44

Background color
Font
Font size
Line height

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
 
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼
          [ JIRE TILO]

(Daga kinta sai bata)

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah
       Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @[email protected]
🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
( ÀDDU'AR Domin Neman Yafewa Ga Abin Da Ya Gudana A Cikin Majalisin)

A'isha, Allah ya yarda da ita, ta ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai taba zama a wani majalisi ba, ko ya karanta Alkur'ani, ko ya yi wata sallah face ya cika da wadannan kalmomi.
سُبْحَانَكَ اَللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَيْكَ.
Subhanakal-lahumma wabihamdik, ashhadu an la ilaha illa ant, astaghfiruka wa-atoobu ilayk
بسم الله الرحمن الرحيم

44

Masu neman Auren  falmata sun zo sun kawo abin da ya dace ba laifi sunyi kokari
A matsayinsu na masu karamin karfi
Sunyi bazata
Ammafa kyallu bata yaba ba saboda ita anata ganin bai yiba,
Falmata kuwa godia tai ta yiwa ÀBDULJABBAR,
Yaji dadi a ranshi,.
  Alhajijo ya zauna yaga kayan ,
Ya cewa hafsee ta rubuta abin da babu zai bada kudi a sayo mata wasu,
Bintu kuwa sai iyaye take zuba wa wai wannan kayan bai kyau ba sam 'ya za'ayi ace sun kawo wannan kayan tsabar renin hankali ai ko rabin rabin na jidda bai kaiba,
Ki saurara idan ke bai miki ba ni yamin,
Saboda kuntun gatarinka yafi sari ka bane,
Ke rufa min baki banza kawai,
Niba banza bace,
Kyallu ta katse su,
Bana son shashanci
Yo mama akan mi zata raina min kaya ai shi arziki na Allah ne
Kuma bai zama dole don mun taso a cikin gata ba ace  dole mu samu yadda muke so ba
Ki karata ni dai nafi karfin wadan nan
Falmata ta tashi ta tafi wurin
Aunty hafsee suka cigaba da tsare tseren su ansa biki wata daya kacal
A ka cigaba da shirye shirye
Alhaji Bukar ne ya dau dawainiyar gado
  Mahaifinta ma ya mata gadon ta tashi da gadaje biyu
Jiran rana kawai ake yi,
Alhajijo kuwa yayi bakam abinshi ya zuba ido wa bintu,

Aisah dai yanzu ta faso gari itama
Tasan miye aure
Nan da nan ta murje tai kyau
Idan aka ga ISLAM da MUSLIM  za'ayi tsammanin yan wata uku uku ne tsabar girma,
   Gashi Allah ya taimaketa basu da riki ci kullum tare dasu safiya suke kwana,
Ta fara samu chanji a jikinta amma batayi tunanin komai ba,

