BAƘAR ASHANA 16•17

Background color
Font
Font size
Line height

*BAƘAR ASHANA*

*Safnah Aliyu jawabi*
(His Noor)

Page 16•17

*PERFECT WRITERS ASSOCIATION*

Follow the PERFECT WRITERS ASSOCIATION channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vad1bE05a249vbEcab0r

*You are the missing piece I never knew I needed, the missing beat in my heart, and the missing chapter in my story. I love you."*

*_ I lOVE YOU MAN_*🥰🥰

Ba tare da ta furta ko kalma ɗaya ba ta nufi gun jakarta tana ƙoƙarin cire kayan da za ta saka. Janyota jikinsa ya yi da karfi  duk yadda ta yi don ta ƙwace kanta amma ta kasa. Tana ji tana gani ya sanya harshansa yana lashe hawayan dake gangara kan fuskarta tsigar jikinta ce ta fara tashi cikin sauri ta shiga ture shi da duk kan karfinta. Amma ya hana dan kuwa ya yi mata kyakkyawan riƙo cikin salo ya haɗe bakinsu guri ɗaya.

Cikin salon Ya ke sumbatarta tun  tana kaucewa har ta fara mayar da martani dan kuwa sosai ya kiɗimar da duniyarta cire bakinsa ya yi ya na kallon fuskarta,

" Me yasa kika fi ya kyau ne?"
Murguɗa masa baki ta yi  sannan ta ce,
"Me yasa ka fiya mugunta ne?"
Ko sauraranta bai yi ba ya shiga sarrafa duk wata halitta ta jikinta tun suna a tsaye har ƙafafuwarsu suka gaza ɗaukar gangar jikinsu. Nan suka shiga gusarwa juna da ƙishin daya daɗe yana addabarsu amma jin kai da izza ya hana su bayyanawa.
Wani irin sauti duk suke fitarwa a tare wanda ke nuni da sosai suke jin daɗin abin da suke aikatawa (Ya subhanallah) wani irin so da ƙaunarsa ta ji yana fuzgarta so irin wanda ba ta taɓa ji ba a tsayin rayuwarta Mansur namiji ne wanda ko wacce mace za tai burin mallaka a rayuwa. Jarumi ne ta ko wacce fuska, salonsa salo ne mai tafiyar da hankalin mace, tabbas wannan shi ne namijin da ya dace da ni ina son shi kuma ba zan taɓa bari wata mace ta kusance shi ba wannan nawa ne ni ɗaya.

Haka ta rinka sambato ita kaɗai a zuciya, shi kuwa tuni har ya yi bacci dan lokaci mai tsayi suke ɗauka suna gamsar da juna dole da gajiya a jikinsa abin da ta faɗa ke nan yayin da ta nufi ban ɗaki dan tsarkake jikinta.

A tare suka kwana tana rungume a jikinsa kamar 'yar tsana ko da ya farka sumbatar ta ya yi a saman goshi. Sannan ya janye jikinsa daga nata, sai da ya yi wanka sannan ya fito har lokacin tana bacci cikin kwanciyar hankali. Murmushi ya yi sannan ya ɗauko caki na kuɗi ya rubuta mata kudi masu yawan gaske sannan ya saka hannu. Saman katifarta ya ajiye ya fice daga ɗakin.
Ko da ya isa shiga motarsa sai dai ya tsaya shiru ya na tunano yadda suka kasance daran jiya murmushin ya yi ya ce,
"Tabbas kin shayar da ni ɗanɗano mai gamsarwa sai dai Aman ba ya maimaita aji, wannan dalilin ya sa zan tafi na bar ki amma ke ɗin ta daban ce kyakkyawar halitta."
Ita kuwa ko da ta farka sosai ta cika da mamakin rashin ganinsa a gefanta kamar yadda ta yi tsammani abin da ya fi ba ta mamaki da ruɗarwa kuwa bai wuce ganin wannan cakin a gefan katifarta ba, tabbas kuɗi ne masu ɗumbin yawa, amma shin me hakan ke nufi ke nan?
Haka ta yi ta tufka da warwara ƙarshe dai ta yanke shawarar kiran shi don jin dalilin tafiya ba tare da sallama ba sannan wannan kuɗin kuma fa.
Abin takaici duk nambobinsa a kashe babu wanda ke zuwa haka ta yi ta gwadawa tsayin ranar, amma duk abu ɗaya suke faɗa a kashe wayar take.
Sosai ta shiga tashin hankali sai kuma ta ji Abuja ya yi mata zafi don haka ta tattara kayanta ta dawo garin Kaduna. Cike da kasala da damuwa a ranta haka tambaya ɗaya ke yawo a ranta, me ya sa ya tafi ba tare da sallama ba, kudin na mene ne?

