6

Background color
Font
Font size
Line height

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

🖕🏼Gaskiya Daya ce🖕🏼
( Daga kinta sai bata)


اهدى هذه الصفحة الى زوجى الغالى العزيز ابو ايمان 💋💋💋

بسم الله الرحمن الرحيم

06

     Kamar kullum masu gadi na tsaye a bakin gate din makarantar Allo idan kazo da shigar kamala su baka hanya ka shige idan da akasin haka kazo ka koma inda ka fito, haka ya kasance yayin da mani driver yazo shiga   suka dakatar dashi daya daga cikin masu gadin wanda ke sanye da unifoam ya leka ta tagar mota ya ganta sanyi da Abayarta ta yane ganta da dankwalin Kayan, sukai musu nuni da su shige dai dai hall ya  ya ajiye motar ta fito yana mai tambayarta ya tafi ne ko ya tsimaye ta ,ummm to lectures daya nake dashi zaka iya tsumayata, amma idan kana da uxuri to kaje ka gabatar, a'a ranki ya dade bani da wani uzuri da ya wuce naki, to shknan ga can inuwa ka zauna can saboda yau an tashi da rana mai zafi,to ranki ya dade.

  Sai ta ji wani bawai saboda babu abokiyar tafiyarta shafa ''sabo turken wawa'' nan samari da yan mata masu son shige mata sukai ta kawo gaisuwa ita kuma ba kamar shafa ba, saboda shafa ce mai mutane ta gaisa da wannan ta gaisa da wancan, ta samu waje ta zauna, bata dade da zama ba mal yuguda ladan ya shigo ya fara lectures cikin gwanancewa da zurfafawa a fagen ya kammala tare da basu Assigment akan faruwar BIG BANG THEORY EXPLUTION sukai Attandance ya fita, suka tattara taiwa wanda suke zaune musabiha ta fita ta lalebo wayarta samfurin BLACKBERRY ta kira shafa,''Marhabaan''. Marhabaan'' suka gaisa ta zayyana mata an bada ''wajibul manzil''  na Astronomy ta dafe kai tace mun banu daga dawowar mu, kinsan ba sanya idan zaki sammako to, sukai sallama,

Nan ta buga waya taji number ya haisam a kashe, da yake tambayar tana da nasaba da abinda ya karanta saboda shi cikakken ASTROUNANT ne can sai ta tuna da binazir ta kirata ,sis yya kike? lfy yasu Ammi Abbu hajja kaka. Da sauransu, kowa lafaiya sis, don Allah ya haisam yana nan kuwa? na kira wayar shi a kashe, la  baya nan,wurin aikinshi sun ne meshi Russian's Aerounatic space Agency, kai! yace min kamar suna shirye shiryen harba jirginsu ne zai tafi duniyar  mars '' JOURNEY TO MARS''  duniya ta hudu bayan EARTH, wayyo kinsan an bamu Assighment ne akan BIG BANG THEORY EXPEREMENT. nan zan samu details sosai a wurinshi duk da cewa idan na shiga GOOGLE zan samu amma nasan yawancin Assighment a GOOGLE mutane suke yi ina son namu ya banbanta, eh haka ne  sis, idan ya kira ni zan mishi baya ni, sai dai inaso ki turo min tambayar tare da GMAIL Address dinki sai ya tura miki, owk to ngde sis,

    Tana  isa gida ta wuce dakin Aunty yabi,ta zube akan gado,ya kika dawo da wuri haka? Lectures daya muke dashi kuma kinsan shafa bata dawo ba, amma tace gobe zata dawo, ayya Allah ya kawo ta lafiya ai zamfara da nan ba nisa ko,eh to tace dai idan anbi ta shema tsafe ,kwatarkwashi awa uku ne amma idan ta jibia ne awa biyu ne, Allah ya kawo ta lafiya, Amin wato Aunty shiyasa ba'a son haka kawai ka tsani mutum kinga da shafa ina mata kallon mai rawar kai ga yawan surutu kowa zata kula, sai nake baya baya da ita, to Amatsayin muna course guda dole mu'amala ta hada mu, sai daga baya na fahimci tana da saukin Al'amari ita dai nature dinta ne haka, saurin sabo rashin kyaliya yawan murmushi kullum fuskarta a sake take, Aunty yabi tace ai tun randa kika zo kika ce min kin samu mace a course dinku, amma kina ganin kamar taku bazata zo daya ba nace ki bi a hankali, to ke da kanki kinga ba haka take ba, nan Aisah ta fad'a tunanin haduwarsu ta farko a hall a lectures din G.S.E, wanda mai girma wazirin katsina  yake dauka, yana musu bayani akan shiguwar musulunci ta hannu bin fodio da yadda sokoto ta zama seat of caliphate Albarkacin jan gwarzo  shaikh usman bin fodio, ana haka sai ya jefa tambaya mi kalmar FODIO take nufi? Nan wani daga computer science yace. Saboda sunan shi usman ne shiyasa ake ce mashi FODIO,  nan hall ya kaure da iface iface wasu suna cewa hakane wasu suna ba haka ba, aiko nan shafa ta tashi tace  Asalin kalmar Fodio daga fulatanci ne,ana nufin FAKIHUN ,wato masani ilimin fikihu da fulatanci.

