta kashewa Malika aure ta koma bin maza kamar yanda takeyi ko kuma tana auran shaawa ko auran kudi in sun samu abinda sukeso su,rabu da namiji burin nusaiba na biyu shine taga ta auri aliyu inhar tasamu aliyu azaman mijin aure to Babu ita ba fitowa tashiga kenan Dan dun duniya Babu namijin da taji ze iya gamsar da ita kamar aliyu ashinfida kullin da shaawar aliyu take kwana Kuma take tashi Kuma ita tana mugun Jin haushi da bakin ciki yanda malika tafisu samu da kwanciyar hankali Kuma mijinta yafi na kowa acikinsu da kudi da kyau da tsari da Kamala da du wani Abu da da namiji akeso atare da shi Dan haka nusaiba ta dau aniyar ziga malika ta ko wana Hali se ta rabata da aliyu ko ita Bata aure,Shiba nusaiba tin lokacin da malika tafara aiki abanki anan tahadu da nusaiba itama wajan take aiki har aka canja Mata wajan aiki Amma Basu rabuba suna tare kawancan nusaiba da malika se yazo dedai yatarar da Hali Abu dayane malika batayi neman maza Amma du wani Hali da malika take da shi nusaiba na dashi Dan haka kawancansu yazo Daya Kuma du duniya malika Bata da abokiyar shawara kamar nusaiba ko Yan uwanta na jini Bata gayawa matsalarta se dai nusaiba ita Kuma nusaiba ba shawarar arziki take bataba se ta tsiya du wasu kawayan malika na yarinta nusaiba tasa malika tarabu da su

Aliyu yadawo gida wajan karfe bakwai na dare agajiye ko da yashiga gidan kafin yashige nasa bangaran se da yaje bangaran malika be gantaba yaduba ko Ina yaga Bata dawoba abin yabashi mamaki afili yace wato me Hali baya fasa halinsa yanzu du nasihar da akayiwa yarinyarnan har dukanta mahaifinta yayi du batajiba Allah yakyauta to Allah kashiryi wannan baiwa taka Bari naga iya gudun ruwamta yaushe zata dawo Daman ba ki rana take awayaba taji yanake Nima nagaji na Dena kiranta in na ki,ratama cewa take Ina da munta Dan haka na Dena Allah yakyauta tahaka takeso adawo Mata da yaranta hannunta kuma abbah yayarda zaa dawo Mata da su yan,kwanaki kadan da su Amira sukayi ahannun ummiΒ  har sunyi kiba sunyi kyau sun samu kwanciyar hankali

Bandaki yashiga yawatsa ruwa yafito yashirya har yakwanta ciwan mararsa yatashi da ciwan ciki tin yanayi shi Daya har takai yakira Dr yagamasa halin da yake ciki

Dr yace kome yake yadaure yazo asibiti adubashi sosai abin yafi karfin gida Kuma aiki yayi,masa yawa Babu damar yabaro marasa lfy yataho dubashi

dakyar aliyu yasamu Yana dafa bango yafito falo yakira yaranshi awaya suzo su temaka Masa suna zuwa sukaga halin da uban gidansu ke ciki Babu Bata lokaci suka kaishi asibitin da aka kwantar da sadiya Dan Shima in Yana gari anan yake ganin Dr shi da iyalinsa du anan suke ganin likitaΒ  saboda yazuba kwararrun likitoci a asibitin Kuma ba karamin kudi yake kashe musuba mutane na yaban asibitin sosai har daga wani asibitin turo mutane ake zuwa asibitin ranga ranga yaransa suka kawo aliyu daki na musammanΒ  aka ware akasa aliyu lokaci guda likitoci suka hadu akansa suna dubashi

Sun Dade akansa sosai Karin ruwa suka sa Masa akai Masa allura wani Dr ne yafito Yana tambayarΒ  yaran aliyu Ina matarsa

suka ce batanan tayi tafiyi

shuru Dr yayi yagirgiza Kai yace bawani nashi da ku kazo tare

sukace eh ko da matsalane Dr

yace aah yashige yatafi

Wajan karfe goma na dare alyu ya Fara dawowa dedai yace Akira Masa Dr shi gida ze tafi Dr nazuwa aliyu yace Zan tafi gida Dr kome ake ciki gobe kazo gida ka karasa min akwai dalilin da Yasa Zan tafi gida yanzu naji dedai ba abinda yake da muna tafiya zanyi

