Page Thirteen

Background color
Font
Font size
Line height

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*

*Zeeneert*@wattpad

*You might not be able to understand somethings indai baki/baka karanta Rayuwar bintu ba. This's the continuation of that book though a different story line somehow. Abunda kadai zan iya fada muku shine this book is connected to Rayuwar bintu. To get a better glimpse of what I'm writing currently I advise you read Rayuwar Bintu first. Thannk you and happy reading*. 😍

*Page Thirteen*

Yadaga kafa zebi bayanta wayarsa tashiga ruri,maida dubansa yayi kan screen din wayar,Captain Abbas ne kekira,A soldier like him though with more experience as compared to him. Chief of Army ne yahada su awaya yace yaje yasame sa su tattauna akaan case din Alhaji Sammani din yanaso yarakashi,Captain Abbas ma mutumin Adamawa ne,he lives with his family and newly wedded wife here in Yola. Ajiyan bayan Chief of Army yahadasu sunyi akan Muzammil zeje har gida yakaimasa file din case din yagani,picking call diin yayi aransa yana tuhumar kansa da rashin cika alkawari,daman da yanman nan bayan yayi dropping Mami yaso yaje yasamosa sekuma ya tarar da surprise partyn da sukayi masa din. Sallaama yayi a wayar inda Captain Abbas ya amsa daga daya bangaren suka gaisa Muzammil out of guilt yace "Captain kajini shiru koh?" Captain Abbas yayi dariya playfully yace "wallahi kuwa nace ko batan kai kayine barina kira inji" Muzammil yace "Banma tahoba,something came up I am sorry anma nan bada jimawa ba zan karaso insha Allah" Captain Abbas yace "Haba baakomai wallahi. Just take your time anytime katashi I am available" Muzammil yace "Thanks for Understanding Captain" Captain Abbas yace "Bakomai sena jika, Umar koh?" Muzammil yace "Yes,but people call me Muzammil" Captain yace "Toh Muzammil senajika" daganan sukayi sallama. Muzammil garden din yakoma yasamu su Ameera sunfara tattare kayansu curiously yace "Angama picnic dinne?" playfully Ilham tace "Celebrant ya gudu yabarmu yaje yana soyayya toh mezamu zauna mu jira?"Muzammil murmushi kawai yayi batareda yace komai,yasan wanene Ilham indai afannin neman tsokana ne and he don't want to drag it further,bayason yawan hayaniya,wanda sukayi dazuma yanzu haka yana neman yasakamai ciwonkai. Ameer knowing him fully seya dafa kafadunsa yace "Don't mind your Aunt Muzammil,time din tafiyarmu ne yayi. 6pm Daddynku yace mukomaa gida and it is past 6 already" gyadakai kawai Muzammil yayi ayayinda Yan matan suka cigaba da tattare kayansu Mazan nakaiwa mota. Can anzo za'a nade carpet dinda suka zauna akai ana tattare kayan dake kai Ammi tayi spotting side bag din Mami,dagawa tayi ta lankaya a wuyarta sannan tadubi su Ameera tace "nikam ina Addah Mami ne?" Fa'iza tace "Nima tundazu nakeson intambaya bakina yayi nauyi" Ameera tace "May be tanacan waje gurinsu Hamma Sagiru" dede lokacin Muzammil yashigo garden din daukar wani kaya, Fa'iza tace "Yauwa Hamma Ina Adda Mami?" glancing dinsu yayi gabadaya to makesure dagaske Fa'izan take bawasa ba sannan yace "isn't she together with you people?" Ameera tace "dazu daka fita batabi bayanka ba?" Muzammil yace "but she came back here afterwards" Deenah ta girgiza kai tace "Tunda tafita bata dawonan ba may be dai tanacan gurin mota taredasu Hamma Sagiru" Muzammil yace "she's not there dagacan nike" Ilham trying to calm them down tace "Barina kirata may be she's somewhere around toh",dialing number Ilham tayi yana fara ringing sukaji rurin wayar acikin jakar Mami dake hannun Ammi,Ammi tace "Cab aiko ga wayar tabari cikin jaka".