Da haka har ta shiga gida tana shiga Zakiyya na fitowa daga ɗakinta, fuska a haɗe ta ce
"Me kike nema kika shiga ɗakina malama?"
"Ke har ɗaki gare ki cikin gidanna wanda ni Zakiyya ba zan shiga ba Hidaya?"
"Malama amsa min tambayata kawai a wuce gurin"
"Zuwa na yi na duba ki,  ashe  ma dai tafiya kika yi tunda ga akwati a hannunki. Yawwa bayan haka dan Allah maganar gaskiya zan miki akwai bukatar ki tafi ki duba 'ya'yan da kika bari ko da sau ɗaya ne. Baya ga haka ki tuna iyayanki duk suna raye ba mutuwa su kayi ba, amma kuma a ce har yanzu ba kya ko tunanin zuwa gare su ki ga a wani  hali suke ciki ba?dan Allah ki yi ƙoƙari ki samu lokaci ki duba su   dan Allah? "
"Zan duba yuwar haka insha Allah"
"Allah ya sa"
"Ameen."
Da haka duk suka shige ɗakinsu sai dai maganar Zakiyya ya tsaya mata a rai  ko babu komai tana jin kewan iyayanta, amma kuma da wani ido zata kalle su bayan tsawon wannan shekarun da ta ɗauka babu labari.

Ganin abin zai dame ta ya sa ta yi watsi da shi ta kama tunanin Mansur wanda yanzu ya fi komai muhimmanci a gare ta, har ila yau dai lambar ba ta zuwa ita kuma sam ba ta fasa gwadawa ba.

*********

A zaune yake yana karatun Alkur'ani a kofar gidansu muryarsa gwanin daɗi, a nutse yake karatunsa sai da ya sallame sannan ya kwashi sallayar ya nufi cikin gida.
Da sallama ya shigo gidan  fuskarsa ɗauke da annuri sai dai ganin mahaifiyarsa yadda ya bar ta, hakan ya sa gaba ɗaya annurin fuskarsa ya ɗauke kamar ma ba a taɓa wanzar da shi ba. Cikin sauri ya ƙarasa gare ta yana cewa
" Mamina"
Ɗago kai ta yi tana  kallon shi sai a lokacin ya ƙara tabbatar da ramarta dan kuwa ta faɗa, kuma ta yi baƙi da alama akwai abin da ke damunta.

"Mami dan Allah ki faɗa min abin da ke damun ki, Wallahi ba na jin daɗin yadda na ke ganin ki zuciyata ba za ta taɓa jure ganin ki cikin wannan halin ba, ki faɗa min kin ji Mamina?"

Share hawayan da ya  gangaro mata  ta yi sannan ta ce,

"Akwai lokaci insha Allah komai yana da lokaci, ka daina damuwa shin ya labarin yaran nan kuwa?"
"Suna nan , lafiya Insha Allah gobe Asabar a nan za su yi hutun ƙarshan mako"
"Allah ya kawo su lafiya duk su bi su dame mu da surutai"
Murmushi ya yi yana sosa ƙeya ya bar wurin, amma kuma zuciyarsa cike take da tunanin halin da Maminsa take ciki.

********

GIDAN ALHAJI ABDULLAHI MATAIMAKIN SHUGABAN ƘASA

Ban da tari babu abin da yake, hannuwansa ɗaure a ƙirjinsa mutane cike da ɗakin. Zuwan likita ya sa duk suka fita dan a samu damar duba lafiyarsa, cikin hanzari likitan ya isa gare shi yana faɗin

"Alhaji na faɗa maka ka daina yawan sanya damuwa a ranka ko dan tseratar da ranka. Tsawon shekaru ashirin da tara ana abu ɗaya ai abin babu daɗi! Ka duba halin daka sanya 'yan uwanka, ko iya wannan dalilin ya isa ka mance komai kasanyawa ranka salama da kwanciyar hankali".

Cikin muryarsa ta mararsa lafiya ya ce

"Imran wani rai da lafiya kake magana a kai? Wani jin dadi da kwanciyar hankali kake so ka faɗa min? ka fada min amfanin rai da gangar jikina, ka faɗa min ina sauraronka, kai fa abokina ne tun na yarinta, amma kuma kake faɗar wannan kamar ba ka san komai ba?"

"Ko da na sani, Abdullahi mene ne zan yi a kai bayan haka Ubangijinmu mai kowa mai komai ya hukunta."
"Ka faɗi min abin da zan yi ina sauraronka."
"Yanzu dai duk ba wannan ba dan Allah ka kwantar da hankalinka ko dan mahaifiyarka hankalinta ya kwanta, bai kyautu a ce cikin wannan shekaru nata kuma tana cikin tashin hankali irin wannan ba sai dai idan itama so kake ka rasata..

Matsa masa hanji haɗe da ɗagowa cikin sauri da Abdullahi ya yi ne ya sa Imran ya kasa ƙarasa zancansa.
Tuni idanuwansa sun canza launi daga fari zuwa ja jajir,  ya ce
"Ka san me kake cewa kuwa, ka san abin da kake furta min, A haka kake tunani na samu lafiya da wannan bakar maganar da ke faɗa min?"