Dr yace gaskiya yallabai in muka barka katafi gida yanzu komai ze iya faruwa sedai in zakaje wajan madam ne kasauke matsalar da take da munka munyi mamaki kana da aure har da Yara matarka ba saban aure bane Kun Dade tare Amma shaawa ta tarar maka haka Amara Kuma kasan matsalarka kana da karfin bukatar mace akusa da Kai ko da yaushe in wannan matsalar taci Gaba da faruwa se anmaka aiki Kuma kana gaf da Dena haihuwa Gaba daya kakusa rasa Kwan haihuwarka Gaba DayaΒ  in matarka bata gamsar da Kai ka Kara aure Allah yahure maka za ka iya rike Mata har hudu gaskiya kadau mataki cikin gaggawa kafin lokaci yakure maka in ba hakaba da matsala babba Nan Gaba in ma madam tayi tafiyane Bata gari ka gaggauta sawa ta dawo da matsala yanzu muna so kayi hakuri ka kwana zuwa gobe ma sallameka

Aliyu Ido yaruntse yahau girgiza Kai azuciyarsa Yana takaicin abinda yakeΒ  niyar faruwa da shi gashi Allah yadora Masa San Yara jiyayi hawaye na niyar zubo Masa yadaure Dan Kar Dr yagane halin da yake ciki in ma aure zeyi shi wa zema aura yatsani Mata baze Kara aureba gara yakarasa rayuwarsa ahaka tinda yayi beji dadiba bude jajayan idansa yayi Yana kalallan Dr yaja dogwan numfashi yace agaskiya gida Zan tafi yanzu Ina da abin yine naji shawarwarinka na gode gobe kazo gida ka karasa,min abinda yadace

Dr yace to yallabai bazan matsamaba bansan matsalar kaba agidan se goben Zan zo har da sauran magungunan naka yanzu cikin naka da marar sun Dena ciwo ko

Kai aliyu yadaga Masa yasauko daga Kan gadan yabude kofar yafito yaransa na ganinsa suka taho suna tamasa sannu Kai kawai yake daga musu hanyar inda da kin da aka kwantar da sadiya yanufa ze shiga kenan

Sega umma tataho da kula rike ahannunta tace alhaji sannu da zuwa yaaiki

DakyarΒ  yabude Baki yace alhamdulillah yame jiki

Tace taji sauki gobe da safe Dr yace ze sallamemuΒ  shigo Mana yau idanta biyu kanwar taka itama nemanka take Tai maka godiya se sabani kuke du sanda zakazo tana bacci babantama haka Baku haduba har yau

Yace ba komai base na shigaba sauri nake tinda na ganki mun gaisa shikenan se direba yazo gobe kaiku gida kigai da baba kar yadamu base yamin godiyaba

Hannu Yasa a aljihu yaciro wasu kudi masu yawa Shima besan adadinsuba yabawa umma cewa tayi bazata karbaba dakyar yasata ta karba tana ta godiya

Tace bawan Allah yasunanka karkace na dameka gashi Kuma balanlai bane nakara ganinka

Yace sunana Ali umma se da safe yajuya yatafi

Tsayawa umma tayi tana kallan hanyar da yabi da mamaki da kudin da yabata rike ahannunta tace Ali ikwan Allah wlh ban sanshiba Allah kaiwa bawannan naka Albarka Allah kabiya Masa bukatarsa na alheri

tabude kofa tashiga tasamu sadiya zaune Kan sallaya ta idar da sallah tace sadiya Kinga yanzu alhaji bawan Allah yazo dubaki

Dasauri sadiya ta zubawa kofar shigowa Ido tace umma Yana inah Allah yayi Zan ganshi yau

Umma tace ai har mun gaisa yatafi yace sauri yake aimiki yajiki nace Masa kinasan Masa godiya yace base kin masaba agaisheki wlh Ni mutumin mamaki yake bani Kinga uban kudin da yabamu Ni tsorone ma yakamani naki karba se da yamatsamin sannan na karba nai tamasa godiya yace bayaso base na masaba Basu hadu da malam ba har yau Shima Wai sunansa Ali da na tambayeshi

Shuru sadiya tayi bahaka tasoba jitayi hawaye naniyar zubo Mata se taji Babu Dadi azuciyarta Dan taso taga Wanda yatemakawa rayuwarta ahankali tace Zan tamaka adduar alheri bawan Allah naso ganinka Allah be nufaba me temako inah San ganinka Ido rufe Allah be nufaba Ina Zan ganka Kuma shikenan Allah yaimaka Albarka bawan Allah me temako

Rai ba dada ta tashi taje ta kwanta zuciyarta ba Dadi du hirar da umma take Mata bajinta take sosaiba har bacci yadauketa

Alyu da yakoma gida masu gadi yatambaya ko malika ta dawo sukace Bata dawoba rabanta da gida tin safe da ta fita bece Komai,ba yashige cikin gida afalo yazauna Yana jiran ikwan Allah yaga yaushe zata dawo sha Daya na dare dedai har shada da rabi shuru Babu ita ba labarinta waya yadauka yakirata yaji wayarta na shiga har sau uku yakira Bata daukaba

can se ta turo Masa sako ta msm tace,,,,,,,, MALAM KARKA DAMENI KAJIKO KOWA YAI HARKAR GABANSA BARUWANKA DANI,,,,,,,,,,, se ta kashe wayar Gaba Daya