Kallo daya Muzammil yama jakar sannan yajuya yafice a garden din cikin sauri,gurinda yatsaya yayi waya dazu tasameshi yaje yaduba batanan,komawa yayi zaidubata nearsides din garden din yahadu dasu Ilham sunfito daga cikin garden din suna nemanshi,Ameera naganin shi takarasa inda yake tana fadin "Yauwa gashinan,Hamma kaganta ne?" atakaice Muzammil yace "Banganta ba" daganan yawucesu yacigaba da looking around ayayinda suma sukebinshi a baya suna dubawan,can wayar Waleeda tayi ringing,Sagir neke kira. Waleeda tace "Nasan sunga bamu fito bane yasa suke kira barina cemasa muna neman Mami ne they should also look around" cikin sauri Muzammil yatsayar da Waleeda yace "No karkicemasa komai,you guys should go ahead zanjirata mukoma gida tare" Ameera tace "But...." Muzammil yayi sauri yakatseta yace "Banason musu Ameera,just do as I say" haka dole Ameera tayi shiru suka juyo suka tattare sauran kayan a garden after Muzammil yamusu warning karsu fadama kowa ba aga Mami ba,he has this feeling she is just somewhere around so by telling su Sagiru daga hankalin mutanen gida zasuyi unnecessarily tunda basu kadai sukazoba,many of their cousins are here da bazakasan sanda wani zaiyi splitting zancen out ba. Allah yataimaka ma yasu yasune dasuka tsaya tattare sauran kaya sauran duk suntafi gurin motocin dasukazo dasu. Muzammil bayan tafiyarsu Ameera inda sukayi parking yaje yaduba batanan inda daganan yawuce can main gate na park din yama securities din gurin describing Mami dakalar kayan datasaka wai ko Allah zaisa sunga fitarta sukace basuga maikama da'ita tafitaba gaskiya. Komawa cikin park din Muzammil yayi,yaduba restaurants,yaduba playing ground,yaduba shopping mall daduk wani guri dayake tunanin zai iyasamunta acikin mall din anma babu ita babu labarinta,gashi yanma tayi sosai anata kiraye kirayen sallar maghrib a nearby masallatai.Ayanzu hankalin Muzammil yafara tashi,soyake yakira gida yaji ko Mamin nacan anma tsoro yake kar ace batacan din which might also lead to tayarwa mutanen gidan hankali and then Khalipha seya fadomai arai, he's so calm just like him bayida hayaniya. Ba kasafai Magana kefita abakin Khalipha ba sabida haka yayi deciding yakirashi. Over 10 calls yamai beyi picking ba,yana shirin sake dialing number segashi yakira rai bace Muzammil yadaga yace "wai inakashigane inata kiranka bakaa picking?" Khalipha yace "ina masallacine yanzu muka idar da sallah Hamma" Muzammil yafurzar da iska yace "Okay did you by any chance see Mami at home?" Khalipha yace "No bakuna tareba?dazu naji su Adda Ameera nacema Hamma Sagiru zakubiyo mu abaya" in dismay Muzammil yace "she is not here with me Khalipha,I lost track of her don Allah kaje kadubamin cikin gida kota dawo and don't infoirm anyone about this" Khalipha yace "toh" and few minutes later sega Khaliphan yakuma kiran Muzammil yace "She is not at Home Hamma Muzammil" Muzammil katse call din yayi batareda yace masa komai ba,can main gate yakoma this time telling the securities asalin abunda yafaru,hankali tashe securities din sukahau jimami,daya daga cikinsu yace "Ikon Allah!ina tashiga toh dannidai tun bayan sallar la'asar nake zaune anan anma banga wani mekama da yarinyar daka mana kwatancen tawuce tanan ba gaskiya" wani security yace "Kuma kowani mota yashigo kozaifita semun duba cikinsa da wajensa batareda munyi la'akari da ko wanene mutumin ba"Another security yace "Abarma wannan zancen dan tunda aka bude gurinnan nake aiki dasu kuma abu mekama da wannan samsam betaba faruwa ba. Nidai nafi tunanin tana ciki awani gurin dabai duba ba sabida haka muje aduba dakyau" haka suka kwasa suka koma cikin park din,Security daya kawai suka bari a main gate din. Muzammil dawani security garden din suka sake dubawa Mami batanan,suna fitowa security yanuna ma Muzammil bayan garden din yace "Kaduba bayan nan kuwa?" kallon gurin Muzammil yayi ayayinda yagirgizama security kai alamar a'a sannan cikin sauri yanufi gurin dukda kuwa aranshi baya tunanin Mami zataje wannan gurin dakanta sede inkaita akayi dankuwa gurin dajine sosai eventhough acikin park din yake and to his utmost surprise yana isa yahango frame dinta zaune kan wani old used Dam haka tajuya masa baya,ledan data bashi dazu yaki karba yana ajiye gefenta akan Dam din. It looks like she's deeply into her own thoughts.

