A CIKIN IDO....
A CIKIN.. IDO......Kafin zuwan Sufyan Doko cikin rayuwata komai lafiya lau ne._ _Ina baƙin cikin zuwa garin Doko a nan ne na dawo da mummunar Kaddarar da ta shafe babin farin ciki da walwala a cikin duniyata.Rabon da na ji sanyi a raina na manta sai yau da aka shigo min da gawar Sufyan Doko abinda ya jima da tokare min maƙoshina naji ya sauka a hankali a fili na furta Alhamdullilahi!Idanuwan ƴa'ƴan Sufyan Doko naji suna yi mini yawo a jikina sai dai hakan bai saka naji zan duba al'amarin mahaifinsu da sauƙi ba sai da na bishi da addu'ar samun rahama a wurin ubangiji. Abin da na jima ina marari da burin samu sai yau Allah Ya yanke mini, dama ya faɗa ba zai taɓa bari na ba sai dai mai rabawa ta raba......…