11

Background color
Font
Font size
Line height

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

🖕Gaskiya dayace 🖕🏼
( daga kinta sai bata)
  

✍🏼✍🏼✍🏼
  Kulsum Bappah
        Umm Iman
        
  
            TUNATARWA!!!
ADDU'A AKAN ABOKAN GABA
  
ALLAHUMMA MUNXILIL KITABA SARI'UL  HISABA IHZAMUL AHAZABA ALLAHUMMA IHZAMHU WA ZULZULUHUM.

  Kuna heart dina yan dakina💙❤💛
Sameera muhammed
Mrs sulaiman
Aishatu Halilu
Mrs Abubakar
  Allah ya bar kauna 💞💞💞💞💞
  
11
      Kan ubancan!
     Furucin yaana kenan,
   Yaa kime duk iya kokarin ta cije abu ya faskara, tace durun uwata inji matsoraci.
    Nan Alh Umar yace ya zaku mayar mana da gida kamar na maguzawa,
    Yaa kime tace sam bazai yiwu ba,
    Kanwartawa guda daya,
    Ina!
Adda Aisha tace yanxu ke kime a gaban hajja kakar kike wadannan zage zage idan baki ji kunyar idon mazajenku ba , ai gyaji kunyarta,
  Yaa kime ta rasa abin yi,
Nasan wannan duk munafurcinki ne, ta nuna kaltum,
  Yau mi zan gani Bukar? A gabana iyalanka suke haka,
     Ya rasa yadda zaiyi don kullum Kime ta mishi rashin mutum ci idan ya fadawa hajja kaka sai tace yayi hakuri,
      Kafin ya bude baki yayi magana tuni ta ja hannun kanwarta yaana da fuskar tai chaba chaba da hawaye, zo mutafi ayi mugani.
      Alheri zamu ga inji umaru,

Yaya wai dama matar nan ba rusuna tayi ba ai ni nayi tsammanin yanzu tayi hankali,
     Saudat tace tana nan yadda ka santa a baya, 
  Kaltum ce bata biye ma ta amma idan son ranta ne kullum ana cikin tashin hankali da hayaniya,
      Yaya Allah ya kara maka hakuri!
     Hajja kaka tace ka cigaba da hakuri kema kaltum Allah ya kara miki hakuri,
     Ita ko kyallu da yake tafi yaa kime hikima da wayo sam bata nuna abin ya dame ta ba,
Allah kadai  ne masanin sirri, masanin gaibu amma da zata amayar da kunci da takaicin da take ji a zuciyarta kai da sai tafi yaa kime rashin hankali.

Aisah kuwa da kyar take futar da numfashi.saboda bata taba kawo haisam A ranta ba, domin tana daga cikin wanda suke tsammanin binazir yake so,
   Binazir kuwa sai washi bake take, tuwonta manta,

      'Ya'yan kyallu kuwa sai harare harare suke yi kana ganinsu kasan hassada suke muraran,
      Can hajja kaka ta numfasa tace,
Kai mai zamfara yaya za'ayi kenan?
Umaru inaga zamu nemi Adire shinsu sai kaje neman auren .

   Nan Adda Aisha ta fara barkwanci.
    Umaru kasani gidana zaka xo neman Auren chiwu na, kuma ban dauke maka, komai ba da ake yi na Al'adah
   Kaltum ta lura da yanayin da Aisah take ciki.
Tana Allah -Allah kar a gane,
Saboda tasan za'a rina tunda ba dama ai mata zancen aure sai ka ga nan da nan tayi kicin kicin da fuska.

    Binazir kuwa ta fara cewa yauwa Aunty yaakurah mu kuma sai mu fara zancen fidda anko. Ko bintu? Yaa kura? yaakura  yar Adda Aisha ce, ita bare take aure
tace eh sosai ma inada kawa a england a kamfanin sheraton inaga zam mata waya ta turo mana latest din AURA WAX.eh
Aunty harda lace zamuyi fah,
Nan suraj yace ke gandoki ba'a sa rana ba har kuna shirin anko,rashin hankalinki.

Yayi yawa, saudat tace kul daina taba min 'ya kasan zan saba maka, nan ta jawo binazir ta kwantar da kanta a kafadar ummi saudat
ke kuma  Yaa kurah harda  daurewa karya gindi.
      Bintu kuwa kamar basu wurin,
   Nan aka cigaba da tattauna lamurra, Aisah kuwa Allah -Allah take a watse ta zubar da kwallan da ya taru mata,

  Wallahi da ba don cin fuska bai da amfani ba, da ta disga shi,
Kuma ta kara daurewa ne, saboda makiya tasan tana cewa uhm, sun samu nayi,
Kuma mahaifiyarta bazata taba jin dadi ba, uwa uba ummi tana son su tsakani da Allah,
Bazata taba bari a fahimci halin da take ciki ba.

