28

Background color
Font
Font size
Line height

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
 
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼
          [ JIRE TILO]

(Daga kinta sai bata)

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah
       Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @[email protected]
🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
Addu'ar Neman Biyan Bashi

اللّهُمَّ اكْفِنِي بِحَلالِكَ عَنْ حَرَامِكَ، وَأَغْنِنِي بِفَضْلِكِ عَمَّنْ سِوَاكَ.
Allahummak-finee bihalalika 'an haramik, wa-aghninee bifadlika 'amman siwak.

27

Borno

Dawowar Alhaji malah daga oman ya kira hajja yace Yana ganin a fadawa matar shi kar sai abu yazo taji kwatsam,
Ban tari numfashin kaba Alh,
Inaga a bari sai lokacin ya gabato kawai tunda kaga ita dai ba cikakken hankali ne da itama ba eh da wannan kinga shiyasa har yanzu ban sanar da shatu ba domin nasan zata sanar da ita,
Tabbas kam
   
~~~~~~~~~~~~~~
Sauda ciki ya girma
Duk abinda ake bukatar a tanadawa mai ciki an tanada hajja da kanta ta samo mata ganyen ADURUKU maganin shawara BA YAMMA,
da kuma na rana,
Ta jika mata ZOBO tana sha saboda zaki ,
  Akai ta mata kwadon YAƊIYA tana ci,
  Alhaji ma ba'a barshi a baya ba domin ya sa malaminshi da yake daukan karatu a wurin shi ya mata tofi a cikin ruwan ZAM ZAM da fatan Allah ya saukaka mata nakuda,
da kyar take takawa har ana tsammanin ko yan biyu ne don ranar suna zaune da masu aikin surkayen nasu sai  mai aikin hajja tace ranki ya dade anya ba yan biyu zaki haifo ba cikin ya girma sosai kamar bana fari ba?
  Wai don Allah daina min fatan 2 dayan ma Allah ya kawota lafiya,
Yaa kime tace kai wane ita da haihuwar yan biyu,
Daso mai aikin shatu ta chafe tace ance miki yan biyu wasa ne,
Dayan ma dai Allah yasa ta fito lafiya,
Yaa kime tace Amin kam
Sauda ta murmusa tace insha Allahu lafiya zata iso,
Ai macece kenan,
Allahu A'alamu,
Cewar sauda
    Hmmmmm

    Haihuwa ta tashi mata cikin dare ta gagara  tayar da umar  don ta  sanar dashi jikinta sai rawa yake yi,
Sai safa da marwa take yi tsakanin daki da falo da dayan daki tana ta addu'oi
Ta daure tai Alwala tayi raka'a biyu  da niyyar Allah ya sauketa lafiya tana zaune sai taji kamar tunkuudo mata ruwa ta zabira akan sallayar da kyar ta miki,
Kunkuminta kamar zai fashe tsabar azaba da yake busashiyar nakuda take yi babu zaki ko kadan ,
Da kyar ta lallaba ta shiga daki ta nufi warddrobe  dinta ta dauko ruwan zam zam tasha ta shafe cikinta,
Ai kuwa abu ya taso gadan gadan babu kakkautawa
Juyi da umar zaiyi sai yaji kamar motsin rufe wardrobe din
  Sauda lafiya?
Lafiyar da sauki,
Miya faru?
Abin yazo,
Wani abu kenan?
Kira min hajja,
Kina nufin haihuwa?
Eh ,
Don Allah kiran hajja baya na zai tsage biyu

Ya saka jallabiyarshi ya fita dakin hajja  ya nufa ya fadamata,
Abinka da manya dama ita tunda la'asar ta lura sauda tana ciccije labba,
Shiyasa tun  karfe daya data farka,
Ta kasa komawa bacci,
Tana ta tsumayen su ko za'a zo a tashe su,amma shiru,
Ta dauko gyalen ta ta yafa tace muje naga idan ya isa kaiwa asibiti to a taso mariya ku tafi,
Shigarta yayi dai dai da dukawar sauda,
Umar dauko akwati da aka tanadi kayan jariran futo da ita bari na kira mariya,
Tashi sauda,
Hajja bazan iya tashi ba ,
Bayan gida nake ji,subhanallahi,