"Idan ba ka so hakan ta kasance ka rinƙa daurewa kana kwantar da hankalinka haba dan Allah."

"Ina sonta ina ƙaunarta ka fi kowa sanin haka, ita ce rayuwata idan babu ita babu ni, Imran babu ni babu wani sauran jin dadi in dai a cikin wannan duniyar ne."

Ganin yadda yake sambatu hakan ya sa ya shammace shi ya yi masa allurar bacci cikin abin da bai fi minti biyu ba ya fara bacci.

Hamdala ya yi sannan ya fito ganinsu a takure yasa gabaki ɗaya yaji jikin shi ya yi sanyi.

Mene ne kuma ya rage ban faɗa musu ba, duk wata kalma da zan yi amfani da ita wajan tambayar shi abin da ke faruwa da shi? sauke ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce " A gaskiya Hajiya matsala ce babba sai dai da yardar Allah komai zai dai-daita. Abin da na ke da buƙata kawai shi ne, ku yi iya baƙin ƙoƙarin ku wajan ganin kun bashi kulawa ta ko wacce fuska, don kuwa ita yake da buƙata yanzu, sannan magungunan sa ya rinka sha akan lokaci".

"Duk na ji zancanka kuma na gamsu saidai ina buƙata na san abin da ke damun ɗana ?"

" Hajiya abin da kika sani ne har yau dai Abdullahi bai daina so da ƙaunar Zainab ba, itace mafarkinsa a koda yaushe, haka itace farin cikinsa  tunaninta yasa ciwonsa ke tsananta".

"Innalillahi wa inna ilaihi raju'un, yanzu kana nufin tsayin shekarun nan tunanin Zainab ke wahalar da zuciyar Abdullahi amma kuma ka kasa sanar da ni mahaifiyarsa?"

"Hajiya ki min aikin gafara ba na son ɗaga miki hankali ne, ke kanki kin san babu irin neman Zainab da ba mu yi ba bayan rabuwarsu, amma ba mu same ta ba hakan ya sa muka nufi can garinsu inda Abdullahi ya gan ta ya aure ta, amma aka sanar da mu rasuwar Iyayanta sakamakon gobara wanda ake kyautata zaton har da ita Zainab abin ya afkawa.

Hajiya shi yasa kullum ake so mu rinƙa hakuri da rayuwa, Abdullahi yaro ne mai tsananin biyayya a gare ki da ma sauran jama'ar gari. Amma kuka matsa dole sai ya saki matarsa duk dan ta kasance 'yar talakawa, yanzu ga irinta nan kullum cikin fargaba nake dan idan har aka yi rashin sa'a wannan cutar ta cigaba a haka wallahi tsab Abdullahi zai rasa ransa."
"In sha Allah babu abin da zai faru komai zai tafi cikin sauki da yardar Allah"
"Allah ya sa amma Hajiya dan Allah ke ma ki sanyawa kanki natsuwa da kwanciyar hankali, dan ke ma ki samu isashiyar lafiya".
"In sha Allah"
Da haka ya fita ya na tunanin halin da abokinsa yake ciki.
______

Cikin shiga mai kyau da alfarma ya fito hannunsa ɗauke da jaka da alama tafiya zai yi Mima ce biye da shi ta na share ƙwallar idonta, rusunawa ya yi yana cewa,
" Mima zan tafi albarkarki nake buƙata"

"Allah ya yi maka albarka ya dawo da kai lafiya cikin aminci, ka tsare mutuncinka da na addininka, ka kasance mai riƙon amana, Allah ya yi maka albarka ya dawo da kai lafiya".

"Amin Mimata"

Murmushi Abba ya yi ya ce " Duk abin da zan faɗa ta riga da ta faɗa maka sai dai na ɗora daga inda ta tsaya Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya dan Allah a yi a hankali da yanayi na rayuwa, Allah ya na tare da kai a duk inda kake".

Sai da suka tabbatar ya ɓace wa ganinsu sannan suka dawo cikin gidan, Mima kuwa kuka take babu sassauci wani irin ƙuna take ji a zuciyarta kamar ya faso ƙirjinta, banda sauke ajiyar zuciya babu abin da take.

Kiran sunanta Abba ya yi yace

"Zainab ki ƙwantar da hankalinki komai ya yi farko zai yi ƙarshe in sha Allah".

"Yau rana ta farko da na ji kewa da raɗaɗin abin da suka min, sakamakon haka ga abin da ɗansu yake fuskanta tozarci, ƙasƙanci, da ƙunar zuci".

"Haka Allah ya so koma ya tsara ki tuna ke da kanki kike cewa akwai lokaci to ki ɗauka lokacin ne bai ba ina mai tabbatar miki wata rana komai zai daidaita".

Haka suka cikagaba da tattauna matsalolinsu.


You are reading the story above: TeenFic.Net

#jawabi