Yaana kwananta biyu a wurin kaltume
Suka maidata wurin yaakime
Tana ta yatsina ita zamanta da yaana bazai yiwu ba ,
Yarinyar da ba mutunci ne da ita ba har yaana zatai magana kaltum ta hanata suka dai lallaba suka bada hakuri,
suka tashi suka tafi,
Tun daga nan dai kowa  harkar gabanshi yake ,
KARE BANI KORAR KA BANI BAKA ABINCI NA
  Jidda ta sauka lafiya sauran BINAZIR domin itama ta dawo gida haihuwa
Ba yadda mijin baiyi ba ta zauna acan Abuja ta haihu tunda gashi ga iyayenshi,
Fir take domin BINAZIR
Tana matukar kiyaye abinda zai hadata dasu balle ta haihu ta koma cikin gidansu ta zauna ,
Duk da cewa familyn yan boko ne amma suna fama da matsalar tsegumi ko don mata sunfi yawa ne,
Abu na faruwa fah zaki ga
Wannan ta kira wannan wannan fadawa wancan   ,sai kiga abu ya karade kan yan uwa abin takaicin basu tabbatar da abu suke dorar wa,
Shiyasa ita kuwa tace ina!
Gwanda ta dawo wurin iyayenta ta haihu a gaban su duk runtsi zata samu kula
Saboda ta lura uwarmijin nata macece mai kishi bata kaunar taga BINAZIR da danta suna wasa suna dariya nan da nan sai tayi kicin kicin ta bata rai tun basu fahimta ba har suka fara fahimta
  Wurin ummi sauda ta zauna
Kudi ya tura mata ta Account dinta na sayayyar kayan baby domin tun kafin ta taho ya bukaci  yayi shawara da maman nashi akan ya kamata fara sayayyar kayan haihuwa,
Budar bakinta sai tace wani kayan haihuwa kuma ba gashi ko na kayan auren bata gama dinkawa ba,
A'a ba kayan uwar ba kayan jariri fah nake fada
Owo to ka bari zan kira hajara sai tayi list din da kayan da ya dace a saya,
Yace to yana zaune ta  kira hajaran sukai magana tace zata tambayi mijin ta  idan yaso   ko wuse market ne ta shiga,
Tunda yaji an anbaci wuse market yaji ranshi bai kwanta ba maimakon ace su shiga shoprite ko silver bird,
Bayan kwana biyu da maganar ne suka nemi ya basu dubu dari biyu,
Abin mamaki gaba daya local kaya suka sayo kuma bai kai na kudin ba
Tsabar bakin ciki cewa yayi su ajiye a wurin idab haihuwar tazo sa karba

YA caske mata dubu dari biyar harda na zannunwanta

Ummi sauda ta wakilta Su anty shafa Da Aisah sai matar CAPTAIN da itama cikinta yakai kusan wata hudu dasu je kasuwa suyi sayayyar saboda tana son suma ta dorasu akan hakan domin yanzu su girma yazo musu ya kamata ace su huta 
Kuma Alhamdulillah kansu a hade yake babu zance kai komo a tsakaninsu gashi matar CAPTAIN itace karamar su amma Alhamdulillah ta dauke su hannu bibbiyu kamar yayyunta na uwa daya uba daya
Sun gama shirinsu kenan suka iske yaana a falon Ammi
Aisah zaku fita ne?
Eh Aunty yaana ko zaki je?
Ina kuka nufa?
Kasuwa zamu
Ayyah to muje
Shafa har ta hada rai sai Ammi ta kirata suka shiga ciki,
Tace shafa ba'a haka ki sake ranki ku tafi taren yanzu tana dan shigo mana
Muna son ta dan samu canjin rayuwa ne
To Ammi,
Ai ni tsoro take bani Ammi,
Kar kiji tsoronta ku ringa janta a jiki don Asamu ta shiryu ba karamin lada zamu samu ba idan hakan ya kasance,
To Ammi gaskiya da tsorunta nake ji,
A'a kar ki damu

Suka fito Aisah tabar twins dinta wurin su sholi
Abin da ya basu mamaki Aisah tana hango mai fara sai gashi harda makiyarta a tsaya a saya

Yaushe ki ka hwara cin fara ne kam?
Ai da baki ci
Wallahi haka nan naji ina son cinta idan banci ba kamar hankali na zai tashi
Kai driver ka dakata bamu isa ba
  Tun daga nan take ci nan yaana take tamvayarta amma da dadi kuwa?
Ai tafi min dambun dawisu dadi,
Inaga idan muka shiga  kasuwa zamu samu danyarta sai a soya miki,
Kai wannan aikin wahalar,
Ai ba wahala na iya idan kina so sai na soya miki,
Kai Aunty yaana kar na saki wahala inaga kamar baba safiya ta iya kinsan *KATSINAWA* suma sun iya sarrafa fara,
   Kinsan mi na tuno Aisah
*KULKULE* miye kuma *KULKULE*?
Hmmmmmmm
Kar ki tuno min Amarya,
Haka suke kiran matar captain,
Dami ake yi?
Ana yinshi da busashiyar yakuwa da yajin borkono sai su maggi da kishiri,
Wasu suna saka kuli kuli kadan a ciki,
Wayyo Allah har naji inason sha
Mun shiga uku,
To Amarya kina son sha?
Ai kuwa dole a nemo miki, bamu isa da fitinar captain ba
Yanzu dai bari musai abin da ya kawo mu indan yaso sai mu duba wurin tsofaffi inda ake sai da su fara su yakuwa in yaso ma saya sholi tayi miki,
To Aunty