Saboda kullum a cikin gwasale ta yake,
     Shiko haisam satar kallonta yake,
  Yana tunanin ko zaata ki amincewa.
    Ya dai kasa gane miye a fuskarta,

  Saudat kuwa kamar wacce akayiwa Albishir da Aljanna saboda danta ya zabi Aisah , Aisah akwai nutsuwa da sanin ya kamata. Indai akace tazo hutu to haka kawai zata na shiga. Wurin ummi ( saudat) ta gyara mata daki domin saudat da kaltum basu yarda da mai aiki ta gyara musu daki, ko dakin maigida ba,
Aisah har wardrobe dinta take gyara mata.
   Shiyasa farin ciki a wurina kamar yau sallah.

      Taro ya watse da nasiha da bada hakuri akan zaman tare, da kuma gargadi akan rarra buwar kawuna.
A kullum hajja kaka tana tunasar dasu da su rike gaskiya duk rintsi duk wuya takance musu
'' GASKIYA DAYA CE DAGA KINTA SAI BATA.
Tace ba'a taba cewa GASKIYAR ka ta kare sai dai ace karyar ka ta kare.

   Aisah  ce ta fara mikewa nan ta fara jin kamar jiri yana son ya debeta nan ta rintse ido tana ganin jiri jiri har ta bar shiyar hajja kaka
   Nima na tattara ya nawa ya nawa nayi dakin yaa kime,tabdi jan
Tashin hankali da ba'a saka mishi rana 
Yaana ce take ta risgan kuka kamar ranta zai fita.
Talatu mai aike ne durkushe tana jin bala'i da kata'in da uwar gijiyarta take mata.
Dan ubanki yaya akai haka,
  Allah haj naje,
Sai dai idan Aunty yaana bata bi dokokin abinda akace tayi ba,nasan boka nakan dutse ba yadda za'ayi yace abu, bai kasance ba
Dan kutumar ubanki nayi
Maza ki tashi ki koma kice mishi aiki bai yiba, kuma inaso idan kinje ki hada ni dashi tunda she baya rike waya, nan ta mike cikin hanzari don dama kamar kace mata chassss ta zabura take ji

    Jikinta yana rawa ta fita, tana tunanin tsohonta yana kasa ana narka mishi zagi wai harda yaana yar da take ganin ta haifeta kwadayi mabudin wahala! yanzu mai aikin kaltum da saudat kullum suna cikin nutsuwa, da kamalar su kasancewar daga iyayen har 'ya'yan babu wanda zaka ji ya musu magana cikin daga murya.
   Shegiya kwalelenki. Gwanda ma da aikin bai yuwuba banza mummuna,

Tune mai keke napep ya tsinkayota yace ke kuma da wa, hmmm tai kwafa ba komai ya sauketa tashan dambua ta shiga mota,

~~~~~~~~~~~~~~

Aisah hankalinta ba karamin tashi yayi ba, amma kasancewar ta samu mahaifiya ta kirki. Tai ta mata nasiha har zuciyarta tai sanyi, haba abin ki yiwa Allah godia ,
Minene aibun haisam ga nutsuwa ga sanin ya kamata, bari na fada miki duk wanda ya so ka Aisah ya gama maka komai,
Masoyinka koda wasa yake yafi makiyinka.
Ana haka sai ga Adda Aisha tazo.
Ta zauna Adda Aisha tace takwara na lura da yanayin ki kamar akwai matsala ko. Ta goge hawayen tace babu,
Ki daure kibawa marada kunya haisam bashi da makosa ko kadan kaltum tace nima abinda nake fada mata kenan
Yauwa chiwu.
Goge kwallar ki kar wani ma yaji Addu'ar Alheri muke muku gashi Allah ya amsa mana naji dadi sosai.
   Sannan yanzu yaya za'ayi da kawarkin tasan maganar ne?
A'a bata sani ba to yanzu miye Abinyi?

Ana haka sai ga baanxiye ya shigo yace ni banson na fara  hira da ita sai na nemi izinin iyayenta  kamar yadda sharia ta tsara.

Kayi gaskiya.

Inaga yanxu abinda za'ayi plan zaku shirya mata. Ki kirata kice mata wani dan uwanki ya shiga matsala da EFCC shine kika tuno yayanta shine BOSS ku zata ba da number, shi ko kuma kice mijin yar uwarki tunda tasan mazan familyn mu basu aiki gwamnati, eh inji Adda Aisha hakan yayi yar bado mai wayon tsiya
Baanziye yace eh haka za'a binazir,
  Ai kuwa nan Aisah ta kira shafa bugu daya. Biyu ta dauka,
Kin dawo ne, a'a sai gobe insha Allahu, Allah ya kaimu
Yaya gida su Ammi? Ina binazir iyayen surutu? Ai surutun ku daya ne da ita,
Ko to waye zai kunshe baki  kamar ki,
Kinsan miye? Sai kin  hwadi,
Wani matsala ne ya taso wa mijn sister dina yar yayan Babanmu wacce nace miki naci sunanta eh Adda Aisha ko? Yauwa to mijnta yarta da yake anga yana samu sai mahassada sukai shunin shi wa EFCC shine kika fado min, aiyya duniya kenan kana tare da makashinga baka sani ba,
Dunia kenan Allah ya raba mu da magauta, nan suka ce Amin.
     Tace to bari na fadawa yayan ko? Ko kuma kun fi son na baku number ne? Eh toh yadda kika gani,
Bari na turo muku number shi ki gaida su Ammi Kawata binazir Adda Aisha, ji ki kamar kin sansu, to ga Ammi ku gaisa,
   Assalamu Alaikum,

Ammi ina yini, lafiya, yya karatu, Alhamdulillah nagode,
A dage ayi karatu ko shafa'atu,
Insha Allahu Ammi nagode Allah ya jikan magabata.
Amin tace Amin summa Amin sai binazir ta karbi wayan, Aunty shafa kina lahiya? Hahhhha kina zolayata kenan, to lahiya lau, nima zan koyi  kanuri ai, tabbas zaki koya Antinmu, ai zamu zo gamborun ngala nan da wattanin  inaga biyat, ko to.
Sukai sallama ta kashe wayar, 

       Nan Adda Aisha take cewa na fada miki tunda tare da Aisah suke ba matsala kiji yadda ta rusuna da kika karbi wayar,
To yanzu kwafe min number zaki yi na kaiwa babanki umaru
~~~~~~~~~~~~~~