Muzammil besan sanda yasauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya ba sanda idanunshi suka sauka akanta sannan cikin sauri yakarasa inda take,rai bace ya fizgota yana fadin "What the hell are you doing here?do you know how crazy I almost went looking for you?"Mami tangal tangal tayi zata fadi sanda Muzammil yafizgota wanda hakan yasa tayi saurin riko rigarsa for support,seda ta tabbatar she is safely standing on her feet sannan tasakeshi Muzammil yace "Ba Magana nake miki ba?bakida hankaline zakizo kizauna a dokar dajinnn kekadai hardare munacan muna nemanki kowa hankalinshi tashe" nanma shiru batace masa komaiba. This time reducing the echo of his Voice Muzammil yadafe kanshi yace "For goodness sake what's wrong with you Mami?" Dede lokacin Security dinda suke tafiya tare ya iso,ganin Mami seya Fara hamdala yace "Masha Allah ansameta koh?" Sekuma yamaida dubansa ga Mami yace "Kekuma baiwar Allah meyayi zafi zakizo kizauna a dokar dajinnan kekadai?" Mami ko kallonshi batayi ba bare yayi tunanin samun amsa daga gareta.

Muzammil da shirunta kesake konamai rai looking pissed off yace "Tunda bazakiyimin magana ba seki wuce mutafi gida inmunje can kyayima su Abba bayanin dalilin dayasa kikazonan kikazauna kekadai Kamar wata marar gata" daganan yajuya zaitafi.

Kuka maisauti Mami tafashe dashi wanda hakan yasa Muzammil saurin juyowaya yana kallonta baki sake, Mami cikin kuka tace "Niwai menayi maka ne kake treating dina as if I'm your enemy?" Muzammil in disbelief yace "Like seriously! Sabida namiki fada Ina fada miki gaskiye shine nazama makiyinki? Because I care for your well being shine nazama enemy dinki koh Mami?" Mami still crying like a baby gabadaya hannayenta tayi folding dinsu a fuskarta tace "Aigaskiya ne,you never care Hamma imma kadamu dani ada toh yanzu kadaina" and this time dole Muzammil yakoma kusa da'ita,wannan karan speaking softly yace "And what made you say that?" Mami tacire hannunta a fuskarta given him the view of her face tace "Many things" Muzammil yashiga karema gurin kallo,dajine sosai dankuwa the only difference da gurin yake dashi da asalin daji shine the place is surrounded by fence na park din sannan ajikin fence din ansaka security lights tako Ina so he don't think tsayuwarsu agun for much longer will be of anygood to either of them danhaka seya dubeta yace "Naji,yanzudai mubar wurinnan Mami dare yayi" daganan bejira cewarta ba yariko hannun abayanta yajata suka bar gurin. Securityn daya biyosu kuwa tuni yabar gurin ganin su Muzammil kamar ma basusan dashi ba and he thought they needed privacy.

Kallon Muzammil Mami tayi da mamaki jin yajata sannan tamaida dubanta kan hannunshi dake rike da abayanta following him like a cameloeon harsuka Isa jikin motar Daddy,sakin hannunta Muzammil yayi yabude Mata front seat yayi caging dinta babu hanyar guduwa wanda hakan yasa Mami dole shiga motar tazauna ayayinda Muzammil yatsuguna agabanta yazuba Mata idanu yace "Toh muyi magana yanzu,what where you saying?" Tura baki gaba Mami tayi tace "Cewa nayi tunda kadawo kadaina damuwa dani" Muzammil yace "I heard that,Sonake ki lissafamin abubuwan danayi yasa kike tunanin nadaina damuwa dake" Mami tasa bayan hannunta tashare guntun hawayenta tace "Tunkana South Africa kake ignoring dina anma wannan baidameni ba sabida nasan you were always busy ne but still daka dawo baka koman ma baka canza ba sema abunda yakaru" Mami ta numfasa tace "The day you came back I went to your room muyi hira dadare kayi shoving dina away,harda Cewa inkashe maka wutar dakinka" yanda Mami tayi maganar kadai zakasan abun bakaramin sosa Mata rai yayiba.

Muzammil dake kallonta intently yace "But did you tell me hira kikazo muyi?cemin fa kikayi Ummi ce ta aiko kifah Mami" Mami tace "Anma dana ajiye sakon aina tsaya bantafi ba" Muzammil yace "And when I asked you why you were standing kikacemin Ummi ne tace kicemin inshanye kunun ayana adaren karya baci" tura baki gaba Mami tayi tace "Toh aibashikadaine laifin dakaminba" wannan karan seda Muzammil yadan saki guntun murmushi yace "I'm all ears Mami,fadamin semenene da menene laifina kuma?"