Shafa ce ta buga waya tana tambayar BINAZIR ko an fada mata sex din jaririn da tayi scanning,
Eh nayi scanning amma gaskiya basu fadin sex din ,
Wani kala ne kike so,
Inaga *SKY BLUE*
Kinsan sky blue sex din namiji ne ko?
Kai nikam inaso to,
Komai kuwa wannan kalar suka saya
Babu abinda basu saya ba,
Kayan sawan ne ma  suka aika wa *AUNTY SULAIM* ta sayo musu a lagos
Bayan dawowar su gida ne yaana ta shiga madafin Ammi ta gyara farar ta soya ta
Shafa ne suka kebe a dakin Ammi take ce mata mutuniyar anya kuwa ba karuwa aka samu ba
Wani irin karuwa kuma?
Inaga kamar ciki kike dashi?
Kai rufa min Asiri yara na ko wata uku basuyi ba?
Miye a ciki kuma?
Kai ina nikam babu wani abin da nake ji,
Hmmmmm
To Allah ya nuna mana
Amin
Ayya sannu da aiki Aunty yaana,
Har kin gama eh ai tuni yawunta ya tsinke
Ta fara afawa a bakinta  tare da  bismillah a kasan xuciyarta
Ammi ma ba'a barta a baya ba tasa hannu taci,
  Yaana ta karisa wajen yaakime,
Ina kika shiga tun safe?

Ina can tare dasu Aisah da shafa munje kasuwa sayayyar haihuwar Binazir,
Kut sayayya naga kina wani shishshige musu a tsammaninki zasu so ki ne?
Wani irin shishshigi kuma Aunty yaakime,
Eh mana to ni dai ki kiyaye,
abokan gaban nawa kike so ki hada kai?          Wallahi Aunty sai dai idan kice kika dauke su haka domin su ba haka suke ba kuma da dinma da na biye ki ina musu mummunar a fassara don ban zauna dasu bane sai yanzu dana ke mua'mala dasu na fahimci mutanen kwarai ne,
Kawai dai zargi ne Aunty kike musu
   bari ma kika anjima kadan zanje wurin Ammi domin ta ban kudi na sayo littatafan addini zata fara dora min, 
Ah kiyei a hankali dai Allah yasa ba shigo shigo ba zurfi suke miki,
Ba
Don Allah Aunty ki kwantar da hankalinki wallahi ba yadda kike zato suke ba mutane ne masu saukin hali.......
ke rabani har akwai wata kishiya da zata so ka
Ke dinma kawai saboda kin cika musu buri ne shiyasa suke janki a jiki,
Wani irin buri kuma?
Eh sabanin da muka samu mana kwanakin baya,
Ni kuwa Aunty da saduda kikayi kuka hada kanku zaifi

Ina  dai kyallu ce.
Da kanki Aunty kike cewa basu da mutunci
Kinje shiga dakin mama shatu kinji suna murna da yadda rayuwata ta koma
Har mama shatu na cewa ai ko yanzu bukatar ta ta biya
Babban bakin cikin ma da ba kice kika naskantaba,
Kuma duba kiga yadda kyallu ta karkace ta koma wajen su Ammi
ba don komai bane sai don yanzu yaransu sun taso Allah ya sanya musu Albarka a ayyukansu,
Kuma nan gaba sune masu daukar dawainiyar gidan
Shiyasa ta zubda makaman yakinta take shishshige musu,

Eh haka ne amma bari na fada miki ita kishiya ba yadda za'ayi ta soka da zuciya daya,