    Nan mai girma waxirin katsina ya tambayi. Add no dinta  da faculty din da ta fito, ya jinjina mata kasancewar an raina yan ARABIC LANG gani ake gidadawa ne, shiyasa yace ya bata maki kyauta na C.A.

       Nan Aisah taji wani dadi saboda ita kadai ce mace A ARABIC DEPARTMENT, har malaman suna ce mata ''المراة شقاءق الاقوام'' kallabi tsakanin rauwuna'' bayan an gama lectures din Aisah ta fara wasi wasi taje ta same ta ne ko ko, ita gashi ba ta da sabo, amma haka dai ta daure ta karisa, ta mika mata hannu, tare da  sallama nan ta amsa mata Aisah ta ce mata.'' Ana Aishatu Abubakar min wilayati borno'' ana fi kismi dirasatul Arabiya'' ai ko nan shafa ta rungumeta, tana shaida mata ita sunanta shafa'atu lawal min zamfara, shknan , shafa ta fara mata tambayoyi wani ta amsa wani tai shiru kasancewar ba ma'abociyar yawan magana bace, har suka koma kisim dinsu sukaai lectures din BALAGA, nan wayarta ta katse  taga hoton sis ta dauka tace sis ya akai ne? Ya haisam ne yace baki da number shi ko bai isa ki kira shi, da kanshi bane? Nace mashi ai baki da number shi ta russia,wai ina kare ki ne, ai zaki iya karbar number, yanxu na turo miki number, to sis nagode.

      Dakinta ta shiga ta kwanta tasha baccinta. Sai daf da azahar ta tashi, ta samu safiyya tai musu burabisko da miyar kabewa ta sha tantakwashi, bayan la'asar ne ta dau wayarta tayi dialling number ya haisam,  gabanta sai faduwa yake saboda tasan halinshi,   bata ma san ya daga wayar ba yana ta hello hello sai tsakin shi taje ya kashe wayar, nan ta ankara ta kara bugawa yaki dauka, bayan isha'i ma ta kara kiran sanda tai bugu na uku sannan ya dauka a gadaranci,
   Yaya ina wuni, lafiya, yaya aiki, dama  ya katse ta da yaga ta fara inda inda binazir ta min magana dama kuna course din ne, eh munayi, na zaci yan makarantar Allo bakuyi, musamman ko yan Arabiya, Allah munayi, to bari na miki tambaya, to ta amsa cikin fargaba,   yanxu idan nace define Astronomy???
The word Astronomy is from  greek word astron means ''star'' nomy from nomos '' laws or culture'' literacy mean law of the star. Good ta cigaba da cewa astronomy refers to study of object and matter outside the earth atmosphare, such as: planet galaxes,phenomena,comet,clusters etc.
     Welldone, naji wannan nigeria tana da nata Agency din NASRDA bani pull meaning dinshi, a zuciyarta tace dan rainin hankali,  NATIONAL SPACE RESERCH AND DEVELOPMENT AGENCY, yes ta daura  da cewa obasanjo ne ya kirkira a 2007.

   To shikenan kina da biro a tare dake tace a'a to dauko na fara miki bayani kina rubutawa,  uhmm tace to bismillah
    Ya fara mata bayanin tun daga fashewar BIG BANG inda aka samu ta rabu zuwa gida biyu: primary nebular & secondry seperation,
Cikin tana ganewa har ta fara rubuta shirme, saboda da sauri yake ba don jinin ta bane zata ce ko ya hada dangi da YURI GAGARIN wanda ya fara zuwa wata duniyar da taimakon  KUMBO APOLO, dan kasar soviet,1959. Can sai taji yana kawo mata evedence din BIG BANG, daga suratul Anbiya aya ta uku, yace ke ustaziya ce sai ki duba, wuuuu yaya kasan ustaziya kuwa? Professor kinan fa da yaren larabci, to naji,don Allah yaya idan bazaka damu ba ko zaka min SENDING VIA GMAIL dina, saboda bani da Abinyi ko? Kai hakuri, to mi zai hana bazakiyi GOOGLING BA? tace yaya kowa anan zaiyi shiyasa bana son oh to ke wace da bazaki yi iri daya da mutane ba? Kai hakuri don Allah, to shi kenan amma kar kisa rai a yau ko gobe, ba komai nagode,.

     Gari na wayewa kuwa ta ga alamar sako ya shigo ta gmail dinta tunaninta ma daga bank ne saboda da gmail tayi linking, sai taga daga yayanta haisam ne, nan ta shiga computer room ta booting dinta kai tsaye gmail dinta ta bude tayi COPY dinshi tazo tayi PASTE ta fara EDITING , kafin sha biyu rana ta gama gyare gyare har ta fito musu dashi da yake tana da PRINTER, tai musu PHOTOCOPY ta ajiye saboda zai iya fituwa a xams, ta kira shafa sai dai wayar bata shiga ba tana ganin tana hanya....... .

  🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

You are reading the story above: TeenFic.Net