Hanzarta umar haihuwar ta matso
Sai jitayi sauda na HAUKALA, sai kukan jariri ya fito
  TaYI HAMDALA ,
hajja kam maria ta kira suka bude akwaiti aka fiddo reza da zare aka yanke cibi,
Mai jegon  suka jata gefe,
Aka kintsa su
Anyi sa'a akwai ruwan zafi a heater bayan gida aka wanki jariri da mai jego,
Kafin gari ya waye sunyi tsaf
   Shatu ce keda girki basu san mi ake ciki ba,
  Hajja kuwa bayan Asuba barci ne ya dauketa sai wajen takwas ta farka ,
Ta shiga ta fadawa shatu
Albishirinki  tace goro da yake ita shatu indai tana da girki sai kowa ya gane tsabar anna shuwa da farin ciki da take bayyana a fuskarta,
Kinyi maigida,
  Ban gane ba?
Saudatu ta haifa miki maigida cikin daren nan
To shine ba ko labari,
Ai cikin dare ne,
Kafin a tafi asibiti har ta haifo danta,
Allah shi raya,
Ki sanar wa Alhaji,
Kina nufin Alhajin ma da ya zama mishi dole bai sani ba?
Eh bacci ya kwashe ni kinsan umar ma yana kunya bazai fada ba,
Ina muhammad yazo driver ya kaishi gidansu sauda ya fada musu,
  Shatu ta shiga turakar maigidan tace mishi to Alhaji kayi Aboki?
Masha Allah kar dai ta sauka,
Eh amma tare mukai sallah da umar bai sanar dani ba
  Ta dai sa kai ta fita,
Ta tura mai akinta ta kira mata yaa kime idan ta tashi
Sawunta biyu bata tashi ba haka ta kyaleta,
Bukar da kanshi ya dauki jaririn ya kaishi falo wurin Alhaji akan Alhaji ya mishi huduba,
Alhaji ya umurci Bukar ya mishi,
Ba karamin dadi yaji ba,
Ya mishi huduba Alhaji yace ka mishi da sunan mahaifinta IBRAHIM,
kan kace kwabo gida ya cika da dangi da abokan arxiki,
Sanda bukar ya shiga ya ta sheta sannan yake sanar da ita saudatu ta haihu,
   Tab di ta haihu yaushe?
Mi ta haifa?IBRAHEEM,
    Allah ya raya ta sauko daga gado karfi sha biyu da rabi
Ta nufi wurin shatu tayi kalace, kafin ta karisa wajen mai jeko,
   Fir take daukan yaro wai bata iyaba,
Yan uwan sauda suka ce ai zaki koya idan naki yazo,
  Yasmeen tace Aunty nifa HAISAM xa'ana ce mishi,
Ba damuwa keda danki,
Nan dai ta gama kalle kallen ta ta nufi kofar shatu 
Ansha shagalin suna yan uwa sun nuna bajintarsu kwarai,
Sun samu abin arziki ta kowanni bangare daga gidansu ma Akori kurace makil da kayan mai suna dayar kuma da kayan gara bugu da kari sanda suka canza mata kayan daki da mota,
   Alhaji malah ma ba'a barshi a bayaba domin kyautar gidan mai guda ya mallakawa HAISAM,
tare da bude  mishi Account,.
Duk cinikin da akai a zuba mishi
TABDI JAM,
  Ai wannan abu kuwa ya kona ran su shatu da yaa kime karin bakin cikinta kuma da taga kyallu bata zoba,
Tai waya amma da yake baida kunya sai yace'ke da ganin kyallu inaga sai ta kawo miki jikarki,
  Ba kunya ba  tsoro ya fadi hakan
      
BIKIN BUKAR saura wata daya cif
Anata shirye shirye Alhaji kuwa zuwa lokacin ya gama tanfatsa muku gida na gani na fada
Gidan 'ya'yan nashi kuwa nagani na fada ya musu,
Ga dakuna birjik,
Amma  dakunan sashin bukar yafi na umar,
Shashasha kuwa ko a jikinta tana jira ya cike mata dakuna  da kayan daki dana Alatu,
Sai dai abinda ya bata mamaki bai wuce ganin kaya da aka zuba a dayan bangaren kayan kyale kyale kuwa ba'a magana daga can oman akai ordering dinsu wani abin ma basu san shi ba,
Saura sati biki
Alhaji ya kira shatu da sauda hajja kaka dama tana zaune,yake sanar dasu karin auren Bukar,