Ina ita kanta mama shatu har yanzu bata bar zagon kasa wa hajja ba,
Don dai kawai Allah ya daukaka
'Ya'yan hajja ne shiyasa ba yadda ta iya dole ne ta bita ko taki ko taso,

Kiga fah Alhaji shi yake dauke dawainiyar kowa har yayan kyallu bai bar su a baya ba ,
Komai zai musu kina ganin wannan ma ai dole ya hanata wani abun

Yauwa Aunty ke da kanki kin. Fadi haka
Don Allah ina rokanki kafin hakan yazo miki ki watsar da komai
Na tabbata ba bu abinda baza su miki ba
Kinga dai ba haihuwar zamuyi ba,
amma nasan a raina idan kiga watsar da komai ,
Komai naki zai tafi dai dai,
Tai ta nuna mata misalai
Da dai taga bazata saurare taba  sai ta tashi ta shiga ciki,
Ranar har dare yaakime na nazarin maganganun yaana
Gashi dai tasan gaskiya ne amma shedan yana mata huduba ta wani wajen
Da kyar ta fara gasgata zancen yaana
Tace bari ta gwada ta gani,

Ranar juma'a a an hadu a falon hajja 'ya,ya da jikoki ana ta raha da shewa sai ga yaakime ta shigo cikinsu ta zauna aka fara damawa da ita,
Abin mamaki sai ga bintu ta shigo Aunty yaakime wai mamanmu tana miki magana

Sai hajja tace ina mamar taki bata ga duk an taru ana hira bane,
Tana nan a dakin hajja
Wai kema kizo kuyi hira acan
Yaa kime ta ce kice mata ta shigo muyi ai nan dinma hirar ake yi

Ummi sauda kuwa ta harbo jirgin kyallu so take ta hana yaakime zama a cikinsu

Ita wannan abin yana bata mamaki
Ita kyallu zatai mu'amala dasu amma fir so take ta hana sauran muamala dasu,
Taso ace hafsee da saratu matar muhammad sun  daina kulasu amma hakan yaki ci

To yau kuma ga uwar gayyar yaakime ana zaune ana hira da ita.

Zuwan kenan da kyallu bata yiba
Har goshin magariba ta gabato
Hajja ta koresu tace zata fara lazumin juma'a kowa ya kama gabanshi,
Su sauda da Ammi sukayi Alwala suka shiga sashinsu
A lokacin ta shiga wurin kyallu,
Kyallu ta wani shareta
Ita ko da gangan tace dazu kika aiko nace ace miko muna hira kizo shiru ,
Uhmm
Lalle  yaakime yaushe kika zama sakarai ne kam ace ki rasa iinda zaki je hira sai cikin makiyanki
Don na tabbata su sauda da kaltum ba sonki zasuyi ba,

Ko miyasa ?
Saboda sun sha fada min basu kaunar ki,
Sai yaakime tayi dariya
Tace to idan basu sona ni ina kaunar su
Kyallu na kwance sanda ta miki!
Mi kika ce yaakime?

Abinda kunnenki yaji shi na fada
Sannu lalle wuyar ki yayi kauri yaakime

Kyallu tsaya kiji duk da munafurcin da kike musu bai hana kina shiga jikin suba
Kuma basu taba nuna miki komai ba,
Kar kice ban san abinda nake yi bane
Tas na sani
Lalle matar nan na miki hanya ki shigo amma kina min irin wannan zancen banzan,
Babu zancen banza anan
Kyallu ba tun yau ba na fahimci ba don Allah kuka sa na auri Bukar ba shiyasa tun da na fahimci hakan nayi watsi da duk wani abinda zaku bullo dashi na rungumi mijina domin itace hanyar da zata bullar dani zuwa hanya madaidaiciya,

Owk yaakime wato yanzu kinga dunia ta kare muku shiyasa kika nemi ki hada kai dasu makiyan naki saboda 'ya'yansu sunyi kudi ko,

Kice kika san wannan ni wannan bai damin ba
Da suyi kudi da kar suyi duk daya ne , 'ya'yan mijina ne,
Shatu data fito tace sai yau kika san 'ya'yan mijin kine marar kunya duk ina jinku hamshakiya
Ai kuwa inda **ALKAWARI RUWA BAZAI DAFA KIFI BA*
   Na nawa kuma *ANCE DA TSUNTSU YAYA SUNAN SHI*

Ai tuni kuwa yake dafashi yayi luguf
Har a samu aci.