  Alh ummaru  ya kira ba'a daga ba har sau biyu, yace wata kila bai san number bane sai ya rubuta masa sakon kar ta kwana, .
   Umar Malah sharif ke kiranka, ya tura bai fi sakan biyar ba sai yaga kiran EFCC BOSS,  da kanshi
Suka gaisa yace dama yana son yaji ne, ko yana da lokacin ganawa dashi gobe juma'ah saboda zasu tattauna akan wata muhimmiyar magana,
Nan ya bashi tabbacin yana nan  tare da Alkawarin da kanshi zai je Air pot ya dauke shi,
Masha Allah nagode
Sukai sallama.
    Mamaki ne ya kama Alh Bashir
Yau Mala's ne suka nemeshi, ya ringa tunani kala kala, Allah ya kaimu goben naji da mi yazo.
~~~~~~~~~~~~~~
    
         
            ABUJA
Karfe goma dai dai jirgin ya sauka Da yake da private jet ne shiyasa Alh Bishir baiyi wuyar gane shiba cikin girmamawa ya tarbi bakonshi,
   Sun danyi tafiya mai tazara nan umar yayi ta ganin gidajen mayukansu ana ta hada hada domin kuwa babu gidajen man da zasu iya takara dasu, a fadin nigeria, ko A.A RANO da SHAFAH oil & gas bAsu  kaisu farin jini da daukaka ba.
    Ya kaishi gidan shi ya gabatar mishi da abin sha,da yake harka ce ta manya ruwa kawai ya sha,

nan Alh umar ya numfasa yace, Abinda ya kawo ni wurinka magana ce akan neman kulla sunnar ma'aiki( S.A.W)
Alhamdulillah
Danmu yaga iri a gidanka yana so,

Masha Allah.
  Wacce daga ciki?
Inaga tana makaranta  A Alaqalam,
shafa'atu ce, ah toh Allah ya sanya Alheri, ina murna kaunatace amma hannuna tattashi. Alhamdulillah Allah ya sanya Alheri nayi murna kwarai,
  Kuna yanke sadaki ne?
bamu yankewa kuma bamu karba sai wurin daurin aure.
To masha Allah yayi kyau. Abu guda ne ya kamata yaje can gida ya gaida iyayenmu,
Ba damuwa insha Allah zai je
  Batun rana kuma zan nemi kannena muyi shawara zan sanar dakai,
Eh ba damuwa yayi Allah ya kaimu,
Amin
Allah ya nuna mana
Amin
  ya kaishi Airpot suka tafi cikin mutunta juna.
    
Tafiyar shi keda wuya ya kira su gwoggo ya shaida musu, yace anzo neman auren shafa ta ce Alhamdulillah. A ina mijin yake? Yace maiduguri, nace musu zasu zo su gaida ku, eh ya kamata

Yaushe ne zasu zo? saboda mu shirya
Eh zan tambaye su.
   Inno bata san mi ake  ciki ba
a yata tai miji. Inno ta kau da kai wai ita kunya.......

You are reading the story above: TeenFic.Net