Abin yabawa aliyu haushi Kiran duniya wayarta akashe daki yatafi yaje yadauro alwala du da ba Dadi yakejiba yai nafila raka,a biyu Allah yaimasa maganin matsalolinshi yakwanta yai adduar bacci badadewa bacci yakwasheshi

Da safe wajan karfe Tara na safe Dr yasallami su sadiya likita yadada fadawa umma da malamΒ  sharadi Akan jikin sadiya sukace duka sun dauka zasu kiyaye Babu abinda ze Kuma faruwa yabasu magungunan da zata dinga Sha Kuma yace bayan sati biyu sudada dawowa agwada lfyarta aga komai yakoma dedai

Suna hada kayansu zasu fito su tafi Sega direba inji aliyu yacika alkawari yace yakaisu har gida umma da sadiya ba bakin mgn se mamaki da suke tayi malam ne yake ta godiya yace wannan bawan Allah shi baya gajiya wlh da yabarshi muna fitowa zamu samu abin Hawa yakaimu harΒ  gida

Direban yace ai wannan ba komai bane daga cikin temakwan yallabai ai kome yayi baa mamaki Dan shi wannan abinda yai muku ba komai bane awajanshi yanzu kafin Nan kafin kwana uku yamanta ma da abinda yai muku ko haduwa kukayi da shi se Kun Tina Masa ku su waye Kan yatinoku

Malam yace ikwan Allah kaga na Allah Allah yabiyashi

Dukansu suka amsa da ameeeen

Har kofar gida yakaisu yatsai da motar lokacin su habi sun fito leke kofar gida Yara na dambe suna musu mgn su Bari sukaga mota har mota tana daukan Ido ta tsaya akofar gidansu idan Yan unguwa se yakoma Kan motar ana jiran aga su waye zasu fito daga motar Suma su tala Baki suka saki suna jira suga me fitowa sukaga umma tafara fitowa se sadiya se malam salati su lami suka hau yi suna zare Ido da hanci har suna buge kawuna wajan zuro Kai su kallah sosai Yara akabawa tilin Kayan da suka dawo da shi du siyaiyar aliyu ne da yai musu agabansu Yara suke ta shigewa da shi suna kaiwa da kin umma sallama sukayi da direban suna tamasa godiya da sauri malam yataho yakama hannun sadiya umma ma takama Daya hannun sukasa sadiya atsakiya suna shiga cikin gida sunzo gaf da su habi

malam yadaka musu tsawa yace Wai ku Wana irin jahilcine yakeΒ  damunku da auranku da yaranku kuke leke acikin unguwa wakukaga Yana haka du cikin unguwarnan ko kunga Yar uwarku Khadija nayi dahallah ku shige ciki ku bamu waje kunga mutane ba sannu da zuwa ba komai Kun saki Baki da hanci Kuna kallansu kurufe bakin Dan Allah Kar kuda yashiga Ni malam musu na kwasowa kaina

Umma tace baban sadiya mu shiga da ita ciki karta gaji kasan likita yace Kar tana wahala

Da rawar jiki malam yace to to mushige mu kaita sannu kinji sadiya na barki atsaye inawa marasa tinaninnan mgn

Cikin dakin umma suka nufa da sadiya inda su habi nabinsu abaya har cikin gida ba bakin mgn seda sukaga sun shige Babu alamar malam yayi zamanshi se Hira suke da yaran umma suna dariya

Abin yadada Bata musu Rai sosai tala talailayo wata uwar ashar ta Danna tace akwai Bala,I agidannanfa wlh wlh wlh da sake muzuba Ni da ku malam kaga abin duniya idanka yarufe anje anmallakeka andawo har da motar Wanda yai Mata cikin shegen ma aka dawo da ku aciki kenan malam yasan da cikin shegen da sadiya tayi Dan anrufe Masa Baki da kudi da Kuma layu da rubutu shine yakasa mgn kenan suna ma tare da alhajin da yai cikin kenan wato shine me motar nan ai Baku birgeniba tinda ba auranta zeyiba sedai akare ahaka har abada wlh Dole ma gobe na fita komai yawargaje se mun sake saban Shiri Wai matarnan da yaranta shedanune ko Yaya muyi tamusu aiki sunaΒ  wargaza Mana kuga kudin da muka hada muka saci hanya shekaran jiya mukaje kauyen dakasoye wajan malam gobe da nisa yace Mana gidannan se yafi karfinsu in sun dawo malam ze musu korar Kare sadiya zata shiga duniya bazata dawoba se da yaran shegun da tahaifa har guda uku Khadija zata hadiyi zuciya ta mutu Yan uwan sadiya duka zasu lalace Amma bamuga alamar komai ba Wai me yeke faruwane har fa akwaryar tsafi malam gobe da nisa Yasa muka leka fuskokinsu dukansu mun gansu cikin wahala da kuncin rayuwa waiyo Ni tala wlh bazan hakuraba se burina yacika akan Khadija da yaranta wlh se yaran Khadija da ita kanta Khadija sun zama abin gudu aduniya se kowa yagujesu muzuba Ni daku shege kafasa