Kyallu ta mike tsaye,
Saurara yaakime kar ki fara yiwa shatu rashin kunya da rashin mutunci irin na 'yayan talakwa da basu saba
Da arziki ba ai kuwa ta gama mike komai tunda har ta fiddo ke a kangin talauci har kika aure wanda har rayuwar ki ta kare bazaki iya auran shiba amma  har zaki zo kina sa in sa da ita
Ke auren da  ba don Allah  kuka shirya ba
Kuma bari na fada miki
Wallahi yanzu na fara son uwar mijina
Da mijina kun hanani na kyauta ta musu na samu Aljannata Allah wadai da halinsku

Bintu ta ci Wallahi baki isa kina ma wa iyayena rashin mutunci ina saura ranki ba

Kun haifa kuma zaku ga ranar haihuwa,
Bari kiji yaakime don bazance Auntyn ba
Wallahi koda rana daya kika kara shigowa nan kikace zaki ma wa mahaifiyata rashin kunya zan miki rashin mutunci da ba'a taba  miki irin shiba banza juya kawai wanda basu gaji haihuwa ba

Ai kuwa ta h
Gada tunda gamu nan 'ya'yan mijinta,
To maras kunya wa yasa dake
Anyi dani tunda anyi da matar ubana,
Bintu takai hannun zata mari Binazir  yaa kime ta kama hannunta idan kikace zaki tabata ranku idan yayi dubu zai baci
Yarinya da larurar ta zaki ce zaki mareta

  Wallahi mama yaakime barta ta tabani sai kinyi dana sani banza kiji da damuwar gabanki
Duk kannenki sunyi aure sun barki a gida da yake kin debo halin banza,
Ke dan uwarki waye me halin banza?
Inji  kyallu

Ke binazir wani kike fadawa hakan?
Eh na fada miki bintu

An fada miki kiyi abinda zakiyi

Yaakime ta jawo hannun binazir ta maidata dakin hajja tace zauna nan ki kyalesu da cikin ki kar ki biye su,

Hajja ta dakata da wuridin tace lafiya kime naga binazir a hannunki cewa fa tayi zata je wurin bintu karbar cassette,
Binazir tana huce take mayar wa hajja abinda taji tun farko
Naje  shiga kenan naji mama shatu na cewa wai su maman mu ba sonta zasuyi tsakani da Allah ba
Haba hajja ace rashin son zaman lafiya muraran
Yaa kime tace ki kyalesu kawai
Ta juyo wurin hajja tace don Allah ki yafe min hajja wallahi duk su suka kaini suka baro ne,
Musamman kyallu
Eh dama haka ne amma yanzu ma Alhamdulillah baki makara ba
Ki rike mijinki da  abokan zamanki
Kuma dama ni ban kullaceki ba
Saboda nasan sune suke hana ki wani abun, su kara ingiza ki,
Hakane
Tace kuje kuyi sallar ina son ganinku keda su kaltum da sauda

Bayan isha kuwa yaakime da kanta ta shiga dakin kaltum ta samu tana koyawa yaana fikihu
Suka dakata yaana tace Aunty lafiya
Lafiya kalau hajja ce take son ganinmu harda sauda
To bari na kira sauda na sanar mata

A'a ki tura yaana mana sai tazo mu tafi

Gaba dayansu sun hadu
Nan suka ga binazir a wani yanayi kamar na fushi
Ummi tace yana ganki haka yaata kodai abinne yazo
Ammi tai dariya amma kinsan yarki haka take ko yaushe fuSka a bace idan bata so ba
Sai kace wata Aisah
A'a inji Ammi binazir ce haka,