Mami tace "The Following day when you came to our side kana ganin nafito a dakinmu kamasu Mummy sallama katafi" Muzammil mischievously yace "You missed something here,kikafito kina masifa dai and I was trying to safe Nana from you" hararar sa Mami tayi tace "Jiya darana dakuna zaune dasu Fa'iz a parlour kana ganina katashi kafita fah?" Muzammil ya sosa karan hancinshi cikeda rashin gaskiya this time yace "Uhummm sekuma me?" Mami tace "The way you rejected my offer dadare agaban Ummi sekuma gift dinda nabaka yau kaki karba" Muzammil yace "Is that all?" Gyadamai Kai kawai Mami tayi.

Muzammil yace "Toh kiyi hakuri bazan sake ba,shikenan?" Mami tace "Nidaman banrikeka dakomai ba Hamma kawai abun yadameni ne, this is not the Hamma Muzammil I used to know,ninadauka ma wani laifin nayi maka shiyasa naki nabaka gift dazu aciki nafito dashi daniyar inbaka inkuma baka hakuri incase I did something wrong din but then you shoved me away that time also" Mami takarashe maganar asanyaye.

Muzammil sincerely yace "You did nothing,wallahi bakiyimin komai ba but one thing I want you to know is we are both matured now Mami,muba muharraman juna baneba there is no way we can be like the way we were when we were kids" Mami tace "Nasani Hamma,I know we can't act like before at some instances but why are you treating me differently? Aisu Amina da Ameera da Ammi ma ba muharraman ka baneba but still kana zama kayi hira dasu,inkagansu baka canza hanya,inkagansu baka tashi kabar gurin sannan yauda suka baka gifts bakaki karba ba" and then it hits him he's been hurting Mami quietly bayan kuma akan sabida karyayi hurting dinnata ne yasa yake Jan jikinshi baya ashe shi gudun gara yake yana tadda zago besaniba,feeling sooo disappointed on himself hakanan jiki sanyaye yadubeta yace "I don't really know how to seriously explain myself now but believe me I don't know I've been hurting you this much, I'm sorry" yadaga idanunshi yasaka cikin nata deeply yace "I really am very sorry Mamin Ummi,insha Allah bazan sake ba" and Mami felt guilty for making him this sorry tace "It's okay,yawuce Hamma" Muzammil feeling relieved yace "Can we go home now?" Gyadamai kai Mami tayi tana murmushin yake.
Mayarmata da murmushin Muzammil yayi sannan yatashi yarufe Mata kofar yazagaya yashiga drivers seat,wayarshi daketa ringing tundazu bebi takanshi ba yadaga,Khalipha ne keta kiranshi.

Muzammil yana dagawa yace "I've found her Khalipha" from the other end Khalipha yace "Alright sekun dawo" daganan yakatse wayar

Muzammil seda ya tsaya abakin gate yama securities din godiya sannan sukabar park din. Suna hawa titi Muzammil yadubi Mami yace "Zaki rakani unguwa ko inkaiki gida?" Mami tace "Zanrakaka" murmushi yasakar mata tamayar mai this time genuinely sannan yamaida dubanshi kan titi,awani masallaci yatsaya sukayi sallar maghrib ganin time din sallar Isha'i takusa sannan suka wuce gidan Hajiya Zuwaira,shiya shiga gidan yakarbi sakon Ummi leaving Mami in the car bayan yace mata bajimawa zaiyi ba inda daganan suka wuce gidan Captain Abbas.

Gidan bemasa wahalan samu ba dayake yasan unguwar sosai sannan gidan bawai yanacan cikin wani lungu bane,akofar gidan yayi parking motarsa sannan yakira Captain Abbas yasanar dashi isowarsu yace sukaraso ciki. Haka Muzammil da Mami suka jera suka shiga cikin gidan inda suka tarar da Captain Abbas tsaye cikin harabar gidan yana jiran shigowarsu,karasowa yayi yana ganinsu with a smile on his face yamika ma Muzammil din hannu sukayi sallama tareda fadin "Sannunku da isowa" Muzammil yace "Thank you Captain" Mami dake tsaye gefen Muzammil gaida Captain Abbas tayi tace "Ina wuni?" Captain Abbas yace "Lafiya Lau" sannan yamaida dubansa ga Muzammil curiously yace "You didn't tell me you've a Wife?" Muzammil yayi yar dariya yana girgizakai yace "No she's my lil Sis" Captain Abbas dariyar yayi shima yace "Oh welcome to our home lil Sis" inda daganan yayi inviting dinsu in. Gidane tsararre mekyau dede misali hakanan ko Ina tsaf tsaf dashi gwanin ban sha'awa. To say Captain Abbas is handsome is an understatement,he's cute more than cute and a crush material,Captain Abbas irin kyawawan fulanin yolan nanne da Kallo daya zaka musu kasan asalinsu,maganar sa kadai abun saurarone because of how ascent dinshi ke fitowa gwanin dadin ji. Mami batasan kyaun ba akan Captain din yakare ba seda matar shitafito yimusu sannu da zuwa sanda suka zauna a parlour, she's also cute infact cuter than her Husband and Mami thoughts "How could this two young couple be so selfish? Miyasa zasu auri juna bazasuje sudanyi sirki dawasu mutanen ba asamu wasu sets of kyawawan from different families lol!"