Tare da shaida musu jibi ne tafiya shatu da Aisha da yaakura ne masu tafiya sai matar Alhaji Bukar kachalla uwar goyon hajja, a mata kenan
Baba kace min tatsuniya ne,
Yaa kime hakuri zakiye kuma ki rike girmanki,
Mama shatu kina ji za'a min kishiya, kishiyarma balarabiya, tasa hannu aka ta rafsa kuka,
Shatu tace tashi kime hadin baki ne da munafurci shiyasa aka hada baki ake shirin maki kishiya
Alhaji dai bai tsaya yaji mi zasu ce ba ya sa kai ya fita,
      Mama shatu kiyi wani abin mana,
Mi zance ai da inada mutumci baza'a boye min ba,
Kisha kuruminki ina dai so ake a tozarta ki don iyayen ki masu karamin karfi ne,
   Alhaji ya shigo shatu  ki fara shiri don jirgin safe zaku bi,
Babu inda zani kana son naje dinne ka boye min,
Ita gwanar taka da ka yarda da ita sai taji,
Haba shatu a gaban sirkayenki kike mai dawa Alhaji martani ai inaga bai dace ba,
   Kyaleta kawai hajja ai dama ba girmana take gani ba
Tafiya dole, don ba ke kike  iko da kanki ba,
        Yaa kime kuwa kanta ta mara so take ta tabbatar da gaske ne ko mafarki,
    Hajja ko kallonsu batai yiba ta wuce ta barsu anan,
Dama sanda na fada miki tunda suka san bazan haihu ba baza su barni ba sai sun kawo mai haihuwa wayyo na shiga uku,
Wallahi mama da Bukar yamin kishiya gwanda ya fadi babbar mota ka take shi yafi mishi Alheri
Nayi takaba,
domin rantsuwa nayi wallahi tallahi, Bukar ba dai ya zauna da wata ba bayan ne,
Zama kuwa ya zama dole,
Yo idan ba dole ba wa zai zauna dake,
Ke ba tsafta ba,
Ba kuma gyara kika iyaba,
  Girki wannan baki mishi, kullum ya kare a neman Abinci a wurinsu hajja.

Ke idan ba don Yayan bama  wa zai iya zama dake,
Shatu tace umar harda ni zaka hada ka ciwa mutunci ba itaba nikam a wani dalili kuke sa ido a hidimar Bukar da iyalenshi,
  Ko saboda kun raina mata wayo ne,
Ita yar talaka ko?
  Mama inaga TALAUCI BA HAUKA BANE KUMA BA AIBU BANE
Talaka da mai kudi duk dayane ,
Matukar talakan ya rike kanshi,ya rike talaucinshi, bai banzatar da kanshi ba,
Miye aibun talauci 'ya'ya nawa ne na talakan suke da halin karamci da girma  mi ya hada aure da talauci da arxiki amma sai kuce ana kin yaa kime Saboda talaucinta inaga itama da zata bi dokokin auren da ta zauna lafiya, ta rungumi   aurenta a matsayin IBADA tagani mana ai babban jigon zaman gidan aure sune:
TARBIYA LADABI BIYAYYA HAKURI JURIYA, sune manya manyan  makaman da suke dauwamar da mace cikin gidanta da kuma wurin mijinta kai harda ma wajen yan uwan mijinta ,
Idan kina son ki gyara zaman auren ki baki makara ba,
Tun kafin wata tazo kice an mallake shine,
Yasa kai ya fice,

     Shatu ta kamo hannun yaa kime suka fita ammafa duhu duhu take gani,
Kishi bala'i ne
Ta kira kyallu tana kuka ta sanar da ita,
Tace yayan ne zai kara aure!
Kai sai dai idan sashi akai,
  Haka nake gani nima,
Amma na dade da gaya miki cewa hajja da 'yayanta basu sonki kinga dahir yanzu tunda sun kwakwabo miki kishiya,
Kishiyar ma Balarabiya,
Balarabiyar ma yar Alh saalim wanda shine silar dukiyar mahaifinmu aikuwa sai a hankali ga shi lokaci ya kure,
    Ta ajiye wayar dama da wayar dakin shatu ta kira kyallun,
Ubangiji Allah yasa ya mutu kafin auran,
Shatu tace kar ki mishi fatan mutuwa,
Bala'i da masifa zaki tanada mishi da A duniar ma sai ya kwammace kida da karatu akwai hanyoyi da dama,da zamu bi mu kuntatawa zamansu wanda sai ta zama banza,na miki Alkawarin sai kashi ya fita daraja a wurin Bukar share hawayenki maza kar ki damu,