Nan hajja ta labarta musu abinda binazir ta fada mata  tare da dorawa dacewa  yaakime tace tana neman yafiyarku na rashin fahimtar ku da bata yiba
Sauda da kaltum suka kalli juna amma don Allah da gaske ne
Hajja,
tace na taba muku wasa ne
Can saiga Su Bukar da umar sun shigo gaisar da hajja suka samu wannan zaman
Har zuciyar Bukar ta buga sai yaji umar na cewa ko lafiya na ganku anan

Hajja tace lafiya kalau
Alheri ne
Matar kuce tazo neman Afuwa
Tare da Alkawarin zaman lafiya mai dorewa a tsakaninsu

Bukar yayi Ajiyar zuciya yace
Alhamdulillah
Allahu Akbar Allah ya jikan Alhaji kullum yana cewa nayi hakuri komai zai dai daita babu abinda ba zai wuce ba

Akai yafiya suka miki dama yana dakin yaakime ne
Yace ina abinci tace ni indomie naci amma bari na Aika yaana wurin kaltum naga sunyi tuwo
To nidai Allah yasa ki canza har cikin ranki
Insha Allah
Aka karbo mishi tuwo gashi miyar margi tayi,

Washe gari kuwa haihuwa ta Tasowa binazir yaakime taje gaida  hajja ta samu ana dambarwa tace  miye hakan kuma binazir?
Hajja tace yakin mata ne
Haihuwa ce
Kai Allah sarki ana wahala haka to aje Asibiti mana
،
Eh yanzu nake shirin neman sauda itace zata kaita asibitin
Tace bari na sanar mata sai mu wuce
  Tuni sauda ta dauko akwatin tafiya asibiti amma kar a fadawa kaltum
Tace to bari na dauko gyale na mu tafi
Sun tafi  basu kai awa ba ta haifi danta katon gaske,
Sai lokacin yaakime ta karbi number kaltum tace Albishir !
Goro!
Binazir ta sauka,
Aha wacece ??
Hm baki gane ba ko?
to nice yaakime gata nan  ta haifi danta kato mai kama da baanziye ,
Ikon Allah yaushe kuka tafi asibitin?
Awarmu guda,
Sai anjima zan kira Alhaji
Ta kira Bukar ta sanar mishi
A'a Allah ya raya shi bisa sunna
Sauda ce ta kira mijin
Yace yaya take amma
Lafiyarya kalau yanzu ma za'a rubuta mana sallama
Ina tafe insha Allah

Kafin sun dawo yaana ta daura tukunyar wanka a kofar hajja
Tuni zancen haihuwar ta karade dangi,

kyallu kuwa da taji labarin an tafi da yaakime asibiti sai hankalinta ya kasa nutsuwa ta tafi ta  samu kaltum tace mata
''Yanzu kika bari aka tafi da yaakime kina ganin har zuciyarta take kaunarku ?
to bari na fada miki bazata taba sonki ba balle abinda kika haifa,
Gwanda ma ki kiyaye,
Hajiya kyallu kenan bari na fada miki zuciya daya na dauke ta tun da balle yanzu wallahi nayi imani da Allah baxAta cutar da binaxir ba

Sai muryar yaakime suka ji tana cewa kyallu kinyi asara tabarya mai baki biyu,
Kullum kina cikin hadani dasu kice kar na kulasu ba zasu taba sona ba
Ashe kina zagayowa nan ma kina fada musu haka
Hmmmm ai ba tun yau ba

Wallahi Aunty kime da zan dauki abinda suke fadi a  kanki ai  bazan kulaki bama,

Amma  gwara da kikaji da kunnenki,

Kyallu tayi tsilli tsille da ido ta rasa abin fadi
Sai ga sauda ta shigo
Ta same su a haka
Lafiya na gan ku cirko cirko???????

Ta'aliki
Zaba
Watsa
                       U.K.B AZARE
🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

You are reading the story above: TeenFic.Net