8

Background color
Font
Font size
Line height

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

🖕🏼Gaskiya daya ce🖕🏼
( Daga kinta sai bata)

✍🏽✍🏽✍🏽

      Kulsum Bappah
Umm iman

Ina kike?
Nana Bappah Azare
  
بسم الله الرحمن الرحيم

08

   ..... Ya bude baki zai yi magana kenan sai yaji karar waya, kaltum ta dauki wayar  cikin girmamawa ya gaida mahaifiyar shi, nan ta kwashe abinda yake faruwa ta sanar dashi, ita kuwa  kyallu sai murmushi take yi taje ana ciwa  kyallu taji an  ambaci bintu kuma sai  taji ance yaa ganah, kai Allah wadaran abinda baka sani ba, ( da yake kaltum al'adar tace indai zatai waya da 'ya'yanta ko da mijinta to  da larabci take yi)  kuma tana wayar tana kallonta tana murmusawa, can suka gama wayar. Alh bukar yace Alhamdulillah. Kunga dan halak. A ina yace miki ya samu matar? da yake yana  sauraron  abinda suke fadi kawai dai baya jin amsar da  baanziye yake bayarwa, eh yace ya samu a zamfara, tab tashin hankali da ba'a sa mashi rana!! Tashin hankali gobarar gemu!!!

      Haba haba! yaya yanzu ace ya tsallake jinin shi ya bar garinsu ya tafi har wani gari zamfara?  Inah!  inji kyallu, nan yaa kime tace haba Alhaji  kuma yanxu kai zaka Amince   ya  auro bare?? Haba ai ko an hana ya auri jinin shi ai ka bari ya auri kabilar shi, amma ai kasan Al'adarmu ta bare bari bamu hada jinsi da wanda ba dan kabilar mu ba,
    Zakuwa a fara akan baanziye, a qur'ani ne Allah ya haramta ko kuwa hadisi ki kawo min nassi,  na qur'ani ko na hadisi, to sannu dan gidan sharu saleh wanda yafi kowa haddar hadisi a nigeria, tashi tai a fusace,
    Fuuuuu,  kyallu kuwa wai ita mai hikima ce mashi tai, yaya inaga kar ka biye zugar mace, ai da arxiki a garin wasu gwanda a garinku, agarinkun ma a gidanku, gidankun ma a dakinku, a dakin kuma a kanka.
        To kyallu ga Arxikin yayi tsuntsu ya tsallake yobe, bauchi kano katsina ya sauka a zamfara, idan kin gama zan gana da kaltum,
        Tana ta kunkuni dai ta fice a falon sashin hajja kaka ta nufa, nan ta tarar da yaakime zube a kasa kamar kayan wanki tana ta Aaa A, ( nace ba AA zaki fada ba idan ma Baa ne baza ku samu yadda kuke so ba) saboda duk wani makirci da suke kullawa da ikon Allah, Allah yana warware shi sam TARKON su baya kamo masu komai,
     Koda yake idan ka rike Allah ka mika mishi Al'amarinka to ya isar maka,

~~~~~~~~~~~~~~

Hajja kaka tace kyallu naji abinda yake wakana, yanxu mi kike so ayi? Nan ta karkace. Ta fara cewa yauwa  hajja a hana shi auren bare, yaya za'ayi ya tsallake gida ga kanenshi kyawawa yace duk bai ga wacce ta mishi ba? Eh fah haka ne, to ku barni da bukar din, kyallu da ya kime suka hada ido.

  Ba kunya ba tsoron Allah suka tashi suka bar sashin hajja kaka suka koma sashin yaa kime,
 
  Ita ko hajja ta fadi hakan ne saboda su bar abin domin yadda tasan halin yaa kime da kyallu zasu iya yin komai akan maganar tunda mutane ne masu shige shige basu yarda da Allah ba sam,
    Babu tauhidi a cikin lamuransu, shu'umai ne na kin karawa,  shiyasa ta lallaba su ta yaro kyau take bata karko!

   Hajja kime kinmin dai dai gwanda da kika sameta ai, domin ita kadai ce kawai zata tankwara su, hmmmnn kyallu tace kinsan abin haushi har wani cewa yake na bashi wuri zai yi magana da yar gwal.  Hhhhh ba yar gwal ba ko yar lu'u-lu'u ne za muyi  maganinsu, tunda munyi makircin munyi sharrin, mun bi malaman, amma tana nan daram zamu fada kan ya'yanki kaltum sai kinyi kuka da idanunki yaa  kime ne take fadin hakan..

    Can falon Alhaji kuwa. Yana ganin kyallu ta fita ya dago  kaltum ya zaunar da ita akan cinyarsa, suna fuskantar juna numfashinsu na sarkewa, hayateeeee yace na'am qalbeeee kinga shi kuma inda ya samo mata ko? Eh akwai lauje cikin nadi fah! Mi ya faru?     
   Hmmmmmm!   Kasan fa akwai da babu ne, ta daga ido ta kalle shi kamar yaya kenan? Sau daya ya ganta gidan Ambsdr sageer, na dai takaita maka ko sunanta bai sani ba, bata ma san dashi ba, amma dai yace min yaje gidan  haj kyautan neman karin bayani sai take ce mishi yarinyar tana Alqalam, to yanxu shi tunaninshi. Ita ce ko ba ita bace saboda su uku ya gansu, amma dai yace zai tambayi Aisah ko ta santa,  to! Kira min shi yanzu,,
  
Assalamu Alaikum ya Ammi
Abbu ne ke magana, mamar ka tamin bayani,
Eh
Ka kira Aisah dince?
  A'a
Mi kake jira?
  Ya shafo sajen shi yace zan kira yanxu,
To Allah yasa dai ba'a mata Alkawari ba? 
  Hmmmmm Amin.

  Ammi kinsan wani abun sunan ya bace min kamar ko sha'awa ko shafa, tabb kana da aiki.