    Rannan dai anan ta kwana suna sakawa suna kwancewa, washe gari kuwa sammako tayi ta tafi gidansu domin ta sanar musu,
Rabon da taje kuwa har ta manta saboda ta auri zuria masu kudi sai take kyamatar  yan uwanta,
Tunda mahaifiyarta ta ganta tasan akwai matsala,
Yaya dai uwata?
Wai balarabiya zai aura min,
Mtwssss to ko yar sarkin santan bul ce karewa kyau, a tafin hannun mu suke,
Iyayenta ne fa iyayen gidansu Bukar da mahaifinshi,
  Ke idan yau akace miki yar gidan karuna ce zai aura tsabar dukiyar Su to tazo mu zuba dan ubanta sai ta koma kamar dodanniya a wajen shi kedai sake bakin Aljihu shiyasa idan nace miki ki kawo wani abu ana nema miki hirzi kina ganin kamar zan ci kudin kine,
Ai ko nawa ne indai za'a fasa auren nan zan bayar,
Yanzu dai ki nutsu kici abinci mu tafi wajen malam na kogon tsamiya ,
To, na koshi,
Mu tafi,
      Anje an bata sharudda iri iri a cikin sharuddan akwai rashin yin sallah na  biyu kuma banda taba qur'ani  idan kuwa ta  kuskura ta shafi  ko da shafin qur'ani , to ya  karye bazai yi aiki ba,
Ta sake mishi kudi, suka kara wuta hankalinta ya kwanta anata shirmen
      V hankalinta kwance,
Da cin mutunci shatu. Ta yarda suka tafi oman,
Taje  taga harkar Arxiki, tana jin kanta ita wata  ce, amma dole ta raina kanta BABA MA DA BABAN SHI,
GABA MA DA GABANSHI WAI ALJANI YA TAKA WUTA, nan ta rsina kanta yaa kuraa kam sun zama yan gida itada Aisha sai fantamawa suke yi,anyi hidima anyi komai lafiya amarya ta samu hutu a college za'a tafi da ita nigeria.
Wadanda suka je kuma an mallaka musu motoci, Taga danginshi kafin su koma hutu,
  Sun sauko nigeria cikin Aminchi da salama Amarya an saukar da ita a side din hajja kafin a karisa da ita kofarta,
        Yaa kime kuwa duk da tana da yakinin auren zai warware domin bokan ce mata yayi a daren farkonta zai sake ta matukar tabi kaidojin nan don indai alakar ma'aurata ta shiga tsakaninsu to zance ya kare,
     Nan Alhaji ya tarbesu ya musu fada duk da ita kulsuum larabci ya mata,
Yaa kime da bukar kuma hausa,
Nan ya mika mishi abu yace gashi nan idan ka rike wannan ka rike abinda yake fadakarwa akai ka gama yace hungo kime mika mishi ,bata san miye ba ta karba ta mika mishi dayake a cikin wani akwati mai masifar kyau da qawa yasa hannu ya karba,
   Aka raka Amarya sashinta tare da rakiyar su sauda yaa kura, Aishatu,
      Ango dai ya tare da Amaryar shi lafiya kalau yaa kime taga shiru babu alamar korar Amarya,
     a cikin kwana  bakwai ango  sanda ya canza saboda Amarya bata yarda da ayi Abinci a kawo ba itace take yi samfuri samfuri kansu kuwa ya hade da sauda,
Duk da cewa sauda ta girme mata amma ta kwantar da hankalinta domin taci riba,
      Yaa kime ta koma wurin malam na kogon tsamiya,
Yace kin karya doka ai,
Ke kuma ki bude abinda surkin ki ya baki daren da aka kawo Amarya ki gani,
Kuma Aljanu sunce bazasuyi tafiya dake ba tunda daga farawa har kin saba musu,
To yanzu babu yadda za'ayi kenan,
Kinga kiyi sauri ki tashi ki tafi don na aikesu ne idan suka zo suka sameki zaki dandana kudar ki,

  Ta koma gida ta shiga dakin  Bukar mi zAta gani,
ÀL QUR'ANNNUL KAREEEEM

YI TA'ALIKI
ZABA
WATSA

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

You are reading the story above: TeenFic.Net