Lami tace ke wannan,ne yadameki tala kiga irin cin mutuncin da malam yai Mana agaban Yan unguwa da munafukar matarsa da sadiya me ladabin munafurci kiga jiyama irin cin mutuncin da yataramu yai Mana gaban yaranmuΒ  AkanΒ  bamu tambayi inda matarsa taje,ba saboda shi an asirceshi an rufe Masa Baki Ni tausayi ma yake bani bawan Allah du ta zagayeshi da asiri se mun tashi tsaye in ba hakaba muma mallakemu zatayi muzama bayinta ko ta koremu agidan tazama daga ita se yaranta se tsohuwar guzumar yarta sadiya wlh Nima se nayi abinda malam ze wulakanta Khadija agaban mutane da Yan unguwa se nasa malam yayi watsi da kayanta atiti in dai Ni nacika lami yanzu muka Fara wasanΒ  Ni da ke Khadija zamuga malamin waye yafi zafin aiki tsakanin Ni dake

Nikuwa nace hm lami allanta yafi naki malaminΒ 

Habi tace wannan Karan mun banbanta da juna ko wancanmuΒ  abinda ke ranta daban abinda yabata Mata Rai da ban Ni karairayar da Khadija take Masa tinda tafito acikin shegiyar motar Nan me kyaun tsiya ita da yarta ko bakuga yanda suke wani iyayiba se kace motar ubansu Ni bakin cikina motar da ko tabawaΒ  ban taba yiba bare insamu arzikin shigaΒ  Wai yau Khadija ce da yarta suka fito acikinta lanlai yau karuwanci yaiwa Khadija da malam Rana sun shiga motar da tinda sukazo duniya Basu taba shigaba Wai da zasu shiga ciki lokacin malam yagaMa mana tijara har dawani cewa baban sadiya wlh yanda kika san na shaketa haka na dinga ji har tagama fadar abinda zata fada Masa shikuma mijin tace jikinshi nabari yarike hannun sadiya suka shige daki Wai yarinya tayi abin kunya akaita azubar da cikin da tayiΒ  adinga lanlabata kamar kwai kuji har da cewa likita yace tana hutawa Ni har gobe mamaki nake du ranar da malam yake dakin Khadija har wani rawar Kai yake bini bini kaga yagudo daga wajan sanaarsa yazo wajanta sulume adaki kome suke susuka sani basa tsoran Yara su dawo daga makaranta suga me sukeyiΒ  dare nayi ana sallar Isha,I ze shige dakinta yaki fitowa yazauna da yaranta da itaΒ  suyi ta Hira suna shewa can dare yaran nayin bacci kamar munafukai zasu shigeΒ  dakin malam Basu zakaga sun fitoba se gari yawaye yayi haske ko sallar asuba wataran baya zuwa kome take Sha yake wannan rawar kafar ohoh akin banza antsufa baasan an tsufaba Ni Dan bakin ciki narasa me sukeyi in sun shige har labe nake musu Amma bakajin komai munafukan daga ita har malam din ko irin wankan tsarkin Nan da muke fitowa muyi da safe Ido naganin Ido Banda ita tinda Nazo gidannan ban taba ganin tayiba anyama kuwa tana wankan tsarkiΒ  Kuma Babu wacca yakewa haka acikimun se ita wlh Nima Sena tashi tsaye du ranar girkinta senayi abinda gaban malam ze Dena aiki har yagama kwana dakinta yafito sedai su kalli juna shi da itaΒ  ko na danah Mata kwado na shafe Mata gaba kowa yahuta Naga kofar da zaashiga ai rawar Kan aciki

shewa sukayi su,duka suka tafa

Malam ne yafito yai gyaran murya yakallesu yagirgiza Kai yai ficewarsa wajan Sana,arsa

Baki suka hada atare mun,shiga uku ko malam yajimu irin wannan kallan tsana haka da yai Mana





Bana turawa ta pc Dan Allah Kar Wanda ta biyoni tace natura Mata ta tambaya agrp zatasamuΒ  insha Allahhu













New writer's

Hakan Take
Β  Β  Β Β  *Husba'ahfama* 😍πŸ₯°πŸŒΉ
Β  Β  Β  Β  *'Yar kwalliya* πŸ’‹πŸ’„πŸ’ƒ

You are reading the story above: TeenFic.Net