~~~~~~~~~~~~~~

  Ya kira Aisah kusan sau 7 kenan yana irgawa amma shiru bata dauka ba, abinka da mai zuciya a kusa nan yaji ranshi ya harzuka yana ganin kamar ma da gangan taki dauka, kasan mutum idan yana nema,
  
   Har yayi zuciya can sai ya kara kira, can sai yaji wata murya ta dauka haba ukhti ina kika shiga? A'a ba ita bace,
    Don Allah ina take kuma wace ce ke?
Tana presentation ne, tasa wayar a silent. Naga ka kira ba adadi shiyassa na dauka, owk kit sai ya kashe wayar tace ikon Allah mutum sai  kunata ( kunci ) ta aje wayar yauwa kin ida to naga wani ya Akhee yanata kira na dauka kuma yana ta dumi, yaya na ne fa baanziye da nake fada miki, kai aiko ya faye dumi,
A'a ba haka yake ba sai dai wani abun ke damunshi, bari na kira shi,
  
      Assalamu Alaikum. kat sai wayar ta mutu babu chaji. Nan dabara ta fado mata, ta karbi wayar shafa  mi 'az-zakiyi da wayata?
Abinda akanyi,
    Hahhhhhhaa yau kuma harda koyon hausar mu,
     Tasa  number ta kira shiru, ba'a daga ba tasan yayanta bai fiye daukar number da bai sani ba.
Dabara ta fado mata tai mishi text,
   Ana ukhtika Aisha,  '' ni yar uwar kace Aisha,
     Yana karantawa ya qira  ke ina ta kira shiru baki dauka ba, eh presentation nake ,eh
A ina kika samu mai dawayayyar hausa haka? Hausar shegen ta su Ambsdr sageer amma na wannan yafi damewa?
     Nan tai dariya.
Eh yar garinsu ce da yake su sun dade rabonsu da garin, kuma sunyi zaman kasashe shiyasa tasun take da dama dama,
Ba wannan ba kinsan miya ke faruwa?
   A'a
A ina?
A gida.
    A'a ya bata labari bitalkhees ( a takaice)  na taba ganin wata yarinya a anan oman gidan Ambsdr, kai
    Yaya sunanta? A'a saurara, zumudi! Inaga ko sha'awa ko shafa. Nan ta jiyo ta kalli shafa,
Ina jinka yaya,
  Yaya second name dinta yake? Eh gaskiya ban sani ba kinsan haj kyauta tace min kannenta ne da yayan yayyenta to abinda ban sani ba, bansan wacecce daya ba, turkashi!  dama ka rike sunanta ne to da sauki, amma haj kyauta tace min akwai wata nan a makarantar ku, kai inji haj kyauta?
 
Kawai sai shafa ta kalle ta taji haj kyauta kuma dama taga number code din oman ne, nan ta zaro ido miya samu haj kyautan?
  Kuma wace haj kyautan ake nufi???? 


🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

You are reading the story above: TeenFic.Net