Captain Abbas is also young anma ze iya girmema Muzammil da irin shekaru uku zuwa hudu haka ma matarsa,she could be in her early twenties haka. Anan parlour Captain Abbas da Muzammil suka zauna ayayinda matar Captain Abbas din taja Mami sukayi ciki.

Muzammil yamikama Captain Abbas file dinda yashigo dashi yana fadin "Here are the files Captain" Captain Abbas yakarba yace "I will go through them and give you my feedback inmun hadu ranar Monday insha Allah" Muzammil yace "Allah yakaimu" inda daganan kuma suka hau hira wanda duk akan profession din nasune,Captain Abbas nafada ma Muzammil the little experience dayake dashi daga fara aikinsa zuwa yanzu as a Soldier ayayinda Muzammil yabashi listening ears sosai ayayinda yakuma zage suke hirar dayake fannin abunda yakeso ne. atakaicedai Mami da Muzammil agidan Captain Abbas sukayi sallar isha'i sukayi dinner se after 9pm sannan suka bar gidan. Kira kuwa Muzammil yashashi ba adadi daga gunsu Ameera dasu Deenah wai sunason su tabbatar koyasamu Mamin ganin basudawo ba,seda Muzammil yatura musu text message sannan suka sararamai. Bayan sunbar gidan Captain Abbas agaban wani Suya spot dayasaba sayama Mami naman baroo tun suna yara yatsaya aranshi yana addu'ar Allah yasa haryanzu mutumin nasaidawa yasamu yamata surprise dinda yayi niya. Sauka yayi ya'isa gurin and luckily for him yasamu,kudi yamikamai yafadi nanawa yakeso Akamai packaging a leda sannan yakarba yakoma mota. Muzammil nashigowa motar mikama Mami ledar yayi yace "This is for you" karba Mami tayi tana murmushi tace "Thanks Hammana" Muzammil yace "baki bude kinga menene ba" Mami tace "I know its nama" dankuwa akan idanunta yaje suya spot din yasayo Muzammil yace "Yes its nama but you can't testify wani irin namane" Mami kallonshi tayi curiously tana lallatsa ledar naman tace "Naman kaza?" Muzammil yashiga kokarin tada motar yana fadin "Uhmmm..... you're almost there,kidai bude ledar kigani kawai" bude ledar Mami tayi tayi unwrapping takardar da akasa naman aciki,wani irin wara idanu tayi excitedly tareda fadin "Baroooooooo" Muzammil dariya yasaki ayayinda Mami tayagi cinya jikin dayadaga cikin gasassun baroon takai baki tana fadin "Hamma daman anan kake sayamin kullum?kasan rabona dacin baroo tunda katafi South Africa,koyaushe innazo Yola nace inason cin naman baroo sesu Uncle Ameer suce ba'asamu harna hakura nadaina tambaya" Muzammil yace "you should have asked Daddy yatambaya maki ni ai" Mami tatura baki gaba tace "it never crossed my mind and besides bagashi yanzu kadawoba, I'll eat it anytime I want to" Muzammil yajinjinakai yana murmushi his eyes focused on the road ayayinda Mami tadage secin naman baroonta take hankali kwance hakanan tana ganin sunshiga layin unguwarsu tace yasamu guri yayi parking tagama cinyewa kartaje dashi gida su Ammi susamata yami. Muzammil yana murmushi yace "okay Ma'am" sannan yasamu guri gefen titin yayi parking yayi tagumi yana kallon yanda taketa aikin yagar namar tanaci hankali kwance his smile never leaving his face. Mami seda tacinye naman tas,kasusuwane kawai suka rage cikin takardar sannan tadago daniyar cemasa tagama sutafi idanunta suka fada cikin nashi,taga irin sihirtaccen kallon dayake mata,wani irin matsanancin kunyane yakamata lokaci guda tayi sauri tamayar dakanta kasa. Muzammil yayi chuckling yace "kinkoshi?" ahankali Mami tace "Uhmmhhm" Muzammil teasingly yace

You are reading the story above: TeenFic.Net